《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》PART 2:CHAPTER ONE
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
*MALLAKAR:HAFSAT AL-MUSTAPHA*
*WATPADD:HAFNANCY*
*Gaisuwar ban girma gareku my wadpaddians & Hafnan's novella group,thanks for showing me true love,I also love you all so very much... 💗💗💗💕*
*
BABI NA DAYA🌼
Page 1-3
Ban kai ga isa kofar fita ba,sae kawai naji kaina ya harba,atake naji kamar ana buga min ganga akan,dakatawa nayi tare da rik'e kan da hannaye bibbiyu.
"Muido lafiyarki kuwa? " haka naji Anty Hajaar ta fada.Ni kuwa ko tankata banyi ba sabida wani irin jiri da naji yana nemar kwasheni ya kifar akasa.
Gani nayi tsayuwar na nemar gagarata don haka sena koma da baya na zauna da k'arfi agefen gado.
"Amaryar Nakowa lafiya kike kuwa?" Hakan naji k'awayena sun fad'a tare da tasowa suka zagayeni,wasu ta saman gado ayayin da wasu kuma ke tsaye agabana suna meh jiran nayi musu bayanin abinda ke damuna.
Ash ce ta shigo dakin tana fadin"Oya Fateenah,'yan mata duk ku taso aje ayi ho....... "
Ganin da tayi an zagayeni,sae sannu ake min ya saka ta cillar da mayafinta tare da rugowa da gudu,ture wasu friends dinmu tayi wanda hakan ya bata damar samun kusanci dani.
"Fateenah wats wrong? Lafiya naga kin dafe kai da hannuwa bibbiyu?"
Ash kuwa tsoro ne ya cika xuciyarta fal. Azuciyarta tace"Oh! Yah Allah kar dai ace Fadima ta samu labarin wanda aka daura mata aure dashi shiyasa ta shiga cikin wannan halin?"
Ita Ash tana waje sanda su angwaye suka shigo,sae taci karo da Mahmood wanda kuma aka nuna mata cewar ai shine angon Fadimar.Atake anan taji cikinta ya duri ruwa,ji tayi tana matuqar buqatar toilet awannan lokacin don yadda taji kamar tana shirin sakin gudawa ajikinta.Ai kuwa da azama tayi toilet din.
Koda ta fito,sake komawa tayi,alokacin suka ci k'aro da Suhaima wacce itama kiranta akai da ta fito suyi hotuna da angwaye,itama tana ganinsa wai amatsayin angon yar'uwartata,murza idanuwanta tayi da kyau don ta kara tabbatarwa da lallai ko shi dinne.
Ai kuwa shi dinne dai ba wai kamanni ba,da azama ta koma ciki don labartawa yayartata shine suka ci karo da Ash din.
Ash tace"Ke kuwa kanwa meya faru ne naga kina rafka wannan uban saurin har bakya kallon gabanki kike tafiya?"
Arud'e tace"Hmmm! Anty Ash kin san wa kuwa nagani amatsayin angon Yaya Fadima? Wallahi wannan wan saurayinta Mubarak dinnan na Kano ne.... Kin tunashi ai? Wannan Engr.Mahmood ne yake da suna ko....?"
Ash tace"Wallahi nima na ganshi,ganinsa ya saka nayi toilet don wata gudawa naji ta taho min alokaci guda don fargaba..... "
"Amma taya hakan ta faru? Dama yana sonta ne? Kuma taya akai har ya samu ya shawo kan mahaifiyarsa ya aureta bayan tun ganin farko da tayi mana bata qaunarmu musamman ita yaya Fadimar?mafi daurewar kan wannan al'amari ina shi Mubarak din yake ne da duk hakan ta faru??"
