《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER TWENTY
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
Sorry infinity to you all my Habibtee's for delaying u guys.... Ku cigaba da hakuri dani don mai hakuri shi yake dafa dutse har yasha romonsa.
🌼BABI NA ASHIRIN🌼
Page 95-100
Cikin mintunan da basu wuce goma ba, Mahmood ya isa kofar gidan Mubarak. K'iransa yai awaya ya fad'a masa cewar ya fito ya sameshi awaje don sauri yake.
Mubarak dake zube akasan carpet yayi saurin mik'ewa don amsa k'iran dan'uwan nasa.Gama cin abincinsa kenan ya kwanta awurin, don shi da kansa ya sake shiga kitchen ya dafa masu abinci mafi sauki wato indomie da kwai.
Kallon Hanan yayi wacce ta tsareshi da sexy blue eyes d'inta tana mai jiran yayi mata bayanin wanda ke k'iransa awaje.
"Matar Mubeen kallon ya isa hakanan idan bah so kike na kasa fita bah... " Ya fad'i hakan tare da kashe mata ido daya.
Murmushi tayi wanda ya sanya har sai da dimples d'inta suka lotse cikin kumatunta, tace"Rufa min asiri mijin Hauwa'u.... Wake nemanka awaje? "
"Asirinki arufe matata....Yaya Mahmood d'inne ya iso... " Don dama ya riga ya fad'a mata cewar zaizo.
Da mamaki tace"Laah! Kaji Yaya shine bazai shigo bah? Sai kace wani bako? "
"Wai sauri yake... Or maybe he is thinking the gate is locked.... Lemme go and see him... "
Tun ranar da Labeebah tayi masa gorin rufe gida, toh tun daga ranar ya soma barin gate d'insu abud'e.Sanin hakan ne ya sanya Hanan son jin dalilin daya sanya bazai shigo bah.
Jasmine ce tabi bayansa da gudu ganin ya nufi hanyar waje, sai faman nanata magana d'aya take"Daddy Nima zanje wurin Daddy Mahmood.. "
Bai saurareta bah, ya sanya Kai ya fice tare da rufo kofar falon, don ya tabbatar magana ce zasuyi mai muhimmanci da dan'uwan nasa, shi yasa yaki barin Jasmine d'in ta biyoshi.
Yana jin sanda Hanan tace"Ni dai Allah yasa lafiya dai... "
Mahmood da kansa ke kwance akan sitiyari,yayi zurfi cikin tunani,k'arar bud'e gate yaji, wanda hakan ya sanya yayi saurin d'agowa ya maida kallonsa gun Mubarak wanda yaga ya tunkaro motar.
Lek'o da kansa yayi waje,yayi magana yadda Mubarak d'in zai jisa, yace"Dan'uwa zagayo ka shigo ciki... "
Mubarak yayi hakan kamar yadda Mahmood d'in ya umarcesa.
"Brother barka da dare.... " Mubarak ya fad'i hakan ah sa'ilin daya zauna kan kujerar mai zaman banza.
"Barka kadai.... Ya yinin iyalin naka...? "
"Alhamdulillahi kaseeran!!... Brother lafiya kuwa kake nemana da gaggawa haka? " Mubarak yayi masa wannan tambayar cike da fargabar amsar da zai biyo baya.
"Lil calm down.... Pls kada hankalinka ya tashi,lafiya sumul, sai mah maganar alherin dake tafe dani... " Ya fad'i hakan in a matured voice.
Murmushi Mubarak yayi tare da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya,yace"Alhamdulillah! yanzu hankalina ya kwanta.... amma brother shine zamu tsaya acikin mota muyi maganar? Why not mu shiga cikin gida muyi discussing atsanake? "
"A'ah basai mun shiga ciki bah, as I told u earlier, sauri nake... Ina da abubuwa da yawa agabana... Maganar da zamu tattauna bazai wuce juz 10mins bah.....Afterall, tambayoyi kawai nake son na maka, kuma make sure u give me back sincere answers.... "
Ahankali Mubarak ya furta"Insha Allah brother zan fadi maka abinda na sani....Don haka am all ears. "
Ya fad'i hakan tare da tsare Mahmood da idanuwansa yana mai jiran yaji tambayoyin da zai suburbud'o masa.
