《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER TWENTY NINE
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA ASHIRIN DA TARA🌼
_*Zuwan Dr.Mubarak Zaria*_
Page 135-140
Sai kusan karfe biyu da rabi kafin Mubeen ya kammala ayyukan gabansa,sai daya tabbatar babu wani sauran aiki sannan yaje ya nemi izinin tafiya gida wajen ogan nasu.
Yana barin office din,Dr.Abdullahi yace"Sai shegen daukar excuses kamar shi yafi kowa tarin matsaloli,sai kace akan matarsa aka soma laulayin ciki..... " Shifa duk aganinsa wannan excuse din daya dauka sabida Hanan ne.
Gida ya nufa don shiryawa zuwa Zaria. Ahanya ya tsaya ya siyawa Hanan dinsa gasasshiyar kaza,sannan ya hado mata kayan dangin itatuwa wanda ciki hadda goban da take so.
Afalo ya tarar da Goggo Ladidi har ta riga da ta iso,da Kuma Labeebah,hatta Hanan tana zaune cikinsu ana hira da ita,ga dukkan alamu jikin da d'an sauki sabida yadda ta zage take hira dasu,hakan kuwa ba k'aramin dadi yai wa Mubeen ba,don burinsa akoda yaushe bai wuci yaga Hauwansa cikin farin ciki da annashuwa ba,shi kansa ba'a son ransa yake kuntata mata akan Zahra ba.Cikin jikinta mah ji yake tamkar ya maido dashi jikinsa shi ya cigaba da laulayin ita kuma ta huta.Russunawa yayi yana gaida Goggo.
Yace"Sannu Goggo! har an iso? "
"Eh! Mubarak sannu da dawowa ya aiki?"
"Aiki alhamdulillahi Goggo!...... An yini lafiya?"
Tace"Lafiya qalau..... Ya mai jiki? "
"Jiki Alhamdulillahi tunda gashi naga ai ta ware har ta sami bakin hira daku.... " Ya fadi hakan tare da kashe mata ido daya.Ita kuwa shagwab'e masa fuska tayi adole wai ita tayi fushi tunda har yake tsokanarta.
Goggo tace"Yo! ba dole ta samu bakin magana kuma taji kwarin jiki ba,taya za'ai ace mutum yaji karfin jikinsa alhalin baya cin tuwo sai kayan kwalama..... Ai saida na tsaya na tuka mata tuwon masara wanda yaji kanwa kuwa da miyan kuka wanda yaji daddawa kafin nazo,yanzun nan tama gama ci shine ta sami bakin hiran....... "
Dariya sosai aka saki don kam Goggo Ladidi akwai ta da son barkwanci.
"Sis kina nan har yanzu baki tafi ba? "
Labeebah tace"Yace sai zuwa dare zaizo ya d'aukeni... "
"Madallah an gode" ya fadi ah sa'ilin daya mike yana mik'a mata ledar daya shigo da ita,yace"Ungo nan fruits ce aciki,karbi kije ki wanko muku.... Akwai gasasshiyar kaza aciki,ita kuma ki juye akan plate ki kawowa babyna......"
Goggo Ladidi tayi kwafa tace"Kuji min rashin kunya irinta 'ya'yan zamani,ba ko kunya kake kiranta baby agabana? "
Dariya akai,yace"Kai Goggo! nifa d'ana dake cikinta nake nufi..... "
"Tafi can ja'irin yaro kawai ni zaka saka akwana.?"
Sosai ake ta k'yak'yata dariya.Gani nayi Hanan tana k'ok'arin son ta mik'e tana d'an ciccije leb'enta.
"Meya faru? Ina zaki? Ina ke miki ciwo kuma?" Mubeen ya jero mata tambayoyi alokaci guda cikin kuma tashin hankali.
"Jakar hannunka nakeson na k'arba... " ta fada cikin sanyin murya.
