《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER TWENTY TWO
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
Hafsat Al-Mustapha
🌼BABI NA ASHIRIN DA BIYU🌼
Page 105-110
"Ruqayya Khaleel Lema wacce akafi sani da Rukky wacce kuma itace ke zaune ayanzu take facing d'ina,she was my senior back then in secondary school... Alokacin Ina SS1 ayayin da ita kuma take final year d'inta.Itace Social prefect ah set d'insu..... Rukky dai da kuke gani ta kasance 'yar barikin k'arshe don kusan rabin male teachers d'in makarantarmu tana mu'amala dasu,ba sai na tsaya fassara muku ma'anar abinda nake nufi ba don na tabbatar kun gane.And again,Rukky ta kasance acikin dukka set d'insu babu muguwar prefect kamarta,cin zalin dalibai awurinta ba wani abu bane.Atakaice dai Rukky rayuwarta take ci da tsinke,don mahaifinta 'Khaleel Lema' shine Principal d'inmu.Itace tilon 'yarsa kacal daya haifa anan doron kasar,Mahaifiyarta ta dan jima da rasuwa,kuma tun bayan rasuwarta Khaleel Lema bai sake yin wani auren bah.Dalili kuwa shine,tsoro yake kada yaje ya auro wacce zata dunga musgunawa 'yarsa wacce ya fiso akan duk wani abu.Duk wani abinda Rukky takeso kota halin kaka ne sai ta sameshi,dalilin daya sanya take tsula tsiyarta duk yadda taso kenan ba tare da mahaifin nata ya taka mata birki ba,don sam baya k'aunar ganin b'acin ranta,shiyasa duk wani malami amakarantar ke tsoron wani abin ya had'ashi da ita gudun kada yayi yunk'urin daukar mataki,daga bisani ayi dismissing d'insa kamar yadda aka sha yiwa wasu akanta.Rukky ta kasance gagararriya ga kowa including her father,ko mai tace shi ake bi amakantar,idan tace ga abinda za'ayi,toh wallahi baka isa kace 'No' ba... Atakaice dai mahaifinta na aiki da final decision d'inta ne duk da cewar wani sa'in abin nata na mugun damunsa amma hakan yake d'aurewa yake mata duk wani abin da takeso don azauna lafiya.. "
"Tun sanda Rukky ta k'yalla ido akan Haidar,taji kawai diz is the type of man she is dreaming to have and will get him by all means...Sai kuma tazo ta lura cewar kamar akwai soyayya mai k'arfi tsakanina dashi wanda hakan ba k'aramin bakanta ranta yayi bah.Sannu ahankali ta soma yin close dani wanda hakan ba karamin bani mamaki yayi bah,ganin dai ita Rukky ba kawa gareta ba don kowa tsoronta yake,amma ni dai agaskiya koh kadan bana tsoronta,infact I even hate the bitch...wani abin birgewa da Rukky shine,duk iskancinta wallahi yarinyar akwai brain,don haka ta siyasa ta dunga bugar ruwan cikina har ta tabbatar lallai da akwai soyayya mai k'arfi tsakanina da Haidar.watarana ta kawo min wani mummunar labari wanda har yau bazan taba manta dashi ba,ce min tayi wai tayi bincike akan Haidar,yana da munanan halayya kawai na rabu dashi,halayen kuwa sune,yana shaye-shaye,yana biye biyen 'yan mata(kun gane biye-biyen da nake nufi ai?) Sannan mafi munin halin data lissafo wanda shi yafi d'aga min hankali shine wai Haidar d'ina d'an Luwad'i ne. At first,banyi taking maganar nata serious ba,sai mah zaginta nake tayi kuma again ban fad'awa Reedah ko Leedar abinda ke going bah.Sannu ahankali maganganun Rukky suka soma yin tasiri agareni har naji na soma tsanar Leedar.Kafin ah ankara har na soma juya masa baya wanda hakan ba karamin tada hankalinsa yayi ba,and the worst part is dat ya kasa gano bakin zaren da kuma dalilina na juya masa bayan.Reedah whom use to be my very good friend itama na soma juya mata baya,tayi iya bakin k'okarinta don jin abinda ya sanya na juyawa yayan nata baya amma naki gaya mata komai.Har watarana take fad'a min cewar itafa bata yadda da wannan closeness d'inmu da Rukky bah diz days,abin yaban haushi harna zazzageta,tun daga ranar naga ta fita aharkata wanda koh kusa banso hakan bah buh I also hav to stay away from her da kuma brother d'inta. "
Advertisement
