《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER THIRTY ONE
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
_This chapter is dedicated to all the Fatima Zahra's in the world,if ur name is Fatima,then diz page is for you.... Ina yinku the Fatima's... Haj.Nafeesah pinky araba kowa ta samu._
🌼BABI NA TALATIN DA DAYA🌼
Page 145-147
Tunda garin Allah ya waye Mubarak keta gwada layin Fadima amma still abu daya ake ta maimaita masa wato switched off.Adaddafe ya shirya ya tafi wurin aiki don zuwa yanzu ya gama aiyanawa aransa cewar lallai Zahran tasa bata lafiya because da wuya kaji wayar tata akashe balle ita da take d'iyar manya,koda kuwa an dauke wutar nepa ne toh generator nanan standby.
Zaune yake kan kujera acikin office dinsa duk ya kasa tabuka wani aikin kirki tunda yazo sabida wani irin kasala da kuma rashin kuzari da suka saukar masa ajiki,duk yabi yayi wani sukuku dashi kamar wani mara lafiya,Kuma duk tunanin Zahran tasa ce ya haifar masa da hakan.Daukar wayarsa naga yayi don sake gwada layinta ko wannan karon za'a ci sa'a ya shiga.
Maganar dai d'aya ce da ake ta maimaita masa wanda izuwa yanzu ya riga ya zame masa tamk'ar waka akunne wato 'switched off,please try again later'.Wani dogon tsaki naji ya saki uwa wani tsaka.
Afilli yace"Yah Salam!!... Wat the hell is going on?Anya zahrata tana lafiya kuwa? " Ya fadi hakan tare da watsa yatsun hannun damarsa aka,ya shiga yamutsa tattausan bak'in kashin kansa cike da damuwa daya bayyana k'arara asaman fuskarsa.
Dubansa yakai kan katon wall clock dake manne ah yammacin bangon office din. Karfe goma da rabi ta safiya yaga ake nema.Sake sakin tsaki yayi tare da b'ata rai,yace"Don wulaqanci dubi fa har karfe goma da rabi ake nema amma mutumin nan be iso ba,kuma shi yace 10:00am dot no african time,amma gashi shi ya shanya mutane kamar wasu kayan wanki........"
Bai gama rufe bakinsa ba,yaji anyi knocking kofar ofishin,ya bada izinin shigowa,wata 'yar matashiyar nurse ce ta shigo take sanar masa da isowar CMD,ta k'arashe da "Sir! he said dat the meeting will b holding any moment from now,don haka wai ku sameshi ah office dinsa... "
"Ok" kawai ya iya ce mata,ayayin data juya ta fice.Tashiwa yayi ya nufi wata k'aramar frizer dake office din.Budeta yayi ya ciro bottle water.Da hanzari ya balle murfinta,at once ya kafa baki ya hau shan ruwan non-stop,don sosai yake jin kishi,gashi komai be saka acikinsa ba tunda garin Allah ya waye,haka yazo office with an empty belly,sai yanzu daya bud'e baki da ruwa.
(lolx Zahranmu ashe an damu dake haka?pls you guys should compare,who is showing more care to her between the two brothers?)
Kut!kut!Kut!! Kawai kakeji,sautin da mak'ogoronsa ke badawa kenan ayayin da yake had'iyar ruwan,sai kuma k'arar sautin iskan da wata standing fan ke badawa itama.Sai da ruwan ya rage kadan sannan ya haqura don jin cewar he's satisfied,kan frizer din ya ajje gorar don ba wani ruwan Kirki ne ya rage aciki ba balle ya maida fridge.