Suhaima ce take fadin wannna maganar ahankali cike da kuma tashin hankali.Ita kuwa Ash cewa tayi"Wannan tambayoyin duk abakin shi uban gayyar zamu samu amsoshinmu..... Kuma.... "
"Wae Suhaima kuskus din meh kukeyi ne tsaye anan baza kizo ayi hotunar ba kun shanye mutane can tsaye arana suna jira? "
Anty Hajaar ce ta katse musu hirarsu alokacin da take kokarin xuwa ta kira Fadimar itama ta fito ayi da ita.
Da sauri Ash ta janyo hannun Suhaima suka rab'a ta gefen Anty Hajaar suka fice waje.Suna fita suka hada idanuwa da Engr.Mahmood,sakar musu pretty smile yayi.
Advertisement
Su kuwa kallon junansu sukayi,Ash ta rad'awa Suhaima magana akunne.Murmushi tayi sannan tayi wajensu don daukar hotuna.ce mata tayi kada ta kuskura ta nuna masa surprise face ko kuma tayi gangancin tambayarsa taya akai ya samu auran Fadima?
Ita kuwa Ash komawa tayi dakin Fadima,Allah-Allah kawai take tayi Fadimar tayi creating wani scene wa Anty Hajaar kamar yadda tayi kwanakin baya,don idan tayi hakan ai babu yadda za'ayi ta fito tayi hotunan.Tasan tabbas Fadima nayin ido hudu da Mahmood amatsayin mijinta,xata iya zauncewa kuma ita bazata so ace Fatin ta nunawa duniya cewar bata san mijin da aka aura mata ba.Shiyasa take ta addu'ar Allah yasa kafin ta isa dakin ta tarar kawai Fadimar ta riga tayi creating wani scene.Ai kuwa dadi ne ya kusan kasheta ganin yanayin da Fadimar ta shiga duk da cewar ba hakan taso ba.Ta fison koda Fadimar xatayi wani tashin hankalin toh ta bari sae bayan an kaita gidan Mahmood din amma ba wai tayi anan idan ta ganshi ba.
(Back to the scene).
Dakyar na budi baki nace"Ash wani azababben ciwon kai ne naji ya saukar min yanzun nan..... "
"Subhanallah.... " ta fada tare da kai hannu tana taba wuyana.
Zaro idanuwa muka ga tayi tana fadin"Fateenah wallahi jikinki har ya dau zafi,zazzabi ke shirin rufeki..... "
Anty Hajaar ce tayi saurin taran numfashinta wacce take tsaye tun dazu take kallon ikon Allah,cewa tayi"Iskancin banza da wofi.... don kawai nazo kiranki ayi hotuna dake shine xaki kirkiro wata k'aryar banza can....? "
Ash ta kada baki tace"Haba Anty wannan wacce irin magana ce kike yi haka? Kema zo ki taba jikin nata kafin ki karyata zancen.... "
"Yi min shiru anan! mara kunyar banza da wofi ai daga ke har ita jirgi daya ce ta kwasoku ta rashin kirki da mutumci..... "
Karkata akalar zancen nata tayi xuwa gareni"Ke kuwa Fadima ni abin naki ya dena bani mamaki sae tsoro donni de ban taba ganin amarya irinki ba,ranar da aka kawo gaisuwarki some mana kikai,yau kuma daga cewa ki fito ayi hotuna kin kirkiro xancen rashin lafiya,ko dae auran ne kawai bakyaso ayi miki ita gaba daya? "
"Anty Hajaar don Allah ni ki tafi kawai kada ki k'ara mata wani ciwon akan nada..... " acewar Ash wacce ta soma fusata da xancen Anty Hajaar.
"Eh! tatacciyar mara kunya ai dama wucewa xanyi yanzun nan kuwa,kuma ke Fadima bari mah kiji na gaya miki,gwara mah ki bar wannan k'aryar rashin lafiyar don ko kina shure-shuren mutuwa ne anjima zamu kaiki dakin mijinki,kuma ai ke kikace kina sonsa don haka ya zamar miki dole ki zauna dashi don an riga an dauraku kuma anjima kadan xamuyi miki rakiya xuwa gidansa..... " (lol kai Anty Hajaar din nan 'yar gari ce).
