ใ€ŠRAYUWAR HUSNA (hausa novel)ใ€‹part 17 &18

Advertisement

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒน

*RAYUWAR HUSNA*

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐ŸŒน

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_๐Ÿ”ฑ((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

*WRITTEN BY ZAYNAB* _(zeexee)_

๐Ÿ…ฟ๏ธ:1๏ธโƒฃ7๏ธโƒฃ-1๏ธโƒฃ8๏ธโƒฃ

_Bismillah_

Husna na kuka ta fita daga dakin Umma. Tana fita taci karo da Yaya Mubi. Ya na ganin ta ahaka sai yarikice. Shi a zaton sa ko umma bata yarda bane, amma in umma bata yarda, miye na kuka kuma ? This is serious. Kar dai umma ta marai ta ne. Duk a zuciyan sa yake wayan nan magan ganun.

Husna, ya kirata. Yaga ko juyawa ma batayi ba. Ya kara kira still bata juya ba. Kawai sai ya shawo gabanta.

Keh Husna ba da ke nake ba. Sai ta tsaya, but still tana ta hawaye. Miya samai ki?

Bakomai, ta amsa masa ba yabo ba fallasa.

Babu amma kuma kina kuka.

A, ai dai naga kuka na ne ba naka ba.

Bangane ba, daga tambayan ki kuma sai kirinka mun magana kaman ni din tsaranki ne ?

Kaga yaya karka ga ko don Ina baka grima ka dinga mun yanda kake so. Kai kacai najai wajan umma in mata magana. Amma bansan kana da other plans ba.

Keh dakata mallama. Ko dai wasa yayi yawa a tsakani na dake ne. Quite alright ni nace ki je ki yi wa umma magana, amma kuma ban san zancen wani plan ba. Mind the way you talk to me.

Please yaya bana son dogon surutu. Duk amsan da kake so, kajai wajan umma zaka samu. Excuse me. Taja tsaki ta wuce. Tana shiga dakin ta, ta dauko hoton Faiz, ta zauna akasa ta fara kuka maicin rai. Yanzu yaya da kana nan ne, baza a mun haka ba, just imagine wai na aure shi Fisabililahi. Ni yanzu an maida ni object kenan ko? Na zama trash bin din kowa ko, ta na fada tana kuka. Ina zata sa kanta. Ita kam ta shiga ukun ta.

Shiko yaya Mubarak, ya ji zafin kalamun ta sosai, har cikin zuciyar sa. Amma dai bakomai. Shi zai shiga wajan umma dan yaji abunda ya faru. Dama yasani tun farko bai ce wa Husna ta mata magana ba, da yayi da kansa.

Assalamu Alaikum .Mubarak yayi sallama.

Waalaikumus salam umma ta amsa.

Sai sukayi gaisuwa, amma da kyar umma kai amsa sa. Sai tace masa toh ya akayi.

Daman, na hadu da Husna ne, tana kuka, sai na tam baye ta mike sata kuka, sai tace min wai nazo wajan ki zan samu amsa.

Hahhhh, umma tayi wani irin dariya. Sai tace Husna kenan. Wato ba zata fada maka kenan ba, sai dai kaji daga bakina ko. Hahh, umma ta kara wani dariyan.

Advertisement

Gaskiya Mubarak ya dan tsorata da yanda umma keyi. Bai iya caiwa komai ba, sai kallon ta yake.

So ta zo min ne da maganan budurwar ka. Kaga ko plate din data kawo min abinci a ciki ma bata dauka ba. So data zo min da Zan can, na ce mata bazan yarda ba.

Please umma kiyi hakuri, if I heard you clearly, don kin ce bazaki yarda ba, sai ta fara kuka?

Yazata yi kuka don nace bazan yarda ba. Ai sai ka tsaya na kai aya kafin ka fara tambaya ko.

Ya hakuri umma, am just curious ne shi yasa.

