《RAYUWAR HUSNA (hausa novel)》part 36 &37
Advertisement
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*RAYUWAR HUSNA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹
*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*
*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*
*T.W.A*
*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_
🅿️:3️⃣6️⃣-3️⃣7️⃣
_Bismillah_
Dedicated to my yar cukula friend (Hafsat). Ina yin ki sosai kawally.💞🌹💖.
_"Wani yarda kuma kake son in maka, bayan idanuwa na sun gane min komai." ta fada ta na hawaye._
Farida ko, sai murmushin mugunta ta ke, at least tayi achieving goal din ta. Da zata fita, saita buge Husna ta fita.
Husna ma na shirin fita kenan, Mubarak ya riko hanun ta.
"Wallahi my treasure, sharin Farida ne, wallahi banyi komai da ita ba."
"Toh miyasa na ganta ajikin ka?"
"Tana kokarin balla min botton ne na ke hanata. Amma wallahi ba abun da mukayi."
"Ban yarda ba, irin situation din dana gan ku, bai tabatar min da abunda kake fada ba." Tana magana ta na kuka, ga shi jiri take ji. Da Mubarak yaga kaman ta na loosing din balance din ta, sai ya je kusa da ita, zai rike ta tace ya kyale ta. Duk gabobin jikin ta sunyi weak, da kyar ta iya bude kofar office din ta fita. Tana fita shima yana biye da ita a baya. Bata yi tafiyan 5 mins ba, kawai sai tayi collapsing. Da sauri Mubarak ya tare ta daga fadiwa. Allah ma yayi cikin asibiti ta fada, so da sauri aka kaita wani ward. Wata female doctor, ta shiga ta duba ta, dan a fadan Mubarak, shi bazai iya shiga ba, kuma ba zai bari male doctor ya shiga ba.
Yana ganin doctor din ta fito, ya je wajen ta. "Doc Hafsat, me ya sa me ta." sai doc Hafsah tayi murmushi. Tace lets go to my office please.
Suna isa office din ta, tace "have a sit."
Sai ya zauna. "Doc please tell me what is wrong with my wife, and stop smilling."
Sai ta gyra muraya, tace" Congratulations Doc, kai ma ka kusan zama father."
Maganan ta ya mai kamar a na buga kararrawa ne acikin kansa. Sai yace "Me a Father?"
"Tace yes, and its a month old".
"Alhamdulilah." nan taa ke, yayi sujudu shukur.
Sai kuma ya kara magana "shikenan, ba abun da ke da munta." dan yana jin tsoron kar ace Bp ta yayi high.
"Aa akwai, she is stressed up ne, ka dinga sa ta tana hutawa, ta dai na ayiyuka masu stress."
"Toh shikenan nagode sosai."
"Zaka iya shiga ka ganta, dan ta tashi."
"Thanks so much doc, nagode sosai, Allah ya bar zumunci."
Advertisement
"Amin kani na" tin da man, haka take ki ransa.
Tana ganin ya shigo ta juya mai baya. Takai ci kawai take ji. Yaushe yaushe suka fara zaman lafiya, da har zai nuna hali.
"Na san baki son ganin fuska na, amma ina son ki san gaskiya na fada miki. Amma kuma zan so kiyi trusting din abun da nake fa. Ni ba ma zinaci ba ne."
Har ya gama magana, bata juyo ba. Sai ya cigaba da magana "Yanzu dai ina son inyi congratulating din ki on the journey of becoming a mother." sai a lokacin ta juyo ta kalle shi. Sai ya kara mai mai ta abun da ya fada. Haba saita fashe da kuka.
"Ai yaya ka cuce ni, me kake son in fada ma daa ko yaa ta, Ince mai/mata me, Uba ka/ki ma zinaci ne."
