《RAYUWAR HUSNA (hausa novel)》part 38 &39

Advertisement

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*RAYUWAR HUSNA*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

🅿️:3️⃣8️⃣-3️⃣9️⃣

_Bismillah_

"Awwwn yaya kar ka sani kuka. Ai ni ya kamata na rinka maka godiya. Because katsaya dani da duk wulakancin da nake maka, although dai kai kaja hatsari na. But still nagode sosai. Thanks for loving me. Suna cikin fada wa juna kalamun soyayya, akayi knocking.

"Ooh, waya zo bata mana moment din mu." Mubarak ya fada. Sai ya amsa, "who's there"

"Doc Hafsat ta aiko ni, wai madam ta zo."

"Owk kace mata tana zuwa ." sai ya kalle Husna, yace "Toh my treasure, zo kije a gwada ki."

"Alhamdulilah tunda babyn mun na lafiya. Ko na kaiki gidan Umma ne? Tinda ba yanzu zan dawo ba, kuma bana son ki rinka zaman kadai ta."

" Toh shikenan"

Yana dropping dinta a bakin gate ya juya, sai ta karasa ciki. "Assalamu alaikum" tayi sallam.

"Waalaikumus salam Baby girl" Aunty Khadijah( maqabciyar umma) ta amsa.

"Laaa, mamana"

" Ba wani maman ki yanzu kam, ai kin manta da ni."

Sai ta fara hawaye. Wannan cikin na sata kuka sosai. Abu kadan sai tayi kuka.

"Aaah baby me ye na kuka kuma?"

Sai Umma ta fito daga kitchen, tace ai sabon saranta kenan. Ai umna na magaba, sai yayi kaman ance mata ta kara volume ne. Sai Hajiya Khadija tace" gaskiya hajiya ki daina sa baby na kuka. Abun daya kamata ki rarrashe ta?" Hajiya Khadija ta tashi, taje ta riko hannun Husna, ta zaunar da it kan cinyoyin ta.

" Ku kuka sani" Umma ta fada, ta koma kitchen.

"Karki amsa mata, kinji." Hajiya Khadija ta fada, sai Husna tayi nodding din kanta.

" aha babyn mama." sai ta yi murmushi, ta kwantar da kanta kirjin Hajiya Khadija.

Umma na fitowa daga kitchen, tace "Iye mamana, kina shan shagalin ki fa, yanzu baki jin tsoron ki karya mata kafa?"

Sai ta kara fashewa da kuka, ta tashi akan kafan Hajiya Khadija, tana kuka tana bubbuga kafa kamar wata karaman yarinya. "Ni umma yanzu, kin tsane ni, daga fitowar ki parlor, ko gaisawa ba muyi ba, kika fara tsokana na?"

"Ni asuwa, ai albarka nake nema. Gashi ana dauke da yar kanwa ko kani na, ai ban isa in bata maki rai ba." sai ta janyo ta jikin ta, tana share mata hawaye. "Ya isa baby, ki daina kuka." kai kawai ta jijjiga. Sai kuma ta fara hamma.

Advertisement

" har yan barcin sun zo ne suma?" ta kara jijjiga kai. "Toh ki tafi dakina kiyi barci "

"Zanyi a parlor ne."

"Toh shikenan uwata"

Gaskiya Husna na samun kulawa sosai ba karya. Duk inda taje, kamar kwai ake yi da ita. Ga ciki ma sai girma yake mashaAllah. Yanzu har cikin yayi 7 months.

Ita da Mubarak na kwance a dakin sa, suna hira. Sai tace" Ni wallahi yaya, balangu nake jin ci?

"Balangu by this time, ai dare yayi. Kuma na san baki son just anyone, sai na Mallam dabo."

"Ni de ka kawo min ko wanne ne please."

"Anyone fa kika ce?" sai ta jijjiga ma sa kai.

"Toh bari na duba miki."

"DanAllah in ka samu gashashen masara ma."

"Gwanda ma da naman, amman masara @ 10 something, ai zaiyi wuya." sai idanuwan ta suka ciko da hawaye. "A'a fa, ba cewa nayi bazan siya ba, kawai ina fada miki ne, da kyar in samu.

"Toh ai da duk surutun nan, da kake yi, da kaje ala ka dawo yanzu.

"Toh bari in je kar nayi wa baaba ta laifi."

Mubarak ya fita neman balangu, da kyar ya samu. Saura masara, baa inda bai dubaba, sai ya yanke decision din siya mata popcorn. A lokacin daya koma gida, har 11:30 yayi, sai ya shiga kitchen ya dauka plate, ya bude fridge ya dauki lemu, da cups.

"Ki tashi kici."dan lokacin daya shiga dakin, harta fara bacci. Sai ta amsa masa da "toh".

Sai ya zuba balangun a plate ya mika mata. Sai ta kalle shi tace "masaran fa?" sai yace mata ta fara cin balangun, zai bata masaran in ta gama ci.

"Wato yaya ka san inda ake siyarda irin wannan balangun, shi ne kake siya min na Baba Dabo ko?"

"Yayi dadi ne?"

"Sosai ma, ya fi na Baba Dabo."

"Toh bani nima in dandana."

"Ka dauki guda uku kawai."

"Haba first lady, ban sanki da rowa ba fa?"

"Toh ai bani kadai ke ci ba, baka ganin wannan koton cikin ne?"

"Toh duk abun da kika ce zanyi."

