《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》PART 2:CHAPTER ELEVEN

Advertisement

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/

*💘

*page 29-30*

Ummata na k'ira wacce muna gama gaisawa ta rufeni da fada,wai dole na ajje wannan baccin safen nan agefe wanda ya riga ya gama bi min jiki,tace idan ban kama jiki na watsar da kiwiya agefe na dunga kula da mijina ba,toh kuwa namiji shi babu ruwansa,idan yaga bakya masa abunda yakeso toh kuwa yana iya banka miki kishiya wacce zata zo ta dunga kula da bukatunsa da kuma tattalinsa,ke kuwa awatsar dake agefe ki koma 'yar kallo.Mun jima tana min nasihu meh ratsa xuciya,daga bisani mukayi sallama.Shima Abbana na k'irashi mun gaisa.Har yake labarta min irin yanayin da Umma ta shiga alokacin da take ta k'ira amma babu amsa.Dariya nayi sosae tare da jin wani irin soyayyar Ummata na ratsa jinin jikina.

Kai tsaye na latso _*My Ashwairiyya*_.

Ita kuwa awannan lokacin ta fito wanka kenan,tana gaban madubi tana taje kanta,so take taje taga dakin Suhaima.Wayarta dake gaban madubi taji ya dauki kida,da hanzari takai hannu ta dauketa.

*' shine sunan data gani yana rawa akan screen,gabanta ne taji ya bada rasss!.... Jefar da comb din hannunta tayi tare da mik'ewa da sauri har jikinta na dan rawa don tsananin tsoro da kuma fargabar abinda zataji daga sahibar tata.

"Hel....lo... Fateenah'...... " haka ta fada cike da in-inna ah sa'ilin da tayi picking call din.

Bushewa da wani irin dariya nayi don nasan abinda take yiwa wannan rawar muryar,wato atunaninta tsantsar tashin hankali zata tsinta daga gareni shiyasa take cike da tsoro. Allah sarki my Ayush komai yayi chas-chas ahalin yanxu.

Nace"Malama idan zaki daidaita muryarki toh tun wuri mah ki daidaita don ni yanxu babu abinda nakeso sama da mijin da kuka hana min saninsa da wuri sae akurarren lokaci...... "

Kwashe komai nayi na gaya mata tun wucewarsu,tarewata da kuma rigimarmu adaren farko,sae kuma sabuwar rigimarsu Momi da kuma xuwarmu gidan Baba Mu'azzam da kuma nasihunsa agaremu,sae kuma sulhun da aka nema.

Wani wawan ajiyar xuciya Ash ta sauke,cike da murna tace"Wayyyo! Fateenah' ina zan saka kaina don murna? Agaskiya naji dadi ba kadan ba da har kika haqura kika rungumi mijin kaddararki,fateenah wlh believe me Mahmood shine kalarki ba Mubeen ba,wlh ni dama can ina ta miki kwadayin aurensa sae gashi lokaci daya Allah ya amsa addu'ata,ya zamo mallakinki,yanzu dai addu'armu shine Allah yasa Mubarak ya fahimceku ya kuma gane cewar wani baya taba auran matar wani,haka zalika wata bata taba auran mijin wata........ "

Cike da sanyin murya na amsa mata da "ameen." Tace min tana shirin xuwa gidan Suhaima ne,nace yanzu Muna gama waya ita zan kira.Mukayi sallama.

"Nima ahalin yanxu babu abinda nakeso kamar matata wacce naki bayyana kaina agareta sae akurarren lokaci..... "

Da sauri na waiga tare da watsa masa wani Irin kallon soyayya,ware min hannayensa yayi.

Ahankali ya furta"Babyna I nid a warm hug...... "

Babu b'ata lokaci na isa gareshi tare da fad'awa jikinsa,sannu ahankali ya maida hannayensa ya rufe yana meh dada kankameni.kunnuwana dake saman k'irjinsa ya sanya nake iya jin yadda xuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.Ahankali na lumshe idanuwa ina meh jin wani irin sonsa na ratsa jinin jikina.