"Tausayin Haidar da kuma tsananin son da nake masa ya sanya na kasa barinsa completely.koda ya nemi jin dalilin canza masa,ce masa kawai nayi ya manta da batun.Sannu ahankali muka cigaba da gudanar da soyayyarmu har muka shirya da my Reedah.That bitch notice dat kamar soyayyarmu k'ara k'arfi yake.watarana during break period,tazo ta jawoni ta kaini wani wuri inda babu dalibai,anan na gane cewar abinda take son nuna min yana bukatar privacy.Isarmu keda wuya,tayi saurin janyo hannuna ta damk'a min wasu pictures masu d'an yawa tana fad'in......"Gal see it for urself..... ai ina yawan baki labarin munanan halaye na Haidar kinki ki rabu dashi har wani k'ara lik'e masa kike right? Toh yau ga zahiri nan ki gani awannan hotunan dake hannunki..... B'arin jikin Mey kike yi? Ki duba mana.... "
"Da sauri na soma duba hotunan cike da tashin hankali.... Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un....abinda na gani ajikin hotunan ya sanya nayi kokarin sakin ihu,I juz can't believe it,Haidar d'ina wanda nake mutuwar k'auna ne akwance atsakiyar 'yan mata,sun rungumoshi, dukkansu zindir haihuwar uwarsu,ga gwalaben giya ijje agabansu,wani hoton dana duba kuma,shine tare da maza yan'uwansa suna aikata abinda Allah yayi tsinuwa ga duk mai aikata shi wato 'Luwad'i'..Sauran hotunan suma duk babu d'adin gani,ga yanan kuma fuskar Haidar yafi na kowa d'aukuwa adukka hotunan.Koda na tambayi Rukky inda ta sabo wannan hotunan,ce min tayi kawai na manta tunda dai naga abinda tasha gayamin ayau.Anan kuma tayi confessing cewar itama ada can ta soshi amma data ji labarin munanan halayyarsa da kuma irin son da ni kuma nake masa shiyasa ta jah baya. "
"Reedah itace wacce na soma nunawa wannan hotunan,hakika Reedah ta shiga cikin wani irin tashin hankali,ce min take tayi... "Wallahi Suhaima wannan bah Yaya Haidar d'ina bane,wallahi ba halinsa bane sharri ne kawai,so ake ashiga tsakaninku,please ki fad'a min wanene ya baki wannan hotunan? Ta fad'i hakan tana kuka "......... Ce mata nayi"Wannan bah matsalarki bace,ki bari shi Yayan naki zai mana bayani da bakinsa donni sam ban yadda dashi bah."
"Koda na nunawa Haidar wannan hotunan har kuka sai da yayi,ya matsa min wai alallai dole saina fad'a masa wanda ya bani hotunan,tunawa nayi da gargadin Rukky agareni ah inda tace"Karki kuskura ki fad'awa kowa cewar nina baki wannan pictures d'in... Idan har kuwa kika yi gangancin yin hakan,toh I promise to make your life miserable and dat of ur family too".... Nasan cewar Rukky zata iya aikata abinda ta fad'a,shiyasa koda ya matsa min naki fad'a masa cewar itace.Mun kai kusan shekara d'aya da rabi muna soyayya da Haidar,adalilin wannan matsalar data kunno kai ne yayi sanadiyyar rabuwarmu,babu yadda Haidar da kanwarsa basuyi bah donna hakura kuma nayi accepting cewar sharri ce kawai akayi masa amma naki ji.Haka shima ya hakura dani har ya daina zuwa makarantarmu bayan alot of begging da yake tayi amman naki saurarensa,shine yayi zuciya ya rabu dani,koda zai tafi,kwace hotunan yayi ahannuna yace" Insha Allahu Suhaima koba jima koba dade wallahi sai gaskiya ta bayyana kanta,and I will make sure dat the culprit behind diz pay for tarnishing my image... Saduwar alheri Ruheena💗"...... Hakika nayi kuka sosai kuma nasan na rasa mai sona tsakani da Allah,but the fact is dat,har yau zuciyata ta kasa yarda da cewar Haidar d'ina yana aikata wannan munanan halayen,gashi na kasa bashi chance ya kare kansa,Ahakan kuma friendship d'inmu ni da Reedah ya yanke don har yau haushina take ji sosai... Kwatsam! wani sabon al'amari nazo naga wai Haidar d'ina ke dating 'yar'uwata wanda hakan ya sanya tsanarsa dada linkuwa acikin zuciyata....... "
Advertisement
Tana kaiwa nan da labarinta tayi shiru,ayayin da kuka ya biyo bayan shirun,kuka take rerawa mai daga hankali kuma ga dukkan alamu ya nuna babu mai niyyar lallashinta.
