《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER THIRTY TWO
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA TALATIN DA BIYU🌼
Page 147-152
**
Tun sanda Leedar ya labartawa mahaifinsa zancensa da Suhaima,se yake ganin kamar sam be kyautawa Fadimar ba,be kamata ace yaje kai tsaye kurum ya fallasa secret dinsu ba tare da ya nemi go ahead din ita Fadimar ba.Komai ya kwashe ya gayawa Dad dinsa don shi mutum ne da sam be iya karya ko kadan ba,zancen aljanu ne kawai ya boye masa.Hakik'a mahaifin nasa ko kadan beji dadin wannan al'amarin ba,kuma sosai yae masa fada na raina musu hankali da sukai.
Alhaji Ahmad mai daula kamar yadda ake kiransa,yasha mamaki sosai da Justice Sa'ad Mai Nasara yafi shi daukar zafi da wannan al'amarin sanda yaje masa da zancen,Sanin da yayiwa Justice Sa'ad mutum ne mai sanyin hali,haquri da kuma tawakkali,kuma yasan mutum ne da ko kadan baya amsar raini da wulaqanci,amma be taba tsammanin cewar wannan al'amari nasu Leedar ze zafeshi haka ba da har ya sanya ya yanke hukunci meh tsauri agame dasu ba.
Ce masa yayi"Toh idan har dan naka da gaske yake yana qaunar ita Suhaimar,toya gaggauta turo magabatansa ayi zancen aure,ita kuma Fadimar nasan maganinta,na baku nan da sati biyu cur! akawo gaisuwarta da kuma sadakinta atake,sannan wata daya na tsaida lokacin biki,babu ragi haka kuma babu k'ari don na tabbata kudi dae ba matsalarmu bace daga ni har kai balle ace sai an shirya....... "
Alhaji mai daula beyi wata gaddama ba,sabida sosae yake respecting din Justice Sa'ad kuma dama can da dadewa yana yiwa Leedar sha'awar auren daya daga cikin 'ya'yan Justice Sa'ad sabida sanin da yai na cewar tarbiyya da kuma sauran home training sun gama ratsa yaran,dalilin dayasa ya kasa yi masa gaddama kenan illa wani irin farin ciki da yaji ya ziyarceshi da jin wannan hukuncin na Justice.
Koda Alhaji mai daula ya labartawa Leedar zancensu da Justice,zuciyarsa tai farin ciki sosai amma kuma yanayinsa ta sauya zuwa yanayi na damuwa wanda har sae da mahaifinsa ya lura da hakan.
Cewa yayi"Son ya naga bakayi murna ba?ko dai ka kamu da son ita Fadimar ne kuma? "
Cike da damuwa yace"No Dad ba haka bane,kawai gani nayi yanzu ake maganar zuwana service,and again bani da aikin yi da har zanyi tunanin aure ahalin yanzu,ka tuna fa,idan na dauke Suhaima daga gaban iyayenta yanzu,zata komo karkashin ikona,kuma hakkinta zae sauka daga kan mahaifinta ya koma kaina,toh da meh kukeso na dunga ciyar da ita,shayar da ita,suturtata da dae sauransu bayan bana aikin komai?"
Murmushi yae na takaici,kana yace"Dad wat am simply trying to say is dat,am not ready for marriage now,kuyi hakuri ku d'an k'ara min lokaci har naje service,na kuma samu aiki,sannan itama alokacin ta kammala final year dinta,idan yaso sae muyi auren......."
