《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER THIRTY FIVE
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA TALATIN DA BIYAR🌼
Page 160
Wayyo! ni Fadima hidimar biki ya sanya na sha'afa,na manta na gaya muku cewar ana saura sati guda aka kawo lefen Suhaima,an narka uwar dukiya ba kadan ba,komai aciki meh dan k'aren tsada ne.Ni kuwa tawa lefen sai ana sauran kwana biyu ah soma shagulgulan biki aka kawo nawa.
"Subhanallah! Masha Allah Fadima 'yar gata kaya sunyi Allah ya sanya albarka... " shine albakacin bakin da kowa ke tofawa akan lefena.Lefena ya shalleke gaban na Suhaima.Akwatuna set biyu aka kawo masu shegen kyau kamar ka sace ka zura aguje.Komai na ciki babu meh arha sae uban tsada.
Lefena ya xama abar kwatance agari,sae yadawa ake ana yiwa mutane kwatancen abubuwan dake ciki sae kace akaina aka soma narka uban dukiya akan lefe.Da su Umma suka ga bakin mutane yayi yawa sae kawai suka dena fitarwa agani.Acan master bedroom na Abba aka jera akwatunan namu aka rufe dakin gudun kada ta ajje anata dakin ayi 'yan sace sace don mutane zasu cika su batse ne anata bangaren.Ana gobe 'Bridal shower' danginmu na Adamawa suka diro Zaria.Kawayen Umma gogaggun mata sae iyayi da feleke ake tayi,kowa tana son ta nuna cewar ita din wata ce.Kawayenmu daga ni har Suhaima suma ba'a barsu abaya ba,sae shirye-shiryen yadda za'a k'ure wuri ake.
*SHAGALIN BIKI*
*THURSDAY,23 NOV. 2017
*DAY 1:BRIDAL SHOWER*
Tun wuraren sha biyu na rana masu wedding decorations suka iso suka soma decorating bangaren lambun gidanmu (wurin shaqatawa) ah inda zamuyi bridal shower din.Na musamman aka nemo 'Fati mamza' one of the best make-up artist don yi mana kwalliya da kuma shiryamu har ah gama bikin.
'Fati Mamza' itace ta kawo idea din muyi using black colour for the shower,because black is cool kuma yana haskakawa musamman ga farare,sae kuma sky blue,light pink and silver.Idan kun tuna 'black,silver,pink & 'blue' issa bae.
Ta shiryani cikin wata black fitted material lace gown wanda bayansa ke jaah sosae akasa,ajikin bakin lace din akwai ratsin silver colour daya dan bayyana kadan-kadan ajikinsa.Sae ta taje min suma wanda ya sauka har ya wuce kafadata,ta gyareshi sosae tare da yanko wani style.Kana ta kafa min wani k'aramin silver color crown akai wanda hakan yayi min dan banzar kyau.Sai aka sanya min 'Sky blue bridal sash' across my shoulder zuwa k'uguna wanda aka masa bakin rubutu akai 'BRIDE TO BE'.Takalmana masu dan tudu shima silver color masu igiya abaya,ta saman takalman wasu white stones ne keta aikin zuba uban k'yalli.
Kawayena kuwa,'long black straight pencil skirt' suka sanya,sannan suka aza 'sky blue' shirt asamansa wanda akayi customizing gabansa da 'BRIDE MAID'.Kowaccensu an gyara mata gashinta,aka musu different hairstyles,sannan aka zagaye musu kan da flowers masu shegen kyau.
Ita mah Suhaimar exactly irin shirina akai mata,Haka mah friends dinta suma irin shigar tawa friends din sukai,sae dai tasu kalar shirt din 'Light pink' ce wanda agabansa an rubuta 'BRIDE MAID'.Suma anyi musu different hairstyles sannan aka zagaye kan nasu da beautiful flowers.Ita kuwa Suhaimar 'Light pink sash' aka zura mata wanda aka masa rubutu da black 'BRIDE TO BE'.