Fuuu! ta juya ta fice kamar kububuwa.Sae ayanzu hawayen da suka makale acikin ramin idanuwana suka samu damar gangarowa.Sam Anty Hajaar bata dauko halin Umma ba,Umma sam bata da wani hayaniya kamar Anty Hajaar,komanta da sanyi take yinsa,maganarta mah cike da salo da karairaye murya,sab'anin Anty Hajaar maganarta da fada take yinsa,shiyasa sam bata cika shiri da mutane.
Kawayena sae sannu suke ta min.Haka aka gama hotuna banje anyi dani ba.wasa-wasa sae da zazzabin nan ya kwantar dani,har allurai biyu sae da madam Iyabo ta min (da yake ita din nurse ce). Jama'a kuwa sae cewa suke wai amarya na zazzabin bankwana da iyayenta ne.
Ash ta gargadi Suhaima da kada ta kuskura ta gayawa Fadima cewar Engr.Mahmood ai shine mijinta,ta bari idan aka kaita ta sani kuma tasan dole zata haqura ta xauna.
Advertisement
Ni kuwa sae ji nake ana 'amaryar Mahmood Nakowa' azuciyata nace"Nakowa shine sunan mijin nawa? "
(Dayake su Mahmood basa amfani da sunan Nakowa shiyasa bata sansu da sunan ba.... Kai Engr. akwai brain,shi ya bada wannan sunan awajen daurin aure don kada Fadima tayi saurin d'agowa don ta siyasa ya tambayi Mubarak ya gaya masa cewar be taba fada mata family name dinsu ba...)
Shi kuwa Mahmood picture daya ya dauka sannan suka fice da tawagarsa don be ga amfanin tsayawa daukar hotuna ba bayan babu sahibar tasa aciki.Shi kansa was juz like Ash,yayi murna ba kadan ba da addu'arsa ta karbu,Fadima bata fito ba balle ayi tashin hankali,dama can Anty Hajaar ce da iyayinta tace ya tsaya ta kira Fadimar suyi hotuna.
***
Wuraren karfe hudu da rabi aka bugo musu waya cewar ga 'yan daukar amarya nan tafe na ita Fadimar.
"Fadima lallab'a ki shirya tunda jikin naki da dan sauki,ki hanzarta don an bugo wai 'yan daukar amarya na kan hanya....... "
Da sauri na tari numfashin mama Jamila wacce k'anwace ga Abbanmu"Mama ina za'a kaini? "
Mama tace"Can kano za'a kaiki don nan danginsa suke,idan yaso daga baya shi mijin naki da kansa zai maido dake nan Zaria gidan da zaki zauna...... "
Wani kuka ne ya kufce min jin cewar kano mah za'a kaini garinsu Mubeen dina,nace"Gaskia ni dai mama babu kanon da zaku kaini,ni dai kawai awuce dani gidana kawai..... "
Bud'e baki tayi tace"Ikon Allah! yau ni Jamila gani ga mara kunyar amarya,Muido ina kika tab'a jin anyi haka?kul! kada mah ki bari wani yaji don dariya zasu miki suce kuma baki da kunya,an san kina mararin zuwa dakin mijinki amma ki bari asoma mik'aki ga danginsa kafin ki koma dakinki kamar yadda akeyi ah al'adance.... "
Wani haushi ne ya rufeni ganin ita sam Mama bata fahimci abinda nake nufi ba,ita azatonta kawai zumud'in tafiya gidan miji nake.
"Ki tabbata kafin na dawo kin shirya kanki,maza kawayenta ku tashi ku taimaka mata ta shirya kanta.... "
Had'iye wani muyau meh daci nayi,kana nace"Mama banda lafiya fa,haka kuke son ku kaini?"
