《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER TWENTY SEVEN
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
🌼BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI🌼
Page 127-130
Yau Litinin wacce ta kama week din da Engr. ya fada min cewar zai soma aiki ah ABU.Inata saka ran naga kiransa aranar amma shiru kake ji,haka na yini ranar amakaranta babu wani kuzarin kirki da kuma walwala atattare dani,wanda ko ni kaina ban san dalilin shiga cikin wannan damuwar ba kan wanda bashi da wani muhimmanci acikin rayuwata.Ash ce ta lura sam yau ko wata hirar kirki naki bari ta shiga tsakaninmu.Bayan mun fito daga wata 4-6 lecture ta tsareni da tambayoyi.
"Wai girlfriend lafiya kike yau din nan kuwa? " Ta fadi hakan fuskarta cike da damuwa.
Ahankali nace"Meh kika gani Sahiba? "
"Gani nayi sam yau baki da wata cikakkiyar kuzari kuma na lura yau hirar kirki bata wani shiga tsakanina dake ba kamar yadda muka Saba...Shin kawata kun sami wata matsalarce keda Mubeen? Ko su Abba sun tayar da maganar aurenki ne? Ko kuwa wata damuwa ce can daban take damunki?... Pls girlfriend talk to me let me see if I can help,kinga dai duk fadin jami'ar nan baki da aminiya kamar ni... "
Tabbas maganar Ash gaskiyace,bani da aminiya sama da ita,ah ABU muka hadu har Allah ya had'a jinina da nata.Komai namu tare muke yinsa,shak'uwarmu ta sanya har iyayenmu mata ma suka kulla k'awance.Tun ranar da Ash ta nuna min bacin ranta k'arara akan boye mata abubuwa da nakeyi,toh tun asannan na daina boye mata komai nawa sabida lura da nayi da yadda ta daukeni more than a friend.
"Ash wallahi kawai am worried ne ganin har yanzu shiru-shiru banji kiran Yaya Mahmood ya fada min cewar ya iso ba kamar yadda ya tabbatar min da cewar yau zai soma aiki.... Shine nake tunanin anya is everything alright at all kuwa? " Na fadi hakan kamar zan saki kuka.
Dariya Sosai Ash tayi tare da nuna ni da 'yar yatsa,tace"Wow! can't believe diz..... My girlfriend is inlove with her boo's brother ............ "
Da mamaki na tari numfashinta"Ke! are u sure u are okay kuwa? Don kawai na nuna damuwa da kulawata akansa shine zaki ce am inlove with him? Ki sani fah ko bakomai ya cancanci na nuna kulawa akansa ko don darajar Mubeen...... "
"Oho! ni dai bazan fasa fadar gaskiyar nan dai da ba'a sonta ba.... ai dama daga nuna care din soyayyar take farawa ko Kuma idan wani na birgeka bazaka san lokacin da zaka soma crushing akansa ba... Ko ki yarda ko karki yadda,believe me u are already inlove with Engr. Mahmood........ "
Kafin nakai ga bata amsa,naji wayata ta hau ruri Kuma adaidai lokacin muka k'araso wurin da nayi parking motata.Da sauri na zaro wayar daga cikin Jaka,wow can't juz believe 'Sir. Mahmood' na gani ajikin screen din wayar.
Cike da farin ciki na kalli Ash nace"Ash wallahi shi yake kirana......"
Tace"Toh pick the call mana... Dadina dake Fadima kina so kina kaiwa kasuwa,jan ajinki tana yin yawa sosai, Allah wallahi idan baki rage wannan ego din taki ba,toh wallahi watarana zaki fad'a kogin dana sani...... "
Nasan kwarai da gaske gaskiya ta fada shiyasa kala bance mata ba illa banka mata hararar da nayi.Na kai hannu zan danna 'receive', cikin rashin sa'a call din ta tsinke.Na kasa kunnuwa ina sauraron sake jin wani call dinsa ta shigo amma shiru kake ji, har muka shige mota muka bar makarantar bey sake kira ba.Bakin ciki ne ya cika min zuciya sosai har yayi nasarar bayyana kansa k'arara akan fuskata.