Abin se ya bada wani kala,'black,sky blue,siver & light pink'.Tsaya kwatanta muku haduwarmu ze iya cinye wannan chapter din.kowacce sanye take da decorative mask,wasu kuma rike da word stick ah inda aka rubuta 'Am next', 'Taken', 'Wanted','Single let's mingle', 'Will you marry me?' Da dai sauransu.Wuraren biyar saura aka soma because Fati mamza tace evening period is more cool for a bridal shower.
Advertisement
Kawayena suka tsaya ata gefena,ayayin dana Suhaima suma suka tsaya ta gefenta,sae kashe mana hotuna ake,en mata kuwa sae canza style ake tayi.Masu kallo kuwa sae ihu ake ana yaba haduwarmu don kam sae kallo daga nesa.Ash ta Kasa ta tsare tace wannan programme din ta yan matane zallah babu tsohoffi ko yara kananu aciki,don haka babu wanda ya isa ya shiga sae classic ladies dat's we.Cake dinmu hawa hudu ne,anyi decorating dinsa sosae akayi masa kwalliya asama wanda ya bada 'mask outlook'sae abin yayi kamar real mask ne aka kafa asaman cake din.Sae wasa da cake din muke atsakaninmu,dangwalar butter dinsa muke muna lak'atawa fuskokinmu cikin farin ciki da wasanni.Gaskia akace jama'a rahama ne,don kam friends dina sunyi nasarar k'awar da damuwar dake tattare dani,sae ji nake kamar auren soyayya nake.
Wannan kenan!!
*****
*FRIDAY,24 NOV.2017*
*DAY 2:KUMBO WALIMAH*
Wata sabuwar decoration akai na 'kumbo walima',wannan karon acikin filin gidan akai don filin nada girma sosae.Ya ilahi! tsaya fada muku haduwar wannan wurin ze zama kamar k'auyenci Fadima Sa'ad ke zubawa.Abin de se wanda ya gani.Shigarmu ta yau da k'awayenmu yafi na jiya mugun k'yau.Shima abin se wanda ya gani.muka bar Suhaima da kawayenta adaki suna kashe hotuna kafin asoma walimar.Ni kuwa da tawa tawagar classic ladies din lambu muka nufa don kashe kala kafin Malama Ummulkhairi ta iso.Walimar 4-6 ce.
🍃
Mutane an cika gidan makil,manyan mata sae dira suke tayi acikin manya-manyan motoci.Abinka da bikin manya,'ya'yan the whole chief justice of Zaria ai dole mutane su cika su batse.Muna cikin hotuna wata Goggona tazo take sanar mana da zuwar malama.Kawayena suka sanyani atsakiyarsu.Sukayi forming two lines,biyar ta gefen haguna,haka mah biyar ta gefen damana,dayar data rage kuwa,ta bayana ta tsaya tare da rik'e min farar gown dina dake jaah akasa.Cike da takun kasaita muke tafiya,su Suhaima muka hango suma wata style sukayi da nata kawayen,suna tafiya ayangance,su suka soma samun wuri suka zauna.Daga baya kawayena suka min rakiya zuwa wajen zamana akusa da Suhaima.Abin namu ba karamin birge mutane yayi ba,wajen zamarmu kadai mah abin kallo da bud'e baki ne.Malama Khairi tayi wa'azi sosae tare da jawo ayoyi acikin alqur'ani meh girma wanda ke nuni da muhimmancin aure da kuma hakkokin miji akan matarsa,haka kuma hakkokin mata akan miji.Daga ni har Suhaima munsha kuka sosae ba kadan ba.Malama ta bukaci da kowaccenmu ta fito ta karanta abinda ya sauwaka daga cikin alqur'ani meh girma.Haka muka fito muna yi muna hadawa da kuka.Ash da Bilqis best ladies suma sae da aka bukaci da su fito suyi karatun.
