《RAYUWAR HUSNA (hausa novel)》part 32 &33

Advertisement

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*RAYUWAR HUSNA*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

🅿️:3️⃣2️⃣-3️⃣3️⃣

_Bismillah_

_Amma miyasa baki sona?_

Saita yi shuru, ta kasa bashi amsa.

Shikenan tunda bazaki amsa mun ba. Don rashin amsa ki ma yabani amsa.

Sai ta dauke idonta, tana share hawayen ta.

Gaskiya Faiz is a lucky guy, I wish nima zan samu wacce zata soni haka. Yana gama magana ya bar wajan.

Kwanan su biyu kenan, basu haduwa. Ita Husna, tana tashi da wuri, ne sai tayi aikin gida, tayi breakfast, in lokacin lunch ma yayi ta girka, in dinner ma yayi zata girka. Tana kamala komai, zata dibi nata abincin ta kai dakinta, sai ta bar masa nasa cikin food flask akan dinning table.

Yauwa ma kaman kullum ne, yana dawo wa daga masjid, ya shiga dakinsa, ya koma barci.

It kuma Husna na idar da sallah, tafara girki. Abinci bai dau wani lokaci ba, sai tayi serving din nasa, tasa akan dinning, sannan ta dau nata ta tafi dashi daki.

Mubarak bai tashi ba, sai 8am. Yana duba time, yatashi da sauri, ya shige toilet. Da sauri sauri yake shiri, dan ya makara. Gashi yau yayi resuming. Yana gama shiri, ya wuce cikin motan sa straight. Bai ma bi takan abinicin data ajiye masa ba.

Ita kuma Husna, tana jin karan mota, ta leka ta window, taga yafita. "Ko ina zashi oho mai". Tafada a ranta.

San da tagama shiri, kafun ta fito parlor. Tana parlor tana kallo, sai flask din dake kan dinning yayi attracting dinta. Sai ta tashi, taje dinning area, tana isa wajan, taga plate din data ajiye mai, yana nan yanda ta barshi. So yaya baici abincin ta ba yau. Kuma gashi ya fita bai fada mata ba. Aiko ba komai, ya kamata atleast ko letter ne ya rubuta ya ajiye mata, mtchww ta ja tsaki.

Hak rayuwa taci gaba da gudana, har tsawon two weeks basu hadu. Husna tafi cutuwa, tinda baa koma school ba, so zaman gida take. Shiko Mubarak yana fita aiki, so abun baya wani damun sa. Gashi tana abunda ya kamata.

Yau saturday, Husna nata jiran taji motsin motar Mubarak ya bar gidan, amma sai taga bai fita ba. Ita gaskiya zaman nan da suke yi yafara damun ta. Zaman da ba ko sallama a tsaka nin su, kawai kowa na harkan gaban sa ne. Gaskiya ita bata saba da irin wannan zaman ba. So saita kudura a ranta, zata je dakinsa bayan zuhur suyi ta, ta kare.

Yana dawowa daga masjid, ya je dinning striaght. Daman, ta riga tasa masa abinci sa a dinning. So daya gama cin abinci yayi clear din table, ya wuce dakin sa.

Ita kuma Husna, ta na jin motsin kofar sa, tafara practicing din abubuwan da zata fada masa. San da taga ta tsara masa speech mai kyau, sannan tayi addua ta tofa, sai ta tashi daga kan gado, sai taje dakinsa striaght.

Tana isa kofar dakin tayi sallama, bata tsaya jin ko zai amsa mata ba, ta shiga dakin.

Tana shiga, tagan shi dauke da laptop dinsa akafa yana aiki.

Daman yayi niyar ajiye laptop dinsa kenan, yaji sallamata, sai ya kara bude laptop din yana dan nawa kaman aiki yake.

Tana ganin shi haka, sai tafara doubting ko takoma ta dawo anjima ne ko ko a'a. Sai wata zuciyar tace tamasa magana kawai, tinda tasamu opportunity din ganin sa yau. Kawai sai tayi nodding din kanta, sa mi ta fada zuciyar ta cewan zatabi last option din.