Advertisement
Sosai na lura da yadda Ash keta gumtse dariyarta,amma sai na dada had'e rai sabida kada taga fuska tayi min iskanci.Ai kuwa ban tsira ba,don muna had'a idanuwa ta rushe da dariyar shed'ancinta wanda ta saba yi idan har zata yiwa mutum sharri.
"Ke Kuma meke sunkulinki haka da har kika cika min dodon kunni da dariyar banza? Na fadi babu alamun wasa atattare dani.
Wata sabuwar dariyar ta sake saki wanda ya dada min bacin rai,nace"Ni dai wallahi idan haka zaki cigaba kina sanyani agaba kina dariya kamar kinga mahaukaciya sabuwar kamu,toh wallahi ba zamu shirye dake ba... Ke! infact daga yau na daina daukarki acikin motata,shi sarauyin naki ya dunga miki wannan jigilar amma bani ba..... "
Tofa! kuji inda na bullo kuma... Don kawai na mantar da ita zancen Engr. Wanda na tabbatar ni takewa dariya don ganin yadda na had'e rai adalilin rashin sake kira da baiyi ba akaro na biyo,shine na kamo wannan maganar da ko kadan babu kai.Dayake su Ash rufin asiri ne kawai garesu,her Dad is not dat rich da har zata mallaki motar kanta,shiyasa na lura ta d'an ji zafin maganar nan tawa.
Azuciye tace"Malama please saukeni anan.....ai ba sai kin min gorin cewar bamu da arziki ba da har zan iya mallakar motar kaina ba,amma ina son ki sani,duk da cewar bamu da dukiyar,hakan bai taba sanya munje maula gidan uban kowa ba... In dan taimaka min da kike kina kaini gida acikin wannan motar taki mai suffar kifin ne yasa kike neman gaya min maganganu son ranki toh don Allah daga yau kamar yadda kika fad'a karki kuma idan har ke din 'yar halak ce.......... "
Da k'arfi tace"Malama I said stop the car let me get the hell out...... "
Ji kake kiiiiiiiiiiiii!! naja wani wawan birki don sosai maganganunta duk dad'a min b'acin ran daya fi nada,duk da cewar nasan nice bani da gaskiya.Sam bai kamata ace nayi mata irin wannan zancen ba koda ace ina son na mantar da ita zancen Engr. din.Toni miye nawa na damuwa akansa haka?Ni karan kaina mamakin kaina nake yadda nake neman zaucewa akansa.Anya hasashen Ash akaina ba gaskiya bace kuwa?.
"No it can't be.... I don't love him" Na fadi hakan acikin zuciyata tare da bugar sitiyari.
Idanuwana sun kada sunyi jajur don b'acin rai,abinka da wanda baya hawa da wuri sai idan an tab'oshi,nace"Ke 'yan mata karki nemi ki kawo min rainin hankali anan kina jina ko? Ke kanki kin san am not ur mate makarantace kawai ta hadamu da kuma had'in ubangiji.... If not ke baki isa kiga ah hanya ki nuna kin ma Santa ba balle ta kaiki ga magana da ita...............abin daya fi bani haushi ga halayyarki bai wuci yadda kike d'aukar komai da zafi ba,yanzu miye wani abin fad'a anan ko kuma gori don nace shi saurayinki ya cigaba da yin jigilar kaiki gida? Ko kinji na ambaci kalmar 'talauci' ko kuma 'maula' acikin zancena huh? "
"ina fatar kin kwana da sanin cewar ni ba illiterate bace ko?.... Ke! bari kiji ko wanda bai taba sanin 'A' ba idan kika masa wannan zancen dole yace goranta masa kikai balle ni da take kokarin had'a B'tech dinta..... Ke ni ki manta da zancen nan bani da time naki tunda na lura wannan guy din nema yake ya zautaki,don na d'agoki Fadima so kike kawai na manta da batunsa dats why kika fada min maganganun da kika tabbatar zasuyi hurting dina don nasan sam bada gangan kika fada min hakan ba,rasa abinda zaki fada kikai,dats why kika zab'i da nima ki bak'anta min rai,toh Malama kinyi nasara,yanzu jaah mota mu tafi ni yunwa nakeji sosai........... "
Advertisement
Ta fadi hakan tana hamma,na gane nufinta,ba wani yunwar da take ji,so take kawai mu kulle wannan chapter din.Ayshana hoo!! akwai rigima,ni kadai kawai nake iya hak'uri da halayyarta.