Sae hotuna da videos ake ta mana.Sae wuraren shidda da rabi ta yamma aka tashi taron,aka rufe da Addu'o'i tare da sanyawa aurenmu albarka wanda za'a daura karfe goma na safe ah washegari.Kafin atashi an rarraba sovernior wacce manya-manyan different colors of bags ne meh dauke da rubutu akai 'Happy married life Fadima Sa'ad Mainasara & Suhaima Sa'ad Mainasara'.Kananan jugs ne,butoci masu kyau,takaddu meh dauke da hotunanmu,set of complete qur'an irin one-one din nan,da dai sauransu ke cikin jakar,kuma kowanne dauke yake da sunanmu,se kuma kayan ciye-ciye da shaye-shaye.
Da daddare aka sanyamu ah lalli,gida ya rud'e da kalolin muryar rangad'a gud'a ta jama'a.Mu kuwa sae aikin kuka muke ganin fa ashe da gaske mun kusa rabuwa dasu Umma.
Ko naira biyar daga cikin sadakinmu iyayenmu basu taba ba,hasalima tun kafin asoma shagulgulan biki akaje aka zuba mana kudaden acikin account dinmu wai hakkinmu ne don haka ko sisi ba'a cire ba.
Advertisement
Wannan kenan!
*****
"Inna barka da dare.... " Tijjani ne ya russuna yana gaida mahaifiyarsa Goggo wacce take zaune saman wata k'aramar kujera akofar dakinta.Shi kuwa daga masallaci yake,yana dawowa daga kasuwa ya tsaya amasallacin unguwar yayi sallar magrib har data isha'i gaba daya sannan ya taho gida.
Ta amsa masa tare da tambayarsa yadda ya baro kasuwa. Ya amsa da "Alhamdulillahi! kasuwa yau tafi na kullum riba..... "
Tace"Masha Allah! haka akeso,Allah ya sanya albarka... "
"Ameen Inna nagode bari na shiga ciki" ya fad'a tare da mik'ewa zai bar wurin.Har ya soma tafiya zuwa bangarensa sae tayi saurin dakatar dashi.
Da sauri tace"Dawo nan dama zaman nan da nayi anan zaman jiran dawowarku nake kai da Buhari,amma tunda kai ka rigashi,sae kazo ka zauna ka saurari abinda xance,idan yaso idan ya dawo ka isar da sakon xuwa gareshi don ni bacci nake ji baxan xauna jiransa ba.......
Da hanzari ya dawo da baya hankalinsa atashe,yace"Inna lafiya dai ko? Ko wani laifi su Bintoto su kai miki?" Yana nufin matansu.
Murmushi tayi tace"A'ah kwantar da hankalinka babu abinda suka min,ai tsakanina dasu sae zallar mutunci da girmama juna,Allah dai yayi wa matanku albarqa d'an nan,yadda suke kula dani ina rok'on Allah yasa suma 'ya'yansu su bauta musu fiye da yadda suke min.... "
Ya amsa mata da"Ameen Innata...".....kana ya saukar da ajiyar xuciya jin cewar ba wani rashin kunyar matan nasu suka yiwa Innar tasu ba kamar yadda yayi tunanin hakan afarko.Sake russunawa yayi akaro na biyu yana fadin"Toh! Innata menene? gaya min damuwarki na magance miki ita yanzun nan,idan kuma har ba abinda xan iya yi bane,toh Insha Allah na dau alqawarin sanyaki cikin du'a'ina..... "
Goggo tayi murmushin jindadin kalaman dan nata,duk cikin 'ya'yanta tafi qaunar Tijjani sabida ya fisu sonta,tattalinta,kula da ita da kuma magance damuwarta.Tijjani dan albarqa ne,akullum addu'arta be wuci Allah ya basu aikin daya fi wanda sukeyi ayanzu ba duk da cewar tasan zeyi wuya su sami aiki irinta su Mubarak tunda ba wani zuzzurfan karatu sukai ba,hasalima iyakacinsu babbar secondary suka tsaya da karatunsu.
Inna tace"Tijjani bani da damuwa ko daya,dama so nake na fada muku cewar xuwa gobe ku shirya ku halarci daurin auren Mahmood dan gidan kawunku Mustapha...... "
Cike da mamaki yace"Inna Mahmood zeyi aure gobe-goben nan shine aka kasa samun wanda zaizo ya fada mana sae akurarren lokaci?ko don an raina mana arziki ne?Toh! gaskia Inna kiyi haquri amma ni dai babu inda xani,sae dai ko shi Buhari yaje......."