Waje yayi don amsa kiran oga kwata-kwata,the chief medical director(CMD) wato Dr.Shamsudden Garba Audi wanda mutane sukayi wa lakab'i da 'Dan Aljannah' sabida shi dattijon kirki ne na sahun farko kuwa,meh kuma taimakon al'umma,wallahi ko baka da kudi idan har kazo asibitin yana nan,toh kuwa k'yauta ze sa amaka treatment,haka ze dauki lokaci na musamman,ya zagaya duka wards din asibitin,zebi gadajen marasa lafiya daya bayan daya yana Kara duba lafiyarsu tare da tambayarsu inda ke musu ciwo cikin fara'a da wasanni dasu,akarshe yai musu k'yauta kafin ya tafi musamman ga mabukatan.Dalilin daya sa kowa ke qaunarsa kenan,suke kuma k'iransa da d'an Aljannah.Tunda Mubarak ya soma aiki ah asibitin ya lura Mubarak din kamar zeyi koyi da kyawawan halayyarsa don ya lura akwai shi da tausayi da kuma hazaka wurin aiki,dalilin daya saka ya jawoshi ajiki kenan,sosai yake jinsa arai tamk'ar dan daya haifa gashi be taba haihuwa b,amma kuma duk da yana babban likita gashi be iya magance ma kansa wannan matsalar ba,duk iya yinsa shi dai yaga lafiyarsa qalau haka ma duka cells dinsa ya nuna qalau suke,haka matarsa mah qalau take,haihuwarce de bata zo musu ba, haka de ya haqura tare da cigaba da kaiwa rabbis-samawati kukanshi,ya sanya aransa cewar haihuwar daga Allah take,idan har da rabon ze ga kwansa aduniya toh zefi kowa murna, idan kuwa babu rabo,toh Allah ya bashi nashi rabon gobe kiyama.
Advertisement
Mubeen shi de har zuwa yau be wani sake jiki dashi ba,Mubarak wani irin bahagon mutum ne mai dan wuyar sha'ani,bashi da saurin sabo da mutum,he hardly trust,ko kadan bashi da yadda ga wani bare,ba ruwansa ne da kowa sai family dinsa,don ko abokin kirki bashi da idan ka cire Bilal wanda shima din abokin fatar baki ne kawai.
(Lol buh Fadima has really changed Mubeen,ya zama mai yawan son fira da fadace fadace akanta.... #teamFadimaSa'ad# can you indicate by saying 'HY' for me to notice you?)
Abinda shi de ya sani,kawai yasan yana son Dr.Shamsu kuma sosai yake tausaya masa na rashin samun haihuwa,amma ko kadan baya shige masa kamar yadda shi Dr.Shamsun ke jawoshi ajiki.'Yan asibitin mah ce masa suke 'Yaron dan Aljannah' sabida yadda shima yake behaving juz lyk Dr. Shamsun,da kuma lura da sukayi da yadda Dr.Shamsun ke mugun ji dashi akan sauran likitocin,sun gane cewar he is juz he's favourite Doctor among all.
Meeting ne daya kamata yayi holding karfe goma daidai kamar yadda Dr.Shamsu ya tsara,amma daya shigo asibitin,sai yaga ya dace ya dan baiwa mutanensa koda dan 30mins ne daga cikin lokacinsa,toh azagaye-zagayensa ne ya gano wani dan karamin yaro mai kimanin shekaru goma sha biyu yana fama da ciwon ciki ta appendix,an bashi gado kuma iyayen basu gama hada kudin da za'a masa aiki ba,sunfi karfin sati uku acikin asibitin ba tare da sanin Dr.Shamsu ba don kam ya kwana biu beyi zagayensa ba sabida tafiyar da yayi.Hakik'a beji dadin wannan al'amari ba,ya tabbatar musu da su shirya aranar za'a masa aiki kyauta,sosai sukai murna tare da rakashi da kwando-kwandon godiya,toh dalilin daya sanya ya dan makara kenan shine Mubeen keta masifa shi daya.
Meeting ne da Dr.Shamsu ya shirya musu tare da abokan tafiyar nasa,su uku ne,shi,Dr.James,sannan Dr.Vera....Orientation ne yake son ya musu agame da course din da za'a turasu yi akasar Indiar.Tafiyar tasu gobe ce,komai na bangaren visa an riga an gama musu processing,don haka 4pm flight zasu bi.