"Ash ta Bash am so sorry.... Wallahi I didn't mean to hurt u.... Afuwan amaryar Bash.... "
Ina bata wannan hakurin ne adaidai lokacin dana tada motar mukayi gaba. (Karku manta Fresh sunansa ne Bashir ayayin da mahaifinsa ne Abdulbasi).
Kala bata ce min ba har muka iso na sauketa. "Thanks" kawai ta iya ce min Sannan ta shige cikin gida.Ni kuwa ko ah dankwalin kaina don nasan kafin washegari mun shirya. Lol dats friends for you,zomu zauna zomu sab'a.
Misalin takwas da rabi na daren ranar sai ga k'iran 'Sir Mahmood' wanda tuni ni nama riga da na watsar da lamarinsa ganin yana nemar dagula min lissafi acikin en kwanakin nan.Kuma abin mamaki,amaimakon naji haushinsa tunda ya sakani cikin bakin cikin rashin jin daga garesa dazun,a'ah,sai na sami kaina da jin wani tsananin farin ciki mara misaltuwa.Wannan k'aron ban wani jaah aji ba nayi picking call din don na lura shima din akwai iya nuna shegen class.Idan ba haka ba,daka kira sau d'aya ba'a daga ba,ai yaci ace ka sake maimaita k'iran akaro na biyu,idan kaga still ba'a dagan bane toh sai ka haqura,kila wannan baya Kusa ne ko kuma baya son yayi picking.lol amma fah hakan daya yi ya birgeni,I so much love men with pinging class!!!!!
"Haba! sister inlaw ko darajar sallamar mah bazan samu ba? "
Ajiyar zuciya na sauke,kafin nace"Sir! wallahi nayi... Ina ganin kaine dai baka jini ba..... "
"Auzubillahi!.... ba'a fa sansu Fadima Zahra da k'arya bafa..... "
Saurin taran numfashinsa nayi"Da gaske fa nake Sir nayi amma ak'asan mak'oshi..... " ban san meyasa na sami kaina dayi masa wata shagwab'a ba.
Shi kuwa mutumin naku kad'an ya rage ya zauce jin wannan shagwab'ar da Fadima ta masa.Ji yayi kamar ya zama tsuntsuwa yaje ya rungumeta ya lallasheta kamar yadda ya saba yiwa marigayiya *Zaynab* d'insa.
Ajiyar zuciya ya saki wanda na jishi har cikin dodon kunnena,kana yace"Okay na yarda kinyi don nasan k'anwa ba zata yiwa big brother d'inta k'arya ba.... Dazu na k'ira naji ba'a d'aga ba sai nayi tunanin kila u are busy ne ko kuma ana kusa,kawai ba'a ga damar dagawar bane....... "
Da sauri nace"Haba dai ya zanki d'aga call din boss kuma babban yayanmu? Kawai dai bana kusan ne...... "
Sosai yaji dad'in kalamanta,yace"Alright!.... Dama dazun shigowata Zariyar kenan nace bari na hanzarta k'iran matar kani na Sanar da ita isowata... tun jiya mah ya kamata ace na iso amma zirga-zirgar nemar transfer din nan ce ta sanyani gaba,amma alhamdulillahi everything is now steady.......... "
Ahankali na sauke ajiyar zuciya,cike da farin ciki nace"Masha Allah!.... Allah ya sanya alheri Sir!.... "
"Wato ke dai har yanzu ba zaki dena k'irana da wannan sir din ba ko? "
Toshe bakina nayi jin ina kokarin sakin dariya,nace"Kayi hakuri wallahi bakina ya riga ya saba da fadar hakan ne.......... "
Nayi shiru ina sauraron abinda zai fada,can naji ya sauke ajiyar zuciya yace"Da fatar za'a zo asanyawa office din babban yaya albarka gobe?"