Ahankali tace"A'ah dan nan karkace haka,toh ko maihaifiyarsa mah ita karan kanta bata da masaniya akan auran nan da zeyi,kaga kuwa ai an mana karamci tunda har kawunka Mu'azzam shi da kansa ya tako har nan gidan dazun da goshin magariba yake sanar min da xancen.... "
Mamaki ne ya sake bayyana karara akan fuskar Tijjani.
Yace"Inna nifa ban gane ba,taya za'ai d'a yayi aure ba tare da sanin mahaifiyarsa ba?taya kike tunanin wannan auran xatayi albarqa....? "
Da hanzari ta tari numfashinsa tace"A'ah Tijjani ance ka fadi alheri ko kayi shiru,nima Yayah Mu'azzamun be fada min dalili ba,yadai ce min xancen da tsawo amma asabar ta sama za'ayi meeting agidansa don jin dalilin b'oyewa mahaifiyar tasa maganar auren nasa,amma don Allah maganar nan ta tsaya daga ni sae ku,banda surutu awaje don Yayah ya rok'eni kan nayi shiru da bakina banda yadawa don ba'a son mahaifiyar tasa ta sani har sae bayan auran....... "
Shi dae Tijjani jikinsa ne yayi sanyi qalau,sam ya kasa gane inda wannan xance na Innar ya dosa,ahankali ya budi baki yace"Insha Allahu Innata zaki sameni da bin maganarki,bayan Buhari mah ko matanmu baxan bari su sani ba,amma Inna ina ya samo mata? "
"Zaria akace.... Yace kuma gobe qarfe takwas tayi muku agidansa don tare xaku wuce zariar.... " tana nufin gidan Baba Mu'azzam.
"Insha Allahu Inna Allah ya kaimu,kuma da zarar Buhari ya dawo xan isar da sakonki gareshi.... "
"Madallah jeka kada Binto ta jika shiru,Allah yayi muku albarqa... "
"Ameen Inna" ya fada tare da laluban aljihun wandonsa,ya zaro dari biyar ya mik'a mata yana fadin"Inna gashi kya siye goro da wannan ba yawa.... "
Bin hannunsa da kallo tayi tace"Kai Tijjani wai kai baka gajiya ne?kullum fah idan ka dawo sae ka bani kudi fa? A'ah gaskia yau baxan k'arba ba...."
Ta fad'a tare da dauke kallonta daga gareshi.
Ahankali yace"Haba! Innata ai albarkanku muke nema akoda yaushe,kuma hakkinmu ne mu kula dake mahaifiyarmu kamar yadda kuka nuna mana gata alokacin da bamu kawo da zamu mallaki na kammu ba,don haka don Allah Inna ki amsa don yanzu lokacinmu ne muma mu nuna miki tamu gatar..."
Hawaye ne ya xubo mata tana meh kara godewa Allah da irin 'ya'yan albarqan daya axurtata dasu,yanzu shima Buhari yana dawowa haka zaizo ya bata tasa kyautar,ko kudi ko kuwa wani abin amfanin daban ko na ciye-ciye.Haka mah matansu ba karamin girmamata da tattalinta suke ba.'ya'yanta mata mah haka suke kawo mata abubuwa,mazajensu mah haka suke hidima da ita.kai agaskia ita de Goggo Ladidi ta godewa Allah,abin se dai ace Alhamdulillahi! kawai.
Karban kudin tayi tana meh shi masa albarqa,ya wuce bangarensa ita kuma ta shige dakinta don kwanciya bacci.Goggo bata wasa da bacci,kamar kaza take (lol).
Alh.Mustapha mahaifinsu Mahmood shine babba,sae Baba Mu'azzam meh bi masa,Inna Zaynabu wacce kuka fi sani da Goggo Ladidi itace autarsu.Duk kuma ciki d'aya suka fito.Mahaifiyarsu har wa yau tana nan araye,Baba Mu'azzam ke rikonta agidansa dake 'sharada'.