Daddy ya d'an buga kafadarsa,kana yace"Son na fahimci bayananka kuma am very proud of you,amma abinda nake son ka gane shine,wannan shine last chance da justice ya bamu,kaga kuwa idan har muka sake mukayi wasa,toh tabbas zamuyi loosing and surely the game will be over,ba kai ba auren Suhaimar,kaga kuwa ka rasa ya kuma ka rasa kanwa..... "
"Kuma dukiyar da nake tarawa don su wa nake tarawar? ba don ku 'ya'yana ku amfana dashi bane? Don haka karka tada hankalinka akan da meh zaka dunga ciyar da ita,shayar da ita,suturtata da dai sauransu,Ni mahaifinka zan dauke maka wannan nauyin har zuwa lokacin da zaka sami aikin kanka,Zancen service dinka kuma kamar yadda nace,zan shige maka gaba har mu samu abarka anan garin,Shi kuma zancen aikinka,dama Justice yace idan ka gama karatunka ka kai masa credentials dinka Insha Allah ze taimaka maka ka samu aikin tunda field dinsa ka karanta wato 'LAW',ba fata nake ba amma idan hakan bata samu ba,zan baka daya daga cikin kamfanonina kayi maneji,Inda zaku zauna kuma zansa agyara part dinka amarya ta zauna anan tunda part din ba laifi yana da dan girma,idan yaso daga baya idan komai ya daidaita sae ku koma can gidana dake 'kofar gaya'.... yaka gani Son tsarin yayi maka?idan beyi ba ka gaya min yadda kake son ayi,idan kuma auren ne kwata-kwata bakaso ka fada min,don farin cikinku shine nawa farin cikin.......... "
Advertisement
Tabdi!wae kuji Daddy da wata magana,taya za'ai Haidar yaki Suhaimarsa?Taya za'ai gangar jiki yaki Ruhinsa?Taya za'ai su ruguza ranar da suka dad'e suna mafarki da tanadin zuwanta na su kasance da juna har abada? Daddy Haidar and Suhaima are born for each other,so nothing like baya qaunar auren.
Beyi wata-wata ba ya rungume mahaifinsa,kana ya fashe da kuka abin tausayi,yana meh jin wani irin sabon qaunar mahaifinsa na fizgarsa,yace"Daddy wallahi komai yayi daidai,Dad ban san da wasu irin kalmomi ya dace nayi amfani dasu wajen nuna godiyata agareka ba,Daddy nagode sosai da sosai,hakik'a kai uba na gari ne mai son ganin farin cikin 'ya'yansa akoda yaushe.... Father Allah yasa ka wanye da duniya lfy.... "
"Haba d'ana idan ban muku ba wah ze muku?
Ya cikashi daga rungumar da yae masa,kana ya dubeshi yace"Gaskiya babu idan aka cire sweet mother... Daddy zuwa dare insha Allah zanje na nemi gafarar Abban su Suhaima don gaskia hankalina atashe yake daka fada min cewar ya dauki zafi sosai akan Fadima,ni dai fatana Allah yasa kada ya yanke shawarar aura mata wanda bata so,infact my heart is telling me dat something is wrong,Fadima na cikin wani hali.... "
Shiru Daddy yayi,don da kamshin gaskia acikin zancen d'an nasa,shi kansa Justice be fada masa hukuncin da ze zartar akan Fadimar ba,kawai fada masa yayi cewar yasan maganinta.
Yace"Gaskiya ne son,ni kaina ina ji ajikina cewar something is wrong,fatana dai Allah yasa ba wani hukunci meh tsauri Justice ze yanke akan innocent child din ba,kayi kokari kaje ka dubo mana anjiman..... "
"Ok Dad insha Allah..... "
Sweet mother sosai tayi murna da wannan zancen,nan bada jimawa ba mafi soyuwar d'anta ze zama magidanci,ita kuma ta kusa samun sirika,dad'in dad'awa mah acikin gidan zasu zauna na dan wani lokaci kafin su tare ah kofar gaya.Haka mah Reedah,kusan zan iya cewa babu wanda ya kaita murna idan ka cire gogon naku,acewarta,'atlast burin love birds din na zama ma'aurata ya kusan cika'.Suhaima zata zamo matar wanta,zasu koma kiran junansu da sister inlaw,abangare daya kuwa,har wa yau suna nan as best of friends,k'awancensu ze dad'a yin karfi idan ta auri wanta.