"Wallahi Husna ni ba ma zinaci bane. Ki yarda dani please. Kina ma iya tambayan Laiq, tun lokacin da muka yi aure ta ke shishige min. Amma yau Allah yabata nasara, tun da har kika gani. Amma indan ke ma zaki duba sosai, zaki ga tura ta nake, tana shi shige min.
"Zan yarda dan kana rantsuwa, amma bazan iya mantawa ba, kuka da kyar in zan yafe."
"Okay duk yanda kika ce ne treasure. So can I get a hug?"
"Ka min laifi kuma kace kana son hug?"
"A mana, ba kin ya fe ba?"
" I don't think so."
Suna cikin maganan su Doc Hafsat ta shigo. Sai ta gyara murya "hope dai bana damun ku ko?"
"A'a ko kadan aunty" Husna ta amsa.
"Toh, first of all congrats tawan. Second of all, zaki iya zuwa gida yau. Zan ba kanina list din Magunguna."
"Okay nagode."
"Dan Allah ki kula da kanki, ki dai na sa ma kanki damuwa, zai iya affecting din baby kin, kuma lastly ki daina stressing din kanki."
Abun da Mubarak bai sani ba ne, da ta tashi, sai doc ta mata magana akan stress din da ta ke ba kanta, sai ta ga tana kuka."me ke damun ki"
"Tace mata bakomai. "Bakomai amma kuma kike kuka?"
"A'a abu ne ya shige min ido."
"A na ga alama ai. Nifa mace ce, kuma na sani idan mace kama na tana cikin damuwa."
"Bakomai fa, kawai stress ya mun yawa."
"Ohh stress ya miki yawa kike kuka?"
Kawai sai ta kara fashewa da wani sabon kuka. Sai ta fada ma Doc Hafsat komai.
Doc taji tausayin ta sosai, sai yace"ni na san kanina ba zaiyi haka ba, sai dai Farida. Ba wanda bai san Farida ba a wajen aikin nan na mu. Haka wasu matan ke zuwa nan suna ci mata mutunci, amma ko a jikin ta. Kuma kince sai rantsuwa yake. Believe him, kuma nima shaida ce. Kawai dai tana son ta rabaki ne da mijin ki. Sabida cikin kwanakin nan, naji tana magana da kawar ta, wai sai tayi frustrating din auren ku."
Advertisement
"So gaskiya yaya na ke fada wai shari kawai take mai?" Doc Hafsat tace "Ae".
"Nagode sosai. Amma mai ke damuna?"
"Zaki ji a wajan mijin ki."
Shi dai Mubarak bai san ta riga ta yafe mai ba. Dan bata nuna mai alaman haka ba.
Suna cikin mota zasu gida, sai Mubarak ya kalle ta, yace "Yana ga kaman baki ji dadin news dinnan ba?"
"Na ji dadi mana, at least nima zan samu mai kira na Ummi." ta fada ta murmushi.
"Toh Alhmdulilah, tin dama nayi tambayan ne sabida banga kina zumudi ba."
"Da ka gama bata min rai zanyi zumudi?"
"Allah sarki Hayati, ina ta miki rantsu wa, amma baki yarda ba." Suna wuce wa ta hango mai agwaluma, ta kalle shi a shagwabe tace "Yaya ka siya mun."
"Toh my treasure, dayawa ko kadan?"
"Anyhow de"
Sai ya siyama ta, sai ya kara tambaya "mi kuma kike so?"
"Sai tace ice cream."
"A'a ba dai ice cream ba, it's not good for the baby fa, at this rate nutritional food ya ka mata ki rinka ci, and yes da abinci da zai rinka baki energy.
Sai ta fara hawaye, "ni dai icre cream na ke so."
" okay amma yau fa kawai zan siya miki, kuma zan miki list din abincin da ya kamata ki rinka ci."
"Ni sai yanzu ma nake regretting din auran doctor" ta fada tana murguda ma sa baki.
"Sai na buge bakin rashin kunya."
"Ka buga, nima na buga cikin"
"A'a baza muyi haka da ke ba."