Toh, yanzu sai ka budai kunan ka. Yacai toh. Sai umma taci gaba da magana. So ta zo tacai wai inyi hakuri na yarda, tinda abunda kake so kai nan. Haka dai umma ta fada masa ko mai, amma banda zancen cewa ta fada wa Husna ta aure shi, kawai sai tace ya jira zai ji sauran in Abban Husna da yayan sa su ka zo.

Toh umma. Amma umma baki fada min abunda yasa kanwata kuka ba.

Toh ai shi yasa nacai maka ka jira su Abdallahi ko?

Okay. Amma umma dan Allah miyasa baki son abunda nake so ne. Wallahi umma ina sonta sosai. Umma dan Allah ki ba soyayyan mu chance dan Allah please umma. Just this once please.

Inbaka son bacin rai na toh kafita, in bahaka ba tohm.

Jiki a sanye ya bar dakin. Shi bai san abun da yasa bata sonta ba. Yana tunani, zai shiga dakin kanwarsa, ya ji tana kuka, har yanzu bata daina ba.

Allah kadai ya san abunda umma tafada mata haka. Sai yayi sallama, amma bata amsa ba, sanda yayi sau uku kafin ta dago kai. Duk idanuwan ta sunyi ja'a.

Husna what is it please. Dan Allah ki fada min, umma ma ki fada min.

Ba'a baki na zaka ji ba. Ka jira duk ranan data so fada maka. Tana gama maganan, ta shige toilet.

Shi Mubarak mi zaiyi in ba kallon ikon Allah ba. This is serious gaskiya.

Throughout wannan week din Husna na ta boye wa yayanta. Ko yace tazo ya kai ta school, sai tace ba'a lokacin zata ba, ko kuma kafin ya fito ta wuce. In ma tana school kuma ya kirata yace ko yazo ya dauke ta ne, sai tace basu gama lectures ba, ko kuma yayan su Aisha zai zo daukan su. Shi dai yaya Mubarak ya kasa gane abun da ke faruwa take gudun sa ne. Ga shi Farida ma ta fara matsa mai. Shi yama kasa gane abun da ke faruwa ne.

Advertisement

Husna ma da umma sai dai gaisuwa. Bata wani hira da ita. In kuma tana jin hira, sai ta jai gidan Hajiya Khadija.

Toh yau ne ranan da Alhaji Abdullahi, "Abban Husna" da yaya Salim za su zo. Sai aiki akai, umma ma sai kai komo takai. Duk da cewa Husna bata iya magana da umma yanzu, sanda suka yi yau. Shi kuma Mubarak, sai addua ya ke kawun sa da yayan sa su biye mai, balai ma kawun sa. Dan ya san suna yarda umma ma zata yarda.

Karfe 5pm sharp su Abba suka iso. Husna na ganin abban ta, ta jai da gudu ta rungumai shi. Sannu da zuwa Abbana.

Toh Abban ki kadai kika sani ko. Yaya Salim ya fada.

Am sorry yaya, sannu da zuwa.

Kai kunma tuna dani kuwa ? Mubarak ya fada

Gaskiya kam bamu sanka ba.

A'a ni kam na san shi, tunda da'a na ne.

Exactly uncle, ka fada musu.

Zo son mu shiga ciki, ka bar su a nan.

Ba damuwa, zo kanwata muma mu shige ko, tace toh.

Duk suka shiga ciki. Umma ta ji dadin ganin su sosai. Sai yi take kaman zata cinye su. Ta ba su refreshments kala kala.

Kowa ya gama cin dinner, duk suka hadu a parlorn umma. Umma da Abban Husna suka zauna a waje daya, yaya salim da yaya Mubarak suma suka zauna a waje daya. Sai Husna ta zauna ita kadai.

Abba yayi sallam, yace, da fatan kowan nan ku na cin ko shin lafiya ko?

Duk suka amsa da a. Yace toh MashaAllah.