***

Ash cike da farin ciki ta Latso su Leedar da Fresh take labarta musu zancen Fadimar,suma din sosae sukai murna tare da musu fatar alheri da kuma addu'ar Allah yasa Mubeen ya fahimcesu.

*

Cike da rawar jiki ta mik'e tana fadin" Momi kunnuwana sun kasa gasgata zancen da kike min? Taya za'ai Zahranmu ta rikid'e ta zamo matar Yah Mahmo?abu sae kace ah wasan kwaikwayo?"

Advertisement

"Toh wannan maganar da nake miki wasar zahiri ce bata kwaikwayo ba,Fadima de ayanxu matar Mahmood ce wacce ya b'oye mana auranta da yayi.... " acewar Momi.

Cike da al'ajabi Hanan tace"Tabdijam! agaskia Momi Fadima da Yah Mahmo sunci amanarmu,Fadima ta manta cewar itace farin cikin mijina,shine don ta ruguza wannan farin cikin nasa shine ta tashi ta auri Yah Mahmo?dama can ni nasha fadawa Mubarak cewar nifa ina ganin kamar Fadimar bata qaunarsa kamar yadda shi yake hauka akanta,amma sam yaqi saurarona sabida makauniyar so daya rufe masa ido,yanxu ga irinta nan,ta tashi ta aure masa dan'uwa wanda na tabbatar ba k'aramin yaki za'ai ba kuwa idan ya dawo........ "

Ta rushe da kuka tare da ficewa da gudu tabar dakin,Momi kuwa sae Binta da kallon mamaki take,ahankali tace"Kai! kai! kai!!! Wayyo ni Bintu d'iyar hassan nide wallahi ban tab'a ganin shashasha marasa k'ishin mijinta kamar Hauwa'u ba,in banda abin sokuwan ai wannan al'amarin ah dadinta kenan tunda anyi nasarar raba mijinta da wacce yake fifitata akanta,amma jibi abinda wawiyar ke fada,yanxu duk suruntun da nake tayi ya tashi abanza kenan?tunda ta kasa fahimtar cewar ita Fadimar mah bata da masaniyar mijin da aka aura mata sae bayan an kawota....."

Taja tsaki tare da mik'ewa don gabatar da sallar la'asar.

**

Awannan daren mun gurji amarcinmu,Mahmood ya fanshi kudin sadakinsa ba kadan ba,ni kuwa nasha kuka har na baiwa uku lada,lallashi da sanya albarqa kuwa har Mahmood ya gaji da yinsu,sae cewa yake "Matata ubangiji Allah yayi miki albarqa,nagode kwarai da gaske da kika tsare min mutuncin kanki har kika kawoshi gidana.....*'ina sonki matuk'a fiye da tsammaninki,Allah ya k'ara mana qaunar junanmu,Sannan kuma Allah ya azurtamu da 'ya'ya nagari....."

Cike da farin ciki na amsa da "Ameen ngd my *'

Da safiyar ranar kuwa,sae ga Usee da kayan breakfast wai Momi ce tace akawo mana.Sosae abin ya bamu mamaki matuk'a tare da jinjina al'amarin,Mahmood ya k'arbi basket din yace"Usee kace mata muna godiya sosae sae mun shigo.... "

Da sauri Usee yace"A'ah tama ce suna nan tafe gobe duka dasu anty Meema.... "

Gabana naji ya yanke ya fadi jin abinda ya fada,amma sae na kada baki nace"Allah ya kaimu kanin miji,sae mun gansu..... "

Murmushi ya sakar min yace"Toh! matar Yayah,sae anjimanku.... "

Muka had'a baki wajen cewa"Toh mu jima da yawa.... " ya fice.

Wani uban tsalle naga Mahmood ya daka yana fadin"Yessss! My family have accepted my Zahra da hannu bibbiyu........ Sauran mana kaninmu.... "

Murmushi kawai nayi abina.Daga haka muka soma cin breakfast wanda ferfesun kan rago ce,sae kuma kayan tea.