Tsawon dak'iku goma Mahmood ya d'auka ba tare da koh tari yayi bah,da alamun ya rasa ta inda zai soma maganarsa ne.Can ya tattaro basirar da Allah yai masa ya soma magana.
Advertisement
In a classy way, yace"Mubarak maganar ce ta kawoni nan.... "
"wacce Fadima Zahrar? " Mubarak ya fad'i hakan cike da mamaki.
"Fadima dai budurwarka.... " Mahmood ya bashi amsa immediately.
Mamaki ne ya kusan kashe Mubarak azaune, don shi bai taba tunanin yayan nasa zai k'ara gangancin shiga cikin zancensa da Zahransa bah idan akayi la'akari da fadan daya shiga tsakaninsu kwana biyar da suka shud'e.atunaninsa cewa zaiyi " Fadima Jasmine d'iyarka nake nufi".... Sai kuma aka samu akasin hakan.
Mubarak bai gama shanye mamakinsa bah,yaji Mahmood ya soma jefo masa farkon tambayarsa wanda ya sanya jikinsa yin sanyi kalau.
Cewa yayi"do u truly love
Tambayar yazo masa azuwan kamar rainin hankali,tunawa yayi da cewar matambayin wansa ne, hakan ya sanyashi yin calm.
Yace"Brother ban gane inda wannan tambayar taka ta dosa bah... da'ace bana son Zahra ai kai kanka kasan bazan taba yin rigima da family d'ina akanta bah..... "
"Bana son wata doguwar surutu....har yanzun sonta kake da aure koh kuwa a'ah ka hakura da ita kamar yadda ka fad'awa Mummy shekaranjiya? "
Ahankali Mubarak ya iya furta"Hakika son da nake yiwa Fadima Zahra, So ne na tsakani da Allah.... Kuma am ready to marry her idan har Mummy ta bani izinin hakan.. "
Wayyo! Hakika wannan maganar ta Mubarak tayi nasarar cakar zuciyar Mahmood.wani irin zazzafar kishin Fadima ne yakai masa mugun cafka acikin zuciyarsa.Ji yayi zuciyar tasa na tafasa da sauri kamar zata faso kirjinsa ta fad'o waje.Sannu ahankali, wasu tears of sorrows suka soma gangarowa saman cheeks d'insa bah tare da Sanin Mubarak ba,sabida duhu daya karade wurin.
Ta maza yayi, yace"Shikenan I have heard u... tambayar karshe itace... Kana da bukatar taimakona acikin lamarin nan naka? "
Cike da mamaki Mubarak yace"Brother idan na fahimceka.... U mean zaka tayani shawo kan Mummy har na samu na cimma burina ta mallakar Zahrata?"
Wani d'aci Mahmood yaji aransa ah sa'ilin da Mubarak yace"Zahrata."
Azuciyarsa yace"Zahran Mahmood Mustapha dai not yours Mubarak Mustapha."
Azahiri kuma cewa yayi"Yes hakan nake nufi.... Insha Allahu!! zan tayaka shawo kan mahaifiyarmu har ta amince ta baka izinin aurota...amma kuma da sharad'i....... "
Da sauri Mubarak yace"Meye sharad'in brother? "
Murmushi Mahmood yayi,kafin yace"Sharad'in shine..... Bana son ka sake tada maganar Fadima agun mahaifiyarmu tunda hakan na janyo tashin hankali...kabar komai ahannuna, ni nasan yadda zanyi na shawo kanta da siyasa..."