Wannan kenan!!!!
***
Ita kuwa Ashwairiyyarku bata da masaniyar wainar da ake toyawa.Lol! sorry guys don't be mad at me,Ash queen nake nufi.Tayi wa garin Zaria nisa,suna kammala exams babu wani b'ata lokaci washegari tayi Abuja gun wata k'anwar babanta dake auren wani Soja,captain Abubakar Sani Bello.Tunda su kayi waya da Fadima ta sanar mata da ziyarar da Mubeen ya kawo Zaria,basu sake ba.
Yau Litinin,tun daren jiya take ta gwada layin Fadima amma sam yaki shiga har zuwa yammacin yau shiru kakeji.Sosae hankalinta ya daga don da wuya ka latso layin sahibar tata ka ji shi akashe.Abinci suke ci ita da 'yar Antinta wato Basma,wacce take kusan sa'anta.Shekara daya cur! Ash ta bata.
Basma ce ta lura sam kamar hankalin Ash baya jikinta,abincin da suke ci mah kusan zata iya buga kirji tace tafi Ash din ci.
Sake kai dubanta ga Ash tayi akaro na ba adadi wacce sai tsakurar abincin take kadan da kadan tana kaiwa baki kamar wacce akace dole sae taci.
Ahankali tace"Anty Aysha ya naga bakya cin abincin sosae? Kin kyaleni ni daya sai hadama nake tayi? ko wani abin ne ke damunki? "
Murmushin takaici Ash tayi,alokaci daya kuma ta saki ajiyar zuciya kana tace"Kin tuna da wannan kawar tawa da shekaranjiya kika gan picture dinta awayata?har kika ce tayi miki kina sonta? "
Advertisement
Da sauri Basma tace"Okay na ganeta,kina nufin wannan 'yar balarabiyar meh shegen k'yau kamar ita tayi kanta,gaya min wani abin ne ya sameta? "
Girgiza kai Ash tayi alamar "a'ah",kana tace"Hmmm! nima abinda nake tunani kenan,kila wani abin ne ya sameta don tun jiya da daddare nake ta trying layinta har zuwa wannan lokacin da nake maki magana wallahi yaki shiga,kuma da wuya ka k'ira layinta kaji akashe,koba wutar nepa toh kuwa generator nanan standby,so I dnt think rashin charge ne,kuma bana tsammanin cewar wayartace ta lalace...... "
"Toh kode sace wayar akayi ne? "acewar Basma.
Dan Jim Ash tayi,kana tace"Gaskiya bana tsammanin hakan,ni nasan gidan da Fadima take,idan har wayar lalacewa tayi ko kuwa sacewa akayi toh Insha Allah awannan ranar zata sake mallakar wata sabuwar waya,yarinyar da duk bayan wata biyar-biyar take canza waya,Ke! Sister jikina ya bani cewar something is wrong with Fateenah..... "
Ta fadi hakan alokacin da hawaye ya gangaro saman kumatunta.Sosai Basma ta tausaya mata kuma ta kara tabbatar da lallai akwai shak'uwar meh karfin gaske tsakanin Ash da Fadimar.Lallashinta ta shiga yi tare da karfafa mata gwiwa tana meh assuring dinta da cewar insha Allah everything is fine with Fadima.
Basma tace"Anty baki da lambar wani nata ne ki kira kiyi confirming? "
Tunawa tayi da cewar tana da lambar Ummun Fadima,ta rasa meyasa tunanin kiranta bezo mata aka ba.Da hanzari ta dauki wayarta,ta shiga searching 'Ummunah' kamar yadda tayi saving ah phonebook dinta. Tacewa Basma"Ina da lambar mum dinta,bari na kira..... "
**
Akalla an samu kusan awanni shidda kenan tunda Abba ya kira ya gaya min cewar bak'ona na nan tafe anjima kadan.Daga anjima kadan gashi har an share kusan awanni shidda,yanzu haka biyar da rabi na yamma ake nema,babu bak'on babu kuma dalilinsa,kuma Abba be k'ira yace mana gashi-gashi ba.
