《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》PART 2:CHAPTER THREE
Advertisement
*💘
BABI NA UKU🌼
*
"Mama bara naje nima na kimtsa kada su wuce wajen reception d'in nan bani..." acewar Anty Hajaar wacce tana gama fad'ar hakan ta mik'e tabar dakin xuwa sashin da aka saukesu.
Kaka rigima ta rakata da "Toh! adawo lafiya Hajara,Allah sarki an girma ba'a san an girma ba,yanxu fisabilillahi taron k'ananun yara mah sae sunje.... Koda yake Allah ne ya kawo mu xamani..."
Ai dole ne Anty Hajar tama je wannan reception din ko don taje tayi ciye-ciye ta kuma nunawa duniya cewar ita din fah uwar amarya ce.Maminsu Hafeezah mah zataje don ita da Mahmood suna mugun d'asawa da k'yau.
Ash ce xaune tare da Zuzu ah barandar sashin da aka saukesu.Hirar Khaleed Zuzu ke bata wanda ga dukkan alamu ya nuna cewar gayen ya gama tafiya da imaninta.Ita Ash din mah da akewa hirar amsawa kawai take da "uhmm" ko kuwa "a'ah",don kusan xan iya cewa gabaki daya hankalinta ya tafi ne ga su Fadima.Sae ayanxu ne take ganin wautarta na k'iran shi Mahmood d'in daya zo ya lallashi Fadimar bayan tasan muddin Fatin nata na had'a idanuwa dashi amatsayin mijin da aka aura mata,toh kuwa komai na iya k'wab'ewa,anything can happen!.
Oh! Allah!! akace dana sani yakan zo ne bayan ka aikata ba daidai bah,akan k'irashi da ,data sani kawai ta lallab'ata ta saka kayan don tasan Fatinta komin fad'arsu de tana jin maganarta,kuma tasan xata sauko ne har ta haqura taje reception din,amma da yake iyayi yayi mata yawa,kai tsaye ta k'ira Mahmood din da yaxo gareta,iyayinta ya janyo tana neman haifar da tashin hankali acikin jama'a wanda ta fison ace sae an kai Fadimar gidansa,asannan kowa ya kama gabansa kafin tasan wanene mijinta,tasan duk wani tashin hankali da ze biyo baya alokacin zai iya xuwa da sauki.Wurin reception mah ba lalle ne Fadimar ta gane Mahmood din ba tunda duk'ar da kai zatayi tayi,balle mah tasan halin Fadimar sarai da alkunya,zaiyi matuk'ar wuya ta masa kallon tsaf acikin jama'a.Koda ace tama gane shi,tasan Fadimar baxata tab'a kunyatar dashi idanuwan mutane ba har sae sun k'ebe.
Toh! yanxu gashi ta janyo k'ebewar tasu da wuri tun mutane basu gama watsewa ba,kuma tasan anything shitty can happen.
Axuciyarta tace"Ohh! ni Ayshatu wat have I done? meya kaini k'iransa? "
Xuciyarta babu abinda yake yi illa bugawa da sauri da sauri,kasa kunnuwa tayi tana meh jiran ta jiyo hayaniyarsu Fadimar sannan tayi ciki wuf!.Zuzu de data ga sam hankalin Ash din baya gareta,sae kawai taja bakinta tayi shiru,ita Allah-Allah mah take su Fadimar suyi su gama soyayyarsu kamar yadda take tunani sannan ta shiga taje ta tsalawa Khaleed dinta kwalliya.
Anty Hajaar ce tazo shiga sashin,da hanxari Ash ta mik'e tare da shan gabanta.
Wani irin kallon banza ta jefawa Ash din,kana tace"marasa kunya meye kuma haka? Ko de wata sabuwar salon rashin kunyarce ta motso miki shine hadda wani shan gabana?"