"A'ah zauna abinki na hutasheka ko baki ga baki da lafiya bane? "
Bata bashi amsa ba ta nufi inda yake,sam bata lura da kafafuwan Goggo dake mike akasa ba,kawai taji taci karo dasu,ai kuwa tayi tangal-tangal zata fadi,da sauri Mubeen ya tarota ta fado jikinsa.
Goggo tace"Ai kinga irinta kenan!.... ana ce miki ki zauna ba wani isasshiyar lafiya gareki ba amma dayake shegen son miji ya rufe miki ido dole kiyi gardama...... "
"Kai Goggo! wannan fa duk cikin tips din kula da mijine fa... " acewar Labeebah
Goggo ta juyo gareta tana fadin"Ai kuwa tana da aiki sosai agabanta don namiji dai da take gani ba dan goyo bane...... "
Advertisement
Hanan dai karban jakar hannunsa tayi ta wuce dakinsa ayayin daya biyo bayanta.
Azuciyarta tace"Maganarki gaskiya ce Goggo!.... Sam d'a namiji ba d'an goyo bane haka kuma ba kanwar lasa bane......"
ji tayi ya rungumota ta baya yana fadin"Hauwa'unah mace ta gari... Allah yai miki albarka matata.... "
Ahankali ta furta"Ameen mijina.... Bari na hada maka ruwan wanka,idan ka fito sai kaci abinci ko?"
Da sauri yace"A'ah babyna jeki kici kazarki zan hada ruwan da kaina...... hadda gobar mah na samo miki ita..... "
Cike da farin ciki ta juya ta fuskanceshi tare da kankamesa da kyau tace"Nagode mijin Hauwa'u Allah yabar min kai..... "
"Ameen matata" ya fadi hakan ah sa'ilin daya kai hannu ya shafo cikin nata,dukawa yayi ya soma magana da cikin"Babyna pls ka daina wahalar min da matata abar qaunata hakanan.... Pls stop suffering ur sweet mother okay? " yakai wa cikin peck.
Ita dai Hanan babu abinda takeyi illa murmushi na shirmen Mubeen,shirmen da yakeyi kenan akoda yaushe yata magana shi daya da cikinta.
"Deserved tuwon da Goggo ta kawo zakaci ko kuwa jollof rice da sister ta girka?"
"Tuwon zaki kawo min don nima naci nayi k'arfi kamar yadda Goggo ta fadi..... " Dariya sosai sukai sannan ta fice don deb'o masa abinci ayayin da shi kuma ya tub'e ya shige wanka.
Yana fitowa yayi Zaman cin abinci wanda tuni Hanan ta kawo ta ijje masa sannan ta koma wajensu Goggo.Dama ya riga yayi sallar Azuhur ah masallacin asibitin kafin ya taho,don haka ya hau cin tuwon hankali kwance,sai zuba santi yake don agaskiya miyan kukar taji daddawa da busasshen kifi (Lol waya ga su Mubeen dan gaye da cin tuwo miyan kuka).
Yana gama cin abincin yaji an soma kiraye-kirayen sallar la'asar.Tashiwa yayi yaje ya dauro alwala sannan yazo ya sauke farali.Da hanzari ya soma shiryawa cikin wata dakakkiyar australian gezna shadda fara kal,surfaninta baki,rigar tazarce ne, kayan sunsha guga har wani kyalli suke badawa.Ya kafa hularsa baka tare da sanya takalminsa bakake.
Subhanallah! Karku so kuga yadda mijin Hauwa'u yayi dan banzar kyau,abinka da bak'in mutum sai kayan suka haskakashi ba kad'an ba.
(Ni kaina Hafnan sai dana kyasta wannan wankan tasa).
Hanan ce ta shigo dakin don dubawa koya kammala cin abincin?.Ganin kwalliyar daya sha ne ya sanya gabanta faduwa.Sakin baki tayi ta bishi da kallo kamar wata wawiya.
"Matar Mubeen nayi k'yau ko? " Ya fadi hakan ah sa'ilin da yake saka agogonsa ta luxury ah hannun hagunsa.