Ahankali ya tura kofar ofishin ya shiga,idanuwansa ya sauka fes akan mutanen ciki,duk abokan tafiyar nasa sun rigashi zuwa,ashe shi kadai ake jira,sai kuma CMD daya hakimce kan wani kujera yana mai jin wani irin farin ciki na ratsashi na ganin favourite dinsa,sai kuma medical director (MD) wato Dr.Abdullahi da wasu likitoci biyu manya.Gaidasu yayi sannan ya nemi wuri ya zauna kusa da 'yan'uwanshi.
Cike da qauna,Dr.Shamsu ya dubi Mubeen wanda ya saddar da kansa k'asa yana kokarin son fadawa kogin tunanin Fadima,ji yayi Dr.Shamsu ya katse masa wannan hanzarin.
Yace"Son yi haquri don Allah an fada min cewar tun dazu kake ta sintirin zuwa nan don dubawa kona iso,ka gafarceni,Ina isowa sai naga dacewar na dan arawa mutane koda 30mins ne tunda na kwan biu ban zaga naga lafiyarsu ba,,dat is the reason why am late.... Agafarce Dad.... "
Dan muskutawa yayi yace"Its nothing sir! Karka damu ba wani abu bane kuma ni raina bema b'ace ba... " (Haha Mubeen fadi gaskia dai)
Ga dukkan alamu zancensa yai wa ogan nasa dad'i,don fadada fara'arsa naga yayi,yace"okay thanks for understanding my son."
Alokaci d'aya kuma naga ya dauke fara'ar tasa tare da tattaro dukkan nutsuwarsa,kana ganin yanayin fuskarsa kasan zance ne yake shirin shigowa da ita mai matuk'ar muhimmanci wanda kuma dalilin taruwar nasu kenan.
Yace"Ina fatar ba sai na sake maimaita dalilin wannan taruwar tamu ba don kowa nan ya fini sani musamman matafiyan.....And am very sorry da wannan tafiyar gaggawar da aka matso muku dashi kusa,don Allah muna son ku mana uzuri.... " Amsawa sukayi da "No worries sir."
Advertisement
Dakatawa yayi,can ya cigaba"Dr.Mubarak,Dr.James and Dr.Vera,kamar yadda kuka sani dai wannan karon sunayenku ne suka fada cikin wayenda muke son turasu 6months course,wannan karon kuwa,kyautar da za'a muku ya banbanta dana sauran,kuma ya ninka nasu,gwamnati zata ninka albashinku times 2,sannan kuma there will be a large share dat will be awaiting u guys,ciki kuwa hadda karin matsayi da za'a muku,infact! wani abin mah sai kun dawo tukun..........."
Tafi suka dauka cike da murna Banda Mubeen da shi de baze iya cewa yana murna ko akasinta ba,gashi nan dai yayi wani sukuku dashi.Yanzu ya fahimci dalilin daya sanya aka nace sai yaje,wato akwai rabon da ze samu sosai idan har yaje wannan course din da ake son turasu,dats why CMD ya saka sunansa,atake anan yaji mutumin ya sake samun wani matsayi acikin zuciyarsa.
Dr.Shamsu ya cigaba"Abinda kawai mukeso daga gareku shine,don Allah ku maida hankali sosai kan abinda zakuje yi,I know u three so very much,kuna da kokari,fahimta da kuma hazaka musamman kai Mubarak,akwaika da jajircewa wajen aiki,so am pleading with u guys to please make us proud.... Za'a turaku kasar India ne don k'aro ilimi akan two different courses of different field of study.. "
"Renal medicine/Nephrology shine farkon course din da zaku soma studying for the first 3months,Nephrology kamar yadda kuka sani is the study of 'kidney',atakaice dai zaku karanci komai daya shafi bangaren kod'a....'Gastroenterology' wanda field ne na bangaren daya shafi 'digestive system' and its 'disorders',shi kuma zakuyi studying dinsa acikin sauran wata ukun da suka rage,duka-duka ya tashi 6months kenan... "
Haka de Dr.Shamsu yayi ta masu orientation tare da k'ara enlighten dinsu kan wannan courses din cikin k'warewarsa,yana mai dada nuna musu yadda ake matuk'ar bukatarsu da suje karo ilimi abangarorin field din daya lissafo.
