《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER THIRTY FOUR

Advertisement

💘SHIN SO DAYA NE?💝

TARE DA ALKALAMIN

📝

HAFSAT AL-MUSTAPHA

_Watpadd:Hafnancy_

🌼BABI NA TALATIN DA HUDU🌼

Page 157-159

*RAYUWAR MUBARAK AKASAR INDIA*

Rayuwar Mubeen akasar India rayuwace yake yinsa adaddafe sabida har Xuwa wannan lokacin be samu ganawa da Fadimarsa ba kamar yadda yayan nasa yayi assuring dinsa cewar washegarin tafiyarsa zata mallaki wayar da take ta jira.Toh kuwa tun awashegarin ranar yake ta gwada layinta don shi ya kamata ya kira because ita bata da lambarsa ta nan,se de idan ba Mahmood ne ze tura mata ba,kuma koda ya turan mah ai bazata juri kiran layin k'asar waje ba sabida it will caused alot of charges,gwanda shi ya kira ze fi sauki.

Zuwa yanzu ya riga ya gama yardarwa kansa cewar raina masa hankali Mahmood yake,kwata-kwata beje gidansu Fadimar ba.Har yanzu de maganar daya ce da yake gaya masa.

"Wayar har yanzu be shiga hannunta ba,ita kuma taki kowani waya wai se wannan din..... "

Sam wannan maganar ba abinda hankali ze dauka bane,taya za'ai yace masa taki kowani waya se wannan? Ita ko kadan bata tausayin halin da shi ze iya shiga ne idan beji daga gareta ba?

Idan yayi wannan tunane-tunanen se yayi ta ganin kamar raina masa hankali Mahmood din yake masa.Jiya mah bata dadi suka rabu dashi ba awaya.

Ce masa yayi"Anya Yaya Mahmood kaje gidansu Fadimar nan kuwa? Kodai k'aryace kake min don kawai hankalina ya kwanta.?..... "

Azuciye yace masa"Yanzu Mubarak don rashin kunya ni kake nemar karyatawa? Ba damuwa gobe mah ai ranace.

Mubeen be sake cewa komai ba ya yanke call din.Abokan aikinsa Dr.James da Dr.Vera idan suka gansa cikin damuwa tsiya suke masa don aganinsu kewar matarsa Hanan ce ke damunsa,basu san cewar damuwar ta antyn Hanan dince bane (lol).

****

*KAWO GAISUWA*

*BAYAN SATI BIYU*

*SATURDAY,4:00PM*

Misalin qarfe hudu ta yammacin ranar asabar aka kawo gaisuwar Fadima Sa'ad Mainasara da kuma 'yar'uwarta Suhaima Sa'ad Mainasara.Ah bangaren Haidar,Kanin mahaifinsa Mal.Bala,abokin Babansa Alh Nafiu,se kuma wan mahaifinsa Alh.Tanimu suka zo.Bangaren Mahmood kamar yadda akace shine wanda ze auri Fadimar,Alh.Mu'azzam wanda kanin mahaifinsa ne,yazo da tasa tawagar mutane har biyar,shine cikon na shida.

Bangaren masu k'arbar gaisuwar kuwa,bayan mahaifinsu Fadima Justice Sa'ad,akwai kannensa biyu da kuma wansa wadanda suka taso tun daga Adamawa don k'arbar gaisuwar 'ya'yan nasu.Daya daga cikin kannen nasa,wan Haj.Kareema ne (idan zaku tuna nace muku auren dangi sukai,so duk dangin Justice Sa'ad na Haj.Kareema ne itama).Hahaha! hatta Kanwarta Anty Hajaar seda ta biyosu.