Jim na danyi na kasa motsa baki balle na kai ga furta wani abin.
"Hakan ba zata samu bako? "
Cike da rawar murya nace"Zata samu.... Insha Allah Sir! gobe zanzo naga office din....."
Daga haka mukayi sallama.wani irin farin ciki ne yake ratsani wanda har cikin jinin jikina nake jinsa.Ni kaina har Allah-Allah nake gari ya waye don mu hadu na sake ganin wannan gayun nasa da kuma sanyin halinsa mai birgeni.Da gudu na tashi don zabar kayan da zan sanya gobe don so nake nima na kure shi.(Toh ko miye dalilin Fadima na son birgeshi bayan tace ba sonsa take ba?... Lol muje dai zuwa)
Shima anasa bangaren suna gama waya ya soma murna yana fadin"Yes! ta soma fad'awa cikin tarkona.... "
Can yayi murmushi yace"Amma ban taba tunanin cewar abin zaizo min da sauki haka nan ba............ "
**
Washegari 9am lecture nake dashi wanda ya kasance shine last class namu for the semester don next week Monday zamu soma jarabawa.Tun karfe bakwai da rabi na kammala shirina cikin wata fashion material lace wanda aka mata dinkin skirt and blouse daya zauna cif-cif ajikina.Lace din pink ce mai adon wasu zanen fulawoyi kalar sararin samiya.Sai na kafa daurin wata sky blue head,daurin hawa-hawa nayi wanda kuka fi sani da 'canopy'.jakata da takalmina duk bakak'e,haka gyalen dana dan yafa saman kafad'a b'aka ce.Simple make-up na d'auka,eyebrow dina naja,sai kuma pink lipstick dana dan murza abaki,sai kuma Tara powder ta dana shafa.Ni kaina na tsorota da wannan haduwar da nayi don ban taba yin kwalliya mai zafi sosai haka na shiga cikin makaranta ba.Ko su Ummu Fadima sai da suka yi magana kan wannan haduwar tawa.
Kannena sai Fadi suke tayi"wow!... Anty kin ganki kuwa Sai kace wata sabuwar amarya da ake shirin yin dinner dinta?"
Ummu Fadima kuwa cewa tayi"wannan gayun ta yau daban take.... Kodai sirikin nawa ne zai diro garin yau shine ba'a sanar mana ba? " (tana nufin Mubeen).
Dariya na saki sosai,na dauki makullin motata nayi hanyar waje ina fadin"Kai Ummu Fadima ni dai babu ruwana...... "
Azuciyata kuwa cewa nayi"Wannan gayun ta dan'uwan sirikin naki ne,nayi wannan kwalliyar ne don shima yau na kure shi.......... "
(Hahaha!! Allah sarki Fadima bata san ta gama kamuwa da son Engr. Mahmood ba).
2hours lecture ne,don haka sai kusan 11:30am ma muka fito.Ash bata samu zuwa ba don ta kirani da sassafe wai zazzabi ya dan rufeta.Ya ilahi! karku so kuga irin kallon dana sha yau acikin ABU,wasu matan mah sun raina kansu ah sa'ilin da sukayi tozali da wankan 'Ba wai fa ban sab'a rud'a wuri bane,a'ah kawai wankan yau tafi d'aukar zafi ne kurum.
Zaro wayata nayi dake cikin jakata wacce tun muna aji take ta vibrating alamun k'ira ne keta shigowa.
'Sir. Mahmood' shine sunan dana gani yana rawa saman screen.Da sauri nayi receiving don na tabbatar shine keta k'ira.