Zaune muke asaman gadon Umma ni da Suhaima,muna discussing kan wannan al'amari daya kunno kai.Can Umma tace"Wae ni 'yar Kareematu bak'on naki kodae ya fasa zuwa ne naga shidda har ta kusa babu alamunsa?"
Murmushi meh ciwo nayi nace"Yanzu Ummu Fadima kenan har Allah-Allah kike yazo din? "
Bata kai ga bani amsa ba,muka ji wayarta ta dau ruri tana nemar agaji.murmushi naga ta saki ayayin data kai duba kan screen din.
"Aysharki ce.... "Hakan ta furta.ta sake cewa"Watakila ta nemeki bata sameki ba kenan shine ta kira tanan.... "
Ina jin ta ambaci 'Ayshata' as the caller na mik'e zumbur ina meh farin ciki.Banyi wata-wata ba na kwace wayar ahannun Umma don na tabbatar this call is for me.Allah sarki! my Ayush she so much care about her Fadima Sa'ad.Nayi waje don amsa kiran masoyiyata don muna bukatar sirri.
Juyo Umma nayi tana fadin"Ni de banga dalilin da ze saka Abba seizing wayarki ba hadda wani karya sim cards,Abba ya dau abin nan da zafi,ni de ina jiye mishi aikin gaggauwa gudun dana sani mara amfani,don gaggawa daga shed'an ne.......... Kum... "
Ban tsaya na karashe jin abinda zata fada ba,don zata raba min hankali gida biyu,zanso na saurari maganarta ayayin da rabin hankalina ze tafi ga Ash ne.Shiyasa na wuce dakina straight.
"Hello Ashwairiyyata... " na fadi hakan ah sa'ilin dana baje saman gadona.'Ashwairiyya' shine sunan da mutane ke kiranta dashi wanda tun asali nice na saka mata sunan sabida tsananin kamar da suke musamman ta wurin kwayar idanu,mune muke yankewa da 'Ash'. (Yanzu kunji ta yadda akayi ta sami sunan Ash queen).
"Naam Fateenah are you okay at all? " haka naji ta fada cike da damuwa.
Dama meh neman kuka ne sae aka jefeshi da dunkulen kashin awaki,Kuka na sakar mata meh daga hankali.
Cike da tashin hankali naji tana fadin"Fateenah wats wrong with you? Wani abin ne ya sameki? "
Ban bata amsa ba sae mah kara volume din kukar da nayi.Ji nayi itama ta saki nata kukan tana fadin"I said it,wallahi dama ni jikina ya bani cewar my Fatee is not fine at all,don banga dalilin da ze saka ki kashe wayarki ba,idan kuwa har akwai dalili,then it must be a concrete reason for u switching ur phone har na yini guda abinda baki taba yi ba........... Fatee pls speak,fada min wats going on hankalina atashe yake...."
Dakyar na saida kukan ganin hankalin sahibata yafi nawa tashiwa. kwashe komai nayi na gaya mata ban rage gishiri koh kadan ba.
Da k'arfi naji tace"What???? Aure Fadima??? auren dole Abba ke shirin miki bada Mubeen ba??? Hadda seizing wayarki da karya sim cards???
Murmushin takaici nayi kana nace"Wallahi fa Sahiba...Ashwairiyya pls juz tell me am dreaming!! don Allah ki tayar dani daga wannan mummunar mafarkin....... " na fadi hakan tare da sakin wani sabon kukan.