Ash ce ta mike afusace tana huci,nuna Leedar take da 'yar yatsa don alamu ya nuna maganganun Suhaima akansa sunyi nasarar tasiri agareta,tace"Leedar ashe dama haka kake?ashe dama kafurar zuciya gareka shine muke mu'amala dakai all diz while bamu sani bah?.... What a mess!! Wallahi anyi asarar haihuwa anan.....Kuma bari kaji.............."
Fresh ne ya katseta tare da d'oka mata tsawa cike da jin d'acin munanan kalaman data jefawa amininsa,yace"Enough of that baby gal!!... Ban taba tunanin cewar kema zakiyi accepting irin wannan sharrin da aka lik'awa friend d'inmu bah.... Amma ayau kinyi min proving cewar ke d'in bakida kaifin tunani,ba tare da kinyi wani dogon nazari bah kawai kika yanke hunkunci... Sam Aliyu bashi da alak'a da wannan munanan halayyar da Suhaima ke zarginsa akai.... "
Kallon fresh tayi, irin kallon karka raina min hankali mana,tace"Idan har da gaske sharrin ake masa.... Then let him defend himself... Allow him to talk for himself and not by u attempting to become his mouth piece.....Abdulbasi Bashir please allow him to talk,we need proving..... wen I say proving,I mean practically proving with full of evidence...... "
Tun sanda aka fara wannan labarin sai yanzu Fadima ta sako bakinta cikin zancen,tace"Wai ke Aysha meyasa kike haka ne? Yanzu sabida Allah ace duk tsawon lokacin nan da muka d'auka tare da Leedar bai ci ace kin san halayyarsa bah? Yanzu har kin gama yaddar wa kanki cewar Haidar zai iya aikata abinda ake zarginsa akai? Huh tell me Ash which kind of human are you da ko wani lokaci burinta kawai is juz to make things worst? "
Da sauri Ash ta fuskanci Fadima tace"Kinga Fadima ya isheki hakanan, Karki kuskura ki gaya min bakaken maganganu....... Da kike cewa yaci ace nasan halayyarsa,dayake ina binsa ko'ina ne, ko kuma ina ah tare dashi all the time da har zan gama sanin halayyarsa right?.... Dad'in abin mah ita karan kanta budurwar tasa tana zarginsa akan hakan,so please u guys should not be mad over me..... Better save ur energy don har yanzu we are still on the matter..... "
Leedar shi dai kasa cewa komai yayi tun sanda friends d'in nasa suka soma musayar kalamai,illa rufe idanuwansa da yayi da karfi yana mai jin wani irin zogi acikin zuciyarsa,shi zargin da Ash take masa ko kadan bai taba heart d'insa bah,shi kawai kukan da abar k'aunarsa ke rerawa ne ke masa ciwo wanda hakan na nufin she is really hurt.
Da sauri ya bud'e idanuwan nasa ya saukesu akan Ash wacce sai faman aika masa da sakonnin harara take,ahankali yace"Guys enough!!..... Ku kyale Aysha ta Fad'a min maganganu son ranta, ko kadan karku ga laifinta,haka kuma kar kuga laifin Suhaima because it is not easy mutum yaga hoton masoyinsa ah irin wannan yanayin har ya wani tsaya dogon nazari koh bincike.... Please kar kuga laifinsu don duk wanda yaga wannan hoton,idan ba sanin gaske ya min bah,toh wallahi zai yi wuya ya yadda kai tsaye cewar sharri aka min.... Dad'ina mah d'aya Suhaimar kawai aka kaiwa wannan hotunan wanda ga dukkan alamu nema akayi ashiga tsakaninmu kuma har akayi nasara.....ban san wani irin kallo mutane zasu yi min bah if to say dat pictures have been spread.... Nagode Allah dah hotunan suka tsaya akanta kawai... "
Cike da tsana yake kallon inda Rukky da Yazeed suke zaune wanda kana ganinsu kasan tabbas sunyi nadama kan abinda suka aikata.