"Mugun kyau mah kuwa..... Ina zuwa haka da kaci wannan uban gayun mai zafi haka? " ta fada cike da kishi.
Rasa mai zai fada mata yayi,can yace"Wani abokina ne ke aure,jiya ban samu zuwa daurin auran ba shine nace yau bari na kokarta naje masa reception wanda za'a soma da karfen hudun nan..... "
"Toh! meyasa baka sanar mini ba sai gani nayi kawai kana cin kwalliya zaka fita?Abu Jasmin baka boyemin wani abu naka,koda kuda ne ya tabaka saika fada min..... Toh meyasa ka boye min wannan? "
Rungumota yayi,ya soma lallashinta tare da dan bubbuga bayanta"Haba Hanan d'ita wallahi mantuwa nayi.... Naji nayi laifi pls forgive ur dear husband......... "
"Kodai wajen Sis Zahra zaka? " ba zato babu tsammani yaji ta jefo masa wannan tambayar.
Dan dabircewa yayi,azciyarsa yace"Yaa Salam! zata soma..... "
"Haba matata ki yadda da abinda mijinki ya fada miki.... Ki tuna fa ke da kanki kika ce mijinki baya boye miki wani abu,wannan din mah mantuwa nayi ban fada miki ba,so please kiyi wa mijin naki uzuri..... "
Advertisement
Tace"Its okay.... amma agaskia nifa ina jin tsoron kada kaje wata ta kyasta wannan haduwar taka tazo ta kwace min miji.....please I don't want to share my Mubarak with any lady.. Wlh ko ita Zahran hakuri kawai nakeyi nake kuma danne zuciyata akanta tunda naga kana sonta....... " ta fadi hakan ah sa'ilin da kwalla yadan zubo mata.
Girgiza kansa ya soma yi tare da ciro farar hankici dinsa dake aljihun wandonsa,ya soma goge mata hawayen yana fadin"uhmm uhmm! Hauwanah karki soma... Pls ki dena min asarar hawayenki ko baki san suna da tsada aguna ba? Ki sanya aranki cewar babu wata wacce zata kwace miki ni...... Ki cigaba da min addu'a don kwanan nan ji nake kamar bazan sami Zahran nan ba......... "
Da sauri tace"A'ah mijina daina fadin hakan...... Insha Allahu! idan har ita alherice agareka kuma idan har Allah ya rubuta cewar ita matarka ce toh ba Mummy kadai ba,babu wanda ya isa ya hanaka aurenta komin wuya sai anyi auran......Abu Jasmin zan cigaba da sanyaka cikin du'a'i... Ka tafi naga hudu ta kusa,Allah ya tsare,Allah ya kuma karemin Kai kuma Allah ya dawo min dakai lafiya mijin Hauwa'u..... "
"Nagode mace ta gari.... Hakika nafi kowani d'a namiji sa'a da samun mace ta gari.... Allah yai miki albarka matata...... " Yakai mata light kiss ah lips.
"Deserved kayi mantuwa fa baka feshe jikinka da turare ba.....banji kamshi na tashi daga jikin mijina ba as always..... "
murmushi ya sakar mata cike da kaunar yadda take kula dashi.
Da sauri taje ta dauko turarensa ta soma feffeshe shi ayayin da gabanta ke cigaba da faduwa ganin irin haduwar da yayi.
Koda suka fito falo sai da Goggo ta tambayeshi inda zashi.Abinda ya gayawa Hanan shi ya sake fada mata.Tace toh adawo lafiya Allah ya tsare.Kofar falon Hanan ta tsaya da rakiyarta gudun surutun Goggo.
Yana barin cikin gidan ya soma neman abokinsa Bilal awaya don ya nemi alfarman yi masa rakiya,amma sai akace masa switched off,gashi bashi da tabbacin ko zai sameshi agida.Haka dai ya yanke shawarar wucewa Zariyar shi kadai abinsa.
********
Biyar saura Mubeen ya isa Zaria,abinka da justice Sa'ad sanannan mutum ne shiyasa babu b'ata lokaci ya iso kofar gidansu Fadimar tare da kwatancen mutane.