An karrama bakin sosae,girki kala-kala akai masu kai kace koh ranar bikin ne.Suka nemi auren Fadima da Suhaima wa 'ya'yayen nasu,kuma an basu,aka yanke masu sadaki dubu hamsin-hamsin don nemar albarkar aure.Sukace sam 'yan matan sunfi k'arfin dubu hamsin awajensu.Da k'yar Su Abba suka yadda suka k'arbi dubu dari-dari,don ada mah waliyyin Fadima yayi niyyar bada dubu dari biyu ne kamar yadda saurayin nata yace abayar.Amma Abba yaki yace adai kawo dubu darin.Aka tsaida lokacin biki nan da wata daya cur! babu ragi haka kuma babu kari kamar yadda Abba ya fada tun farko.Toh! Jama'a sae muce Allah ya kaimu lokaci musha bikin Fadima da Suhaima.

"Ayyyiriyiii! Ayyyiryir! yau 'ya'yana sunyi miji Allah ya kaimu lokaci musha biki..... " Anty Hajaar ce ta saki gud'a alokacin dasu Abba suka shigo suka kawo musu goro da alawan saka rana.Ita kuwa Umma sallah take sanda su Abba suka shigo da tulin goron da alawar.Tana meh nuna godiyarta ga Allah daya nuna musu wannan ranar,'ya'yanta sunyi mazaje duk da cewar tasan Fadimar biyayya kawai zatayi ba don tanaso ba.Tana meh rokon ubangiji da yasa taci ribar yin biyayyar nan gaba.

Advertisement

Anty Hajaar ce ta tsallake tulin goron da alawar tayi dakinsu Fadimar tana rangada guda.Su Mamin Ash da Madam Iyabo makobciyarsu suka bita da kallo suna murmushi,don ba laifi Anty Hajaar akwai kaudin bala'i.

Ni kuwa tun sanda naji hayaniyar mutane da nufin wai an kawo gaisuwarmu nida Suhaima,se na sami wuri na xauna adaki na hau cizgar kuka,se cewa nake "Shikenan ta faru ta k'are... Mubeen kana ina? Ashe dama ba qaunata kake ba tunda har ka bari ake kokarin daura min aure da waninka?

(Toh ko yana nan meh ze iya miki?)

Ash kuwa da Suhaima se aikin lallashi suke,suma suna yi suna hadawa da kuka.Gud'a da na jiyo Anty Hajaar ke yi ne ya sanyani tsaida kukan nawa.Da hanzari na mik'e tsaye na k'asa kunnuwa ina sauraron abinda ke fitowa daga bakinta.

"Ayyirihi! nanaye 'ya'yana sunyi miji,biki nan da wata daya cur!... Allah ya kaimu lokaci mu gwangwaje mak'iya kuma suji..... " ban k'arashe jin abinda xata fad'a ba kawai na tsinci kaina cikin wani irin yanayi da ban taba shiga ba.

Duhu ne naga ya karade dakin,can na soma lumshe-lumshen idanuwa,can kuma nayi masa lumshewar k'arshe,daga haka ban sake Sanin inda nake ba.

Rangwaf! Kakeji Fadima ta zub'e saman gado ah sume.Su Ash kuwa tuntuni suka lura da halin data shiga,ganin ta zub'e saman gado ah sume ya sakasu fasa ihu suka nufo zuwa gareta ah rude suna kiran sunanta tare da jijjigata.

Ita Ash sae cewa take"Fateenaaah! Fateenaaah don Allah ki tashi pls karki barni acikin duniyar nan da babu komai acikinta illa dunk'ulen bak'in ciki,tarin wahalhalu da kuma k'uncin rayuwa..... Fadima idan kika tafi nima xan biki Xuwa duniyar da kika tafi,don Allah 'yar'uwata ki tashi........ "

Ita kuwa Suhaima sae cewa take"Yaya Fadima pls ki tashi,I hate myself for putting u in diz condition because don ni kike cikinta,adalilin taimaka min kika fada cikin wannan kuncin rayuwar...... "

Duk sun rud'e sun mah rasa abin yi sae sake zantuka suke suna kuka.