Wata tsawa ya dok'a musu"Zaku soma bada labarin yanda kukai kuka b'ata ni awurinta ko kuwa sai na soma da cin ubanku tukunna?Kai Yazeed na daukeka dan'uwana not juz a friend but kai ka nuna min halin dan'adam....I was suprised da kazo kana confessing cewar wai dakai aka had'a baki aka kulla min wannan sharrin..... Wallahi sai Allah ya mini sakayya.... "
"Dan kutumar ubanki zaki soma bayani koh kuwa so kike na taso na babballaki anan wurin? " afusace yayi wurin Rukky yana fadin wannan maganar.Fresh ne ya taso ya rukoshi because yadda ransa ya mugun b'acin nan,anything bad can happen.
Ya maidashi mazauninsa yana d'an bubbuga kafad'arsa yana fad'in"Relax buddy....act like a man,kayi kokarin fin karfin zuciyarka kada ta sanya ka tafka babban kuskure anan wurin... "
Suhaima ce ta tsai da kukanta ganin Rukky na kokarin soma bayaninta.
Da rawar murya Rukky ta soma da"Tun sanda na soma kyalla ido akan Haidar,naji kawai ya tafi da imanina gabaki daya har naji ina kwadayin son aurensa.Alokacin da nake kaiwa Suhaima maganganu akansa,adaya bangaren kuma inata kokarin cusa kaina awurin Haidar wanda sam ita Suhaima bata san da wannan ba,haka kuma na lura shi Haidar d'in bai taba fad'a mata cewar ina bibiyarsa ba,sai faman wulakanci yake min, infact hadda duka ya taba sanya amin sanda naje unguwarsu nemansa."
"Dukan daya sanya amin bah karamin bakanta raina yayi ba,hakan yasa naci alwashin he must pay for it.... Na dau alk'awarin cewar idan nice tilon 'yar Khaleel Lema sai na rabashi da ita Suhaimar wacce ya fifitata akan kowacce 'ya mace........"
"K'arya kike 'yar gidan mahaukata.... Baki isa ki raba Ruhee💗 da gangar jikinsa💝 ba.... Allah ne kadai keda isa da kuma ikon rabamu ba mutum ba....koda kika yi nasarar shiga tsakaninmu na tsawon lokacin nan,hakan bai hanamu daina son juna ba,gangar jikinmu ne kawai basu atare damu amman kuma ruhinmu na tare da juna...... In that case,Kinga kuwa kafirin burinki bai cika bah.... Ur dirty mission of doing such as failed u ugly bitch..... " Leedar ne ke fadin wannan maganganun cike da tsanar Rukkyn.
Rukky ta cigaba"Haidar ka kirani ko mai kaga damar kirana bazan tankaka ba because ni na janyo mah Kaina wannan cin fuskar.. "
Ta koma kan labarinta"Nazo ina yawan ganin Haidar ah unguwarmu,ashe dai wurin Yazeed yake zuwa don Yazeed d'in unguwarmu d'aya dashi.Yazeed kuma yasha kawo min harin cewar yana sona,amman irin so d'in nan na to get in between my legs,ban taba bashi fuska ba because ni guy d'in ko kadan bai min bah.Ganin ina da bukatar abu awurinsa shine na soma nemansa da Kaina.
"koda na fad'a masa labarin Haidar,dariya yayi sosai yake ce min ai shima ya dade yana jin haushinsa kawai babu yanda ya iya ne,amma tunda nazo da batun yanda zamu rabashi da budurwarsa,zai tayani amma sai na amince zan bashi d'and'ano na koda sau d'aya ne,wanda atake anan na amince da hakan...... "
"Auzubillahi!!! tir!! da wannan hali naki..... Mazinaciya kawai..... " Fresh ne ya fad'i hakan tare da yamutsa fuskarsa.