Ji nayi tace"Amma gaskia Lee ko kadan be k'yauta mana ba,ai se ya bari har ki shigar da Mubeen ga Abba agama komae kafin ya bullo da wannan batun,don na tabbata da'ace sai da komai ya kankama ne Lee ya bullo da wannan al'amarin,Abba bazai wargaza zancenki da Mubeen ba sabida yasan darajar mutane,don haka bazai so ya wulaqanta Mubeen din ba,and again abin bazai wani zafeshi sosae ba tunda kin riga kinyi miji,gaskia Fateenah Lee ya lalata mana komai kuma wallahi zan kirashi na tsassage mashi,ai yasan halina Sarai kamar yunwar cikinsa nake............ "
Da sauri nace"No Ash don't be mad at innocent Lee,sam karki ga laifinsa,laifina ne don nice tun farko na kawo shawarar muyi playing Suhaima,don wasar tayi armashi ta yadda Suhaima zata hankalta se nayi gangancin introducing dinsa ga family dina wanda ashe mah mahaifina yasan mahaifinsa,ashe abokai suke,sae abun namu ya dada karfi,idan baki manta ba har Adamawa muka taba zuwa na nunawa dangi shi...Aysha mun rainawa iyayenmu wayau ba kadan ba,yanzu dawa gari ya waya?bada ni ba? don gashi yanzu su sunyi winning ayayin da ni kuma nayi losing,Abba yaki saurarata da batun Mubeen,haushinsa na biyu kuma akaina dayace na kawo masa wanda nakeso sae nayi burus da zancen,naki kai masa feedback,haushin hakan yasa ya hada laifukana ya yanke wannan hukunci meh tsauri agareni,Ashwairiyyata ina zan saka kaina? Wallahi ban shirya zaman aure da kowani da namiji ba idan ba Mubeen dina ba,gashi kuma tun daren jiya naketa trying layinsa don na fad'a masa abinda yake faruwa amma yaki shiga,Yayansa Mahmood kuma ban sani ba Koya gaya masa kamar yadda na bukaci ya kira ya fada masa,shine ni ban sani ba,yau inata saka ran ganin Mubeen amma shiru nake ji..... Kawata ur friend's life is gradually ruining.......... " na fadi hakan ina meh danne kukan da yake neman cin k'arfina.
Cike da tausayina tace"Sahiba ur life will never ruin sai dai mah the beginning of ur happiness Insha Allah,jikina na bani cewar wannan auran alheri ne agareki Fateenah.... Ni hutun nawa yama kare,zuwa Jumma'a zan diro Zaria......... "
Murmushin dole nayi kana nace"Ke kuwa dududu yau kwananki uku faah shine kike tunanin dawowa? "
"Yo! ba dole na dawo muyi sharing sorrows na wannan batun da babu dadin ji ba..... Ke yanzu ina gama waya zanje na sami Anty Aynarh na gaya mata ran Jumma'a zan koma Zaria,donma kada muyi karamar yaki ne da sae nace mata gobe-gobe zan wuto..."
Hohohoo! Ash d'ita akwai rigima,she will never changed,Dan muskutawa nayi nace"Ash ke dai wallahi anyi 'yar banzar 'ya anan,yanzu sae kiyi rigima da Anty Aynar sukutun akaina idan taki bari ki dawo? "
Dan dariya ta saki kana tace"Yo! toh meh za'a fasa? Mutuwa koh hisabi? "
Haka dai muka ta hira,wani muyi dariya wani kuma mu jinjina al'amarin.
Wannan kenan!!
***
Bayan Ash ta kare waya da Fadima,ta shiga labartawa Basma labarin rayuwar Fadimar da hukuncin da mahaifinta ya yanke ayanzu.
Cike da jimamin al'amarin tace"Allah sarki baiwar Allah,Allah yasa wannan aure ya zamo alherine ke jiranta aciki,amma gaskia na tausaya mata don rabuwa da masoyi babu dadi,Allah dai ya tabbatar mata da alherinsa tunda naji kince mahaifin nata idan ya kudura abu aransa tofa sai ya aikata,Ni dae idan bikinta ya tashi ki min waya wallahi zanzo,naji kince nan da wata daya,kinga kuwa kafin lokacin na gama exams dina har mah mun soma cin hutunmu.... " Basma na schooling ne ah Base university.