Dan murmusawa kawai Ash tayi,kana tace"Yana de gab da motsowa.... So nake kawai nace miki ki d'an dakata,ango na ganawa da amaryarsa aciki........ "
Hab'a Anty Hajaar ta rik'e,kana tace"ikon Allah!... nide tunda na budi ido nayi wayau ban tab'a ganin rashin kunya da da'a irin wannan ba,Muido da wannan angon nata sam basu da alk'unya ko kadan musamman mah angon nata,ai sae ya bari iyayenta su tafi kafin ya shiga wurinta suyi shashancin nasu son ransu........ "
Wani kallo ta watsawa Anty Hajaar,ta dubi inda Zuzu take taga mah sam hankalinta baya garesu,hasalima wayarta take daga can d'an nesa da inda suke tsaye.
Advertisement
Ahankali Ash tace"Dad'ina dake Anty akwai ki da iya jan k'aramar magana tayi tsayi da kuma janyowa kanki raini awajen kananan yara,ina ruwanki da koma meye ya shiga yi? Ina ce ko matarsa ce ba dadironsa ba? Don Allah Anty Hajaar ki dunga kama girmanki kada ya gama xubewa ah idanuwanmu mu yara..... "
Tana gama fad'ar hakan ta koma mazauninta,sae duba agogo take awayarta,yanxu haka takwas ta wuce da mintuna goma,akalla Mahmood ya shafe kusan mintuna ashirin aciki yanxu.Ita kuwa Anty Hajaar jikinta ne yayi sanyi qalau don bata tab'a jin k'unyar kwab'o ba arayuwarta sae yau da Ash ta mata.Sae taga rashin dacewar maganar daya fito daga bakinta.Jan jikinta tayi xuwa ga wani k'aramar kujera ta tsakar gida ta xauna.(lol maganin irinku kenan Anty Hajaar... Ash kin biyani....)
***
Idanuwana dani k'aran kaina mun kasa gasgata cewar wai *'dan'uwan Mubarak ne tsaye agabana amatsayin *'
Sake kai yatsu nayi ina murza idanuwana akaro na uku don tabbatarwa kaina cewar mafarki nake kuma wanda ke tsaye agabana ba my brother inlaw bane.Harda mitsilin kaina nayi wai ko mafarki nake na farka,amma uban Zafin dana ji ne ya saka nasan ba mafarkin nake ba,this is reality!!!.
Da rawar murya nace"Don Allah meh kake yi anan?"
Gaban Engr.ne ya buga wata irin ganga,fargaba da kuma tsoron actions din da Fadima xatayi taking duk ya cika masa xuciya fal! amma da yake shi din namijin duniya ne,sae be bari ta gano weakness dinsa ba.
Fuskar mamaki ya shimfid'a mata,kana yace"Ban gane meh nakeyi anan ba? all what I know is dat wajen matata nazo...... "
"Wacece kuma matar taka? " na fadi hakan sanda naji xuciyata na wani min mugun zogi.
"Of cours! Fadima Sa'ad Mainasaraamaryar Engr.Mahmood Mustapha...... "
Da hanzari na katseshi"k'arya kake mak'aryacin banza,mak'aryacin wofi,you can never be my husband ko amafarki,ni bah kai na aura ba,ni * na aura not because am very pretty sure dat brother inlaw bazaka taba cin amanar d'an'uwanka ba,bazaka tab'a yaudararsa ba,haka kuma nasan bazaka tab'a bin bayansa ka k'wace masa ni ba...... "
Wani irin mugun d'aci ne Mahmood keji aransa na jin irin wannan kalaman da Fadima take jefarsa dashi,yab'onsa take ko kuwa maganace mara dad'i take jefa masa?