Advertisement

Duk abunda takeyi yake gani, amma sai yayi kaman baya ganin ta.

"Yaya nayi sallama baka amsa ba."

Sai ya kalle ta, ya tabamye ta lokacin data shigo.

Kaji raining hankali. "Yanzu yaya zaka ce baka ji sallama ta ba."

"Keh madam, mai da wuka. Kema dai kinga ina aiki ne ko, so bana son damuwa."

"Lallai ma. Daman ina son muyi wata magana ne."

"Ki fadi duk abunda zaki fada, ina jinki."

"Toh karufe laptop din mana."

"Ba saina rufe ba, ke dai kiyi maganan ki, ina ji."

" Toh daman yaya, ina son mukawo karshe wannan rashin maganan mune."

"Ban gane ba, kiyi explaining da kyau."

" Wai yaya miyasa kake mun haka ne, wacce irin explanation kake so kuma. Ni gaskiya na gaji da irin zaman nan, zaman da ko ci kanka ba'a fada ma juna?"

"Hahhh" yayi wani irin dariya." Har kin gaji?"

"Na gaji mana, ni ban saba ina irin wannan zaman ba."

"Ya kamata ki sabi gaskiya, dan yanzu kika fara."

" Yanzu na fara kuma? "

"Of course yanzu kika fara."

"Toh yaya me na maka, da kake min hakan?"

"Baki mun komai ba, illa bana son muamala da wance bata so na, bana son mu amala da wace kanta kawai tasani. Shikenan, any more questions."

Zuciyanta na tafasa, ta bar dakin. Tana shiga dakin ta, tafara kuka. So dan wan nan abun ya daina magana da ita. Ya ilahi, ya zatayi da rayuwanta?

Haka ta rinka kuka, ba mai rarrashinta.

Tana fita ya rife laptop, ya ya rike kansa. Bada son ransa yake mata duk abubuwan nan ba, amma shi yana son taji yanda yake ji ne. Ta san irin pains din da shi yake ji.

Husna ko inba kuka ba, ba abunda takeyi. Tana kan kukanta, aka kira sallah. Da kyar ta iya tashi ta shiga toilet tayi alwala.

Tana idar da sallah, ta zauna akan sallayan, tafara wani shafin kuka. "Ya Allah ka kawo min karshen wannan masifan". Tana ta kuka, ta addua.

Mubarak na dawowa daga sallan isha, ya je dinning straight kaman yanda ya saba, amma yaga ko ina wayam. Ya shiga kitchen, baiga alamun kaman anyi girki ba. Ransa abace, yaje dakin ta. Yana shiga ya ganta kwance akan sallaya.

"Keh!" Ya daka mata tsawa.

A firgice ta tashi ta zauna.

"Miya hanaki girki?"

"Bana jin dadi ne wallahi."

Sai ya taba goshin ta, yaji yayi zafi sosai.

"Meke damun ki"

Sai tafara hawaye, tace "babu"

"Babu! Kuma jikin ki da zafi?"

"Toh ban san abunda ke damuna bane."

Sai yakar taba goshin ta da wuya, sai yace "kaman zazabi ke damun ki, bari naje na siyo mana abinic, sannan na siya allura da magani"

Still ta na hawaye tace "toh".

Gaskiya taba shi tausayi sosai. Kardai shiya kara jawo mata ciwo wannan karon ma. "Ya salam, da ban mata haka ba, da kawai na zaunan da ita munyi magana, mun fainci juna." Amma fa ta hanyan nan kawai zata fada mai inta son sa, so dole yayi pretending kaman ma baisan tanayi ba.

Da sauri ya shiga dakin sa ya dau keyn. Sai yafara zuwa wajan siyan abinci, sannan yaje pharmacy ya siya allura da magunguna.

"Waya tashi kici abnici."

"Bana jin yunwa."