Sanya k'iran Fadima yayi.
Ni kuwa ina zaune cikin kannena muna kallon wata film ta English version na India 'King of heart' hadda Umma mah tana zaune cikinmu ana kallon da ita,amma rabin hankalina yana kan agogo,time to time nake kai idanuwana kan agogon ganin har biyar ta kusa banji call din Mubeen ya fada min ya shigo Zariya kuma gashi awuri kaza ba.
"'Yar Kareematu anya kina ganin bakon naki zai zo kuwa?naga biyar ta kusa amma shiru kake ji,ki fada min ko dai ya fasa zuwan ne shine kika kasa gaya min? " Umma ce ta jefo min wannan tambayar.
Da kyar na hadiye wani miyau daya taimaka wajen smoothing busasshen mak'ogorona,nace"Umma ya bani tabbacin.......... " Maganata ta katse sanda rurin da wayata ta dauka ya karade wurin.
Da sauri na kai hannu na dauki wayar... 'Mubeen' is the caller.Cike da farin ciki nayi picking.
"Hello! Zahra fito na iso.... gani akofar gidanku... "
Cike da mamaki nace"Kofar gidanmu kace fa? Taya akai kasan kofar gidanmu bayan ni dai nasan ban maka kwatance ba? "
"Ke dai ki fito ki gani....... " Ya katse call din."
Umma ce ta lura da tsansar mamakin dake shimfide saman fuskata,tace"meh kuma ya faru?ko ya fasa zuwan ne? "
Murmushi na kwakwulo nace"Wai ya iso yana kofar gidanmu... Amma ni abin da mamaki Ummu Fadima,nasan ban masa kwatance ba amma taya akai yasan kofar gidanmu?"
"Mtswww.. Kedai wallahi zanga randa wauta zata barki 'yar kareematu,gidan naku acikin ruwa yake ko kuwa cikin yashi da baza'a iya ganewa ba?ko kuwa kin manta cewar mahaifin naku sanannan mutum ne...? "
Ai! sai fa yanzu na tuna cewar mahaifinmu sanannan mutum ne don haka sanin gidanmu ba zai yiwa mutane wahalar ganewa ba idan har am maka k'yakk'yawar kwatance.
"Ke Suhaima tashi kije ki dubo,idan har shi din ne sai ki shigo dashi kikai shi falon baki..... "
"Toh! Umma." acewar Suhaima wacce ta dauki hijab dinta dake kan kujera ta sanya sannan ta fice don dubowa.
Koda Suhaima ta fito daga cikin gida,kalle-kalle ta soma yi har ta hango Ash colour Mercedes Benz ML350,sai kuma ta hangi Mubeen ya fito daga cikin motar ya jingina bayansa da jikin motar.
Da sauri ta nufeshi tana fadada fara'arta har ta karasa gareshi tana fadin"Laaah! ashe da gaske dinne kana kofar gidanmu..... "
Murmusawa yayi yace"Wai ku meh kuka dauke ni ne? azatonku k'iranku zanyi nace gani awuri kaza kuzo ku d'aukeni koko? Inaaa ai an bar yayin nan,idan aka maka k'yakk'yawar kwatance shikenan ai an gama komai.... "s
Tace"Hakane kuma faa Yaya Mubeen..... Ya hanya? Ya kuma ka baro iyalin naka? "
Akunyace ya amsa "Duk lafiya qalau suke lil sis.... " sosai ya sami kansa da jin kunyarta don yasan kila yanzu haushinsa takeji don yana da mata,atake anan yayi dana sanin boye musu gaskiya da yayi tun farko.
"Bismillah mu shiga ciki..... " Hakan yaji ta fada.Tana gaba ayayin da shi kuma ya take mata baya.
"Umma gaskia nidai tun wuri ki gargad'i yaran nan kada bakinsu ya kuskura ya sub'uce su fadawa Abba cewar ai wani yazo guna da bayanan...... " Fadima ce take fadawa Umma wannan maganar.