"Sir. Please am so sorry na manta na fad'a maka cewar ina da lecture din safe,yanzu haka ma fitowata kenan..... " Na fad'i hakan tare da rolling eyes dina cike da yanga kamar yana kallona.
Ajiyar zuciya naji ya sake as usual wanda nake tunanin yin hakan ya gama bi masa jiki,kana yace"wallahi har hankalina ya tashi don atunanina something is wrong with you.... Alright are we good to go? "
Na gane nufinsa don haka nace"Yeah.... " kamar banso fadar hakan ba.
"Okay kindly come down to ITS centre,second floor,last office by ur left........Hope zaki iya haurowa? " Ahankali naji ya Fadi hakan wanda muryar tasa ta k'ara zuzutani.
"Zan iya Sir!.... "
"Anya sister inlaw idan bazaki iya ba ki bari kawai kada kafafuwanki suzo suna miki ciwo...... " cike da damuwa naji ya fadi hakan.
"Wallahi zan iya" na fada ina dariya.
"Okay sai na ganki...... " Ya katse call din.
"He is so caring" Na fada ahankali.
**
Ban wani sha wahalar gane office din ba wanda naga an rubuta 'welcome to Engr. Mahmood Mustapha's office... Head of ITS,ABU Zaria chapter...... "
Cike da fargaba na tura k'ofar ofishin tare da sallama,fes idanuwana suka sauka saman damn handsome face dinsa,sanye yake cikin black suit dinsa complete. Ya sanya wata farar long sleeve aciki wanda ya tsuke kwalarta da red butterfly necktie.Kannan nasa da qasumbar nan yasha gyara don sai kyalli suke.Sosai yai min k'yau har naji na rainawa tawa kwalliyar.Idanuwansa akaina har na k'arasa ciki.Mutumin da suke tare da,naga ya mike ya bashi hannu sukai musaha,sannan ya juya ya fice.
"Sister inlaw welcome..... U can have a sit... " Ya nuna min wata cushion dake bayana.
Still idanuwansa akaina.Gaisawa muka yi sosai ina tambayarsa yadda ya baro mutan kano.
Yace"Mutan kano duk sun ce agaidaki... " murmushi kawai nayi don nasan fada yayi kawai.
"Sister inlaw wat can I offer u? "
"Nothing am okay.. " na fada cike da kunya.
Tsareni yayi da oily eyes dinsa wanda yake kara rikitani,tuni na saddar da kaina kasa don bazan iya jure kallonsa har na tsawon lokaci ba.
"Even diz coffee? " ya fadi tare da nuna mug din dake gabansa wanda lokaci zuwa lokaci yake d'an sipping,ayayin da wata karamar flask ke gefensa,tuni na gane cewar coffee din ke cikinsa.
Cike da sanyin murya nace"Sir! wallahi am okay... "
"Toh! naji kar kiyi min kuka..... "
Sosai abin yaso bani dariya wanda har na kasa hakuri sai dana d'an Dara.
"Hope u are preparing for ur upcoming exams?"
"Sosai ma.... "
Yace"Daz good... Wai wani level mah kike? "
"300....... "acewata
Cike da farin ciki yace"wow! kenan 400l kike shirin shiga.... Sauran miki 2years ki zama certified medical doctor/Surgeon..... Toh yaushe k'anin nawa zai taho ya daukeki agabansu Abba? "
Dam!! naji gabana ya yanke ya fadi,sam banso yayi min irin wannan tambayar ba,da k'yar na iya harhada kalamai nace"Tukunna dai... Sai yadda Abba ya tsara lokaci.... "
"Ba dai kina nufin kice sai kin kammala karatunki ba dai ko? " Ya fada cike da damuwa.
"I don't think so.... " na bashi amsa immediately.
"Okay tell me a little about you Fadima Zahra don naji rannan Dr.Ketso ya k'iraki da d'iyar justice.... Kenan ke d'in d'iyar barrister ce? "
Atake na fada masa koni d'in wacece.