Leedar kuma cewa yayi"So dirty..... " ya tofar da yawu.
"Disgusting..... " acewar Ash
"Allah ya shiryeki.... " acewar Fadima.
"Azabar Allah su tabbata agareki..... " acewar Suhaima wacce ga dukkan alamu tafi jin haushin Rukkyn.
Da sauri Rukky tayi Murmushi tace"Haba guys wannan tofa albarkacin bakin na menene haka?..... Ke kuwa Suhaima kar kiyi zaton duk abubuwan nan da nakeyi banda ilimin addini ko kadan.... Idan kuwa hakan kike tunani toh tabbas tunanin naki bai fad'a miki gaskiya ba.... la'antana da kike yi tana iya yiwuwa kina rage min zunubi ne kina d'orawa kanki because,Allah SWT yana fad'in cewa"Karku shiga tsakanina da bawana,Inna so nayi musu Rahma,haka kuma Inna so nayi musu azaba.... Don haka baki da wuta koh aljannar da zaki sakani aciki,idan bazaki min fatar shiriya kamar yadda yar'uwarki ta min ba,toh please kiyi shiru da bakinki, ance ka fadi alheri ko kayi shiru..... So take note Mrs Haidar. "
Gaba d'aya jikin kowa sai ya d'anyi sanyi.
Ta cigaba"Yazeed came up with the idea of photo edition....... "
"Photo edition?? " Suhaima ce ta fad'i hakan cike da mamaki.
"Photo what???? " acewar Ash itama face full of suprise.
Rukky tace"I will repeat myself.... Cewa nayi photo edition... Yazeed yana karatu ne ah UK ah inda yake karantar ilimin kimiyya ta na'ura mai kwakwalwa (computer science),kuma ya tabbatar min da cewar shi d'in computer expert ne don haka da zarar ya koma UK zasu hada hannu shida wani abokinsa suyi editing hotunan batsan nan sannan su sanya face d'in Haidar,kunga abokinsa ne don haka bazai rasa pictures d'insa awayansa ba "
"Ba'a wani dau tsawon lokaci da komawarsa UK ba,ya aiko min da hotunan ta e-mail account d'ina,cike da murna na wankesu na kaiwa Suhaima...Ni kuma tun daga ranar na daina bibiyar Haidar gudun kada asirina ya tonu duk da cewar nasan na gargade ita Suhaima akan kada ta kuskura ta fad'a masa wanda ya bata pictures din,amma still inata tsoron kada ta fallasa,dalilin dayasa naja baya dashi kenan.... Toh nan na kawo karshen labarina... Da fatar zaku hada kai ku yafemun..... "
"Kamar naji kin ambaci yafiya juz now.... Idan kuwa hakane ina son ki sanya aranki cewar kalmar 'SORRY' mah bata existing ah diary d'in Aysha Adam balle 'FORGIVE' idan har abinda mutum ya aikata yayi shine kan zalunci da cutar wani..... Wallahi wallahi Sunana Aysha Adamu kangiwa,don haka mai rabani dake anan wurin yau sai ya shirya....... " cewar Ash queen.
Ita kuma Suhaima mikewa tayi ta nufi inda Rukkyn ke zaune fuskarta babu koh d'igon annuri,tamkar bata taba yin dariya bah........................ 📝
*Masoyana kashi dai nayi kokari nayi muku typing don kada kuji shiru da yawa.ku cigaba da sanyani cikin du'a'inku don har yanzu jikin ba dadi... Nagode.
*Comment
*Vote
*Follow &
*Rebroadcast
TAKU
©QUEEN HAFNAN©
Advertisement
- In Serial35 Chapters
Heretic King
The world ends, game system is invoked, yada yada. After the system set by God causes Thomas Crowe to go crazy, he swears he will kill God, thus getting deemed a Heretic. How will the story go from there? Will he slay God or will he die trying to resist?Mature cause curse words will be used and sex scenes described.. More tags as the story develops.There is references and terms used from other stories. I will link the references If I feel it's not as obviousIf you can give me your opinions in the comments it's my first time writing and I'd love some feedback.Credits to Yang_God_Of_Games_And_Power for the cover!