Can Ash ta fasa wani razanannan k'ara tace"Ummmmaaaa! Mamiiiii don Allah kuzo ku roki Fateenah taki tashiwa..... "

Wani irin gudu ta kwasa ta fice daga dakin tabar Suhaima tana meh cigaba da zuba tata sambatun.Adaidai kofar dakin taci karo da Anty Hajaar wacce take kokarin son tazo ta isar musu da sakon saka rana,sadakin da aka bayar atake,sannan kuma jama'ar mah har an watse,Su Abba sun tafi yi musu rakiya.

Ganin yanayin Ash ya saka Anty Hajaar rud'ewa,tace"Ke! lafiya na ganki asukurkuce haka? "

Ko tankata batayi ba,ta rab'a ta gefenta ta wuce abinta tana ihun kiransu Mami,Umma kuwa har zuwa wannan lokacin tana kan dadduma.Sam Ash da Anty Hajaar basa shiri,acewar Ash Anty Hajaar ta fiye kaudin bala'i da kuma nuna ita din wata ce,bayan babu puss! aduwawun kaza,da dukiyarsu Fadimar take wannan takamar da nuna isa.Ita kuwa Anty Hajaar cewa take sam Ash bata da kunya ko kadan,bata ganin idon kowa da gashi.Ash tace"Yo! idan ka kama girmanka Aysha zata dunga ganin idon da gashi,amma idan kace kai din dan banza ne,kana yadda girmanka agaban yara toh kuwa Ashwairiyya xata tayaka zubar da girman. " Ta tura dankwalin kanta gaba ta wuce tana taunar cingam.Wannan itace fad'ar da sukayi ajiya sanda Anty Hajaar ta diro garin.Sam basa shan inuwa guda. (Kada na cikaku da surutu bari mu koma kan ainihin scene din).

Da sauri Anty Hajaar ta shige dakin.Ganin Fadima ayashe asaman gado bata ko motsi ya saka ta fasa nata ihun kamar wata 'yar daba.Karasawa gunta tayi tana jijjigata"Muido d'iyata meya faru? Suma kikai ne? Maza Suhaima debo ruwa ah bandaki mu yayyafa mata.... "

Advertisement

(Muido simply means 'The patience one',ahausance kuma 'Meh haquri'... Muido ayaren fulfulde kenan,sunan Fadima kenan ayare,amma can danginta ne kurum suke kiranta dashi).

Da sauri Suhaima ta d'ebo ruwa abandakin ta kawo wa Anty Hajaar,ita kuwa ta shiga yayyafa mata ruwan.Adaidai lokaci su Umma suka banko kofar dakin suka shigo afirgice.Sannu ahankali Fadima ta soma sauke ajiyar zuciya da karfin gaske tana dan bud'e idanuwanta kadan da kadan.

"Hajaar meya sameta? acewar Umma wacce ta nufi inda Fadimar take.

Hajaar tace"Addah Karima somewa tayi..... "

Dafe k'irji Mamin Ash da Madam Iyabo sukayi,alokaci guda sukace "Somewa kuma?"

Madam Iyabo ta kara da"Dama bata da lafiya ne? "

Ash tace"Lafiyarta qalau kawai jiyo Anty Hajaar tayi tana rangad'a guda...... " Mamin tace ta harareta alamun tayi shiru da bakinta don basu san Madam Iyabo tasan cewar Fadimar bata son auren kuma akansa ta suma,koh Anty Hajaar mah bata san da zancen ba,Umma ce taki fada mata gudun suturunta kada taje ta yadawa dangi.Ina ganin acikin bare mah Mamin Ash ce kawai ta sani don kawancensu da Umma kawance ne sukeyi na aminci.

Murmushi Madam Iyabo tayi tace"Ai! yanxu na gane kan zancen....my dear har kin soma kewarsu Ummar taki ne shine hadda fainting? "

Anty Hajaar kuma tsaki taja tace"Yo! yau ga ja'irar yarinya,caa! nake keda kanki kika kawoshi azuwan Wanda kikeso kuma Wanda kike burin ki aura? shine zaki zo nan kina some mana sae kace auren dole ake shirin miki? "......... (Hahaha! Anty Hajaar an barki aduhu baki san dawan garin ba, auren dolen ake shirin yiwa fatinmu).