"Toh! naji uwar tsare-tsare.... tashi muje nayiwa Anty zancen tafiyar tawa.... "
Zaro idanuwa Basma tayi kana tace"Yanzu Anty Ashwairiyya tafiyar zakiyi da gaske?" Itama Basmar haka take kiran Aysha don sosae take kama da 'Ashwairiyya Rai' ta Bollywood.Zan barku da kissima kamanin aranku,don idan nace zan tsaya yi muku da kaina,ze iya cinye mana wannan chapter din.
Shek'ek'e Ash ta tsaya tana kallon Basma kana tace"Lallai yarinyar nan da alamu ke kinzo duniyar nan ne don wasa.... Fateenah sukutun ba lafiya sae na zauna anan ina jindadin hutu bayan ita tana can tana cikin sorrows? Inaa! wallahi kinma jawo wa kanki yarinya,kin sake tunzurani na bud'e wuta yau agidan nan don na samu abarni na tafi da yamman nan.... "
Ta fice daga dakin,Basma kuwa binta tayi tana rokonta don tasan halin Ash sarai zata mah iya tafiyarta ba tare da saninsu ba.Da kyar ta samu ta shawo kanta ta yarda cewar zata iya kaiwa Friday din adaddafe.Koda ta sami Anty Aynar da maganar,cewa tayi kawartace zatayi aure shine takeson ta koma.
"Allah ya kaimu.... "Kawai Anty Aynar ta iya cewa don tasan halin Ash sarai zasu iya yin rigima kamar yadda suka sabayi akoda yaushe idan tazo hutu,ta kuma nemi nan da nan ta koma,idan Anty Aynarh ta hana,sae Ash ta kunno musu wata 'yar k'aramar rigima ko kuma tayi wucewarta ba tare da saninsu ba.(Hahaha! Ash ina yinki,Hafnan here is ur fan)
Ai kuwa sae da Ash ta k'irawo Lee ta hau tsassage masa,azuciye yace"Wae don Allah malama ke mahaukaciyar ina ne?naji an lalata muku komae meh zaki iya yi? "
'Yar shewa tayi tace"Ai haka mah kace koh? Lee wallahi haduwarmu baza tayi kyau dakai ba,idona idonka first thing da zan soma shine daka tsalle na dalla maka mari,sauran rashin mutuncin kuma ze biyo bayan marin...."
wata tsawa ya doka mata"Get out! kiyi mah fiye da hakan...... " yana gama fadar hakan ya datse call din yana huci.Ash sam bata da hankali,ta fiye daukar komae da zafi.Toh shi meye laifinsa don ya fallasa komae?ai dama koba jima koba dade gaskiya zata bayyana kanta,kuma dama tun farko se daya nunawa ita Fadimar abinda zeje yazo idan har suka shigar da iyaye acikin wasan nasu,amma se ta turje akan lallai su saka iyaye sabida wasan nasu yayi armashi,ai ga irinta nan abinda yake gudar musu ya faru kuma akanta ya fada.Atake anan yaji tausayinta ya kama shi,ashe hukuncin aurar da ita ga wani Abbanta ya yanke mata? Ba zab'inta ba?.Dama so yake idan ya iddar da sallar isha'i yaje gidansu Fadimar.
Fitowarsa kenan daga masallaci,kai tsaye ya shige motarsa,ya tadata ya fice.Yaso biyawa gun Fresh ya masa rakiya,amma kuma sae yaga dacewar yaje shi daya.ba tare da wani b'ata lokaci ba ya nufi 'Nassarawa G.R.A',unguwarsu Fadimar kenan.
**
Ni da Suhaima mun yanke shawarar idan Abba ya dawo muje mu nemi gafararsa da kyau sannan na rokeshi da yayi haquri ya min sassauci,ya kyaleni na auri zab'ina.