Afusace tace"Kya warke acan,idan kuma mutuwar ta tashi xuwa kya cika adakin mijinki kinga kuwa asirinki arufe tunda kina da aure akanki,sannan ga wata daraja,rahama da kuma haske da gawarki zata samu,kuma mutane zasu fi ganinki da mutumci da kima ah idanuwansu,uwa-uba mijinki meh masifar sonki nasan ze daga miki tafin kafarsa ki samu aljannarki...... "
"Mama pls ki bari banso,ya isa haka jeki xan shirya.... " na fada tare da rushewa da wata sabuwar kuka.Mama cikin jindadi ta wuce abinta don ganin maganganun nata sunyi tasiri ak'wanyar Fadimar.Kawayena kuwa sae dariya suke ta min.Ash ta taimaka ta shiryani cikin wani tsadaddan light brown swiss lace wanda akayi masa kwalliya da flowers navy blue.
Fati mamza wacce dawowarta kenan daga gun wani biki anan Zariar,itace ta cigaba da shiryani,ta min daurin dankwali meh shegen kyau,sannan ta yafa min tsadadden mayafina navy blue meh kwalliya ajikinsa na kyalkyali da flowers.Mayafin daga saman kai ta yafa min ita.takalmana flat ce brown colour kalar kayan.
Ta feffesheni da turare,aka fito dani xuwa bangaren Abba inda anan ne za'a mana fada da nasiha.Gida ya rud'e da rangad'e rangad'en guda.Koda na shiga falon na tarar har Suhaima ta rigani isa,zaune take akasa kusa da kafafuwan Umma,ta kifa kai asaman cinyar Ummar tana rera kuka ahankali ayayin da Umma ke dan bubbuga bayanta alamun rarrashi.Can gefensu Abba ne zaune sae karkada kafafuwa yake yana meh fesar da iskan bakinsa.
Ganin shigowar Fadima da Kuma kukan da itama take rerawa ya saka Umma saurin mik'ewa don bazata juri tsayawa yin bankwana da 'ya'yan nata ba.
Hanyar fita ta nufa alokacin da taga Fadimar ta sami gu ta zauna akasa akusa da Abba.
"Haba! Kareemah dawo ki sallami 'ya'yanki mana,ki dawo kiyi musu fatar alheri acikin sabuwar rayuwar da zasu shiga..... "
Sabon kuka dukanmu muka rushe dashi har Umman,dakyar ta dawo ta nemi gu ta zauna.Abba ya shiga lallashinmu da Kuma ban baki,dakyar muka haqura mukayi shiru don sauraren nasiharsa agaremu.
Abba yayi gyaran murya sannan ya soma jawabinsa"Alhamdulillah! Alhamdulillah! godiya ta tabbata ga mahallicin sammai da kassai,mahaliccin dabbobi,aljan,mutum da duka komai meh rai ko mara rai.Na godewa Allah da ayau ya bani damar sauke nauyin daya rataya bisa wuyana amatsayina na mahaifinku na ganin na aurar daku ga nagartattun mazaje na gari,Fadima hakika nasan ko kadan ban kyauta miki ba dana hana miki auren zab'inki,amma ina son ki san cewar ko kadan banyi kuskure ba,don idan baki manta ba,ah addinance wajibi ne iyaye su zabarwa 'ya'yayensu abokanan rayuwa na gari,don haka karki ka laifina don na aurar dake ga wanda ba zabinki ba,Wallahi Fadima ina meh tabbatar miki da cewar watarana keda kanki zaki zo kice Abba nagode da zab'inka,ashe zab'inka alheri ne agareni.........."
Haka de Abba yayi ta mana fada da nasiha kan mu riki aurenmu da kyau Kuma mu baiwa auren muhimmanci sosae,mu bi mazajenmu sau da kafa sannan kuma mu k'yautatawa danginsa.Haka mah Umma itama tayi mana fad'a sosae.Ashe wai wasu acikin danginmu wayenda suka sanni tare da Leedar sunyi ta mamakin yadda akai ya koma mijin Suhaima,Abba de ce musu yayi haka Allah ya tsara tun fil'azal cewar Suhaimar itace matarsa amma ko kadan be labarta masu komai na game da shashancinmu ba.