"So nima kar ka buge min baki."
"At your service your mi lady."
*************************
Suna shi ga, Husna ta je toilet straight. Tana gama business din ta, ta wanke hannu ta, ta shiga cikin dakin. Shi kuma Mubarak na nan kwance a kan gadon ta. Tana fitowa tace " yaya nima fa very soon zaa fara kira na ummi ko?"
"of my treasure, nikum a kira da Abba. Nace ba, yaushe zamu fada ma su Ammi?"
"Ni dai gaskiya karka fada ma kowa, yanzu zasu fara mun dariya." sai Mubarak ya kalle ta yace "mike ciki?"
"Ai daman ba zaka sani ba, tun da ba kai ke dauke da shi ba." ta fada kaman za tayi kuka.
"Kiyi hakuri Hayati, wasa fa nake. Zamu fada masu duk lokacin da kike so."
Haka ta ita shagwabe ma yayan ta, shi kuma yana biye mata.
Yanzu cikin Husna yayi two months. Gashi yana bata wuya sosai. Da kyar take iya zuwa school. Ga baccin da yake sata. Ko aikin gida bata iyayi. Gashi tun tana boye ma su umma, har sun zo sun gake sabida irin wahalan da yake bata, yau lafiya, gobe ciwo.
*Bayan 4 months*
Yau Husna ta bi Mubarak wajan aiki, sabida zata yi antenatal. Husna na kwance saman kujera, shi kuma Mubarak yana aiki. Sai Farida ta shigo tana cin chewing gum. Tana ganin Husna akan kujera, ta yi tsaki. Sai ta je kusa da Mubarak, "honey pie, yau baka zo office mun gaisa ba fa?" ta fada tana ma tsawa kusa da Mubarak.
"Keh mallama daka ta, kina da kai kuwa?"
"Haba honey me ye haka kuma."
Sai Husna ta fashe da dariya. Gaskiya yau ta yarda Farida ba ta da hankali.
"Ke kuma me ke saki dariya?" ta fada a tsawace.
"Karki kara, ni ba tsaran ki ba ce." Husna na fada, ta kara fashe wa da dariya.
Zata yi magana kenan Mubarak ya daka mata wani irin tsawa."fita min a office, useless girl kawai. Lokacin da ake so, bakin ki bada hadin kai ba? Ni kuma yanzu bana sonki, ko atom haka. So please, dan Allah ki kyale ni."
Sai ta fita a office din ta na kuka, wai yau ita Mubarak ke wulakan tawa. Shi da komi tace ya yayi zai yi. Ya zata yi da rayuwar ta, gashi ta gama bata rayuwar ta da kan ta. Duk samarikan ta sun barta, ga girma yazo. Ta shiga office din ta, ta na kuka. Allah sarki rayuwa. Wai hot cake kaman ta, da maza ke rushing din ta, shi ne yanzu suke wulakan ta ta. Ita ada tayi zaton jin dadi ta ke, amma bata san tana bata rayuwar kanta ba ne.
Su Husna ko, tana fita Mubarak yayi hugging dinta. "Gaskiya Husna nagode ma Allah daya sa kika zama mata ta. Lokacin da aka hana ni Farida, nayi zaton cutar da ni a ke sonyi, amma gashi ina jin dadin zabin mahaifiya ta yanzu. Thanks for loving and caring for me.
_Thanks for reading, please comment. It's your comments that encourage a writer._
_Love_ 💖
_Zeexee_ 🌹💜💖💞
Advertisement
- In Serial29 Chapters
Author Vs Protagonist
Zhang Wei has always been average. His life was so average that he could well have been said to be the epitome of averageness. That all changed when he was caught one day in an accident. "From now on I will dictate your life and forge an epic saga." See the story of the shameless Protagonist and the abusive Author. Edit: The schedule currently is 2-3 chapters a day, each chapter being approx. 1000 words. Hope you guys enjoy. Special note: Guys forgive me, but there was a problem with my laptop that I used to write the chapters. I sent it in to repair and hopefully, by tomorrow or the day after it finishes. Very sorry. (15/4/2018) Note: Well, I still do not have my laptop yet. It seems that They haven't finished yet. Sorry guys but it will take a couple more days.