"I can see dat kai namiji ne wanda idan har yana son abu toh kuwa sai duniya ta sani,wanda gashi matarka Hauwa'u ta riga tasan da zancen Fadimar har take tayaka kafa gwamnati..... Shin Mubarak ka taba tunanin hakan da kakeyi kyautatawace ga Hauwa'u? bar ganin tana nuna maka cewar ta fika kaunar abinda kakeso kace zaka cigaba da bata labarinka da Zahra ko kuma ka cigaba da nuna mata kafi son Zahra akanta.... Sam Mubarak zaka iya rasa Hauwa'u wataran idan ka cigaba da hakan continuously,because yawan danne kishin Zahra azuciyarta zai iya haifar mata da wata cutar watarana, ba wai fata nake bah.... In this case, sharad'ina na biyu shine.... Stop discussing everything with Hanan relating to Fadima Zahra....please Mubarak I don't wanna loose my cousin idan kai u don't value her, I do... "
Hakika Mubarak yaji ciwon maganar Mahmood na karshe, dayace"If you don't value her, I do.." Wato nufinsa Hanan bata da wata muhimmanci agunsa kenan.
shanye takaicin yayi sanda ya tuna da magana mai dad'i daya taho masa dashi, wato maganarsa da Fadima Zahra.
Ahankali yace"Duk na karbi sharudd'anka da hannun bibbiyu brother.... Hakika kai Dan'uwa na gari ne mai son yaga k'aninsa cikin walwala da farin ciki.... Allah ya biyaka da gidan Aljanna, kuma Allah ya sanya alheri akan abinda kake niyyar yi wato taimakona.... "
Advertisement
"Ameen thumma Amin... And dat reminds me.... Ur condition starts working right now.... Karka kuskura ka labartawa Hanan abinda mukayi discussing... Idan ta nemi jin dalilina na nemanka, juz find something dat will cover up.... Is dat taken?"
"Insha Allah brother zaka sameni da bin dokokin daka d'orani akai....
Daga hakan sukayi sallama, Mubarak ya fito daga motar ya nufi cikin gida, ayayin da Mahmood ya bishi da kallo.
Gaskiyar lamari kuwa shine, bah tambayoyin da Mahmood yaso yiwa Mubarak kenan bah,yazo ne yasan full details abouh Fadima sa'ad cikin siyasa.Amma ah sa'ilin da suka had'a idanuwa, sai yaga Mubarak d'in yai masa kwarjini da yawa wanda atake anan tambayoyin daya yi niyyar yi masa agame da Fadimar ya b'ace masa acikin kwakwalwa,sai ya samu kansa da jefo masa wannan unnecessary questions d'in kamar yadda yake gani.
Ahankali ya saukar da wata ajiyar zuciya, yace"Fadima Zahra why do I so much love you tun ban zauna dake nasan halayyarki bah?..... Bai dace ace naje gidanku kai tsaye bah dats why nake nemar naji full details abouh you daga bakin k'anina.... Gashi my mission of doing such has failed... tunda na bige da masa wasu tambayoyin banza ne.... "
Tada motarsa yayi yabar unguwar. Sai aikin tunane-tunane da nemar mafita yake.
"Ta ina zan fara? "hakan ya fad'a in a cool voice.
Ya sake cewa"Or should I pay her a visit tunda cikin kwanakin nan ina da abinda zanyi ah Zaria? "
Bugun sitiyari yayi,yace"No, bad idea!!!... zata nemi sanin dalilin kai mata ziyara wanda she might suspect something immediately...and dat won't make any sense at all... "
Haka dai yata sambatunsa shi kadai, ikon Allah ne dai kawai ya kaishi gida lafiya.
Bangaren Mubarak kuma,yana isa cikin gida, matarsa ta nemi jin dalilin daya sanya Mahmood ke nemar ganinsa da gaggawa haka.