Washeqari kuwa sun cika alqawari,sunzo din hadda 'yan gidan Baba Mu'azzam su Hafeezah da mominsu.Gida ya cika ya kacame da hayaniya,sae fira muke cikin raha da annashuwa.Dama tun safe nida Mahmood muka hada musu lafiyayyar girki kan suzo.

Nace"Anty Meema waini ina Anty Hanan ne? " (Dayake mijina ya fada min cewar yanxu ta koma gidansu Momi da zama tunda mijinta ya tafi,shine nayi tunanin kila tare zasu zo amma kuma sae naga akasin hakan,babu ita aciki).

Momi ce ta kada baki tace"Hanan tana gida kinsan ciki yayi nauyi yanxu,don haka mah bata cika fita,amma tace tana gaidaki.... "

(Gaskiyar lamari kuwa shine,babu yadda Momi batayi da Hanan ba akan tazo suje amma taki,tace babu inda zata,akan dole Momi ta rabu da ita,Jasmin mah ta hanata binsu,ita kuwa yarinyar sae kuka taketa yi amma babu damar zuwa tunda uwarta ta hana).

Advertisement

Nace"Allah sarki! Allah de ya raba lafiya... "

Ni nasan tabbas Momi tade k'are Hanan ne,amma ni xuciyata ta bani cewar haushina takeji sosae don na auri wan mijinta.Oho! Wallahi kome ze faru ya dade be faru ba donni dai yanxu harga Allah ina son mijina kuma bana danasanin aurensa,kuma babu wanda ya isa ya raba wannan auran sae Allah wanda shine ya hada abinsa.Su Momi da Khairat seda suka sake nemar gafarata akan cin mutuncin da suka min da kuma sharrin asirin da suka lik'a min.Nace"Laah! wallahi babu komai,ni wlhy ban rik'eku axuciya ba,Allah ya yafe mana duka... "

Awa daya kacal su Momi sukayi,Sannan suka wuce,su Hafeezah kuwa sae da marece direban gidansu yazo ya daukesu wanda dama can shi dinne ya kawosu.'yan kudade na basu wanda Mahmood ne ya bani akan cewar idan sun tashi tafiya saina basu.

Nace"Afreen gashi ba yawa kwa siyi kayan kwalliya,naso baku acikin nawa ne amma kayan lefena nacan Zaria..... "

"Laaaaah! kuji anty sae kace wasu baki?mufa kannenki ne basai kin bamu wani abin ba,sada xumunci mukazo yi ba maula ba.... "

Ah wasance nakai mata bugu ta goce,nace"kai Afreen yanxu yaya bazata iya baiwa kannenta kyauta ba? Shikenan idan ta basu ya zama maula ce suka yi? "

"Mude kome zaki fada bazamu k'arba ba,ki rik'e abarki bama so.... " tayi gaba su Rafi'ah suka take mata baya,har wajen Mota na bisu amma sam sunki k'arba,Afreen ce ta umarci direba daya tada motar,ya kuwa bi umarninta suka fice.Su Anty Meema mah haka suka min dana ce gashi sa baiwa 'ya'yana susha alawa,suka k'i k'arba.

Asanyaye na koma ciki,gab da sallar magrib ogan nawa ya dawo.Ware min hannaye yayi wai nazo na rungumeshi,babu b'ata lokaci na isa gareshi ina dan bubbuga kafata akasa nace"Anki ah rungumekan,daga cewa zakaje kayiwa abokanka ban gajiya shine kayi zamarka acan ko? Kode sunyi maka wata matarce ban sani ba? "

"Lalalalaaaah! Sunma isa?kuma nima na isa na so wata bayan my Zahmood?wallahi babu ta biyunki acikin xuciyata my Zahra,ke kadai kin isheni rayuwa...... "

"K'arya kake har yanxu kana son Zaynab,kuma itama din ai hakan ka fada mata,kace babu wata da zaka rab'a ko bayan ranta,sae gashi ayau ka k'arya alqawari...... " babu xato ba tsammani kawai naji hawaye ya soma ziraro min saman kunci,hawayen da ban san ko na menene ba? Kota kishin Zaynab dinne ko kuwa tausayin kaina na ganin na kamu da sonsa bayan nasan har yanxu yana qaunar Zeeynsa,kuma ko kusa nasan bazan taba samin irin matsayinta axuciyarsa ba,yafi sonta akaina nesa ba kusa ba.

