《RAYUWAR HUSNA (hausa novel)》The end

Advertisement

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*RAYUWAR HUSNA*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

🅿️:4️⃣0️⃣-4️⃣1️⃣

*THE END*

_Bismillah_

This page is dedicated to the fans of Rayuwar Husnah, nagode sosai for the comments, Allah ya bar kauna.🌹💖💜

*BAYAN FOUR YEARS*

Wata beauty ce zaune kan cinyan mahaifinta, sai shagwabe masa take. "Abba, kasiya mun ice da chocolate in zaka dawo yau." ta fada a shagwabe.

"To my angle."

"Amma karka bari ummi ta gani."

"An gama my angle. A siya ma Suhail?"

"A kasiya masa. Ummi tace in rinka bashi duk abun da nake dashi, wai nice addan sa. Kuna wai shima ya daina mun rowan daya ke mun. Kuma tace muso juna." tun lokacin da yar sa ke magana yake kallon ta. Gaskiya shi yayi dacen mata.

"Toh shikenan her Abba's princess, zan siya masa."

"Me zaa siya?" wata Matashiya mai mugun kyau. Gata ba baka ba, kuma ba wata fara ba. Tafito da wani yaron da bazai fi shekara 2 ba. Su ko suna jin muryar ta sukayi shuru. Sai ta kara maimaita abun da ta fada.

"Babu" yarinyar ta amsa.

"Wai Jawahir bana hana ki karya ba? Ke baki san tun mutum ke karamin ya ke fara karya, har yazo yabi jiki ba?" sai yarinyar ta durkusar da kanta. "Am sorry Ummi bazan kara ba." ta fada tana hawaye."

"Nifa bance ki min kuka ba. It's good, karki bari karya yazama miki way of escaping da ga matsala."

"Tace toh ummi na."

"Ya isa haka my treasure, ki daina sa angle din kuka fa" sai ta kalle shi ta tabe baki, sai tace "Wallahi yaya ka daina biye mata."

"A'a bai kai haka ba my treasure, Allah ya huci zuciyar sarauniyar zuciyata." sai tayi smilling.

"Abba nima ka siya min abun da zaka siya ma adda." Karamin yaron mai suna Suhail ya fada cikin muryan sa na yara.

"In Sha Allahu kai ma zaa siya maka." Mubarak ya amsa.

Advertisement

"Wai me zaa siya ne?"

"Abba zai siya ma nida Suhail chocolate da icecream."

"Zaki ko? Toh Allah ya taimaka. Nima dai kar a manta da balangu na."

"In Sha Allahu. Amma kin san mai naman ma har ya san duk lokacin da nake zuwa kullum, toh kina da ciki ne."

"Wanan kuma shi ya dama."

Da ko wannan su ya gama fadan bukatun sa, sai Mubarak ya dau brief case din sa, ita kuma Husna ta rike mai sauran kayan, suka raka shi har zuwa motar sa.

Yanzu Husna ta kara kilewa, ta kara zama classic lady. Gashi kuma Alhamdulilah ta gama jamia. Although bata aikin govt, amma bata zauna a matsayin house wife ba, so tana aiki catering. Shi ma Mubarak, yanzu shi ma an kara mai matsayi a aiki, kuma shima ya bude na sa asibitin. Rayuwa na zuwa musu yanda ya kamata, amma hausawa sunce zomu zauna, zomu saba. So baa rasa lokutan da suke samun sabani.

Husna na gama school da 3 months, ta haife Suhail. Gaskiya Mubarak ya jidadi karuwan sosai. Ya ci sunan Abban Husna, Abdallahi, amma suna kiran sa da Suhail. Ga tarbiyan da suke ba yaransu mai kyau. Duk inda yaran suke, sai sun haskaka wajan, kowa na shaawan ace da yaran nan nasa ne. Ga kaunan junan da ta sa musu a zuciya. Ko me zaa ma wannan, sai anyi ma daya, basu banban ta, ko da ce wa Mubarak da Jawahir sunfi shakuwa, amm still baya taba nuna banban ci.

Gashi Husna nada cikin wata 8. Cikin sauki, Allah yayi ta haifi yar yarinta. Jawahir da Suhail sunyi Murnan samun kanwa, baa bar Abban suma a baya ba. Ya ji dadi sosai. Taci Sunan ta Afiya.

Tinda gidan su da na Ammi ba wani nisa, so duk weekends suke zuwa da su da iyayen du, amma su Husna basu kwana. Saturday zasu kai yaran, da yaman su koma, sai su bar yaran ran Sunday da yanma driver ya koma da su gida.

Yau ma kaman yanda suka saba, Sukayi sallama suka shiga. Suna shiga Suhail ya je ya rungume kakan sa da gudu. "Oyoyo kanina, kazo lafiya?" kai kawa Suhail ya jijjiga. Sai tace toh sannu ku da zuwa. Sai yace "bakiyi ma Adda oyoyo ba, harda Afi."