Anty Hajaar na kokarin sake magana sae gani kawai tayi Umma tayi mata alamu da ido tayi shiru.Madam Iyabo da Mami suka fice suka koma falo suna jimamin wannan al'amarin.

"Hajaar,Aysha,Suhaima don Allah ku dan bamu wuri xanyi magana da ita..... " Haka umma ta fada wanda ta fadi hakan ne babu alamun wasa atattare da ita,hasalima wani irin daure fuska tayi tamk'ar wacce bata taba yin dariya ba.

Ba tare da sunyi wata gaddama ba suka fice duka.

Ni kuwa tun sanda naji furucin da Madam Iyabo tayi sae naji duk jikina yayi sanyi,dama ashe Somewa nayi? Kallon da Umma ke jefa min ne ya sake dagan hankali har sae dana ji hanjin cikina sun hargitsa.

Cike da rawar murya nace"Um.... mu..... "

Cike da b'acin rai ta tari numfashina"Don't u dare call me ur Umma tunda ke baza'a baki shawara kibi ba,gaskia baki cancanci akiraki da 'Muido' ba,sabida 'Muido' yana nufin meh haquri da tawakkali amma ga dukkan alamu wannan baya cikin tsarin rayuwarki...... "

"Ummmu listen......... "

"Saurara min nan! ba xancen soki burutsunki nazo sauraro ba,nazo na gaya miki cewar abin naki ya soma isata,na gaji da sanyani xubda hawayen da kikeyi,don ganinki cikin kunci ba k'aramin tada min hankali yake ba,Haba Fadima d'iyata why can't u juz try and be strong for me?meyasa kema bazaki watsar da makaman yakinki ba kamar yadda kika ga nayi,ki fawwala wa meh duka komai,ki rungumi xabin mahaifinki don na tabbata muddin kikai masa biyayya toh kuwa bazaki tab'a tab'ewa ba? Ni wanda mah kike haukan sonsa gani nake kamar be damu dake ba tunda har yaki takowa yazo ya duba koh kina lafiya kwana biyu ya jiki shiru,amma ko kadan beyi tunanin hakan ba wanda aganina dama can soyayyar fatar baki kurum yake miki.... "

Jan gwauron numfashi tayi,kana ta cigaba"Pls Muido 'yata nasanki da haquri,duk cikin 'ya'yana xan iya bugan kirji nace kin fisu haquri da tawakkali don tun kina 'yar kankanuwarki kika taso da wannan good habit din,Fadima I want u to pls as from today ki cire Mubarak daga cikin rayuwarki,nasan its not easy ka yakice son wanda kayi nisa acikin qaunarsa,but u juz hav to tunda kinga yau aka saka ranar aurenki da wani kuma har yama riga da ya bada sadakinki........ "

Kuka na sakar mata tare da rungumeta,da sauri ta rabani da jikinta tana fadin"A'ah kinga ni cikani tunda bazaki dena koke-koken bazan da wofi ba,koh kuwa so kike mutane susan bakya son auren? "

Girgiza mata kai nayi alamun a'ah, kana nace"Mum I promise u as from today bazaki sake kuka akaina ba,I promise to be strong for you,I will surely make u proud mother,ina son na saka miki ta hanyar sanyaki farin ciki kamar yadda kike sanyani cikinta akoda yaushe,ba dai so kike na haqura nayi biyayya na rungumi xabin Abba da hannu bibbiyu ba?"

"Hakan nakeso 'yata..... "

Na cigaba"Insha Allah ayau na watsar da makaman yak'ina,nayi surrender xanyi biyayya don samun albarka daga gareku iyayena,Umma am beginning to love diz marriage.... "

Na fada tare da rungumota wanda ni kaina nasan na fadi mata hakan ne kurum don taji dadi aranta,ai kuwa nayi nasarar shimfida farin cikin akan fuskarta,kuma har cikin xuciyarta na tabbata taji dadin kalamaina.