Umma tace"Haba 'yar Kareematu ke kanki kin san cewar kannen naki basu da shisshigi.... 'Fadi ban tambayeka ba' sam basa yin shi...ki kwantar da hankalinki babu wanda zai sanar masa........... "
Adaidai nan Suhaima ta shigo falon tana sanar mana cewar lallai da gasken ya iso har mah ta kaishi falon baki wanda part din bakin daban yake ba'a hadashi da bangarenmu ba.
Da hanzari na mik'e cike da farin ciki.
"'Yar Kareematu ki natsu banda rawar kai.....don sam d'a namiji baya shaawar 'ya mace mai rawar kai,ki natsu and act classicly....... "
"Toh! Umma" Na fada ayayin dana rage zumund'in dake tsingulina,na koma yin taku d'ai d'ai har zuwa cikin dakina.
Gaban madubi na tsaya ina karewa kaina kallo!.Shigar wata dakakkiyar orange colour Shadda nayi wanda akai mata aikin gaba da bak'ar zare,fitted gown ce wacce kuka fi sani da 'A-shape'.Kayan ba k'aramin kyau yayi min ba balle orange kala sai ya dad'a haskaka farin fatata da kuma k'ara bayyana ainihin k'yawun da Allah yai min.Ban wani cika son dauri ba,don haka kawai sai na yane kaina da wani gyalle mara girma sosai.soson powder na dauka na dad'a gyara fuskata,sannan na Kara feshe jikina da turare.Ni kaina nasan basai an tsaya fad'a min cewar nayi k'yau ba.Sai jifar kaina nake da murmushi ta madubin ina kara yaba k'yan da nayi.
Ahankali nace"wow! Fadima kin hadu....... " Na sanya black flat shoes din da Engr. Mahmood ya sayo min sannan na komo falo.
Kallon Umma nayi tare da marairaice murya nace"Ummu Fadima da fatar zaki zo ku gaisa....? "
Murmushi ta sakar min tace"Mara kunya kije zan shigo...... "
Dariya na saki tare da rufe fuskata na fice daga falon zuwa bangaren saukar bak'i.
Ahankali nayi sallama ah kofar falon naji ya amsa min sannan na shiga ina mai kare fuskata da tafukan hannayena.
"Kenan tawar bata maraba dani ne ko kuwa wata sabuwar kunyata ce ake ji? " Hakan naji ya fada cikin wata irin muryarsa mai hargitsa lissafi.Gaskia ba don wani yana iya cewa kila na kamu da son Engr.Mahmood bane,toh da kuwa nace muryar Mubeen na masifar kama data Engr.
Sannu ahankali na sauke hannayen nawa amma still idanuwana arufe suke.Sai rawa nakeyi da idanuwan kamar zan bude'su kamar bazan budesu ba,can na soma budesu kadan -kadan har na gama budewa,fes na saukesu akan gorgeous handsome face dinsa.Sosai yai min kyau ba kadan ba,kayan jikinsa sun taimaka wajen dad'a masa kyau,amma duk wannan kyan nasa sai nake ganin kamar bai kama kafar Engr. Mahmood ba.
"Zahrata wannan kallon fah?ta menene??" Ya fadi hakan tare da kashe min ido daya.
Ashagwab'ance nace"Toh! ai kaine kaci gayu sai kace ranar auranmu.... Wai mah tukunna na tambayeka mana,sis Hanan tana ina har tabar mijin namu ya fito ahakan salon wata ta gani ta kyasta ta kwace mana shi?? "
Dariya sosai ya saki cike da jindadin abinda na fada.Ni kuwa na dai fadi hakan ne don kawai na saka yaji dadi amma gaskiyar magana kishinta ne fal acikin zuciyata.