sassauta muryata nayi,da rawar murya meh had'e da kuka na cigaba da magana"pls brother inlaw meya kawoka gidan surukaina?ko kuwa kaima kana cikin abokan ango ne? kuma ina mijina yake da har ya barka ka shigo har inda matarsa take?okay yanxu na gane,ka samu labarin cewar nayi aure shine kazo kaci min mutunci don na yaudari d'an'uwanka ban aureshi ba..... "
Had'a hannuwa wuri guda nayi kana nace"pls na rokeku don Allah kuyi haquri ba laifina bane nima din biyayya kurum nayi,don Allah kacewa d'an'uwan naka daya gafarceni ba laifina bane,albarqan iyayena nake nema shiyasa na amince da xab'insu.... Pls brother inlaw ka tafi kada mijina ko wani ya shigo ya ganka anan....... "
Wasu 'yan kwalla ne yaji sun ziraro masa saman kunci na tausayin kansu daga shi har Fadimar,da hanzari ya juya ya fice daga dakin kamar yadda ta buqata.k'aron farko daya soma ganin rashin dacewar auren Fadima da yayi gashi yanxu tana denying dinsa akan bashi ne wanda aka aura mata ba don baze iya cin amanar dan'uwansa ba.
Maganar 'cin amanar' data ambato shi yafi tsaya masa arai.Anya kuwa ya k'yautawa Mubarak kuwa? Taya kuma xasuyi zaman aure da Fadima bayan Mubarak dan'uwansa ne,his blood brother,ai kuwa kusan koda yaushe Ze dunga haduwa da Fadimar musamman ah family house. And anything bad can happen!.
Advertisement
Shi fa bema taba tunanin hakan ba,burinsa kawai ya mallaki Fadima shikenan an gama komai.Gashi yanxu ya mallaketa din ba tare da sanin mahaifiyarsa ba,yan'uwansa da kuma shi uban gayyar wato Mubarak.wani irin yakine za'ayi idan Mubarak din ya dawo? amsar da be sani ba kenan.Amma shi de abinda ya sani shine,*'Dama can Allah ya riga ya rubuta cewar Fadima matarsa ce shiyasa lamarin aurensu yazo da hakan.Shi de addu'arsa Allah yasa Fadima ta fahimci dalilinsa na aurenta sannan kuma ta soshi su xauna lafiya.
Koda ya fita daga dakin,wurin Haj.Faiza ya nufa wato maminsu Hafeezah don gaya mata cewar anyi cancelling xuwa reception din,don baze so ya matsawa Fadimar mah azo ayi tashin hankali yadda mah yaga yau idanuwan nan nata atsattsaye suke na shirin sauke kwandon bala'i.baze so ace komai ya k'wab'e musu agaban jama'a ba don su karan kansu Baba Mu'azzam da iyalensa basu san Fadimar bata san cewar Engr. ne mijinta ba,all their taught ta sani kuma tana sonsa shiyasa ya shige masa gaba wajen neman aurenta.
"Haba Mahmood wannan wani iri xance ne kake yi wai an fasa xuwa reception? Kasan fa abokanka baza suji dadi ba don ba k'aramin kudi suka barnatar ba....... "
Mami ce ke wannan maganar alokacin da 'yarta Afreen yayar Hafeezah ke sak'ala mata abin wuya da 'yan kunne.
Mahmood dake tsaye da hularsa ahannu yace"Mum Fadimarce bata jindadi,she's sick........ "
Akid'ime ta mik'e tana fadin"What?? Bata da lafiya? Meke damunta??
"Zazzab'i ce,pls kada ki d'aga hankalinki Mami dama tun acan gidansu ne ta soma rashin lafiyar amma yanzu da sauki,zafin jiki ne da dan ciwon kai kawai...... "
Saukar da ajiyar xuciya Mami tayi,kana tace"Mahmood ina ganin kawai ka kaita asibiti Doc.ya dubata...... "
Cike da faduwar gaba yace"A'ah Mami ba sae an kaita asibiti ba,nace miki da sauki kije mah ki dubata da kanki ki gani...... "
Kafin ya sake magana tayi wuf! ta fice,Afreen da Hafeezah dake tsantsara makeup suka take mata baya.
Shi kuwa Mahmood ajiyar xuciya ya sauke,ahankali ya furta"Ya salam! Wannan wani irin aure ne nayi? Wani irin tashin hankali da bala'i ne nake nemar jajibowa rayuwata?"