Da wayo da wayo, ita da Mubarak suka cinye balangun. Tsoron sa yanzu, shi ne ya fito da popcorn a matsayin gashashen masara.

"Toh yaya ka bani masaran mana" ta fada a shagwabe.

"Ki fara shan lemun tukun."

Advertisement

"A'a ni masara nake so."

"A'a ki sha lemun, zai sa abun da kika ci ya danyi digesting."

"Ni fa ban taba ji ance lemu na digesting din abinci ba, sai kace lemun zaki?"

"Gashi dai kin ji daga bakin likita." Da kyar ya shawo kan Husna ta yarda ta sha lemun har 3 cups. Shi dai baisan yanda zaiyi ya bata popcorn din ba. Kuma plans din shi yanzu, shi ne ta sha lemun, ta koshi sosai, sai tayi barci. Amma Hayatin nasa na da dan karan wayo. Haka taki, har kuka tafara yi masa.

"Toh share hawayen ki, sai ki rufe idanuwan ki."

"A dalilin mi zan rufe idanuwa na?"

"A dalilin zan baki masara."

"Toh naji." ta fara murguda mai baki kafin ta rufe idanuwan.

"Tada suprise!"

Fuska a yamu tse tace "Ya nake jin shi cikin leda." sai ta bude ido. Haba tana ganin popcorn ne, data wani harbe shi da shi ko, har yayi zaton tana da Jinnu ne. Haba sai ta fashe da kuka. Da yaso ya rarrashe ta, ta cije shi a kafada. A ra nan basuyi barci ba har kusan 3. Da kyar ya shawo kan ta yace mata in zai dawo daga aiki, zai siya mata.

Yanzu cikin Husna kam ya shiga watan haihuwa. Umma ta dawo da Husna gidan ta. Ai Mubarak najin haka, yace bazaa barshi shi kadai a gida ba, haka shi ma ya tare gidan Umma. Tun lokacin data kusan shiga wata haihuwa, ta fara kuka, wai ita yanzu rayuwarta na hannun Allah ne. Yana iya yuuwa ta mutu. Most especially in suna tare da Mubarak, sai ta rinka jifan shi da duk abun da ke kusa da it, ta rinka ce wa shi yaja mata. Da kyar yake shawo kanta ta dai kuka.

Ita da Umma ne zaune cikin parlor, ta na ma umma kuka, wai Umma ta gafarta mata, dan ita tana ji a jikin ta kaman bazata rayu ba. Umma ta ce tayi mata shuru, abun da ya kamata ta rinka yi shi ne addua. Da yanma, ta fara jin pins a bayan ta, sai taji bayan ya rike, sai ya kara sakin ta, ya zo kuma ta maranta, shima ya fara. A daddafe take duk abun da takeyi. Da kyar tayi barci. Around 3 abun yayi worst. Ta kasa zama, ta kasa tsayuwa. Tun bata son ta ta shi umma, san da taga azaban yayi yawa, ta tashe ta. Umma ko na ganin condition din ta, ta sa baby bag ta a kusa. Sai ta rike hannun ta suna ta strolling cikin dakin.

Ana idar da sallan Fajr, Mubarak ya kai su asibiti. Ga labour na damun ta, amma kan babyn yaki fitowa. Ita ko Husna in ba kuka ba, ba abun da take yi. Gashi ko kallon Mubarak taki yi. Bata ma son ta ganshi kusa da ita.

Sanda tayi labour na kwana 3 kafin Allah yayi aka samu karuwan Baby Girl. Tun a inda aka fada ma Mubarak yayi sujud.

Doc Hafsat ta kalle shi tace "kaman ba likita ba, kabi kadamu, ka bada likitoci yau."

"Aunty bazaki gane ba. Wallahi sai yanzu na san yanda mazajen patients dinmu ke ji. Wallahi it's not easy at all."

"Toh Abban baby. Congrats once again my dear brother, Allah ya raya."

"Amin nagode." sai ya fita a office dinta. Straight ward din ta treasure dinsa take ya je. Duk workers din da suka san matar sa ta haihu, na ta congratulating dinsa, shiko sai washe hakora yake. Yana shiga dakin, bai ma kula Umma na cikin dakin ba, yaje ya rungume matar sa, rabin ransa. I love you Husna, I love you with all my heart Husna. Thanks for this gift, this is the best gift you have given me. Ita ko sai murmushi ta ke, dan ta galabaita sosai. "Toh Mallam a dai tuna ina nan." sai kunya ta kama shi. Sai suka fara kiran dangi da abokan arziki. Ana fada ma Nana, tafara tsalle, yay MashaAllah itama ta zama small mummy. Ba wanda bai yi murnan haihuwan Husna ba, especially fams dinsu da suka san yanda ta sha wuyan labour.

A ranan suna, Baby taci sunan Umma wato *ZAYNAB*, amma suna kiran ta da Jawahir. Ga yarinya nan yar chubby abun ta. Gaskiya ranan suna, uwa da yaa sun sha kyau sosai. Mubarak ma baa barshi ba wajan wanka, yayi kyau sosai. Bakin sa ko bai rufu ba, sai murmushi yake yana nuna 36.

_Thanks for reading, please comnent. It's your comments that motivates a writer._

_Love_ 💖

_Zeexee_ 🌹💜💖💞

    people are reading<RAYUWAR HUSNA (hausa novel)>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click