Sai cewa take"Allah yayi miki albarqa Fadima Muido Insha Allah u will never regret getting married to Mahmood...... "

Gabana ne naji ya buga wata irin ganga sanda naji ta ambaci 'Mahmood' amatsayin wanda xan aura.

Ahankali nace"Umma sunansa kenan? "

Batayi mamaki da bansan sunansa ba,don tasan tunda bana son auren,haka tasan ban tab'a tunanin tambayar sunan mijin ba se yanxu dana ji ta ambaci sunan nasa.

Tace"Sunansa kenan..... "

Shiru nayi ban sake tambayarta komai akansa ba don zuwa yanzu na tsani duk wani meh suna Mahmood sabida haushin abinda Engr.Mahmood ya bani na kin zuwa ya duba halin da nake ciki har wa yau.Dalilin daya saka na tsani duk wani Mahmood kenan,gani nake all the Mahmood's are heartless,mayaudara ne,tunda shi ai yaudarata yayi ta hanyar nuna min fake care wanda ada nake jin yana birgeni sosae ashe dai green snake under green grass ne.

****

Engr.Mahmood ne na gani xaune saman wata sofa dake barandar gidansa,sanye yake cikin wata three quarter da wata white sleeveless shirt ta sportmen.Iskar dake bugarsa ta wannan yammacin ba k'aramin jefashi cikin nishadi yayi ba.Rik'e yake da wata magazine,ya bada hankali sosae wajen nazarinta.Lokaci xuwa lokaci yake kai hannu ya dauki wata mug dake saman karamin table din dake gefensa,hot coffee ce acikinta wacce yake sipping time to time.Mahmood is a coffee freak,(yana bala'in son coffee).

Kana ganin yanayin Mahmood kasan yana cike da farin ciki sabida yadda murmushi ke sub'uce masa lokaci xuwa lokaci.Farin cikin dani Hafnan baxan iya ce muku ko ta mecece ba.Can k'aramar wayarsa ta dau ruri tana nemar agajinsa.

Murmushi ne ya sake sub'uce masa akaro na ba adadi ganin call din da yake ta expecting ne.

Da hanzari yayi picking,bayan sun gaisa,Mahmood ya kasa kunnuwa yana sauraron bayanin da ake koro masa.

Can naga Mahmood ya sosa k'eya tare da fadada fara'arsa yace"Abba nagode kwarai da gaske insha Allahu nima xan shigo kanon cikin week din nan don mu tsara yadda abubuwa xasu kasance..... "

Yadan saurara,can yace"Alhamdulillah Ala kulli halin.... Masha Allah kawu nagode agaida min dasu Kaka rigima..... "

Yayi ending call din.Wani irin tsalle naga ya doka yana furta"Yes! Fadima ta kusan xama tawa insha Allah..... "

Can kuma naga yayi fuskar tausayi yace"Ehya! so sorry my Lil u hav loose..... "

"Bari na latso bestyna na gaya mishi abinda ke going.... " ya fada tare da latso na hannun damarsa Khalid.

Bayan ya dauka,ko gaisawa be jira suyi ba yace"Aha! ku shirya nan da sati hudu zaku dauko min amarya..... "

Cike da ihun murna Khalid yace"Buddy are u damn serious?? yau abokina shida kansa yake ambaton kalmar 'zeyi aure' abakinsa?wow surprising,halan atlast ka samu wacce take kama da Zeey din taka ne?"

Runtse idanuwansa yayi yana meh kokarin danne gyambon da Khaleed ke nemar fama masa,ahankali yace"Idan lokaci yayi zaka sani...... "

Be jira ta cewarsa ba ya datse call din.