Koda ya dawo,sae da muka tabbatar ya huta kuma ya kammala duk wani uzururrukansa sannan muka nufi 'main falo' inda anan ne muka jiyosu suna hira dasu Faruq.Muka shiga falon muna wasu 'yan kame-kame kamar wasu marasa gaskiya,hijabanmu sae jaah suke akasa kai kace koh wasu sababbin malaman islamiyyace aka dauka.(lol)
Umma tana ganinmu ta mik'e don barin falon,don dama can haka muka tsara da ita,idan muka shigo zata bamu gu muyi magana don kada yayi zargin da hadin bakinta aciki.Tasa kewar su Faruq tayi sukayi ciki.
"Abba barka da dare..... " muka fada tare da zubewa akasa kamar masu neman gafara.Yo! ai dama neman gafarar muka zo yi.
Shi kuwa kicin-kicin muka ga yayi don yasan abinda ke tafe damu.
Advertisement
- In Serial142 Chapters
Return of the Woodcutter
Aito Walker was a self-proclaimed martial artist, a criminal, a broken man, and a fishing slave who later became a woodcutter before dying due to his heavy consumption of alcohol.With thousands of other humans, he is forcefully revived into a boundless grey space by the gods of a foreign world, Iris, to take part in a never-ending war waged against Fearmongers. A race capable of corrupting living beings and inducing fear, even the bravest of warriors cannot resist—when the Fearmongers do not kill them, that is.To bait humans into this conflict, the gods offer the mortals powers in exchange of eternal servitude and the completion of trials before finally entering Iris.Even though Aito doesn’t agree with it, he sees in Iris a chance to atone for his past misdeeds, in this fantasy world of swords and magic filled with many races, where everything seems possible.He will pave his own path despite the gods he despises trying to manipulate him into doing their bidding.Aito will start with almost nothing but his wit, a peculiar system, and increased strength—much like other revived humans.Bearing a sin—he could not, cannot, and will not forget—haunting him to this day, Aito will strive to regain what little honor he has left.He will suffer and, at times, fail. Taking advantage of his weaknesses, the Fearmongers, demigods, gods, and many others will hinder his path.But a powerful yearning will keep him from falling apart. An ever-burning flame melting away the despair and welding back the broken pieces of courage.A single desire.«I will find redemption no matter the cost.»………Or not, hun, who knows? The book isn’t done yet. Haha—SLAP!«Who put this guy in the synopsis narration?! Get him out of here and launch the warnings! Now!»***WARNINGS:— The MC is human. If you’re looking for a perfect MC, you’ll only be wasting your time here. However, if you’re looking for an MC who will LEARN, GROW because of his flaws. An MC who will try his hardest to overcome adversity, then you’re in the right place.— No harems. However, it doesn’t mean the characters can’t fool around without having love interests. A relationship isn’t necessary for people to satisfy their physical desires.— You will find a few typos, grammatical and wording issues, that’s certain. I’ll do my best to bring you guys quality content and such issues will either be nonexistent or extremely few. However, one man can only do so much. If I get enough support, I’ll hire an EDITOR that will look at the chaps with a fresh eye. And POOF! Issues no more. Improved quality. Happier author and reader. Not sure if the editor will be happy tho.— The first three chapters are fast-paced as to quickly get into the nitty-gritty but slow down afterward to give the story the time it needs to progress accordingly.— The book can, never mind, it will contain «strong» language, gore and violence.— Comedy, as you know it (and if you don’t, now you know) is subjective. So you might not like the jokes.— If you truly read that until the end you have my virtual congratulations ‘cause I sure as hell wouldn’t have done that.