***
Yadda naga rana,toh haka kuwa naga dare,kusan zan iya cewa koh gyangyad'awa banyi ba.Kwana nayi ina abu daya wato kuka da kuma nafilfili,ina meh kai kukana ga rabbis-samawati,don shi Al-gafur Al-rahim ne,shi kadai ne nake ganin ze iya share min hawaye ahalin da nake ciki ayanzu.Bana jin zan iya rayuwa koda na minti daya ne ba tare da Mubeen dina ba.Wani abin mamaki shine,ban san meyasa nake jin haushin Engr.Mahmood ba,gani nake kamar be damu da halin da nake ciki ba,don aganina yaci ace tun jiya da daddaren nan yazo ya tayani jaje.Yo! Jaje ya kamata nace mana donni dai ji nake kamar mutuwa aka min,ko kuma nace ana neman kaini early grave na karfi da yaji because nasan nan bada jimawa ba zuciyata zata buga sabida bakin cikin wannan al'amarin.Tun daran jiya nayi ta saka ran ganin zuwan wani acikin kannena yace min ai wani na sallama dani akofar gida,amma har zuwa safiyar yau da nake magana ayanzu shiru kakeji.Ashe dama munafukar kulawace yake nuna min?
(No Fadima pls don't underestimate the young guy... Ni nasan cewar Engr.na cikin wani hali wanda yafi naki ahalin yanzu,Koya kukace #teamEngrMahmood#?)
Ni de Addu'ata daya Allah yasa ya sanarwa Mubeen dina.Daga yau zan soma saka idanuwa akan hanya,zan jira yazo don mu san abin yi kafin ya wuce India.(Lol ayya Fadima ta manta mahaifinta ya haneta da fita ganin wani & am so sorry my dear washegari Mubeen ze daga kasar India not nan da sati biyun da kika sani again).
Zaune nake saman darduma,na iddar da sallar walaha,ina jan carbi naji an shigo dakin nawa da sallama.
Ahankali na juya don son ganin wanda ya shigo,sosai wuyar ke min ciwo,dakyar nake iya juyata,kai kace ko ciwon sankarau ne ya kamani.Dalilin langwabe-langwaben kan da nake tayi adaren jiya ne ya haifar min da ciwon wuyar.
Ummu Fadima itace ta shigo,gani nayi ta nufo inda nake da sauri-sauri da waya kange akunnenta.
"Eh! gata nan...... " haka naji ta fada,kafin nayi tunanin wanda take waya dashi naga kawai ta miko min wayar tata.
Kallo kawai na bita dashi ina meh son ta min bayanin wanda ke son magana dani.
Kamar kuwa tasan abinda nake jira kenan,naji tace"Abbanki ne ke son magana dake..... " gabana ne naji ya yanke ya fadi,tsoro ya sake cika min zuciya don ban san meh kuma ze ce min ba.
"Karbi wayar man kin tsaya kina kallona... " acewar Ummu Fadima cikin dan tsawa.
