《RAYUWAR HUSNA (hausa novel)》part 22 &23

Advertisement

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*RAYUWAR HUSNA*

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

🌹

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_🔱((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(Zeexee)_

🅿️:2️⃣2️⃣:2️⃣3️⃣

Am dedicating this page to my friend like sister *FATIMA ZARAH EYMAN*. I can't love you less wallahi, you have been a big pillar. Nagode sosai, Allah yabar kauna. Gaskiya School bus tayi rana.🙈🙈🌹💜

_Bismillah_

_Toh! Miye matsalar sa. Mubarak ya tambaya._

Naga you guys still need space kafin bikin, amma shifa baya son ayi fixing din bikin yayi dogo dayawa. Shi yana son arinka abu sharp sharp ne. Umma ta amsa.

Akwai matsala. Dan da tani ne, sai nan da shakara 2.

Wai miyasa kake haka ne Mubarak, kai baka san bai kamata irin wayan nan maganganu na fita daga bakin ka ba? Haba danAllah, saiyi kake kaman kai kadai ne baka son auren, ai Husna ma bata so, amma ni nasan abun da na hango yasa nace kuyi aure. Amma ku biyu kullum sai kun bata min rai, ko ban isa ince kuyi abu bane?

A'a wlhi umma bahaka bane. Mubarak ya fada.

Toh ya ne. Nifa na san abun da na hango, amma sai yi kuke kaman na cuce ku ne. In short ma zan fada ma suran family, a fasa auran kawai. Kai Mubarak ka aura Faridan ka, ke kuma Husna, ki jira duk lokacin da Allah zai cire miki son Faiz, sai ki aura wani. Oya ku tashi ku fita. Umma ta fadi rai a bace.

Umma dan Allah.... Husna na son tayi magana, Umma ta katsai ta.

Bana son inji komai, kawai kufita min a daki.

Jiki a sanye su biyu suka fita daga dakin. Suna fita daga dakin Mubarak ya daka ma Husna tsawa.

Keh! A firgice ta kallai shi.

Advertisement

Kinga abun da kika ja ko, tinda kika fara zama a gidan nan komai ya fara cabewa.

Minayi yanzu. Bakai kake maganganu a gaban umma ba, kuma mi........ Bata kai aya ba kawai taji mari a fuskan ta.

Inalillah wa inailaihi rajiun. Mina maka yaya, laifin mina maka. Dan zan fadi gaskiya?

Kimun shuru! Wata uwar gaskiya zaki fada enh, umma bata taba fushi da niba, amma da kika dawo gidan nan, ta fara fushi dani. How sure am I that bake kika fada ma umma kina sona ba.

Wa iyazubillah. Mi zanyi da kai, kaga ina baka girma yanda ya kamata, amma yau ka tabo inda bai kamata ba. Arayuwan nan, ba wanda ya taba mari na amma yau kai, kai dana dauka as best brother na, ka mare ni. Kai daya kamata ka tare min duka, nagode sosai, Allah yabada lada. Kuma kacai a dalilina Umma ta fara fushi da kai ko, toh In Sha Allahu zan bar maku gida. Gobe In Sha Allahu nima zan koma gidan iyaye na.

Tana gama magana, ta bar wajan. Tana shiga dakin, tafara jera kayanta cikin akwatin ta tana kuka. Wai ita yaya Mubarak ya mara yau. Tana cikin yin haka kawai wata tunani tazo mata. Kawai sai ta dau hijabin ta, da purse, ta sa takalminta flat ta fita.

Shiko Mubarak, tana wucewa, shima ya kama hanyar dakin sa. Can you imagine, shi yar yarinyan nan zata wa haka. Yarinya ana ganin ta shuru shuru, amma maganganun bakin ta yafi karfin ta. Yana tsaye a gaban windown dakin sa, ya hango ta tanafita daga gate. Sai yafara magana da kansa, Kar dai yau zata koma gida, amma ina akwatin ta? Yana ganin ta fita, shima ya dau wayarsa, da sauri sauri yabi mata baya. Ai sai ya san inda zata.

Husna na fita daga dakin, ta tari keke, tace ya kaita federal lowcost gidan su cousin dinta Fatima.

Advertisement

Mubarak na fita ya ga ta shige keke, luckily ya samu acaba, sai yacai masa ya bi keken abaya.

Suna fara tafiya, Husna tasa kanta akan cinyoyin ta, ta fara kuka. A yau ita aka ciwa mutunci haka. Bata taba tunanin yaya Mubarak zai ci mata mutunci haka ba. Ga umma ma tayi fushi da ita. Miyasa komai ke cabe mata ne, for one year yanzu, saidai ta shiga wanan problem din, inta fita, ta kara shigan wani. Tana kuka tana tunani.

Suna cikin tafiya, Mubarak na biye da su abaya, suna kaiwa wajajen bumps din dake hanyar Federal lowcost, sai break din wani babar mota yayi failing. Inda mai keken ta ke kokarin matsawa, kawai sai ya bugu da wani poll, haba sai ga su Husna acikin kwalbati.

Inalillahi wa inailaihi rajiun, Mubarak yafadi. Bai ma san lokacin da ya sauka akan acaban ba.

Jini sai fita ya ke a jikin Husna da mai keken. Ai kuwa kamar jira ake abu yafaru, mutani suka cika wajan, shi kuma Mubarak sai tura mutani yake. Yana ganin condition din Husna ya kara rikicewa. Sharp sharp ya kira asibitin dayake aiki suka taho da ambulance, aka dauki Husna da mai keke, aka sa su cikin ambulance.

Mubarak na kokarin wucewa, ya ji ana janshi, ya juya kawai yaga dan acaban daya dauke shi ne. Kabani kudi na mallam, dan acaban yafada. Rai a bace, Mubarak ya fita da kudin da bai san adadin su ba, ya bawa dan acaba. Yana bashi, ya je yashiga ambulance din shima, sai asibiti.

Acan gida kuma, Umma ta fito daga dakinta ta ji koina shuru. Taje dakin Husna, kaga wayam, yaje dakin Mubi, shima haka. Sai ta fita compound, taga motan shi, sai tafara mamaki, ina toh suka je. Kar dai sun fara daidai tawa. Hmmm, wannan kuma nasu, dan ita fa she has madeup her mind. Auran nan bazai faru ba kuma.

Awa daya, biyu, har uku, bataji hurdan su ba, haba sai hankalin ta yatashi. Taje wajan mallam Garba gate man, ta tambaye shi ko yaga su Husna, sai yace a, Husna ta fara fita, sai shima Mubarak ya fita. Ta kira layin Husna taji shi akashai. Nan fa hankalin ta ya kara tashi. Sai ta kira na Mubarak, yayi ringin kusan sau biyar kafin ya daga.

Mubarak wai ina ka ajiye wayarka ne, bar zancen nan ma, kuna tare da Husna ne, dan na ita kiran layinta amma akashai yake.

Sai yafara tunani yafada mata ne ko kar yafada mata.

*Ya kuka gani, ya fada ma umma ne ko dai a'a*. _sai naji feedback_

Thanks for reading, please comment. It's your comments that motivates a writer.

_Love_ 💖

_Zeexe_ 🌹💜💖💞

    people are reading<RAYUWAR HUSNA (hausa novel)>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click