"Kar ki bari nayi fushi, ki tashi kici."

Da kyar ta tashi ta zauna, sannan yafara bata abaki. Da kyar taci 5 spoons, tafara masa kuka wai ita ta koshi. Da kyar ya lallabe ta, ta kara 5 spoons.

Advertisement

"Toh saura allura ko?"

"A'a ni bana so, in nayi barci zan warki."

"Shuuu, I don't want to hear anything."

Da kyar ya mata allura, sannan ya bata magani. Sai ya dauke ta ya sata akan gado. Yana gyra mata blanket kenan, wayar sa ta fara ringing. Yana ganin mai kiransa, ya fara murmushin mugunta. "Ko kin ki ko kin so, sai kin furta min kalaman soyayya inkika ji conversation din nan." Sai ya daga call din.

"Hello darling, how are you?"

"Allah sarki my jewel, kice dai work was stressful kenan yau."

" Jewel kuma" so har yaya ya fara son wata kenan?

Sai taji kaman ana caka mata wuka a zuciyar ta. Sai wasu zafafan hawaye suka fara zubowa daga idon ta.

"Kai jewel, baki gajiya da tsokana. "

"Nima nayi missing dinki sosai."

"I love you too my jewel. Please kiyi barci yanzu, karki zo ki makara baki tashi sallah da wuri ba gobe."

"Aha, that my jewel. Kina burge ni sosai."

"Okay bye l love you, don't allow the bed bugs bite. "

Yana katse wayar, ya kalli Husna wace fuskan ta yagama yin cabe cabe da hawaye.

"Miya faru kuma?"

"kai na ke ciwo." Ta fada tana hawaye.

"Ai gashi na miki allura, kuma na baki magani, kedai kiyi barci kawai."

Tace "toh"

Shi ko sai boye dariyan sa yake. "Kai amma Laiq ya iya game dinnan sosai." ya fada azuciyar sa.

"Nasan zaki furta soyayar ki bada jimawa ba."

"Sai da safe." Fada yana dada gyra mata blanket.

Kai kawai ta iya jijigawa.

Ai yana fita ta cigaba da kuka, sai kuka take kaman ranta zai fita. "So yanzu yaya baya so na, wata yake so. Nashiga uku, in zansa kaina?" Tanata kuka, har barci barawo ya dauke ta.

Shi kuma yana shiga dakinsa, ya fara dariya.

"Kai jamaa, ai kin kusa fadan abuda ke zuciyar ki." ya fada yana dariya, harda rike ciki. Yana cikin dariya, kiran Laiq shigo. Sai ya asma kiran. Sai suka fashe da dariya.

"Aikin mu yafara kyau ko?" Laiq ya tambaya.

"Sosai ma, ina da assurance din cewa zata furta very soon."

"Allah yasa"

"Amin main. Sai da safe kenan."

"Allah yatashe mu."

" Amin."

Da kyar ta iya tashi tayi sallah, so tana idarwa ta koma kan gode, ta rufa jikin ta da blanket, dan wani irin sanyi take ji, musan man ma inta tuna da wayar da Mubarak yayi jiya agaban ta.

Da kyar ta samu ta yi barci.

"Madam ki tashi ki ci abinci ki sha magani."

Ba musu, ta tashi.

Yana jiran ta gama ci, sai ga kiran Laiq.

"Assalamu Alaikum honey bunch."

"Kin tashi lafiya?"

"Haka ake so ai."

"Karki damu, mudin muna raye, auran mu yazama dole."

Sai taji zuciyar ta, ta bugawa, kaman zai fito daga kirjin ta.

"Shikenan, yaya yasamu wace take son sa, ya barta da jinya."

Mubarak yafi 30mins yana waya. Daya gama wayan, sai ya mata allure, zai bata magani kenan, tace kar ya damu, zata sha da kanta.

*Bayan sati daya*

Mubarak bai canza ba. Sai ya ganta yake hira da budurwa. Ita ma Husna ta samu suki sosai.