8 202 - In Serial9 Chapters
The Wax Wind Conspiracy
Spirits were high when the luxurious Wax Wind skyship made its maiden voyage from Clementine one warm Noonsday evening. But the Wax Wind would never reach its destination. And its passengers would never be heard from again. Follow the stories of these passengers as they struggle to survive the nightmare they'd unknowingly stepped into, and unfurl the cryptic conspiracy that had devoured them all. The Wax Wind Conspiracy is a fantasy murder mystery set aboard a massive airship in a world of strange creatures, awful food, and weird magicks. But, in the end, it's a story about people. Updated every Monday and Friday. Stay safe.
8 179 - In Serial10 Chapters
Changement : Version Face [French]
Notice: This story is in French, not in english, mainly because of my poor english. I may translate it later if I get better, and hopefully I will. _ Les cris de souffrance résonnent dans ses oreilles, dans sa tête et dans son coeur. Cette dernière image, ces derniers instants, ces morts incompréhensible, rien ne sera plus jamais pareil pour Nils Nocquat. Il sombre, et dans les ténèbres, découvre la fache cachée de son monde. Qui est coupable? Démon, Ange et autres Sonen, tous se renvoient la faute, et maintenant, Nils Change, il doit faire un choix. Indécis, il lance une pièce. Face. Il a choisi son camp. Il deviendra un Ange, le meilleur ou le pire de tous, ce n'est qu'une question de point de vue. - Author's note: this story is a concept. During the first chapter, the main character is faced with a major decision, which will change his life forever, and, not knowing what to do, he decide to play heads or tails, and let fate choose for him. And so there will be two versions of this story, one for each of the result, and their consequences for the main character, as well as all those around him. Here, he got heads. Note de l'auteur: Comme dit plus haut, cette histoire sera en français, car je ne suis pas assez bon en anglais. De plus, cette histoire est un concept un peu particulier, le personnage principal va se retrouver face à un choix décisif qui va changer sa vie pour toujours, et, ne savant pas que faire, il va jouer à pile-ou-face, en laissant le destin décider pour lui. Il y a donc deux versions de cette histoire, une pour chacun des résultats de son lancer. Lien de l'autre version: https://www.royalroad.com/fiction/28317/changement-version-pile-french Je vous encourage à ne pas lire les deux versions, ou en tout cas, à ne pas les lire en même temps. Elle sont assez peu similaires, mais des choses vont, logiquement, être répétées, et les confusions risquent d'être rapides, surtout au début des histoires. Dans tout les cas, ces deux histoires vont s'éloigner assez rapidement, tout en restant intrinsèquement liées par leurs personnage principal. Libre à vous de choisir la version qui vous plaît le plus, sachant que vous n'aurez pas besoin de lire les deux pour comprendre toutes les intrigues, elles sont absolument indépendantes l'une de l'autre. C'est la deuxième fois maintenant que je publie quelque chose que j'ai écrit, mais ça ne me rends pas meilleur en terme d'orthographe et de grammaire, donc si vous relevez une erreur, où même si vous remarquez des incohérences, n'hésitez surtout pas à me le faire remarquer. Toute critique, qu'elle soit positive ou négative, est appréciée. En terme de rythme de publication, je pense sortir un chapitre par semaine dans chacune des deux histoires.
8 149 - In Serial41 Chapters
A Sirius Matter [Harmione]
AU A few days after being rescued from the dementor's kiss, Sirius Black decides to share information with Harry about his destiny. The story continues on from there.DISCLAIMER: THIS STORY IS NOT MINE THIS BELONGS TO witowsmp. THIS IS ORIGINALLY BEEN POSTED IN FANFICTION.PORTKEY.ORG BUT THAT WEBSITE IS NOW DOWN. I AM ONLY POSTING IT HERE FOR YOU GUYS TO ENJOY IT. THIS STORY IS NOT MINE THIS BELONGS TO witowsmp.ART BY : -Metempsychosis-
8 167 - In Serial35 Chapters
the black phone preferences
the black phone preferences (maybe some imagines)(only finney and robin until part 34)
8 163 - In Serial11 Chapters
Scenes from my life as an ABDL
Hey! I decided to write some real scenes from my life as an ABDL, just so I can have a nonfiction story on here.
8 178