Haj.Aishatu tsohuwa meh ran karfe kenan,babu ruwanta amma idan ka tabota faa anan za'a jiku,sam bata daukar kaniya daga gun uban kowa,ga son jama'a da kuma son ibada.Ana kiranta da 'Kaka rigima' wanda tun asali Mahmood ne ya saka mata sunan sabida akwaita da Zafi idan ka takata da gangan.
Wannan kenan!
****
*SATURDAY 25TH,NOV.2017*
*WEDDING FATIHA*
Engr.Mahmood ne na hango gaban madubi yana shiryawa don halartar daurin aurensa.Shigar wata farar dakakkiyar gezna naga yayi wacce gabanta tasha aiki da brown zare.hannun rigar meh links ce wacce ta rik'e tsintsiyar hannun nasa gam!.Ya aza babbar rigarsa asamanta wacce kuka fi sani da 'Malum-malum',itama gabanta yasha aiki sosae da brown zaren.Sae ya kafa hularsa wacce take da multiple colours ajikinta,'brown,green,black & white'. Ya saka bakin agogonsa meh shegen tsada,takalmansa kuma cover shoes ce bakake.Akarshe ya feshe kansa da kalolin turaruka masu shegen kamshi da tsada,tun daga saman hularsa har xuwa wandonsa ya feffeshe.
Ya ilahi! Angon 'Fadima Sa'ad' bada kanka kawai asare kaje gida kace fadiwa tayi (lol).Meh kyau acikin kaya masu kyau da kuma tsada,hmm baxan iya cewa komai ba,zan dai barku da kissima irin haduwar da yayi acikin ranku.Idan kuma kun kasa ga picture din dana daukeshi ah lab'e.
Yana fitowa falo abokansa su shidda dake ta jiran fitowarsa suka hau fito,ihu tare da kod'a haduwarsa.
Wani abokinsa Faruq yace"Agaskia abokina ka fito,wannan ai itace ake kira da k'arshen haduwa,kusan xan iya cewa ko abikin Zeey bakayi irin wannan d'aukar wankan ba...... "
Wani irin kallo ya wurga masa ganin yana nemar fama masa k'aton gyambon dake xuciyarsa.Baya tsammanin akwai wata wacce zata iya goge son da yake yiwa Zeey dinsa.Fadima dai yana sonta ne sabida everything about her is juz lyk Zainab amma baya jin xata iya maye gurb'in Zeeynsa.Zeeynsa ta daban ce. (Dan rainin sense haka kake gani ko?).
Key din motarsa ya cillawa Khaleed bestie dinsa,yace"You are to drive the car....".
Ya sake cewa"Am coming pls.... "
Falon Fadima ya nufa inda anan ne aka mata jeran Kujerunta da sauran abubuwan k'awata falo.Kallonsa yakai kan k'aton frame na hoton Zeey dinsa dake manne abango,tayi kyau sosae sae murmushi take xubawa kamar ka kirata ta amsa.
Gefen hotonta,another k'aton frame din hoton Fadima Sa'ad ce,idan zaku tuna ya taba daukarta picture farkon soma aikinsa ah ABU sanda takai masa ziyara,remembered?toh daya daga cikin hoton ya sanya aka wanke masa tare da enlarging dinsa,hoton yayi kyau sosae don yayi capturing dinsa ne sanda ta sanya hannu tana kare fuskarta,shi kuwa ya dauketa ahakan,gefen fuskarta da kwayar idonta d'aya wanda ya cika da yalwar lashes ya dauka,sauran gefen fuskar kuma ta kare ne da tafin hannunta wanda yatsun hannayen suka sha jan lalli.
Sannu ahankali ya taka zuwa direction na picture din Zeey.Dafa hoton yayi ya shiga shasshafa fuskarta.
