《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER TWENTY ONE
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
Dedication:wannan chapter d'in sadaukarwace ga dukkan masoyana to show my appreciation for ur true love and support especially my WhatsApp group members. Ina gaidaku.... One love to u all and also to you my watpaddians.... Am assuring u dat ana mugun tare✌.
🌼BABI NA ASHIRIN DA DAYA🌼
Page 100-105
"Good morning everyone. " Suhaima ce ta fad'i hakan alokacin da suka isa k'arkashin bishiyar.
"Morning to you too amaryarmu." Fresh ne ya amsa mata tare da kashe mata ido daya.Sauran mah duk suka amsa mata.Idanuwanta ne suka had'e dana Rukky, ta gallawa Rukkyn harara ah sa'ilin data zauna kusa da Ash.ita kuwa Rukky jikinta ne yayi sanyi ganin irin mugun kallon da Suhaimar ta jefeta dashi,hakika tayi nadamar abinda ta aikata, fatanta dai Allah yasa Suhaima da Leedar su yafeta.
Suhaima ce tace azuciyarta"wallahi ganinki bah alheri bane you bloody monster... "
"Ina fatar basai na sake maimaita dalilin taruwarmu anan ba,don kuwa kowa ya riga daya sani idan aka cire Ruheena💗 wacce ta siyasa muka samu aka kawota nan..... In that case,babyna am very sorry for that please..... Kinji masoyiyata? "
Leedar ne ya fad'i hakan tare da tsare Suhaima da idanuwansa yana mai jiran ta bashi amsa.Harara ta wurga masa amatsayin amsarsa kenan.
Daga kafadunsa yayi cikin wani salon bagunsa,alamun bai damu bah,don koh dukansa zatayi bazai iya hanata bah sabida tabbas an b'ata mata.
Cigaba da maganarsa yayi"Ruhee💗 kamar yadda kika sani wannan itace Rukky... She's here to tell her part of the story. " Ya fad'i hakan tare da nuna Rukkyn da 'yar yatsa.
"And wannan shine Yazeed, nasan bah wani saninsa kikai bah sabida so d'aya na taba zuwa dashi wurinki...he is also here to tell us the role he played in the story... "
Kallon wanda aka kira da Yazeed tayi, Kura masa idanuwa tayi babu koh giftawa,tana mai son tunano inda ta taba ganinsa.Ai kuwa ta tunoshi,Leedar ya taba kawoshi su gaisa da ita sau d'aya amakaranta.
Azuciyarta tace"Toh shi kuma meye nashi aciki?Allah dai yasa bah wani salon rainin wayon Haidar yake shirin yi min bah.....amma kodai..... "
Leedar ne ya katse mata gajeriyar tunaninta ta hanyar fad'in"Amma before anything,zanso ace ki bada labarin abinda ke tsakanina dake Suhaima.... Karki rage komai kuma kada ki boye komai..... Kiyi mana bayani in full details "
Gabanta ne ya yanke ya fadi jin abinda ya fad'a,kai dubanta tayi bangaren da Fadima ke zaune.Idanuwansu suka had'e,atake Fadimar tayi mata signal d'in ta bada labarin kamar yadda ya bukata.
📣WAIWAYON BAYA📣
Ahankali ta soma da"Kamar yadda dai kuka sani,Sunana ''.... Ina schooling ah 'Zaria academy',wanda ayanzu haka ina final year d'ina wato 'SS3'.Back then in SS1,Fareeda Ahmad use to be my very good friend... Ni da ita we were best of friends.Though,haduwar tamu was just recently,because ah 'SS1' d'in ta shigo makarantar, sab'anin ni dana fara makarantar tun daga 'JSS' class.Shakuwarmu ta wuce yadda mutum ke tunani.kuma abin mamaki,duk yadda muke so close d'in nan,bamu taba kaiwa juna ziyara agida bah,dayake duk iyayenmu bah masu barin 'ya'yansu suna yawon gantali bane, daga gida sai school, sai kuma islamiyya.Ni da ita ah school kawai muke had'uwa, har takai ta kawo wanda suka sanmu tare suna yawan yi mana gorin rashin ziyartar juna."
Advertisement
Dakatawa ta danyi,ta d'ago kanta tana bin kowa da idanu don ta tabbatar ana tare da ita,ganin an natsu ana sauraren labarinta ya sanyata cigaba da gashi.
"Yayun Fareeda biyu kuma duk maza, Aliyu Haidar wanda kuka fi sani da 'Leedar' Shine babba,sai Yaya Suhail,sannan ita Fareedar itace autarsu...... "
"Lee let her go straight to the point tunda duk nan mun riga mun san tarihinka... "acewar Ash wacce tayi interrupting Suhaima.