Although sun daina makalewa a daku nan su, suna cin dinner tare, in zai fita yana gaya mata, suyi kallo tare e.t.c, amma haryanzu basuwa wani magana da juna, sai dai inya zama dole. Gashi Husna ma sunyi resuming, yanzu tana 300l ne.

Kaman kullum, suna zaune a parlor, wayar Mubarak yayi ringing, sai ya daga. Yana ta ma wacce ta kira shi kalaman soyayya. Abun nata kona ma Husna rai. Tuna tana daure wa, kawai sai taji abun ya kai ma ta mako shi, sai ta fisge wayar, ta yar dashi kasa.

"Miye haka Husna?"

"Abunda ka gani."

"Hanya kina da hankali kuwa?"

" Kinsan ko dawa nake waya, kin san mahin mancin ta a waje na kuwa?"

" Wallahi yaya baka da kunya, ai ko ba komai, zaka yi respecting din na. Ya zaka dinga magana da budurwar ka agaba na? Amma sabida ka mai dani bola, ban da mahin manci a wajen ka?"

"Kinga mallam, ki iya bakin ki. And moreover, ai baki sona, so miye na damuwa dan nayi magana da wata?"

"Yaya kenan, wai in iya baki na. Ina ki fa?"

"Zaka dake ni ne saboda wata banza?"

"Komai ma zan iya yi akanta. Zuciya ma na son mai sonta ne. Tinda baki sona, ki kyale ni nayi soyayya da ko waye ma."

Yana gama magana, yayi tsaki, ya dau wayarsa. Zai bar parlorn kenan, tace yasaya.

"Na san am too late yanzu kam, amma kasan yanda nake ji ne kake fada ma wata kana sonta kuwa?"

"Kasan yanda zuciyata ke min bara zanan buga wa kuwa?"

"Of course na sani, tinda kema kina son wani ne. Relation na biyu kenan da zanyi, da matan basu sona, ni nake son su. So yanzu dana samu mai sona, dole na numa mata so a duk in da nake. Shikenan abun da yasa kika tsayar dani?"

"A'a ban gama ba. Amma yaya ka san ta kaicin da yake tattare da son wanda yake sonka, amma unfortunately yasamu wata?"

Kasan irin pains din dana ke ji ne?"

"Hahhhh," Mubarak yayi dariya. "Toh ke kina sona ne, da har zaki ce kina jin pains in ina magana da rabin raina."

"Karka kara kiran wata rabin ranka agaba na. Akwai wata rabin ran data wuce ni ne? Akwai wata data kaini mahin manci ne a gareka?

Miyasa bake mun haka?

Miyasa kake son in kamu da ciwon zuciya ne?"

Shi ko sai kallon ikon Allah yake. A yanzu dai abun da zai sa shi farin ciki, shine inta furta ta na son sa. Dan shi yafara gajiya da wannan karyan kiran Laiq a matsayin na mace.

"Kai yanzu yaya zaka ce baka san abunda nake ji ba? Wato tinda ban baka amsa ba, sai kayi deciding zaka samu wata. Toh ayau nayi shirin fada maka abun da yake raina." tana magana tana kuka. This is really hard, amma in zaiyi saving din auranta, zata fada mai gaskiya.

"A yau din nan zan baka amsa akan tambayar daka dade kana mun."

Sai ta rufe idonta. " ban san lokacin dana kamu da wannan ciwon ba, bansan lokacin da na fara kishin nan ba, bansan yanda akayi ya shige ni ba. Kuma amsar tambayar ka shine tabbas yanzu kam ina sonka har cinkin zuciyata."

Husna na fadan haka, yaji kaman an zuba mai ruwan sanyi tun daga kai har kafa.

_Thanks for reading, please comment. It's your comments that motivates a writer._

_Love_ 💖

_Zeexee_ 🌹💜💖💞

    people are reading<RAYUWAR HUSNA (hausa novel)>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click