So am just going straight to the point. Kai Mubarak, umman ku ta ce min kace mata ka samu wacce kake so, kuma ka nuna mata hoton ta, amma yarinyan bata zauna mata ba ko.

Mubarak yace a haka ne.

Okay. Tana fada min, nima nakira yayan ku na fada mai. So sai muka yanke shawaran zuwa yau gobe mu koma. A gaskiya abun da ya kawo mu shi ne, munzo ganin yarinyar ne da idanuwan mu, sannan mu yanke shawara tare. So ka nuna mana hoton.

Mubarak na nuna wa Abba hoton, Abba ya buga wani uban salati, sai ya ba wa Salim shima ya gani. Salim ma na gani shi ma ya yi salati, yace ina ka samo wannan kuma.

Atoh Kai ma zaka fada ai.

Gaskiya am disappointed in you son, kai baka maji kunyan nuna mana ba. Da'a nayi zaton maybe Adda ta ke exaggerating ne, amma gaskiya yanzu kam nama ga hakurin ta.

Kai yanzu a ganin ka wannan batafi karfin ka ba? Salim ya tambayi kanin sa.

Please Abba da yaya, wallahi ina sonta. Kuma kar ku duba yana yin dressing dinta kuyi judging din ta.

Kana ma da baki. Kai yanzu baka jin kunya, jibi irin kayan data saa, ga kai ba dan kwali. Gashi ma duk ya sha attachment. Kuma ita kake son ta zama uwar ya'ayan ka. It's a pity. Abba ya fadi.

Kana sonta kuma ita ma ta na son ka ko? Yaya Salim ya tambaya. A, muna son ju na sosai. Toh yanzu ka Kira ta, sai ka sa a speaker, kace mata anki yarda da soyayyan ku a gidan ku muji amsar ta. Ko ya kace uncle.

Good idea Salim. Haka su kasa Mubarak ya kira ta. Husna da Umma kuwa sai kallon ikon Allah suke.

Baifi minti uku ba Farida ta dauka. Tana dagawa, yayi sallama da ita, sai tace ita fa bata son wannan sallama, kuma ba tace mai ya daina kiranta by this time ba, sai dai ka man 12 ba.

Maganan ta yasa kowa warai ido.

Kiyi hakuri please, daman akwai wani important maganan da nake son nayi da ke.

Kai mallam, ka fiya naci wallahi, toh ya akayi.

Daman akan soyayyar mu ne, yan uwa na ba suwa son soyayyar mu. Wallahi yanzu ma sunce sai na rabu da keh.

Toh sai me. Tinda ma bawani sonka nake ba, kai ka nacai mun. Ka ga this is a good opportunity. So bye, karka kara kira na.

Hmmm, kuma kake kukan cewa in baka aure ta ba, za kayi ciwo. Yanzu sai ka mutu. Umma kenan tayi magana.

Shi dai Mubarak ji yake kaman kasa ta bude ya shiga.

Ita kuma Husna tasan end din ta yazo kenan, yanzu umma zata yi maganan da tayi Mata.

Kai, har naji maka kunya wallahi. Salim yace.

Toh yanzu Adda, miyai mafita.

Ni dai nayi suggesting, amma bansan yanda za ku dauki advice din na na.

Muna jinki.

Daman nace ko a hada shi da Husna ne.

Ji dukan su sukayi kaman an ka shai fuss ne. Ko ina yayi shuru.

Gani nayi they are both going through break up, so za su iya tai maka wa juna.

Ko me kuka ce

Thanks for reading, please comment, it's your comments that motivates a writer.

_Love_ ๐Ÿ’–

_Zeexee_ ๐ŸŒน๐Ÿ’œ๐Ÿ’–๐Ÿ’ž

people are reading<RAYUWAR HUSNA (hausa novel)>
    Close message
    Advertisement
    You may like
    You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
    5800Coins for Signup,580 Coins daily.
    Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
    2 Then Clickใ€Add To Home Screenใ€‘
    1Click