"Wow! can't believe diz.... Ashe da babbar mace nake zaune da anan ban sani ba?.... Afuwan ur excellency ban tab'a sanin cewar ke din d'iyar justice Sa'ad Mai Nasara bace,adalin alk'ali kenan wanda kasarsa ke tinkaho dashi......"
Sosai naji dadin wannan kalaman nasa na yabon mahaifina,ahankali nace"Thanks for the good comment sir! "
"Da fatar watarana za'a kaini na sada zumunci da family dinki as soon as possible? "
"Why not? " Na fada,sosai Engr. Ke birgeni.
Ya mike tare da d'aukar wayarsa yana fadin"Lemme snap our wife na turowa kanina yaga yadda amaryar tasa tasha k'yau tamk'ar zata je gasar k'yau....... "
Kunyace ta kamani sosai sanda naga ya nufo inda nake zaune yana kokarin son ya d'aukeni hoton.JI nake kamar kasa ta tsage na fad'a cikinta don tsananin kunyarsa data min yawa.
"Come on!! nuno min beautiful face dinki na dauka.... U can even give it a style if you like..... "
Ya fadi hakan alokacin dana ga ya kunna camerar wayar.bani da wani option illa na bashi hadin kai.haka yayi ta daukata har sai dana ce masa ya isa hakan.
Dan matsowa yayi kusa tare da maida cameran gaba wato 'front camera'.
Yace"Oya let's take a selfie duk na tura masa.... "
Haka shima yayi ta d'aukarmu selfin har saida nace masa na gaji sannan ya bari.Ji nayi kamar nace masa ya tura min atawa wayar amma kunyarsa nake ji ta hanani yi masa magana kuma shima na lura sam bai damu yace zai tura min din ba. Nace masa naga office Allah ya sanya albarka ni zan tafi.
"Da wuri haka sister inlaw? Ya fada ah sa'ilin dana ga ya dauko wata k'atuwar leda ya nufo inda nake.
"Wallahi I have alot to do dats why... "
"Okay kindly accept diz small gift from me.... tsarabace karki raina nasan sunyi kadan pls..... " Ya fada tare da miko min ledar.
Bude baki nayi ina kallonsa, kokarin magana nake sai ya rigani tare da datse lips d'insa da 'yar yatsarsa,yace"Shhhhhhhhh!!! Pls don't reject... Sam ba'a maida hannun k'yauta baya..... "
Jin abinda ya fada ya sanya jikina yin sanyi,cike da mutuwar jiki na sanya hannu tare da k'arbar ledar da hannu bibbiyu ina godiya.
Mur! naga yasha yace"Zaki fara sana'ar taki ko? "
Tunawa nayi da cewar baya cika son godia,don haka nayi masa sallama na fice.
Fadima na barin office din,Engr. ya fada kan kujerar data tashi yana maida numfashina, ahankali yace"Ya Allah ka mallaka min Fadima Zahra!!!!! "
*
Koda na isa gida,ledar da Engr.ya bani na bude,na baje kayan saman gado.Wasu uban-ubansun fashion bags ne kala biyu,baka da kuma golden colour.Sai kuma gyalulluwa biyu kalarsu jakukunan,sai takalma shima kala biyu amma bak'i da brown.Bakin nada d'an tudu,ayayin da ita kuma brown d'in flat ce.
Cike da mamaki nace"Toh waya fadawa Engr. Size din takalmin da nake sakawa? "
Sai wasu turaruka masu tsananin kamshin dadi.Da sauri na maida kayayyakin cikin leda na boye ah acikin wardrobe dina.