Leedar ne ya wurgeta da harara,yace"Ash please don't start ur interruption..... Ki bari ta bada labarin abinda ta sani please. "
Ya juya ga Fresh yace"Dude please talk to ur gal, I hate d way she interrupt into a serious discussion... "
"Noted Buddy!! " acewar Fresh wanda ya kai dubansa ga Ash,yayi mata signal d'in kada ta sake interrupting.
"Muna sauraronki Ruhee💗......."
Suhaima ta cigaba"Reedah kamar yadda ake k'iran Fareeda kenan, tana yawan bani labarin yayanta Haidar, irin shak'uwar dake tsakaninsu da kuma irin mugun ji da ita da yakeyi.... Babu ranar da zamu had'u da Reedah ba tare da ta bani labarin new update akan Haidar bah.Takan bani labarin yadda yake da son gayu da kuma yadda Ladies ke rushing d'insa,amma abin mamaki duk had'uwar nan tasa wai baya da budurwa.Idan tana bani labarin yadda 'yan matan ke bibiyarsa abin har dariya yake bani,sai naji kawai yana birgeni tare da soma experiencing wani feelings akansa."
"As time goes on, kawai naji na soma crushing kan mutumin da ban taba gani bah,ji nayi na kamu da wata matsananciyar sonsa,amma koh kadan ban taba bari Reedah tayi noticing bah.wani lokutan mah da kaina nake cewa ta bani labarinsa,duk da cewar na kanji kishi sosai acikin zuciyata idan tana bani labarin 'yan matan dake bibiyarsa.. "
Leedar ne keta aika mata da sakonnin murmushi jin yadda take fad'awa duniya yadda ta soma sonsa tun kafin mah ta ganshi face to face.Shi kansa bai taba sanin wannan labarin bah sai yanzu da take fad'a musu.
Ganin zai iya rikitar mata da kwakwalwa tare da raba mata hankali gida biyu ya sanya tayi saurin dauke kallonta daga gareshi, ta koma kallon wani gefen.
"Watarana muna zaune during break period, nace mata "Reedah nifa zanso naga wannan d'an gayun yayan naki Aliyu. "
Dariya naji ta sake wanda nayi tunanin zancen nawa dadi yai mata, tace"Sahibata!! Kar dai ace kema kin fashewa yayan nawa.... Juz tell me if u are already crushing on my classic bro so soon tun baki gansa bah.... " Duk da cewar nasan abinda Reedah ta fad'a gaskiya ne,amma sai na sami kaina da jin haushin zancen, nace"Allah ya kiyaye.... Ke kanki kin san nafi k'arfin nan wallahi.... Ki sani bana d'aya daga cikin irin 'yan mata da kike bani labarin cewar suna bibiyarsa.... No, sam Suhaima Sa'ad is different... "
Yunk'urin mik'ewa nayi don bar mata wajen,da sauri ta dakatar dani,"Haba kawata! meh kuma yayi zafi haka? Wallahi ni wasa nake miki,ni kaina nasan cewar kinfi k'arfin hakan kuma kin wuce nan, sai dai shi yama fashe mikin.....please kawalliyata am very sorry idan abinda na fad'a ya zafeki. "
Advertisement
Murmushi nayi mata,nace"Dad'ina dake akwai iya lallami da ban hak'ura. " itama murmushin ta maida min tace"Dole na iya sabida bana k'aunar ganin Suhaimata cikin b'acin rai musamman mah idan akace nice silar b'acin ran naki..... Guess what? "
"Not in the mood of guessing.... Ke dai fad'amin abinda ke zuciyarki kawai. " Na b'ata amsa cike da k'osawar son jin abinda take niyyar fad'a.