Da sauri na karbi wayar na makaleta akunne,cike da fargaba na furta"Hello..... "
Da sauri naji ya tari numfashina kamar dama jira yake yaji muryata,yace"Saurareni da kyau... Zuwa anjima kadan zakiyi bako kuma wallahi karki sake naji ance kin masa wulaqanci don zaki gamu da mugun b'acin raina kinji dai na gaya miki......"
cike da rashin fahimta nace"Abba wani bako kenan? "
"Ya wuce wanda ze aureki?kinji de na gaya miki walhi kika sake kika masa wulaqanci idan na dawo zamu saka wando kafa daya nida ke.... "
Be jira yaji ta cewata ba yayi saurin yanke call din.Mik'awa Umma wayarta nayi ta karba,banyi wata-wata ba na saki kuka mai daga hankali.
Da hanzari na tashi na rungumi Umma ina fadin"Ummu Fadima why me?why is Abba trying to punish me in diz way? Umma don Allah kiyi wani abu akai wallahi ni Mubeen kawai nakeso,kice wa Abba yayi hakuri ya aura min shi...... "
Lallashi da ban baki ta dunga bani,ashe ban lura ba itama din hawaye take na tausayina,kuma na tabbatar taji komai da Abba ya fada don wayar ah loudspeaker take.
The question is,who is he?meyasa kuma Abba ke neman ruguza farin cikin 'yarsa akanshi? Na kudurta araina cewar idan har ya sake aka aura masa ni toh kuwa babu wani zaman lafiyar da zamuyi daga ni har shi,zai gwammace mutuwarsa akan aurena.
(lol ran mata ya b'aci... Fadima meh zaki yi? ")
***
Sai bayan kusan awa daya da rabi Mubeen suka kammala meeting dinsu,Dr.Shamsu ya sallami kowa,suka mimmik'e zasu fita har Mubeen.
Da hanzari Dr.Shamsu ya kada baki yace"Son! stay back,I want to have a talk with you.... "
Mubeen ya tsaya cak! Kamar babyn robar da ake controlling,sannu ahankali ya koma da baya,cike da kasaita irinta classic doctors da kuka sani yake tafiya har ya karasa inda CMD ke zaune.
"Hav a sit.... "acewar Dr.Shamsu.
Be musa ba,ya nemi kusa dashi ya zauna kamar yadda ya umarta.Sosai Dr.Shamsu ya shiga nazarin yanayin Mubeen,ahankali yace"Son wats wrong with you?tun dazu na lura da yanayinka,kamar wani abu na damunka don zan mah iya cewa kusan rabin hankalinka baya tare damu,tell me meyake damunka son? Kode tafiyar ce bakaso ayi dakai? "
Kamar yace masa "a'ah" amma sai ya sami kansa da cewa"No Dad ina so... "
Sosai Dr.Shamsu ke jindadi idan Mubeen ya kirashi da Daddy.
Yace"Toh kode sabida lalurar matarkace shiyasa baka son kayi nesa da ita? "
Nan mah "a'ah" yace.
Cike da damuwa yace"Toh fada min meke damunka?" Ganin Dr.Shamsu ya damu sosai ne yasa Mubeen dan murmusawa yace"Wallahi dad babu abinda ke damuna,kasan wani sa'in mood kan canza,kaji kawai baka son yin fira ko walwala,infact to make it short,am already missing my family including you Dad!"
Sosai suka shiga kyakyata dariya dukansu,kuma idan Dr.Shamsu yace beji dadin kalaman Mubarak din ba,toh kuwa yayiwa Allah karya.Dr.Shamsu ya nemi alfarma wai Mubeen ya taimaka ya saka hannu ayiwa wannan yaron meh appendix aiki bayan sallar azuhur,wannan ya zama aikinsa na k'arshe kenan har sai ya dawo.Mubeen ji yayi kamar an aza masa katon tsauni ne aka,Dr.Shamsu ya sake rusa masa plan akaro na biyu,don so yayi ace ana gama wannan meeting din ya kama hanyar Zaria,amma gashi yanzu ya bashi wani aikin wanda baya jin ze iya musa masa sabida nauyinsa da yake ji.