Yace"Tunda bakwa son mijin naku ya dunga gayu don kada wata ta kwace muku shi toh daga yau na daina,zan dunga yawo da tsummokara kamar mahaukaci..... "
Dariya muka sanya duka.Anan muka kawo karshen barkwancin muka shiga gaggaisawa ina mai tambayarsa aikinsa da kuma matarsa da 'yarsa.Muka hau firar rayuwar duniya yana Kara bani hakuri akan abinda Mummynsa taiwa su Suhaima. Na nuna masa sam babu damuwa ai itama uwace agaremu.Ahakan Suhaima sukayi sallama suka shigo ita da Lubna da kuma baby Yasmeen dake biye dasu.Kowannensu rike yake da kular abinci,Faruk muka gani ya shigo shi kuma rik'e da tray mai dauke da Jug din mixed fruit drink wanda ni da kaina na hada masa,sai ruwan faro da kuma tumbler dake akife. Suka ijje asaman centre table dake agabanmu.
Cike da mamaki Mubeen ke bin kulolin abincin da kallo,yace"Zahra wannan kulolin abincin fa? Sai kace za'a kai gidan biki? Ba dai ni aka kawo wa ba dai ko? "
Murmushi nayi nace"Kai Mubeen in banda sharri ina wannan abincin zai ishi mutum daya balle mutane da yawa...?"
"Aganinki ba? Gaskia ni akoshe nake..hasalima mah gama cin abincina kenan sannan na taso.... "
Nace"Tabdi! ai wallahi baka isa ba,bazan bata lokaci na maka girki sannan kace bazaka ci ba... Kila so kake na maka irinta Jasmin...."
Kan yayi magana na juya gun baby Yasmeen,nace"Oya! baby Yasmeen yi maza ki samo min bulala na zane wannan handsome uncle din naki naga bai son yaci abinci....... "
Da sauri kuwa ta juya zata fita tana dariya.
"Dawo baby Yasmeen zanci wallahi.... " hakan muka ji ya fada wanda ba karamin dariya ya bamu ba musamman ni da Suhaima da muka tuna cewa hakan nima na fada sanda Jasmin dinsa tayi yunkurin zuwa samo bulalar.
Ni da kaina nayi masa serving abincin wanda 'onion rice' ce da kuma coconut stew,sai kuma 'sausage rolls' dana zuba masa akan wata plate daban.Sai kuma 'mixed fruit juice' din dana zuba masa cikin tumbler sannan na tura masa table din gabansa sai bina da kallon so yake.
"Oya! bismillah.... Idan ka kammala juz flash me.... " Nayi hakan ne don mu bashi sarari ya kwashi girkinsa amma ga dukkan alamu so yake na zauna yana ci yana kallona muna kuma fira.
Ni kuwa ban biye masa ba nabi su Suhaima muka fice.Bayan kamar mintuna ashirin da fitarmu,sai ganin call dinsa nayi wai har ya kammala.
Na dubi Umma nace"Umma wai ya kammala.... Muje koh?"
Tace"Toh tashi muje don nasan yau idan har banje naga gwarzon nan ba toh kuwa na shiga ukuna agun 'yar Kareematu.... "
Dariya sosai muka sanya ayayin data mike ta sanya hijab sannan muka nufi part din da yake.
**
Russunawa yayi yana gaidata cike da girmamawa wanda na lura sosai hakan ya birge Ummu Fadima kuma na lura ta yaba dashi ba kadan ba.Tayi masa jajen rasuwar mahaifinsa,shima yayi mata godiyar barinmu da akayi muka kai masa ta'aziyya.
Nisawa tayi tace"Allah sarki! gashi kazo mai gidan baya nan yakai ta'aziyyar wani rasuwa da akayi ah katsina kuma sai gobe muke saka ran dawowarsa.... "
Haba! biri yai kama da mutum!.. Shifa tun dazun yake ta son ya tambayi Fadimar inda Abbansu yake amma Allah ne kawai bai bashi ikon yin tambayar ba.Kuma agaskia baiji dadin wannan zancen ba,don yaso ace ya hadu da mahaifin nata susan juna kuma yasan dashi amatsayin manemin Fadimar ayau din nan,don shi so yake ace ya kammala komai na batun shigowa gidansu Fadimar kafin ya wuce India.Amma idan har an daidaita ita mummyn tasa fa?