Kamar dai yadda Mahmood ya gindaya masa sharudd'a wanda ciki hadda yi masa hani da labartawa Hanan zancen Fadima, toh sai ya sami kansa da bin umarnin dan'uwan nasa.
"Zuwa yayi don ya nemi shawara aguna...wani gida yake son ya siya anan kusa damu 'Hotoro G.R.A'... Shine yace gobe idan na taso daga aiki sai muje naga gidan... " Ya samu kansa da shirya mata wannan k'aryar.
Cike da farin ciki tace"Masha Allah!! abu yayi dadin ji... Allah ya sanya alheri... "
Ahankali yace"Ameen... Kunyi sallar isha'i? " Don har anma riga an iddar yana waje tare da Mahmood.
"A'ah... Jiranka muke ka dawo muyi jam'i"
Murmushi kawai yayi, atare suka je suka dauro alwala har Jasmine, Sannan ya jasu sallar.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Yau Jumma'a, wacce ta kama ranar da muka ijje zamu tattauna akan abinda ke tsakanin Leedar da Suhaima.Kuma kamar yadda na d'auki alk'awarin kai musu ita Suhaimar har makaranta don ayi tattaunawar da ita,toh gashi ahalin yanzu am trying to fulfill the promise.Sai dai kuma banyi gangancin fad'a mata cewar gashi-gashi bah, koh kuma ga abinda ke going ba,na dai tsaya akan zan kaita ne taje tayi studying environment d'in ABU as I promised earlier.
Tafe muke ni da ita acikin motata wanda nice ke tuk'in.Sannu ahankali wak'ar 'Let me love you' by 'DJ Snake' ke tashi wanda hakan yayi nasarar jefa dukkanmu cikin wani irin yanayin shauk'in soyayya, musamman ni wacce babu wanda ya fad'o min arai awannan lokacin face Mubeen d'ina.
"Sister baki da Class ne yau? " Suhaima ce ta katse min yanayin dana shiga ta hanyar jefo mini wannan tambayar tana kallona.
"Kin manta cewar yau Lecture free day d'ina ne? "
Tace"Wai.... Wallahi I have forgotten sistyna.. "
Adaidai lokacin text message ya shigo wayata,da sauri na kai hannu na dau wayar wanda ke ijje agefena.
Sak'o ne daga Leedar,na soma karantawa, at the same time ina concentrating akan tuk'i.
"Watsup! best... Duk fah mun hallaru ku kadai kawai ake jira...Kuma na taho da mutane biyun dana miki alk'awarin kawowa wanda sune keda hannu cikin lamarina da Ruheena💗.... So please hurry up don't keep us waiting!!! "
Murmushi kawai nayi tare da aika masa da reply,
"Hey! Cool Dude.... We are on our way, almost close to ABU.... Insha Allahu nan da 5mins zamu k'araso!!!"
K'ara gudun motar nayi.Nan da nan kuwa sai gamu acikin environment d'in ABU.Suhaima sai kalle-kalle take tayi kamar wata 'yar kauyensu Maryam fulani (lol tawar juz kidding).Sai nuna tsantsar sha'awarta take, tare da yaba k'yawun beautiful environment d'in.
"Yaya Fadima please ki fara kaini environment ta department d'in mass com. tunda shine future course d'ina... Lemme start with it... " acewar Suhaima.
Nace"Suhaima dear chill.... U have the whole day to study little places of ABU, don karyarki dai ki gama zagaye ABU ayau d'in nan sabida girmansa..... amma kafin nan let me first see my Ayush akwai maganar da nake son mu d'an tattauna da ita.... "
Adaidai nan muka k'araso wurin da muka Zauna rannan,wanda venue d'in muka sake choosing na had'uwar tamu ayau.Wurin is so silent, kuma students basu wani cika zama ah environment d'in bah, that's why we think zamu fi jindadin tattaunawar tamu anan.