Su goggonnina,mamannina da wasu kawunnina duk se da suka shigo suka mana fada da nasiha meh ratsa xuciya.Ni da Suhaima babu abinda muke illa kuka.Daga k'arshe akayi waje damu don har 'yan daukar amarya hadda na Suhaima sun iso.Sae da akayi da gaske kafin arabamu da su Abba da kannena.
Abba yace baya son tarkacen mutane da nufin kai amarya,sam an bar yayin nan.Mama Jamila,Anty Hajaar,Mama Sadiya cousin dinsu babanmu,sae kuma kawayena biyu,Ash da zuwairah kadai akace zasu bini.
Ita kuwa Suhaima mutane har Kusan goma ne wai zasu bita tunda nan cikin Zariar za'a kaita kuma ayau din zasu komo,kuma duka kawayenta suma zasu bita.Nayi kuka sosae,sae nake ganin kamar an nuna min rashin gata ne.
Ni da Kawayena muka shiga mota daya,ayayin da dayar motar kuma su mamanni ne aciki. Sae gud'a ake tayi har motocinmu suka bar kofar gidan.....
A/N
Hey Fadima sa'ad Mainasara welcome to Nakowa's family!!!
Ina kuke tunanin za'a kai Fadima? Family house ko kuwa gidan Baba Mu'azzam za'a sauketa? Ku biyo.
Sorry guys! chapters na kashi biyu zasu dunga zuwar muku a little bit scanty don novel din ya Kusan zuwa karshe & I want the chapters too be a little bit much..... Yeeeepeeee shout out to Hafnan! Her first novel is about rounding up!!! 💗💗
©QUEEN CE©
Advertisement
- In Serial63 Chapters
The Great Tower
Due to unsatisfactory ratings, the social entertainment program that was humanity has been cancelled. But the studio executives of the multiverse are anything but wasteful; every human has been entered in as contestants in the popular program "The Great Tower," where challengers must fight and struggle, seeking the treasures that await at the top.Before humanity is thrown into the meat grinder, everyone is given a chance to sell parts of themselves in exchange for a little boost. One young man seizes this chance, selling everything. Even his humanity. Nameless, Raceless, and without any clear memory of the past, he is thrown into the bottom level of the tower, with one goal. Survival.**** Cover credit to NohMerci ****
8 132 - In Serial141 Chapters
What Is It Like To Be Eternal? (Completed)
Actual Word Count: 683 925 Words and 2487 pages. Under edition. Chapter 36-44 must be edited. Read the red text below to learn more. Synopsis: Have you ever thought about what is it like to be Eternal? What does being Eternal even mean? Maybe I can show you what it is that you are desiring. What lies at the center of the universe, when you reach the peak of strength and power? Can love reach that place too, or do you lose your feelings the stronger you get? How long can you travel and hold onto yourself, before feeling that you are starting to fall apart, losing your mind to your strength? How long is your road? Your feelings? What's going to win over you? The Darkness and the Hate? The Love and the Light? Or maybe none? Follow me as I show you my colorful yet gray path to eternity. My Discord server: https://discord.gg/XMSzDPH Special thanks to my editors. Azorath1234 (70-99th chapter), BlackStarLine and Kaentyr from the 100th chapter. Cornerstones:9th Chapter - Bonding Through the Night38th Chapter - The Way of Cultivation is a Way of Life54th Chapter - The Universe Is Ever Changing and Evolving69th Chapter - Beyond the bond [Inheritance]83rd Chapter - What I call Art!88th Chapter - What Does It Take To Kill?93rd Chapter - Chasing Rainbows [Loop?]108th Chapter - The Fall of a Creator?109th Chapter - A Family [Descendant]119th Chapter - What Is It Like To Be Eternal? Detailed reviews:http://royalroadl.com/fiction/10058/what-is-it-like-to-be-eternal-completed?review=132372#review-132372http://royalroadl.com/fiction/10058/what-is-it-like-to-be-eternal-completed?review=153956#review-153956 Both the Novel and the Cover picture are copyrighted. The Picture is a result of my commission. Cover Art: Novel: P.S.: I'm also hosting my novel here and on Novel Updates Forum. Nowhere else for now! EDIT: The novel is in rework. The original and the new ones are completely different. Where you see [Edited] it means that I'm done with editing the STORY! Whereas where you don't see it, it's in the old style. For now, I'm editing only the style. Once I'm done with every chapter, I'll run through it once again and correct possible grammatical mistakes. The style will be edited until the 45th chapter.