Da sauri ya kawar da wannan tunanin nasa,yace"Haba Umma! ai babu damuwa wani lokaci mah hadu mu san juna ai...... "
Sosai taji dadin kalaman nan tasa,tace"Madallah! naji dadi daka fahimceni kuma insha Allahu yana dawowa zamu sanar masa da zuwanka..... "
"Nagode sosai Umma.... " acewarta.
Advertisement
- In Serial26 Chapters
Rise of a Rogue Dungeon
Following the unfortunate, or fortunate birth of a Dungeon, in the world Ilyeus where Dragons claim the skies. Titans wander the world. Drakes boast their majestic pride. Wyrms sleep beneath the earth. Humans, Elves, Dwarves, Beast-kin, and many other sapient races mingle amongst each other, for good or bad. Gods descend among mortals with their Divine Vessels. The Dungeon treads unrestricted by the links other Dungeons have. Down a path never walked by any other Dungeon in the world of Ilyeus. Down, A Path of Freedom! A Path of Dominance! A Path of a Savior! A Path that would make Spirits shudder in fear! But first, it must survive, expand, evolve, and create an army that would do its bidding. This is my first time writing something like this, so if you see any grammar or spelling errors, pointing them out would be appreciated. Any constructive criticism is also appreciated! My update schedule is currently as I write them. So that means every time I finish writing a chapter, I will post it after it gets edited. I also release a chapter of A Lone Automaton's Journey To Find Its Operator infrequently as a side thing.
8 219 - In Serial40 Chapters
Fireblight
A young fire elemental, Tya Maraise, has lived her life in isolation for some time while creating a human body to mask the fire within. After managing to create something sufficient that’ll allow her to blend, she begins the process of learning more about human behavior only to find herself dragged into a royal mess she wants very little to do with. [ Book Three. All books are standalone and do not need to be read in order. ]
8 158 - In Serial6 Chapters
Just Your Average Isekai
a guy gets hit by truck-kun and is reincarnated into another world. after learning why he was summoned he said "No" and got thrown out. now he has to figure out how to live without the help of others.
8 53 - In Serial26 Chapters
The Once Simple Life of a Dungeon Skeleton
A simple dungeon skeleton whose sole job was to stand in a tunnel on the first floor of a dungeon and die to any adventurers that cross his path finally gets the chance to change his life.First time writing so criticism is always welcome to help improve my writing. Edit: As of 30/9/16 I'm going to start continuing this series and hopefully finish it. I'm going to be editing the current chapters before I start writing the new ones. It might take a few weeks for new chapters to show up depending on how much time I have to write.
8 50 - In Serial51 Chapters
I am the king of all villainous villian : Volume 1 : against hell devouring beast
"fell in hell , suffered in pain , felt despair and terror for countless time , walked the path of life and death …… he will rise and become the one to rule over dead , spread terror against livings and rule over worlds. ….. mercy isn't thing he knows ,trust ? he doesn't even have one in himself. He , the one who rised from the ashes, crawled out from the depth of hell will now show the world who the true master of the world is ? celestials and demons shall be his vanguard, true dragons and divine phoenix shall be his war mounts , gods and devils shall be his war puppets. heaven shall be his war tetra and everyone remaining shall be his soldiers that follows him with whole heart loyalty. kill anyone that oppose me that's my principle. sometimes when death comes looking for me , I mistake it for my life long friend…..While I mistake life for long lost friend… I shall order and you all shall follow it….. let them show their powers , because a real villain only makes his moves when his pawn and chess pieces has finished their job for the chess master. which is me , a master…….. ……………….be gone thots !!
8 104 - In Serial70 Chapters
Memories | Jenzie Meme Book
A collection of Jenzie, Dance Moms and Brat TV memesEnjoy!**STARTED ON JUNE 27th 2020****COMPLETED ON JULY 7th 2020**
8 72