Kwalla ya dan xubo masa"Zeey dita am very sorry am trying to break our promise today,Zaynab naso ace mun rayu da juna har xuwa lokacin tsufarmu kafin ki tafi,amma mutuwa bata min adalci ba,lokaci daya ta mana yankan qauna,Zeey naso ace naga 'ya'yana wanda suka fito daga tsatsonki,'ya'yan da xan dunga kalla naji sanyi araina, ya'yan da idan na kalla zasu tuna min da Zaynab dita,amma Ina! Allah beyi zaki haifa min 'ya'ya ba kafin Allah yadau ranki,Zeey baki bar min abinda ze dunga deb'e min kewarki ba..... "
Dan dakatawa yayi,ya tsaya yana shessheka,can ya cigaba"ada na daukar miki alqawarin cewar Insha Allah babu ni babu wata 'ya mace da sunan wai matata,but Zeey am getting to 40years,nima ina son naga 'ya'yan kaina kamar yadda nake sha'awar 'ya'yan abokaina,Zaynab nima ina son naga na tara zuri'a irinta sauran mutane,Zaynab permit me to take ' as my wife today,amma hakan ba yana nufin wai na dena sonki bane,a'ah ke ta dabance acikin xuciyata 'Allah yayi miki aikin gafara matata,ina son ki sanya min albaqarka acikin wannan auren da xanyi..... "
Dafa kafadarsa yaji anyi,ahankali ya juya yana kallon Khaleed wanda shine ya dafasa,ya jima da shigowa ya tsaya yana sauraron maganganunsa.
Yace"Dama ni xuciyata ta bani cewar shigowa nan da kayi surutu da hoton Zeey zaka tsaya yi wanda ka saba yi akodayaushe,Haba abokina Zeey ta tafi,fatarmu Allah yaji kanta ya kuma rahamasheta,buh I juz want u to forget Zeey and focus on the present wato Fadima Zahra,am assuring u dat Fadima zata maye gurbin Zaynab
.... "
Advertisement
- In Serial12 Chapters
Legacy Online
Legacy Online is not only the world's first VRMMORPG but also the world's current most popular game that gathered over three billion players within the time span of half a year. An absurdly realistic game where real-life skills and talents mattered; its popularity was so high that jobs and schools were created just for the sake of getting better at the game. Yin Xian is a young adult who recently returned from studying abroad overseas. However, when he returned home after four long years, his family was shocked to find out that his knowledge of Legacy Online--- a game with influences all over the world--- was nonexistent.
8 139 - In Serial72 Chapters
Sovereign
Is it possible to become a supreme being? After his withdrawal from Space Forces, in which he had spent twenty years of life, Captain Sava Gromov desires an extra reason for his existence. With a vague idea of becoming a merchant, he buys a secondhand spacecraft, loads the cargo, and leaves for an adventurous journey through the Solar System. On his way, he receives an SOS coming from a damaged research spaceship. To rescue the crew in a crisis is the easier part; the harder part comes afterward. The research team discovered an abandoned weapon, originating from a forgotten empire. Unfortunately, not everyone considers the vanished empire harmless. There is an organization actively destroying its remnants. Only two choices remain for Gromov: either to die or operate the unknown weapon in a slight hope that the archaic device may deter his pursuers. Choosing the latter, Gromov assimilates with inhuman digital being into the ultimate symbiosis of the organic and digital world. The Universe turned out to be a dangerous place: full of conflicts, threatening aliens, and unpredictable twists. The unmanageable chaos dwells in desperate need of a unifying force. Will Gromov become the Sovereign of the Solar System? Or will he become the ultimate enemy of humankind? There is an official repository for Sovereign on Github. If you are familiar with Github, you can suggest your edits there.