Bashi da option din daya wuce ya karbi aikin da ogan nasa ya sakashi.Cikin rashin kuzari ya mike ya wuce office dinsa.Wani irin azababben ciwon kai yai masa sallama,ga wani irin ciwon ciki daya tasan masa,kuuuuuu! kake ji cikinsa ya rud'e alamun yana matukar bukatar toilet.Babu bata lokaci ya nufi toilet dake cikin office dinsa.Gudawa ce ta kamashi,yana fitowa duk yaji jikinsa ya mutu (lol ba dole ba,zawo wasa ne?).Tunawa yayi da cewar tun abincin jiya ke cikinsa,beci komai ba tunda garin Allah ya waye idan ka cire ruwan daya sha,gashi ana neman sha biyu beyi breakfast ba.
Ahankali yaja jiki zuwa inda flask dinsa yake wanda mint green tea ne ke ciki wanda baiwar Allah Hanan ta lallab'a ta dafa masa ganin yana sonsa sosai.Kadan ya zuba ah mug,sugari mah kadan ya zuba,sannan ya dan yanko banana bread dinsa wanda tasha lullubi da soyayyan kwai.Aikin Hanan kenan,idan har Mubeen yaki tsayawa yin breakfast agida,toh kuwa bazata taba barinsa ya fito hakanan ba sai ta hadosa da flask din abinci.Bayan ya gama cin abincinsa,ya ballo Maganin ciwon kai dana tsaida zawo yasha.Da hanzari ya dauki wayarsa ya sake latso layin Fadima amma still switched off aka ce masa.Kallon agogo yayi,yaga sha biu da mintuna goma,yaushe yaje Zaria har ya dawo kafin bayan azuhur da ze shiga aiki? Wani tunani ne ya fado masa arai,da sauri ya latso Engr.
********
Engr.dake aiki ah office dinsa yaga call din Mubeen ya shigo,dama yasan hakan zata faru,dole idan Mubeen be samu Fadima awaya ba toh tabbas ze nemeshi.Cike da faduwar gaba yayi picking.
Bayan dan gaishe-gaishe,Engr.yace"Brother ya naji muryarka somehow? Wats wrong?
Saukar da ajiyar zuciya Mubarak yayi,kana yace"Brother tun daren jiya nake ta trying duka layunka Fadima amma har yanzu am not getting her,bro am worried kada de wani abin ne ya sameta don wannan al'amarin yafi k'arfin ace rashin chargy ce....don mah zanyi wani aiki ne yanzu dana shigo Zariar,amma ina gamawa zan daure na shigo komen dare na dubota..... "
Gaban Engr.ne ya tsananta faduwar gaba,dabarun da Allah ya bashi yayi amfani dashi wajen convincing Mubeen,yace"Haba bro karka damu tunda ka turomun lambarta naje gidansu sau daya muka gaisa,so don't worry I promise you anjima zanje na dubo maka ita ba sai kazo ba,juz concentrate on ur work,will hala u wen I get there.. "
Cike da farin ciki Mubeen yace"Thank you lovly bro,amma fa ka sani idan har da kwai wata matsala,tofa zanyi kokari na shigo gobe kafin na tafi,kai if possible zan iya fasa tafiyar mah..... "
"No bro dena fadin hakan,insha Allah I pray dat everything is fine with her,later zan kiraka idan na isa.... "
Daga haka sukayi sallama.
*****
Koda Mubeen ya fito daga dakin theater,fever mai zafin gaske yaji yana neman rufeshi,tun adakin yake tajin signs dinsa amma daurewa kawai yake tayi.Atakaice dai sai daya karbi allurai kusan uku atake don ya tareshi da wuri kafin gobe.Adaddafe ya isa gida,Hanan ta rasa inda zata saka kanta taji dadi,miji ba lafiya.
Kuka ta saka masa tace"Abu Jasmin dina kodai zaka fasa tafiyar nan ne tunda baka da lafiya?" Rungumota jikinsa yayi yana lallashinta"No Hanan d'ita bazan iya watsawa Dad kasa ah ido ba,don't worry insha Allah kafin gobe I will be fine kinji matata? " (yana nufin Dr.Shamsu)
"Ok mijin Hauwa'u Allah ya baka lafiya... " ya amsa da Ameen.