Ficewa yayi daga dakin,ya nufi waje,Su Ash na ganinsa suka mik'e,so take ta masa magana amma sae kuma taga ya daga mata hannu yayi gaba da sauri-sauri.Da hanzari Ash sukayi ciki gabanta na meh cigaba da dukan tara-tara.tabbas tasan wani abin ne ya faru don yadda taga Mahmood ya fita babu walwala akan fuskarsa.Toh koma meye ya faru Fatin ta birgeta,don basu ji wata hayaniyarsu ba,komai silently sukayi shi.
**
Ina ganin ficewarsa naja jikina dakyar na xauna agefen gado da k'arfi tare da rik'e kaina dake barazanar fashewa don azabar ciwon kai.Hawayena sun kafe sunki zuba,abubuwan daya faru yanxu tsakanina da Engr. sun girmi k'wak'walwata don so nake nayi tunani da kuma nazarin kalamansa amma brain dina ya gaza yin hakan,k'wak'walwar tawa ta kasa bani damar tunanin komai.
Ina cikin wannan halin ne naji muryar Mamin Hafeezah tun kan ta k'araso dakin tana fadin"Fadima d'iyata kina ina? "
Axuciyata nace"Ban gane ina ina ba? ya wuce dakin da kuka saukeni....? "
Ganinta nayi ta shigo arud'e tare dasu Hafeezah biye da ita,sae ayanzu hankalina ya tashi kar de ace sunga fitar Engr. daga cikin d'akina??
"Fadima yah kike jin jikin naki yanxu da sauki de koh? Idan babu tun wuri muje asibiti... "
Sae ayanzu hankalina ya dan kwanta ganin ba abinda nake tunani akai bane,kafin nayi magana naji sallamarsu Ash,biye dasu Anty Hajaar ce dasu Mama Jamila wanda ga dukkan alamu dawowarsu kenan.
"A'ah kaina ne kawai ke ciwo Mami.... " na bata amsa cikin sanyin murya.
Tace"Toh bari na kawo miki maganin ciwon kan.... "
Da sauri nace"A'ah Mami karki damu akwai ah purse dina.... "
Da hanzari na dauko purse din na ballo paracetamol,na dibi dan ruwa ah jug na hadiye maganin.Sae sannu ake ta min.Su mama Jamila mah sae duk suka ji ba dadi da kuma tausayina,duk aganinsu zazzabin bankwana dasu nake don lafiyata qalau sae yanxu dana soma jin jikina ba dadi.
So nake nayiwa Ash wasu yan tambayoyi amma presence din su mama jamila da dangin mijina ya hanani k'eb'ewa da ita.Agaskia naga gata sosae awurin dangin mijin,nan da nan suke tayi dani kamar wata kwai da ba'a son ta fashe.
Ina ke miki ciwo? Meh kike son kici?duk tambayoyin kenan wanda rana ta farko kenan dana ji na soma qaunar wannan auren.
Amma shi mijin nawa ina yake ne da har yanxu banga ko inuwarsa ba?
**
Shi kuwa Mahmood yana fita,sae da aka kai ruwa rana kafin abokansa su haqura da xancen reception din.
Ce musu yayi"Idan ta kudin da kuka barnatar ne shine kuke jinsa ajiki,toh kuyi haquri xan biyaku amma ni lafiyar matata ya fiye min komai...... "
Sae kuma suka ji duk jikinsu yayi sanyi da maganarsa.Haka de kowa ya kama gabansa duk rai babu dadi.k'iran wasu abokansu sukayi wa'enda suke venue din already suka sanar dasu cewar an fasa,Suma din sunyi d'an korafi amma da sukaji dalili se kuma suka dan sassauta. Shima Mahmood din wucewa gidansa yayi dake 'court road' don baze iya sake komawa cikin gidan ba.Gobe mah sae dare ze taho d'aukarta,don zasuyi kusan sati uku akano kafin su koma Zaria.
Washegari wajen qarfe goma akayi walima acikin filin gidan,ba wasu jama'an Kirki ne suka zo ba kamar namu ba,kuma ba laifi malamar tayi nasiha meh ratsa xuciya wanda nayi kuka sosae.