8 105 - In Serial103 Chapters
NEW EARTH - A World of Chaos
In 2050, an unprecedented nuclear disaster forced all human beings to seek refuge in underground refuges. Not knowing when the level of radiation will reach acceptable levels, the world leaders decided to bet everything on the next generation. They reallocated all their resources into a single project. A new VRMMORPG about to be released is redesigned to accommodate the world population. It will not only provide people with a goal and leisure but also serve as a test to find the future leaders that will rebuild Earth. Follow the adventures of an orphan as he climbs from nothing to the very top. He will face many difficulties, venture into a boundless world and finally build up his own kingdom. Caught in the storm of the struggles for power, he has no choice but to grow stronger. This is the story of the man to be known as the Emperor of Chaos. Here's an edited version available on Amazon: Book 1: https://amzn.to/2MuPDF6
8 128 - In Serial18 Chapters
Infinity Force: Heroes of Yesterday
The modern world, where superhumans are respected and adored, was not always the way it was. Decades before, the world held a different view in regards to those with godlike abilities. Observe the happenings of this era through the eyes of Harold Farwell and his friends, as they make their way through a not-so pleasant world, trying to save it from what seems imminent catastrophe. Spinoff of "Helix Academy of Superhuman Development." [Participant in the Royal Road Writathon challenge]
8 108 - In Serial14 Chapters
How To: Think Properly
I'm Alive ——— This is the ultimate fantasy. Don't kill yourself
8 154 - In Serial58 Chapters
Rise of the Night Witch
Demons, vampires, witchcraft, abandonment; Marissa Carter has problems others don't see. As the daughter of a banished witch and a normal human, she lives between two worlds.Once the Veil breaks and demons attack, she must decide. Will she learn magic at the Cunning Folk Academy or continue her normal high school life?She has time until Halloween to find the leader behind the monsters' invasion of the human realm. Life's a witch.[-]Updates on Tuesdays and Saturdays. Also on Geeke. (If this book is on a site other than Wattpad or Geeke or a Wattpad account other than "Auraptor" or "PASharp", it's likely stolen. Also, there are now thousands of accounts claiming my book is stolen. If you check them, you'll see they have no followers and no conversations. They're fake accounts, don't listen to them.)#123 Creepy out of 40.3K stories (30/08/2022)#98 Paranormal out of 86.6k stories (21/11/2022)#406 Anxiety out of 60.7k stories (29/08/2022)#53 Darkfantasy out of 7.9k stories (09/08/2022)#306 Monsters out of 37.5k stories (19/08/2022)#75 Demon out of 55.2k stories (19/08/2022)#70 Fae out of 7k stories (19/08/2022)#22 Secret Identity out of 4.9k stories (05/09/2022)#14 Superpowers out of 26.2k stories (09/10/2022)#255 Magic out of 254k stories (27/09/2022)#73 Supernatural out of 177k stories (21/11/2022)#100 Witch out of 80.7k stories (27/09/2022)#38 Urbanfantasy out of 7.4k stories (21/11/2022)#16 Horror out of 302k stories (21/11/2022)
8 177