Shima din idan yace ya manta Zeeynsa toh kuwa yayi k'arya,yasan yana mugun son Fadima,amma Zeeynsa ta dabance acikin xuciyarsa,yasan tabbas watarana Fadimar tana iya maye gurbin Zaynab din acikin xuciyarsa idan har ta iya bi dashi yadda ya kamata amatsayinta na wayayyiya.

Rungumota yayi ya soma lallashinta,cike da kissarsa da kuma salonsa ya mantar da ita batun Zeey.Atake anan suka shiga farantawa juna rai,suna meh jin sabuwar qaunar junansu na ratsa dukkan wani gab'ar jikinsu.Ya tambayeta yadda sukayi da bak'in nata,anan ta bashi labarin yadda sukai dasu Afreen,sosae yayi dariya hadda k'yak'yatawa.

Yace"Ai nasan halin Afreen sarai bata son ana mata irin wannan k'yautar,sae tayi ta ganin kamar malauce tazo yi,yanxu mah idan ba sa'a kikaci ba,toh kuwa tana iya jera miki kwanaki kafin ki sake ganinta agidan nan.... "

Waro idanuwa waje nayi nace"Akan nayi mata k'yautar kudin?"

"Naki wasane yarinyata,toh bari kiji akwai wani saurayinta Arham dake masifar sonta,toh wlh ko kwandala ya bata,toh shikenan daga ranar ta dena kulasa kenan har sae iyaye sun shiga cikin maganar,yanxu maganar da nake miki,babu wata k'yautar kudi da take k'arba daga gareshi,ita fa ta gwammace ayi mata k'yautar wani abin can daban amma bawai kudi ba,aurenta mah nan da wata uku masu xuwa insha Allah.... "

Ahankali nace"Allah ya nuna mana.... Agaskiya nide ta birgeni,sam abin duniya basu rufe mata idanuwa ba kamar wasu matan..... "

"Ai Aysha Afreen tayi ne,wallahi da'ace ni meh sha'awar auren dangi ne,toh kuwa wallahi da ita xan aura sabida halinta yayi ne... " ya fada tare da kashe min one eyes.

Wani irin kishinta ne naji ya tokare min qahon xuciya,lokaci daya na sakar masa kukan shagwab'a,nace"Nasan kila auran mah dakai za'ayi,b'oye min kawai kake kamar yadda ka b'oye min aurena dakai...... "

Rik'e cikinsa yayi yana dariya yace"Babyna ji yadda kika koma lokaci guda,don't tell me kema kina da kishi sosae juz lyk Zee...... "

B'ata fuskar da yaga nayi ne ya sakashi yin shiru,ya sosa k'eya tare da fadin"Am sorry my Zahmood bazan k'ara k'iran sunanta agabanki ba.... " sae kuma naji duk ya bani tausayi.Haka muka cigaba da wasanninmu na ma'aurata kafin daga bisani muka mik'e don gabatar da sallar magrib,bayan ya dawo daga masallaci kuma muka zauna cin abinci.

****

Kwanakin amarcin daya biyo baya kuwa ba'a magana don sosae nake samun kulawa da kuma daddadar soyayyar mijina agareni,nima ba laifi ina gwada masa tawa kulawar da soyayyar akoda yaushe.'Ya mace kenan,ko kuma nace xuciya ita de babu ruwanta,da zarar ta sami Wanda yake bata kulawa da kuma damuwa akanta,shike nan saita mace akan son wannan din,gashi ayau son da nake yiwa Mubarak ya zama tsuntsu ya koma kan Mahmood.Ayanxu Kam ina masifar son Mijina Wanda har nake jin bazan iya cigaba da rayuwa babu shi ba,tofa kullum muna mak'ale da juna baya fita,koda ace ya fitan ne,toh kuwa baya jimawa yake dawowa,dalilin daya sanya muka k'ara shaquwa dashi kenan.