Itama Suhaima anata b'angaren,qarfe goma akayi walima ah k'ayatacciyar filin gidan,ana gamawa direct akayi da ita b'angaren da xata zauna,sannan jama'a suka watse,tayi kuka sosae sanda kawayenta da wasu mamamninta suka zo wucewa wa'enda suka kwana.Dakyar ta bari suka wuce tana kuka wasu mah suna kuka.Yanzu ya rage ita kadai acikin dakinta,sae angonta da xata jira.
Su Mama Jamila ne suke ce min zasu wuce,ai kuwa kuka na sakar musu ina cewa nima binsu xanyi.
Mama Sadiya ce tace"Yau ga sakarya,Yo! ai wannan itace ake kira da auren ai,gashi mun kawoki gidan mijinki inda kike ta mararin xuwa..... kinga ni cika min gyale..... "
Haka su Mama Sadiya mah suka min,suka tureni suka fice har su Ash. Sae kuka nake wiwi kamar wata k'armar yarinya,su Mami kuwa sae aikin rarrashina suke.
Sae bayan isha'i akace min nazo mu tafi ga angona ya taho daukata,mamaki nake tayi wai ace da daddaran nan ne xamu kama hanyar Zaria? Kamar na tambayi su mami ko Zariar ce zamu tafi da daddaran nan amma sae naji na kasa.
Falon Baba kamar yadda naji ake k'iran mahaifinsu Hafeezah aka kaini,anan naga angon nawa Xaune akasa yana sauraron jawabin Baba.
Kun san wanene mijin nawa?? Its still Engr. Mahmood Mustapha dai nake gani zaune agabana,sae ayanzu na tabbatar da cewar Yes! shi din ne de mijina.
Tuni naji wani irin tashin hankali ya min sallama,taya akai ya sami aurena? meh yayi wa mahaifina har ya bashi aurena? Dama ze iya cin amanar Mubarak ban sani ba? Inasu mummy da sauran kannansa don ga dukkan alamu ya nuna cewar basu da masaniyar auren,kamar b'oye musu yayi,sannan kuma su waye Baba Mu'azzam da kuma Mamin Hafeezah agareshi? Anya ba hayar iyaye yayi ba don su tsaya masa akan wannan aure ba kuwa?
Wani murmushin takaici nayi ina meh raya wasu al'amura araina,ni kadai kurum nasan tashin hankalin da zan haifar muddin muka sanya kafa muka bar nan gidan.Ni kadai nasan tanadin dana yiwa Engr. Mahmood bayan ya gama labarta min dalilinsa na auren
A/N
Tofa my people mun fa iso gun.... Wani kudiri ne kuma ke ah cikin ran Fadima? Meh take shirin yiwa Engr. Mahmood? Ku dai biyoni.
Advertisement
- In Serial37 Chapters
An Unknown Swordcraft
A strange accident hurls a man thousands of years into the future to find that disasters have transformed the world into a fantastical setting of monsters and magical swordsmen. Our protagonist does not become a hero. Instead he is recruited into a heretical cult led by a foul necromancer. To survive this new world, he must adapt to life as one of the dark lord’s evil lieutenants, carrying out impossible orders, scheming against his rival cultists, avoiding the real heroes out to kill him, and developing his own personal brand of magical swordcraft. [participant in the Royal Road Writathon challenge] (Placeholder title until I come up with something better.) Features: – Minion to Dark Lord progression. – MC lurking undercover as an evil lieutenant. – First true spellcaster in a world of magic swordsmen. – Wuxia power levels. – Minor base building / project management. – A little bit of crafting. – Meandering progression/plot. – Dumb comedy.