Advertisement

"Toh kanina zan musu.

Yanzu dai Umma ta fara tsufa, shekara almost biyar ai ba wasa bane, amma yanda Umma ke dressing kuma ta ke daukar kanta, baza ka ganta kace tsohuwa ba ce. Duk wanda ya kira Umma da tsohuwa, toh sai sunyi ta. Ta tsani a kira ta da tsohuwa.

Da suka gama cikin abinci, sai Umma ta sanar dasu cewa su Yaya Salim ma zasu zo. Sai suka amsa da sun sani. "Awww waton kun sani shi ne bakuyi magana ba, sanda na gama magana? Kun san yawun bakina na wasting kuwa?"

" Allah ya huci zuciyar yar Asma'u." Husna ta fada. Sai Mubarak ya amsa da Amin.

Can Suleja ma, Ammi da Abba kadai ke gida yanzu, don ita ma Nana tayi aure. Ta aure wani dan kasuwa ne a Kano. Akwai rufin asiri sosai. Ba zaka ganta ka raina ta ba. Dan ta daya, mai Suna Sadiq. Duk december, sai Husna da Nana sunje gida wajan iyayen su. Akwai shakuwa sosai tsakanin Husna da kanwar ta, kuma a tsakanin yaran su.

Farida ko, duk abun duniya yabi ya ishe ta, tarasa inda zata sa kanta. Kullum sai tayi mamakin kanta, wai ita maza ke guduwan ta, ita da ko bata kulla ka ba, sai ka nemo inda gidan su yake, wai itace duk suka guje ta. Dana sani, na damun ta sosai. Data sani kawai ta auri Mubarak, da ta rufa ma kanta siri, amma ina tasa ma kanta son abun duniya da kwadayi. Duk ran da ta tuna da ire iren rashin mutunci datayi masa, sai tayi hawaye. Ita har yanzu tana son sa, amma shiko tuni ya manta da ita. Bata son su hadu da Mubarak ko kallo ne, bata son ya hada su. Shi ko Mubarak bai ma san tana yi ba. Dan haryanzu bai bar wajan aikin sa ba.

*BAYAN SHEKARU 10*

Husna ne da Mubarak kwance akan gado. Sai Mubarak ya kallie Husna yace " Baby har munyi shekara 15 fa kenan da aure."

"Toh Alhamdulilah, haka Allah yake tsara abunsa."

"Amma wallahi my treasure, lokutan nan da baki sona, ji nake kaman ana soka min abu azuciya. Kullum sai nayi tunani, hanya ko zaki taba mantawa da Faiz? Duk da cewa tun farko, mu biyu mun ki auran, amma na riga ki kamuwa da son ki."

"Hakane gaskiya, koni ban san ta inda soyayyar ka ta shige ni ba. Nayi zaton bazan taba son wani ba bayan Faiz, amma ikon Allah, komai ya canza. Na so Faiz gaskiya, amma he is my past kuma haryanzu yana cikin addua ta, but kai present din na ne. Kuma ina son ka sani, zan soka har karshen rayuwata."

"Nima haka baby, Allah ya hada mu a Aljannah. Gaskiya biyayya ga iyaye shi ne komai. Kin san inka yi biyayya ga iyaye, sai komai yazo maka dai dai. Ga hakuri kuma, hakuri shi ne jigon komai arayuwa."

"Haka ne yayana. Kuma Allah ya cigaba da bamu hakuri, kuma ya bamu ikon yin biyayya ga iyaye."

"Amin suka amsa tare."

_Godiya mara adadi ga ubangijin mu mai komai mai kowa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin mu sallallahu Alaihi Wasallam_.

_Nagode wa Allah da ya bani nasarar kammala littafina na farko, fatan Allah ya sa mu karu dashi ya kuma yafemin kuskuren danayi a cikin. Kamar yau na fara sai gashi cikin ikon Allah na gama da taimakon yan uwana, kawayena at the same time and my guidance,I really appreciate ur goodness, da kuma encouraging dinna da kuke yi, shiya kawu ni wannan matakin. Bazanyi kasa a guiwa ba wajen lissafu sunayenku tare da jinjina ta musamman gareku bazan taba mantawa da hallacin ku a gareni ba_

_Ummi ta da kanwata_

_Fatima Zahra Eyman_

_Phateema Xahra_

_Ummi El Habib_

_Zulaihat_

_Asma'au_

_Surayya_

_Salifa_

_Hafsat_

_Members din zeexee novels da duka fans din rayuwar Husna_

_Da kuma shugaban mu Zaynab Chubado da members din TAMBARI WRITERS ASSOCIATION. Ina matukar godiya da kulawarku_.

_Thanks for reading, sai mun hadu a littafi na nagaba_

_Love_ 💖

_Zeexee_ 🌹💜💖💞

    people are reading<RAYUWAR HUSNA (hausa novel)>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click