8 228 - In Serial10 Chapters
Shade Hunter
Damien Sinclair, despite his bizarre name, was a relatively ordinary young man, fresh out of high school with few prospects in his life. Then, through a cosmic accident outside of everyone's control, he ends up on Xaunis, a world both familiar and foreign to his own in several ways, not the least of which being the fact that magic is real, he's seeing screens straight out of video games, and the very fundamentals of what he understands about reality is inherently wrong. But despite these challenges, Damien will meet them with a head held high and a smile on his face. After all... one does not cheat death and simply waste a second chance. Updates every Friday at 12:00pm MST
8 206 - In Serial34 Chapters
Heavenly Will
The world of five continents. It’s a world of no magic. A world were martial cultivators stand at the summit. A world where the strong prey on the weak. A world…of immortals. Qing Yun. A name that stood at the peak of the world of the five continents. It was the name of a young man who stood between the strong. A young man known as Asura. A young man known as a heavenly saint. He killed millions, he saved thousands. He was known as the weak whom the strong feared. A young man who…reached the end of his life at the age of 21. But…it was not the end. Who was the one that spoke to him in his last moments? It was a voice that sounded so domineering that it could shake the heaven itself. It was the voice that will change Qing Yun’s destiny forever. Being given a second chance to live, Qing Yun was reborn in this world of immortals again. With a new life and a new family will he be able to protect his loved ones this time? Will he be able to save those whom he let down in his previous life? Follow the story of this young man on his journey to immortality and his struggle…against the heaven…
8 205 - In Serial12 Chapters
Becoming Itachi Uchiha in a Different world!
Good bit of your time. (maybe...not) Based off of Naruto and IDWWNS. Warning : Contains profanity usage, a bit of sexual content, and gore. Introduction: 37 year old, Charlton Triston was a huge fan of Naruto. At first, he thought it was some random anime his colleagues wanted to torture him with, but as he watched episode after episode, he became addicted to the fighting secenes, justus, but most of all, The Sharingan. (Most thought he was too old for something so childish. However he didn't mind.) His favorite character was Itachi Uchiha, because of his tranquility and intellegence. He even admired Itachi for planning the future for Sasuke. On one saturday morning, Charlton Triston was driving to the store where popular manga was sold, he was caught up in an accident (truck-san), so in order to keep his childern safe, he sacrifced himself... ........ "Welcome Charlton, atlthough it feels rushed, but you shall be reincarnated into a world that will be similar to the anime you will choose." Happily said the odd voice. Ranks for Different World: -G,G, -F,F, -E,E, -C,C, -D,D -B,B, -A, A, -S, S Academy Student, Genin, Chuunin, Jounin, Special(SS) Jounin, Kage, Other : Medical-ninja, S-class, Missing-ninja, Hunter-ninja, Courier-ninja, Disclaimer : I do not own Naruto nor anything associated to it. As it is owned by Kishimoto. Any images or quotes are owned by their respective owners. I'm not accurate with my naruto knowledge, so please, deal with it.
8 117 - In Serial32 Chapters
Fake Dating the Bad Boy
Highest rank in teen fiction #7Highest rank in #boyfriend #2Started 28th August 2016 COMPLETED 8th January 2017Not edited(update - I wrote this book when I was 14/15 so I do apologise for any misspelling or mistakes in the book)Olivia Valentine wants revenge on her ex boyfriend, Aaron Black, who cheated on her with, as Liv would like to call her, the blonde haired bimbo who is only popular for her fake boobs, and what better way to get revenge than to date the one and only Cole Williams, the hot school bad boy, who girls swoon over and who Aaron Black just happens to envy. Oh fake date that is.Olivia Valentine, the girl who isn't labeled, by which I mean she is not called the nerd, the slut, the normal student, nor is she the most popular girl in the school, she is just Liv. Many boys fancy her, whilst many girls envy her. Olivia Valentine has it all, the pretty looks, the long silky hair and an extremely rich mother, despite all this, she is most definitely not a horrible, snobby, stuck-up cow, if anything, she is the exact opposite.Okay, so now add Cole Williams into the picture. Cole Williams, the one who is definitely labeled, the one labeled as the hot school bad boy. He practically has every girl just dropping at his feet and he is constantly getting into fights with other jocks. Like Liv, he also comes from a rich family, which is probably one of the reasons why he is an arrogant, cocky, self-obsessed hottie. But deep down he might just have a heart of gold.Liv and Cole have never really spoken because of Aaron, but surely when it comes to getting revenge on Aaron Black, the two can make Parties, high school drama, fights, kisses, cat fights.Your classic teen fiction.
8 109