8 213 - In Serial24 Chapters
You're a God, go.
Jason wakes up one day and his reality is shattered. He's dead, so what now? He decides. Cover art courtesy of ColorGob. Check his DevianArt out. https://colorgob.deviantart.com/
8 151 - In Serial17 Chapters
Savage
A nation divided in two. An Empire wary of its past mistakes. An enemy that sticks to the shadows and sees everything. The death of magic. The rise of science. And behind it all, the wheel of progress, turning relentlessly. As the peninsula of Tahor waits once more for the great rain to arrive, a chain of strange events threatens to end the peace that has lasted for nearly seventeen years. Now, armies mobilize, men seek to uphold an order fraught with injustice, and a people thought all but extinct rise anew to claim powers that could turn the tide. An inexorable conflict brews between the Empire and the Kuuth, and it seems only a a matter of time until Tahor will be plunged into a Third Great War. Yet some are beginning to ask questions.
8 214 - In Serial43 Chapters
My Cruel Mates
Claire lives in a world where dragons, werewolves, vampires and other supernatural beings treat humans as meat and toys. All she wants to do is live a simple life away from anything that goes bump in the night. She does well, until the Dragon King sniffs her out, along with his werewolf mate.How will Claire adjust to the terrifying new turn her life has taken?*Trigger Warning*This story is much darker than my others. There are themes of abuse and suicidal ideation. Please consider this before reading.________________________________________"She smells good, doesn't she Bennett?" The deep timber of the man's voice rings out through the still night and my body shivers in fear and disgust. Suddenly another man is at my side, twining his fingers through my hair. I can't see either of them clearly in the dark. The man, Bennett apparently, leans down close to me and takes in a large lungful of my scent as well. My knees begin to shake in terror and a low growl rumbles from his chest."She does smell good. She's pretty too." He says, pecking a kiss to my cheek. My face crunches in despair as I try to pull from their hold. "Let me go." I beg and the first man chuckles. "Awe. The little human is nervous." He says, amusement evident in his voice. A sob breaks from my lips as I try to pull my arm from his grasp."You're hurting me." I say, tugging my arm again."Let her go, Rowan." Bennett says, making the larger man grunt."Don't get attached to her. You know what happened to the last one."Cover made by @ViaAlyssaNicole
8 561 - In Serial55 Chapters
Seoul Mates | OT7
Soulmates no longer connect. Most people don't even believe in them anymore since it has been over 70 years since the last soulmates lived and loved. Are soulmates really extinct? Or are people ignoring their destiny?Ma-ri returns to South Korea after swearing to never return when she left 12 years ago after the heartbreaking death of her mother. When she heard the news of her father's passing from a sister she never knew existed until a couple weeks prior, she broke that promise and traveled to the place that served as the bane of her existence for far too long before escaping.With plans to simply attend the funeral and leave the country immediately after, Ma-ri does a simple favor that changes her life in the most amazing way.June 2021 -Best Rankings#1 Polyamory 6/19/22#2 Seoul 7/2/22#10 Fanfiction 7/12/22#5 Korean 9/9/22#1 soulmates 9/13/22
8 59 - In Serial11 Chapters
Red Roses (XianWang-English Version) - END
Wei Wuxian and Lan Wangji's Second Life after Reincarnation, but this time Wei Wuxian didn't want to be the underdog to Lan Wangji. ️ Top/Seme : Wei Wuxian Bottom/Uke : Lan Wangji this is Xianwang area, not Wangxian! here Lan Wangji is the uke/bottom! those who don't like don't read, ok? Areas: Yaoi, BxB, BL, Homophobic get out of the way!
8 197