"Yaya Haidar shi da kansa zaizo daukata yau d'in nan idan an tashi.... Ina yawan masa gorin cewar tunda na fara makarantar nan bai tab'a zuwa daukata bah shine yamin alk'awarin yau insha Allahu driver ya huta shida kansa zaizo..... For the first time ayau zakuyi ido hud'u da Yaya Haidar d'ina, my best yaya don ina yawan bashi labarinki. " Cike da mamaki nace"Are you serious? "
"Ta tabbatar min da lallai da gaske take.Bazan iya fassara muku yanayin farin cikin dana shiga bah jin cewar I will soon get to see 'my dream man' for the first time.Sai dai ban nuna mata tsantsar murnata bah gudun kada ta sake suspecting wani abin.Koda aka tashi,muna jiran yayan nata yazo daukarta kamar dai yadda tace ya alk'awaranta mata.Shiru-Shiru babu labarin Haidar kuma babu alamunsa,har naji abin ya soma bani haushi kamar na saki kuka sabida yadda naci burin ganinsa ayau d'in nan.Itama Reedah na lura abin ya sosa mata rai ba kadan ba.Can sai gani mukayi driver d'in gidansu yazo d'aukarta instead of Haidar da muketa saka ran gani.Driver d'in ya tabbatar mana da lallai abbansu Reedah ne ya saka shi yi masa wani aikin,dalilin daya sanya shi aka turoshi d'aukarta kenan. "
"Muka rabu da Reedah duk zuciyoyinmu babu dadi.Ana haka ne muma driver d'inmu yazo d'aukarmu ni da Lubna,dayake alokacin mu biyu ne ke ah secondary.Hakika ranar naci kuka har na godewa Allah na rashin yin four eyes da mutumin da ban tab'a gani bah,wanda na bashi suna da 'My dream man'.Ni kaina har mamakin kaina nake ganin yadda nabi na damu da batunsa arana daya,wanda har 'yan gidanmu sukayi tunanin koh bani da lafiya ne.Washegari mah hakan ta kasance ban samu damar ganinsa bah kamar yadda Reedah ta tabbatar min da cewar alallai yau babu fashi yana nan tafe.wannan karon matsalar daga bangarena ne,don driver d'inmu yayi saurin zuwa daukarmu da wuri aranar.Haka na tafi nabar Reedah cike da d'acin rai,abangare daya kuma ji nayi zuciyata na nemar yin bindiga. "
"Washegari Reedah ta tabbatar min da cewar shi d'in kuwa yazo d'aukarta ajiyan.Afarko,na aza koh zolayata take, amma sai data min rantsuwa sannan na yadda, wanda bah hakan naso ba wallahi, naso ace ni da kaina na gansa bawai naji labari bah.I couldn't believe wat I heard, sanda take fad'a min cewar shima baiji dad'in rashin ganina da baiyi bah. "
"Allah mai iko,sai gashi aranar tun kafin atashi yazo d'aukarta,ashe da biyu ya doko wannan sammakon sabida kawai mu samu ganin juna nida shi.... "
Dakatawa tayi,can ta cigaba"Toh jama'a awannan ranar itace mafarin soma haduwata da 'wanda cikin kankanin lokaci wata soyayya mai k'arfin gaske ta shiga tsakanina dashi, tun daga ranar kuwa Leedar ya tsiri zuwa d'aukar Reedah sabida kawai ya samu ya ganni don naki barinsa yasan gidanmu,kuma duk abin nan ban tab'a gayawa kowa agida cewar ina da saurayi bah gudun hukuncin da zan fuskanta daga Abba don ya tsani yaga 'ya'yansa da saurayi at secondary level stage.Dan har Yaya Fadima ta gama Secondary d'inta bata da saurayi ko d'aya duk da cewar tana samun many crushes amman fuskace kawai bata basu. "
Kallon inda Rukky take zaune tayi,sannu ahankali kuka ya sub'uce mata,nuna ita Rukkyn take da 'yar yatsa,tace"Wannan da kuke gani mai fuskar shanun itace tayi sanadiyyar rabani da masoyina kan wasu dalilai dani kaina har yau naki baiwa Haidar damar explaining kansa..... Yarintar dake d'awainiya dani alokacin yaki bari na bashi damar kare kansa,kuma har yau zuciyata ta kasa yadda da abinda idanuwana suka gani agame da abinda Haidar d'ina ya aikata........."
Da rawar murya Ash tace"Shin wani laifi wannan baiwar Allahn ta aikata agareku? Fad'a min kanwata don ashirye nake na soma cin malfar ubanta...."
Leedar ne ya koma kusa da ita yana d'an matse k'walla don tausayin masoyiyar tasa,duk shine ya sanya take tunano baya"Ruheeta💗 kalli cikin kwayar idanuwana.... "
Da sauri tayi yadda ya umarceta,Idanuwansa ta gani sunyi jajawur dasu kamar jan gauta,ga wasu k'walla sun tarun masa acikin idanuwan.
Yace"Kin yarda cewar na aikata hakan? "
Sanyi jikinta yayi,tayi saurin dauke kanta daga kallonsa,zuciyarta na son ta yadda dashi ayayin da wani b'angaren ke tunatar da ita halin d'a namiji.
Ahankali yace"Fine..... Tukunna bada labarin laifin ita Rukkyn don Ash ce kawai take acikin duhu..... "
Bud'e baki tayi ta soma magana........................ 📝
Kai habibtee's diz typing is not funny at all.... Ku cigaba da hakuri dani.