8 3235 - In Serial74 Chapters
My Blind Familiar
Familiar, a magical creature of any kind that a mage channels mana through to perform magic or tasks. Familiars are all different and each mage can have only 1 and it can only be summoned in Magic Academy due to the preparation for this being in these locations.The age that these students obtain this is when they start their second year in the magic academy. The first year was purely to teach the students how to gather mana and improve their capacity as well as to weed out those without talent for gathering mana. The entire year teaches the students breathing techniques, meditation and teaches the basis of how magic works. Our story starts with a young man that summons the most uncommon Demon, the imp or so called the Ash Golem. Hi ppl, new and very advanced story as well as one i will publish. I won't release many chapters of this one so it is more a teaser.
8 158 - In Serial7 Chapters
A Broken World [Rewrite]
In a world of floating islands of stone in the sky, where rivers flow through the air and defy gravity from one island to another, and ancient ruins can be found containing wonders beyond what can be produced by the lands current inhabitants- a millenia long war rages. In the distant past, beyond recorded history, when the crown of humanity's glory, the city of Uri, had stood whole against the enroaching demon swarms- even as hope seemed lost, a band of heroes, against all odds, managed to steal powerful magical knowledge from the demons. With the demon's forbidden knowledge, in the heart of Uri a new ritual was made. Called, "The Millenial Summoning," the ritual had the power to call a being from another world that would have the power to change the world forever. The first being summoned became known as "The Speaker," and he brought the power of the Gods to the world. With the blessings and power of the new priests, the unstoppable demon hordes were finally halted. A thousand years later, the ritual was used again and "The First Sorceress" was brought to the world. She brought the knowledge of advanced magics, and techniques to find and refine magical talent. With the magic power now added to the battlefield, the stalemate was broken. And for the first time, the demons were pushed back. Another thousand years later, and all of humanites hope for a final victory were dashed. Traitors slew the ritual's participants and took their places, and humanity quaked as The Demon King stepped into the world. His name, his nature, where he came from none of these are known, but what is known is his overwhelming power and his brilliant strategic leadership of the formerly formless hordes. Still, despite their position being even more dire than it has ever been since history has been recorded, humanity held on for another thousand years. Aided, thankfully, by The Demon King not taking the field after the first few years and battles. Now, the ritual is being cast again and a new hero is being summoned. In our world, after nearly three decades of study and hard work, Lucas Jaeger is making his dreams come true. With a double doctorate in both genetics and microbiology, as well as an associates degree in accounting, he has finally, after nearly driving himself mad from stress and sick from overwork, been able to put to together a presentation and ask for a business loan. His long time dream, earned by his own blood and sweat, to start his own commercial genetic company is finally coming to fruition. Lucas's car never left the banks parking lot and Lucas was never seen again in our world. This is a rewrite of "A Broken World." It is basically the same story, just a thousand times better and with decent length chapters!
8 189 - In Serial229 Chapters
Mana System - Hello, World! [Complete]
What would you do if your world collapsed and you had less than an hour to choose a suitable role that would allow you to survive? Would you give in to despair? Paul choose to fight for survival, now he has to face off against predatory animals, monsters, and even the land itself all modified by the Mana System. Eventually, he will have to face off against a foe even deadlier than the rest. Humans! I feel I need to add this disclaimer because some people really get their panties in a twist when they reach the second arc. This is not a grimdark story. Yes, there are portions that are dark and grim, including slavery which is why I have the traumatizing content box checked. If you can't stomach a little slavery and torture, probably best to find a different story to read. Complaining that you felt lied to isn't going to make me change my story. If this offends you, leave a review.
8 214 - In Serial18 Chapters
Class Systems
A random young man wakes up in a random new world rife with violence, magic, and power. Finding himself in a body that already has abilities, he has to learn to manage his rage if he wants to survive.
8 102 - In Serial7 Chapters
The Whispering Blade
In the blink of an eye, Ezra Nyx’s life changes forever. As an ordinary college student that only wants to get by, he he doesn't have high expectations of his future, but one night, he experiences something life-changing. He now knows something that no one else does, humanity is not alone. Unknown forces are finding their way to Earth, making it their little playground. Follow Ezra’s journey as he navigates through all the chaos and becomes more than he ever thought he could be.
8 203