Hakan yake gasu Suhaileedar,sun wani k'ara shaquwa da wani irin mugun son junansu daya qaru,sosae leedar ke tattalin Suhaima kamar wata sarauniya,haka mah iyayensa da kannensa ke masifar ji da ita.Rayuwa tayi mata fari kal,ga soyayyar miji ga kuma na family dinsa,agaskia Suhaima ko kadan bata da damuwa.

Ana gobe zamu koma Zaria,Mahmood ya kaini gidajen 'yan'uwansa,gidan goggo Ladidi muka soma zuwa,sae gidan Anty Meema,Anty Labeeba,anty Khairat,duk kuma sun rasa inda zasu sakani don murnar ganina,kuma bamu tashiwa sae mun dire musu abubuwan alheri.Akan hanya Mahmood ya tsaya daidai wani saloon.

Yace"Zahmood oya fito muje awanke miki kai,idan yaso Afreen ta miki kitso don ta iya sosae.... "

Banyi wata gaddama ba na fito don ni Kaina Ina buqatar awanke min kan don jinsa nake kamar yana wari mah sabida ruwan da yake sha kullum😁(Kun gane Ai).

Mun cimma mutane ba laifi acikin saloon din,Mahmood ya narka musu uban kudi don kawai asamu ayi min da sauri,su kuwa sae washe haqora suke don ganin sun yaqi naira da safiyar nan,nan da nan suka wanke min kan sannan aka shigar dani dryer,retouching kawai nayi.Ana gama min ban wani b'ata lokaci ba na fito na sameshi zaune awaje yana jirana.Murmushi ya sakar min tare da mik'ewa daga inda yake,ya tako ya sameni ah inda nake tsaye.

Yace"Zahmood har an gama? "

"Yo! ba dole agama ba tunda ka narka musu uban kudi kamar baka san zafin nemansu ba? retouching kawai da zanyi shine ka tashi ka zabga musu uban kudi..... "

"Can do more than that for you my Zahmood,wallahi kinfi karfin komai awurina,kudi kuwa yanxun mah na fara bararwa indai akanki ne... "

Sosae kalamansa sukai min dadi,ya kamo hannuna yana fadin"Zahmood tunanin meh kike haka?taho mu tafi.... "

Na soma k'ok'arin kwatar hannuna"Haba my dear meye haka? Sakar min hannu kaga fa mutane na kallonmu..... "

"Yo! toni ina ruwana da mutanen? Inace ko halali ta na rik'e? Idan kuma basu yadda ba toh suzo su duba foreheads dinmu zasu ga an rubuta *'

Sosae abin yaban dariya,har muka iso gidan Baba Mu'azzam fira muke tayi da kuma wasanni.Acan suma rasa inda zasu sakani sukai don murna,ji suke tamkar su hadiyeni don so,mahmood ya tafi yace anjima zai dawo ya daukeni.

Afreen ta yaryara min kananun kitso meh k'yau,tace"Anty Zahra jan lallinki mah harta soma gogewa bari na aiki Rafi'ah ta dauko mana meh lalli anan bayan layinmu.... "

Nace"Afreen wlh dama kin basshi kada ya dawo ya zauna zaman jirana don kinsan lalli bata saurin bushewa... "

"A'ah wallahi anty sae fa an miki don yayana ya gani ya kusan zaucewa,in banda abinki mah ai lalli itama adoce ga 'ya mace,nifa wlh mijin da xan aura idan har baya son lalli da k'amshi tofa bazan aureshi ba.... "

Da mamaki nace"Akan lallin?"