Advertisement
White Queen Ascending
She was abandoned by her family and sold as a slave. She was forced to kill her fellow children inside a cage while being watched by nobles as an entertainment. She has grown into a beautiful flower filled with thorns. She promised herself that someday, she'll rise and ascend to the top. But, is she a fated person or a cursed one?
8 122Neither Snow Nor Rain
Humanity is impotent, no magic can be found in their blood. The hordes of Beasts lack no such problem and wields magic as one would breath. Fortunately for Humanity, though they lack in the spirit, they are adaptable and resilient, because of course... magic isnt the only way to kill a man. This will be a story of betrayal and love. A tale of the most pious kings and of rightous revolution. The world isnt as it seems and the old order is collapsing. What was once buried, will come to the top for the whole world to see.
8 202seventeenth entry | daragon
❝ journal entries to ease her heart. ❞I wrote this when I was a lot younger and I am thinking of re-doing it because it was kind of clichè. REWRITING THIS SOON. Thank you for all the love!
8 2391855 American Tycoon
1855, this is the best era, the extended railway, the roaring locomotive, the flowing gold casts the towering tower of the sky; this is the worst era, in the dark shadow of the tower, the north, and the south are opposite. , the disparity between the rich and the poor, the strong prey on the weak. If you don't want to stay in the shadow of the Babel Tower and let others trample on it, you must climb to the top of its brilliant tower and trample everything under your feet. In this world full of noise and turmoil, conspiracy and deception, light and darkness In the Gilded Age, see how a traveler who is familiar with history will turn the tide and create an era of his own.
8 197Labyrinth of Anchored Moments
While dreaming, a hard working family man is approached by a child-like god that has become bored of their custom created gaming world. Allowing the man to choose whatever 'Class' he wants, he chooses to become a 'Time Wizard'. He's dropped off in a city above a labyrinth with only this directive. "You just have to play my game, which is styled after your world’s dungeon exploration RPGs, level up, and save the world. Or don’t. I don’t care."
8 129As They Rise (The Eva Series #1)
A Wattpad Featured story. As seen on The Huffington Post. Book One of The Eva Series, which has over 3M combined reads!A kick-ass young girl, a nation swarming with zombies, and a sweet romance that grows amongst the ruins. You'll find all that and more in this exciting and action-packed apocalyptic YA story. Readers have said it's had them on the edge of their seats, reading all through the night and still craving more.Eva was just an everyday girl, working as a waitress, hanging out with her friends, and falling in love. But her whole world changed overnight when a powerful virus spread throughout the country, transforming it into a wasteland of deadly disease and crazed zombies. With Australia cut off from the rest of the world and rampant with terror and chaos, Eva and her friends must do whatever they can to survive.Set in Australia, blood, gore, friendship and true love collide to make this tale of survival stand out from the rest. The Eva Series is guaranteed to make you smile, scream, cry and fist-pump the air as you go on a wild and dangerous ride with Eva and her friends. And it all starts here, as they rise. Are you ready? Hit the Start Reading button and get ready for a heart-thumping adventure.Previously titled 'Eva Wilde Vs The Zombie Apocalypse.'AS THEY RISE is the first in a series of books following her dangerous journey as Australia becomes an apocalyptic island.THE EVA SERIES:Book One: AS THEY RISEBook Two: WHILE WE FALLBook Three: BEFORE IT FADES**Please note: This is the first draft. Please excuse any typos or grammatical errors. I've just done a big re-write, edit and expansion of this, and it's now available on Amazon Kindle, iBooks, Kobo, Nook + Google Play here: jenmariewilde.com/books**Tweet me: @JenMarieWilde / #TheEvaSeries(Completed 01/01/2013)
8 89