***

*Agurguje pls*

Lokacin biki se matsowa kusa yake,xuwa yanzu na gama watsar da komai araina na fawwala wa Allah komai,na rungumi xabin mahaifina da hannu bibbiyu,na dena maganar Mubeen da kuma tunaninsa amma har yanxu burbushin sonsa nanan mak'ale cikin xuciyata.Na danne xuciyata na shiga hidimar bikina.Abba yace shi baya son wata bidi'a adaiyi walima se kuma daurin aure.Ash ce ta rokeshi akan mu danyi 'bridal shower' acikin lambun gidan (wata kayatacciyar wajen shakatawace acikin gidan),se kuma 'kumbo walima' wacce walima ce za'ayi inform of Kumbo.Ash har ta fitar da ankon yinin biki data 'bridal shower' data 'kumbo walima',haka mah bangaren Suhaima k'awayenta sun fitar da tasu ankon daban.

Ash kirjin biki ta zage se rabon I.V takewa kawayenmu da course mates dinmu.Itama Suhaima kawarta 'Bilqis' ce ta dauke mata wannan hidimar don Reedah ce ya kamata tayi wannan aikin amma idan kun tuna itama akwai biki gidansu wato 'Haidar'.

Anty Hajaar musamman ta dauko wata kawarta 'yar Maiduguri meh gyaren amare.Kusan sati biyu aka dauka ana gyaramu,dilka ne,kayan tsimi ne,turaren amare da dai sauransu duk mun shasu.Sae kyawunmu ta asalin fulani ko nace kamaninmu da larabawa kamar yadda mutane ke cewa ya dada fitowa.Nan da nan farar fatarmu ta kara haskawa da wani irin shek'i da take badawa hadi da wani fitinannen kamshi da take fitarwa.

Duk kuma abin nan fah be saka munyi wasa da shan magungunanmu ba,sae mah kara bada himma da mukayi.

Abinda Fadima bata sani ba kuwa shine,Leedar da Fresh sun je har gidansu Ruqayya Lema,suka sanar da mahaifinta halin da ake ciki,hakika yayi kuka sosae tare da musu godiya hadda kyautar kudi wanda suka ki qarba,acewarsu tsakaninsu da Allah sukai na fad'a masa halin da 'yarsa ke ciki bawai don ayi musu kyauta ba.Cikin kankanin lokaci Khaleel Lema ya shirya musu tafiya K'asa meh tsarki shida 'yarsa don dagewa da du'a'i sannan kuma 'yarsa ta nemi gafarar Allah kan sabon da tayi-tayi.

Wannan kenan!

*****

Duk mazajenmu sunce basa son matayensu su taho da ko tsinke gidansu,matan kawai sukeso.(abu sae kace hadin baki?) Abba kuwa yace sam be yadda ba dolene yayiwa 'ya'yansa jere gudun gori wataran.Musamman yayi ordering kayan gadaje da kujeru daga Dubai,Umma kuwa aka batta da bangaren kayan kitchen wanda idan kun tuna business dinta ne.

Ana saura kwana hudu asoma shagalin biki aka kai jere don dukansu ah Zariar zasu xauna.Agaskia an fidda su Fadima kunya,duk yadda ake yiwa wata 'yar gata kayan daki toh hakan aka yiwa su Fadima.

Ana gobe 'bridal shower' muka je saloon aka wanke mana kai tare da tsarawa gashin wata irin style meh dan karen kyau.Muna komowa gida kuma meh zanen fulawa tana nan tana jiran dawowarmu. Ta yayyara mana zanen fulawa masu shegen k'yau.Idan ka ganmu awannan lokacin kana iya tunanin cewar wasu 'yayan sarkin india ne sabida haduwarmu bazata iya kwatantuwa ba.

Ku biyoni don jin yadda Zata kasance ah babi na talatin da hudu (Shagalin biki)

*Hafnan's watsap group duk wacce take ra'ayin xuwa bikin su 'ya'yan justice tamin magana don akwai free bus to Zaria da aka turo,sannan kuma an bani anko kyauta wanda xan raba ga duk meh son xuwa... Lol sena jiku! Ni de zani don baza'a banni abaya ba,xani daukar rahoto.

    people are reading<SHIN SO DAYA NE? (Complete)>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click