8 75 - In Serial37 Chapters
Broken Sky and Shattered Earth: Apocalypse Convergence
Participant in the Royal Road Writathon Challenge! (Updates sporadically) Wilfred had been thinking about ending it all, but then it all ended before he could.The apocalypse came in a matter of hours. Not from weather, not from nuclear strikes, but something far worse. Mankind lost its dominance over their own planet in a short afternoon, and now Wilfred is one of but a handful of survivors who must make sense of the catastrophic nightmare world that they once called their own.While the Earth is many things after the end, it is anything but the sole domain of humanity. As Wilfred and other survivors discover, their planet was not subject to just one world-ending event, but several. The undead roam the once proud metropolisis, and inhuman beasts stalk the countryside. The physical fabric of reality itself is twisted beyond repair in some places as unnatural distorions that warp physical laws appear across the landscape, and even a simple jog across an empty street can prove fatal to the unwary.The ones who died in the initial catastrophes never had to face the horrors that followed. And for Wilfred, a man who found no purpose in life before the apocalypse, what is there to be found after?
8 78 - In Serial11 Chapters
Life in a Red World
Born with a unique eye color, student Retter Hanson has had to deal with isolation and bullying for the majority of his life, leaving him as an antisocial, depressed person. However, a chance meeting at lunch one day may finally give Retter the chance to turn his life around, and reconnect with the people who care about him. "Life in a Red World" is a story of how, even if life seems bleak, a change in perspective and understanding can lead to a more fulfilling existence.
8 80 - In Serial34 Chapters
Just a random Zodiac Book in the Internet
I really love the zodiac signs so I decided to write a book about them. Ps. This about what the zodiacs would do in certain situations. NOT THE PEOPLE WHO GOT CANCER OR VIRGO BUT IF THE SIGNS WERE HUMANS. So don't feel offended.
8 618 - In Serial26 Chapters
The Magical Girl Substituting me is...my Uncle?!
Amidst all of the issues that any teenager girl usually has, Aika Tsunaboshi also secretly an Magical Girl. Much likes the ones you would typically see in anime and manga. Except these ones also hunts demons on the side. One day, while fighting against her nemesis, she is forced to make a decision and temporarily transfer her powers to someone in her family. Which according to her partner (AKA Sacred Beast) Nyamo, the Nekomata, was intended to go to her older brother, Akira Tsunaboshi. Who is always mistaken for a girl and barely able to form a full sentence towards strangers, which leaves him prone to many misunderstandings. Akira is already in his third year and everyone in the school still recognizes him as one of the most popular "girls" on the school. Making him quite unapproachable for most students, who thinks Akira lives in a higher place than the rest, rendering him to be quite a loner. However, during the transferring process, Aika got cold feet at the last second and her partner, alongside her magical powers were sent somewhere else. About to be stricken down by her assailant, Aika is saved by a strange fat man. Her savior... just happened to be one of her teachers, Shinjirou Tsunaboshi... and her uncle, who just happened to be passed out drunk in the gym storage nearby. Which she so utterly despises due to his being drunk more often than not, near perpetual state of hangover, his carefree nature, unrensponsible and perverted tendencies that earned him the title "Ero-Sensei" which caused many antics and headaches for Aika to deal with most of her life. The shock of seeing her uncle wearing her uniform, a frilly dress, alongside a set of cat ears, tail and everything made her pass out on the spot. By the time Aika woke up, not only he was casually partying with both her partner Nekomata and the demon, became best friends with them, as well but also convinced the two to form a strange alliance between himself, her demonic nemesis and through Nyamo, sent his unprecedented proposal to Arcadia, the group behind managing and recruiting all Magical Girls. Would Arcadia even consider Shinji's suggestion and his abnormal circumstance? Will Aika be able to handle yet another stress placed on top of her social life? Will Aika's powers ever return to her? Even if it does, will she be able to manage to put up with her troublesome uncle for the sake of justice until then? Only one way to find out!
8 126 - In Serial9 Chapters
Backwards rollercoaster || Mairimashita! iruma-kun
[ "Don't walk in front of me... I may not follow. Don't walk behind me-I may not lead. Walk beside me... just be my friend." ] -Albert CampusBecoming the demon King was quite the task for Iruma, but to rewind all of the hard times again with the same people? Had God finally come down with his hands-punishing Iruma for his sins?*This story will be purely imaginative after the latest manga chapters. All words aren't canon unless the creator released more manga chapters the same as this (storyline.)This is a fanfiction for Mairimashita! Iruma-kun.
8 152