"Anty naki wasane wlh....... "

Ta kwalawa Rafi'ah k'ira tazo,ta aiketa gidan meh lallin,ba'a wani jima ba sae gashi sun dawo da meh lallin,zuwansu yayi daidai da gama kitsonmu.Aka zana min jan lalli meh k'yau,abinka da farar mace sae ya zauna das ajikina,abinci mah abaki Afreen tayi ta bani.Bayan an gama ta biya kudin lallin,inata cewa ta basshi zan biya amma taki.Kai agaskia nide ranar naga gata awurin wa'ennan bayin Allahn.Sae bayan sallar hudu Mahmood ya dawo daukata,yana ganina ya soma cewa"wowww! Afreen wlh nasan aikinki ne wannan,ngd sosae kin fitar min da amarya,yanxu ni wacce irin k'yautace zan maki daze nuna lallai naji dadin wannan gyaran.....?"

"Yanzu brother shikenan donna gyara anty Zahra shine sae an bani wata k'yauta?nasan da'ace Khairat ce ko Labeeba bazaka yi musu wannan maganar ba,don Allah ka bari bannaso,idan kana hakan sae nayi ta ganin kamar baka daukemu daya ba kamar yadda mu muka daukeku.... "

Ahankali yace"okay am sorry kanwas bazan kuma ba.... "

Sun cikani da sha tara ta arziki,sukace insha Allah suna nan xuwa Zaria ganin gida,Kaka rigima sae tsiya take ta min waina kuke sae gyaran jiki nake,adole wai ina son na fita matsayi agun megidan namu,dariya ni take taban ba.Maminsu Afreen ita tata k'yautar ta tsimi ce,tace kada na kuskura nayi wasa da amfani da ita don mace sae da gyara.Akunyace na k'arba ina mata godia.

Amota kuwa Mahmood kamar ze hadiyeni don sha'awar lallina,yana tuki amma rabin hankalinsa na kaina ne,ya jawoni yana meh cusa kansa ajikina yana shak'ar kamshin jikina,hadda lallin kafata dana hannayena ya hau shafawa,ah rud'e nace"Haba dearnah tuki fa kake,pls concentrate on it.... "

"Ai ke dince Zahra kike nemar zautani da wannan adon taki,agaskia yau sai kwalliya ta biya kudin sabulu.... " ya kashe min ido daya,ni kuwa na gane nufinsa don haka sae nayi rau-rau da idanu kamar xan saki kuka,ganin hakan ya sakashi sakin dariya yace"Wallahi ayau babu zancen daga kafa,na fayi haquri kwana kusan uku kenan na zuba miki idanuwa ina kallonki amma yau babu daga kafa...... "

Tuni na sakar masa kukan shagwab'a,ya shiga lallashina har muka karaso Family house.Bansan meyasa nake jin faduwar gaba ba idan har akan komai daya shafi su hajiyar Mahmood ne,lfy lau muka baro gidan Baba Mu'azzam,banji wani faduwar gaba ba sanda mukaje amma gidansu Momi saina tsinci kaina da jin tsananin faduwar gaba.Kila kuma don wannan zuwan shine karona na biyu shiyasa.

Mahmood ya lura da yadda yanayina ya sauya,yace"Zahmood pls cool down,Momi has totally changed wlh believe me babu abinda Zata miki kinji matar Mahmood? " kai kawai na daga masa.

Ah main falon gidan muka tarar da Hanan da Usee suna hira.Muna hada idanuwa da ita sae naji gabana ya tsananta bugawa,ji nayi kamar Mubarak dinne nayi ido hudu dashi.

"Oyoyo matar Yaya.... " Usee ya fada tare da mik'ewa,awasance Mahmood yace"Dakata malam ince dai ba shirin rungumar min mata kake ba? "

people are reading<SHIN SO DAYA NE? (Complete)>
    Close message
    Advertisement
    You may like
    You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
    5800Coins for Signup,580 Coins daily.
    Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
    2 Then Click【Add To Home Screen】
    1Click