Kuyi hakuri da kadan d'in da kuka samu cuz am busy diz days, sai dai fah bazanyi gangancin manta daku bah,zanta updating duk sanda na samu lokaci,all I want u guys is dat kuyita appreciating the little u get!!!
Nasan tarihi babu dad'in ji kun matsu akoma ainihin labari.... Amma idan zaku duba ya kamata ace an warware muku dangantakar dake atsakanin Leedar da Suhaima kafin acigaba da gashi. Thanks.
*Gaskiya u guys ain't proving ur love for me at all..... Votes and comments sunyi kasa da yawa. *
SAHIBARKU CE
💟©QUEEN HAFNAN©💗
Advertisement
- In Serial26 Chapters
L'Empire de Cendres
Devenez un chevalier du troisième millénaire! READ IN ENGLISH Au temps jadis, l’humanité régnait sur Terre et rêvait des étoiles. Mais cette époque est désormais révolue. La civilisation telle que nous la connaissons n’existe plus. Irrémédiablement balayée à la suite d’une mystérieuse catastrophe, elle est aujourd’hui à l’agonie ; oscillant entre un passé brisé et un avenir sans espoir.Erol, archéologue et aventurier du IIIe millénaire, parcourt dans le secret les ruines souterraines de l’Ancien Monde. Bravant la maléfique Inquisition et son obscurantisme, il réalise un jour une remarquable découverte. Dans un sarcophage de verre au plus profond des dangereux labyrinthes, repose une jeune femme ultime témoin du cataclysme.En quête de réponses, Erol va provoquer des évènements en suspens depuis mille ans et libérer des forces qui auraient dû rester ensevelies à jamais. L'Empire De Cendres est le tout premier roman de Quentin Raffoux et Aliénor Rossi, auteurs de l’irrévérencieux KITTY KITTY - Le futur qui ne fut jamais. L'histoire, qui se veut plus sombre, vous maintiendra en haleine jusqu’au dernier acte de son antihéros, Erol Fueurhammer. Pour plus d'informations, visitez notre site internet: raffourossi.com Le livre est disponible en kindle et broché sur amazon Les chapitres seront téléversés sur Royal Royal tous les Jeudi, 15:00 - heure de Paris
8 153 - In Serial11 Chapters
Interstellar World Struggle TV
Ever wondered how an apokalypse could happen in other countries beside the US ?Arn Tschiller, a student of the Karlsruhe Institute of Technology, makes a tourist cruising drive at the north sea. Suddenly, a big explosion illuminates the horizon, and the ship braces for its impact of the airstruggle. As the effects go by, everybody on the ship gets a note :Welcome to Interstellar World Struggle TV....Author's note :Hello everybody, this is my first attempt to contribute to this site. As written above, I wanted to submit a fiction of an apokalypse in another country then the US. Don't misundertand me, I love this sort of stories, like Once a hero and Apocalyse now (2) , which are clearly also 2 of my role models.But nor the whole world circulates around the US, as also Insania online can show.So i would be delighted about comments, reviews and suggestions to this fiction.Thank you in AdvanceDARTHKECKS
8 104 - In Serial14 Chapters
The Kingdom
A young man wakes up in a dark room only to find out that he does not who he is. With his determination to unlock the mysteries of his past, he starts an adventure.
8 73 - In Serial9 Chapters
Fundy x Reader
REQUESTED FANFIC FUNDY - 2020 AUTUMNthis is a big ass joke, i literally gave up half way through but someone kept telling me to keep writing so..also i ended the story thingy short coz it's annoyingtell me if I should take it down if any news comes about that he doesn't like this stuffNo pictures are mine But will be edited by me(fem reader)REPUBLISHED AFTER ACCOUNT WAS ON STANDBY
8 217 - In Serial37 Chapters
Death Note Boyfriend Scenarios
Hey guys!!!! 👋≧◉ᴥ◉≦Thank you so much for clicking on this story xD In here are a bunch of Death Note Boyfriend Scenarios! Death Note is my absolute favorite and I always love reading scenarios so I thought to make some of my own for you guys ;).Inside are scenarios for: Light, L, Mello, Matt, and Near.Please feel free to suggest any scenarios for me. I'm sure I'll need some help along the way :P Thank you guys, and enjoy!
8 119 - In Serial32 Chapters
Idk You Yet 『Bakugou Katsuki x reader textfic』
【 When an "accidental" wrong number leads to a lot of different emotions, y/n and Katsuki have to try and figure out what they feel for each other before they meet after tests. 】》Started: November 9, 2020》Start of posting: December 30, 2020》Completed : January 31 2021Inspired by the song Idk You Yet by Alexander 23Idk You Yet Bakugou Katsuki x reader Textfic
8 85