Advertisement
- In Serial162 Chapters
The Man Who Killed the First Monster
Jason Park, a man with ambition. At a ripe age of twenty-nine, he took the risk to struck big at the cut-throat world of finance at Wall Street. Like any human in the whole world, money is everything. Yet for him, things didn't happen as he expected. Burnt out and failing another one of his job interviews, he dragged his feet over the sidewalk of New York City. Yet something unexpected happened, a cry for help coming from the dark alley of the city. A city well-known for its two sides of light and dark. He hesitated at first but his morality swayed him. He came to help but what he found only opened a door that he wishes it wouldn't open. He was the first and it wouldn't be the last. From green dollar bills to blue game-like windows. His reliance shifting to the latter. An encounter that will bring forth a New World order. A world hungry for blood, sweat, and tears. Disclaimer: This is a work of fiction. Names, characters, businesses, places, events, and incidents are either the products of the author’s imagination or used in a fictitious manner. Any resemblance to actual persons, living or dead, or actual events is purely coincidental.
8 164 - In Serial40 Chapters
Soulless: A free slave
To appease the demons that are coming into the world through a newly-opened portal, and get on their good side, the Emperor decides to give them one of his high-ranking slaves as a gift. Now, she must use all of her wits not only to survive among them but also to learn as much about them as possible if her people are to have any chance of survival. However, she quickly realizes that these demons are nothing like she expected them to be. Chronologically speaking, this book is a sequel to Twisted hell. But it has a new cast of characters so you don't need some knowledge from the previous book to follow this one.
8 132 - In Serial11 Chapters
Realm of the Stars Volume III: War for the Crown
The concluding volume of a space opera trilogy inspired by the Arthurian mythos, sequel to The Endangered Crown War has come to the Dozen Stars. The interstellar kingdom is threatened on all sides, from the mighty legions of an ancient empire determined to take back what its ruler sees as rightfully his to the brutal barbarian raiders invading from the galactic rim. Caught between these dire threats, the Dozen Stars seems doomed to fall. Artakane ast Carann has secured her throne from interal threats, but can she hold her nation together in the face of such powerful external threats? Now she, her companions Latharna and Pakorus, and the entire Dozen Stars will be put to the ultimate test. As battles rages, alliances are forged, and secrets are revealed, Arta must unravel the true secret of her enemies' horrifying power before it is too late. If she succeeds, she will save her people and win such glory as few in the galaxy have ever known. If she fails, then all humanity may find itself crushed beneath the boots of empire. The final struggle has begun... Updates Monday and Friday
8 145 - In Serial12 Chapters
Dungeon Sect
On hiatus. Just have too much that happen in succession to have regular updates. will keep writing just wont be posting chapters for a while Jade was once a human on earth, many eons ago. He died and went to a cultivation universe. Sadly he was never heaven's choosen with heaven breaking luck. He was average and bland. When his brother was shining light he was the stabling post supporting him. Many sought to take down the light, but knew they were nothing to light so they tried to take down the post. Jade died in the cultivation universe, not without learning more than most in their billion year life times. He was not a genius by any means he was just well learned. Now he is a dungeon, with mana instead of Qi. Still he can cultivate and learn again. Who will he teach and help become a shining light Warning I am not the best writer, and it will take awhile to build to more of an action adventure story with dungeon building as a side as the story will shift from Jade the dungeon to his choosen students I use Cultivating Dungeon, and The bound dungeon as systems to build off of, but the story is all mine
8 141 - In Serial44 Chapters
Scars (Remus Lupin)
A girl who fucked up her family tradition A girl who fell in love with a beast A girl who turned into a wolf once a month, but was not a werewolf A girl who has three older sisters A girl who's name is Cassiopeia Black
8 83 - In Serial6 Chapters
Submissão Feminina
Nesses textos,pretendo introduzir minha concepção da submissão feminina ,suas características comportamentais e sua importância para o estado psicológico sadio de uma mulher sobre a perspectiva evolutiva.Sou um defensor da submissão feminina por parte de um homem na posição dominante,este tema é frequentemente abordado por diversas bases de conhecimento,mas muitos não a compreendem da forma devida e sua real importância.Entendo que cada base de conhecimento(pelo menos as que eu estudei,BDSM cristianismo e islamismo) que tem esta temática possui conhecimentos que podem ser combinados para o melhor aproveitamento da energia sexual e conjugal da fêmea submissa.Não uso de dogmatismos para enxergar a realidade.
8 106