Atare muka fito daga motar,Suhaima ta zagayo ta b'angarena tana cigaba da kalle-kallenta har idanuwanta suka kai gun mutanen dake zaune ah k'arkashin bishiyar dake agabanmu.
Karaf! Idanuwanta dana Leedar suka had'e.Ai kuwa nan da nan naga ta shiga cikin wani yanayin rud'ani.
Da rawar jiki naga ta juyo tana kallona,cikin in-ina tace"Yaya Fadima jeki kawai zan jiraki anan... "
"meyasa? Koh don kinga Leedar awurin ne? "
Bata bani amsa bah, illa sake kai dubanta tayi tana studying duk mutanen dake tare dashi awurin.
Ahankali naji ta furta"What??? Rukky?? Mai takeyi anan tare dasu Leedar? Meke shirin faruwa ne? "
Rukky tana d'aya daga cikin bak'in da Leedar ya taho dasu.
Murmushi nayi, azuciyata nace"Baby gal save ur questions sai mun k'arasa wurinsu sai ki sami damar amayo musu da tambayoyin taki.... Ni da Leedar mun shirya kawo k'arshen komai ayau d'in nan. "
Kafin nakai ga magana ah zahiri,naji tace"Sister ni zan tafi gida kawai... "
Magana nake kokarin yi,sai aka kuma katse mini hanzari akaro na biyu,Leedar ne ya k'araso wurin da muke tare da jefo min signal,alamun na basu waje suyi magana.Da hanzarina na bar wajen nayi wurinsu Ash queen dake ak'arkashin bishiyar.
Ganin Fadima tabar wajen kuma ga Leedar yana kokarin isowa dab da ita,hakan ya sanya tayi saurin juya masa baya,ayayin da zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri.
Da hanzari ya samu ya shawo gabanta.
Cike da tsiwa tace"Aleeyu bani hanya na wuce...... Tukunna mah meka fad'awa sister d'ina agame da abinda ke tsakanina dakai for so long? And again what the hell is Rukky doing here?.... Good and fine, wallahi koh baka fad'a min komai bah, ni zuciyata ta riga ta raya mini cewar you have finally exposed our secret kamar yadda kasha yunkurin yi ina hanaka... amma ayau kayi nasarar barar da ruwan tulun....... "
Ta fad'i hakan ah sa'ilin da hawaye ya soma wanke masa fuska.Idanuwan Leedar ne suka kad'a sukai jawur dasu tamkar garwashi,Wanda at any moment shima yana iya rushewa da kuka.
Cike da kwarewarsa afagen soyayya,ya soma rarrashinta"Haba Ruheena💗.... Wannan ruk'on ya isa hakanan mana, u are killing us both silently.....Ni dake mun san cewar muna k'aunar junanmu,toh then why are we punishing ourselves in this way?..... Kuma wannan kaddarar data shiga tsakaninmu bah wata matsala bace,abu ne dah idan an zauna tabbas za'a fahimci juna,amma Sam kinki ki bani damar hakan....... Suhaimata please ki baiwa Haidar d'inki dama yayi explaining kansa ayau...... "
K'okarin magana take, yayi saurin katse mata hanzari"Please Ruheena💗 don't say know..... Permit me to explain everything today.... "
"Ok" kawai ta iya furtawa wanda hakan bah karamin dadi yayi wa Leedar bah.Itama idan tace har yanzu bata k'aunar Leedar toh tabbas tayi K'arya.
Sannu ahankali suka soma takawa zuwa k'arshin bishiyar dasu Fadima ke zaune.kowa sai kallonsu yake,ayayin da kowannensu da abinda yake rayawa acikin zuciyarsa agame dasu.............................. 📝
Agaskiya ur votes and comments sunyi k'asa da yawa... Bazanyi typing bah har sai na gamsu da number of comments.... Thank you!!
SAHIBARKU CE
💓QUEEN HAFNAN💓
Advertisement
- In Serial24 Chapters
You're a God, go.
Jason wakes up one day and his reality is shattered. He's dead, so what now? He decides. Cover art courtesy of ColorGob. Check his DevianArt out. https://colorgob.deviantart.com/
8 179 - In Serial51 Chapters
The Clockwork Sea
Everything that breathes is slowly turning into machines. A boy yet to fully turn sets out to sea to find the man responsible for it, the Mad Tinker. Enter the world of the Twelve Seas where clockships fly on invisible timelines and the color of your wizard hat determines your profession. The Twelve Seas are governed by the three fundamental laws of Chronodynamics. Whether it be through magic or technology these laws must be adhered to: Time is a parabolic entity. It must always move forward. Timelines cannot be created or destroyed. The slowing or acceleration of time will result in an opposite and equal reaction.
8 117 - In Serial7 Chapters
The Adventures Of Heegan, Bleegan, Hoogan, and Bloogan: The Search For The Enchanted Toad Of Delarmir
This is a tale of four young goblin brothers, whose adventures and calamities are told as legends and jokes throughout the land. But they were first inspired by legends they heard, before ascending into one themselves; a reminder that simple beginnings can be the start of something great. Written for my D&D 5e party after they demanded I write an actual story about a children's book they found in one of our sessions, so I wrote it as it would appear in game as a childrens story. I took a very different approach on writing it, so do not be too disappointed when you find out it's not written at first grade reading level. Feedback is much appreciated, as I have never produced anything like this and I do hope I manage to entertain at least a few of you. New chapter releases to be within 3-5 days of one another (Work is now complete, do not expect new chapters).
8 101 - In Serial7 Chapters
Kata Street
Number 225, Kata Street, is filled with a complex mix of characters and personalities. From the beautiful Maya, to the curvy Josephine, to the dark and terrifying Mama Akunna. This masterpiece carries great humor, , romance and real time happenings in Nigeria and beyond seen through the eyes of these robust characters. Riveting, mesmerizing, reality altering and deeply immerses..
8 189 - In Serial39 Chapters
Fire Touched
Chosen by the god of fire as his champion in the mortal realm, Sarah Wycombe wants nothing more than to live the free life of an adventurer with John, her childhood friend. She finds herself having to fend off the forceful attempts from the Fire God’s faithful while investigating a mysterious cult who seeks to elevate their minor deity to godhood. In the magical world of Sera Thun, the orcs, fresh from a catastrophic defeat, seek to elevate the deity of night creatures to the pantheon in an effort to save their outcast people. Sarah Wycombe is part of a group of adventurers that uncover the grisly truth of how the worshipers of the night goddess intend to achieve their goals and seek to put an end to their ambitions. Along the way, she discovers that she has been chosen by the god of fire to act as His vessel in the mortal realm. As the Chosen of Agni, she is the keeper of the blue flame, which grants her considerable power. She must use this power to aid her band of outcasts to put an end to the night goddess’ ambitions while trying to avoid the zealous worshippers of the Fire God who seek to force her into a life of devotion towards their deity. New Chapters on Monday Wednesday Friday
8 198 - In Serial11 Chapters
Souls
To be summoned to another world of swords and magic is the dream of anyone who wants more from life. With the chance of becoming a master of the sword, to grow more powerful than anyone could ever imagine. All this could be Leon one day. If he was the Hero. Instead, he along with his entire school was summoned into this world to fight the demon race whose king was recently died for unknown reasons, all to protect the people who Leon could really not care if they die. He mainly just wants to use magic and fly. But why has the Demon King died? How were these people able to summon people from across dimensions? And how could such a plain-looking boy like Leon ever hope to survive in a world where everyone, including the demons, don't really like him. They don't hate him, but they would rather not have anything to do with him. Disclaimer: My grammar is crap, and you have the right to tell me just how much I suck at writing. Also if your feeling like this series is very much like Arifureta, then I'm sorry. Because the beginning of this story will sound very much like that series.
8 230

