《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER NINETEEN
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA TARA🌼
Page 90-95
Yammaci ne mai tattare da ni'imomin ubangiji.Sararin samaniya ya mugun hade rai alamun dai kiris ya rage ruwa ya sakko.Ga wani daddadar Iska dake tashi ahankali Wanda na tabbatar awannan lokacin, zuciyoyin al'umma na cike da nishad'i sabida dadin iskar.Adaidai wannan lokacin ina kwance saman gadona,operating my system, ban wani dade da dawowa daga makaranta bah.
Gani nayi iskar da ake ta soma yin karfi da yawa,hakan ya sanyani mikewa naje na kulle windows din d'akin.
Rigar sanyi na dauko na sanya donni akwai ni da saurin Kama sanyi. Gama sanya rigar keda wuya,naji an doko sallama cikin d'akin. Suhaima ce,ina gama amsa mata sallamarta, na haye gado tare da maida hankali kan abinda nake. Don tun randa taci mutuncin Leedar agabana, ban sake bata fuska bah.
Zama tayi akan gadon,duk na lura jikinta asanyaye yake.
"Yaya Fadima barka da warhaka... " hakan naji ta fad'a cikin sanyin murya.
"Yauwa barkanki.... " Na bata amsa atakaice.
"Lovely sisturh am very sorry for my rude actions the other day.... Please kindly find a place in ur beautiful heart to forgive ur lil sis...... " Ta fadi hakan almost in tears.
"Never mind my dear... Haka rayuwar take, no one is beyond mistakes....Suhaima na tambayeki mana? "
Da sauri tace"Ina jinki sis... "
"So nake ki fad'a min tsakaninki da mahaliccinki.... Shin akwai wani abu ne daya dad'e yana damunki azuciya? Koh kuma wani ya taba miki laifi ne da har yau kika kasa yafe masa?.... Ki fad'a min gaskiya kinga baki da 'yar'uwa mai Sonki kamar ni.... " Nayi mata wannan tambayar tare da tsareta da idanuwa.
Lol! Kar kuso kuga yadda yanayin Suhaima ya koma,remember yadda yanayin Wanda yake shirin k'arya yake komawa right? Toh hakan yanayinta ta rikid'e ya koma.
"Seriously sis babu abinda ke damuna wallahi..... Buh why diz questions? Koh kinji wani abin ne? " Yanayinta mah ya nuna she's so confused.
"No, juz feel lyk asking u such questions... Toh naji.... Yaushe zaku soma exams? "
"Ran Monday insha Allah... " acewarta
Nace "Good, Allah ya bada sa'a.... Would u be free on Friday? Jibi kenan?.... "
"Yea... Throughout ina gida... "
"Alright ki shirya..... ranar zamu je ABU tare,want u to study the environment kafin ki samu admission anan.... "
Cike da murna tace"wow sis thank you so much wallahi kamar kin san ina masifar son naje naga environment d'in ABU kafin na sami admission.... amma hope ke da kanki zaki sanarwa su Umma...?"
"Wannan bah matsalarki bace... I will take care of dat as usual... tashi ki tafi please kada ki cikani da surutu, kinga am doing something very important here kar kisa nayi mistake... "
At once ta mike ta fice daga d'akin ba tare da ta min wata gardama bah.Tunanin Mubeen d'ina ne ya fad'o min arai.Agaskiya ni kaina nasan nayi matuk'ar missing d'insa wanda atake anan naji zuciyata na son taji daga gareshi if he is really okay at all.
Samun kaina nayi da daukar wayata,nayi dialing lambarsa,ai kuwa nayi sa'a call d'in ta shiga har ta soma bada wannan boring tune d'in nan wato 'bum-bum'
Adaidai wannan lokacin kuma, Mubeen na kwance saman gado thinking abouh Fadima,ayayin da Hanan da Jasmine na bathroom suna wanka.
Jin wayarsa na ringing ya sanyashi jan tsaki, atunaninsa k'irace daga wurin aikinsu, don bai dade da dawowa bah, kuma ya gaji sosai ba kadan ba,because he attended to many patients today.
Advertisement
Ganin 'My Zahra' akan screen d'in wayar as the caller ya sanya murmushi sub'uce masa,mamaki yake wai ayau Zahransa ita da kanta ta nemeshi.
Sai daya bari call d'in ya tsinke, sannan shi ya k'irata.
Tana daukawa tace"Hey! Mubeen d'in Zahra are u okay at all? Kwana biyu na jika shiru that's why I called.... Meya faru rannan because yanayin voice d'inka ya nuna cewar there was something wrong going on at dat moment....... "
"Babyna calm down zanyi miki bayani......har yanzu na kasa yadda da cewar wai ke kika kirani kina tambayata koh ina lafiya, abinda baki taba yi bah My Zahra.... Diz is suprising wallahi.... "
Allah sarki Mubarak sonka ne ya janyo hakan, and again shawarwarin friends d'ina ne yayi tasiri akaina.
"Karka yi mamaki masoyina.... Mubarak ina matuk'ar sonka wallahi... Pls dear ka fad'a min abinda ya faru dakai rannan am worried wallahi.... " Na fad'i hakan cikin tsananin damuwa.
Allah sarki Mubarak, arayuwarsa da wuya kaga ya boye maka wani abin acikin zuciyarsa, sai dai idan ta Kama. Kuma koda ace ya boye maka d'in yanzu, toh insha Allah zaizo ya sanar dakai nan gaba.Don haka ya sami kansa da yiwa Fadima bayanin abinda ya faru, amma bai fad'a mata cewar akan k'ishi ne Hanan tayi hakan bah.
"Sister d'inki ce ta yanke hannunta da wani glass cup, amma yanzu da sauki. " acewarsa.
Har ga Allah Fadima tama manta da wata Hanan sai yanzu.
Arud'e tace"Subhanallah!! My dear how comes? Taya hakan ta faru? "
"wallahi nima I can't give an account of wat really happened... Buh I think tsautsayice kawai.... Baby kada ki d'aga hankalinki da sauki...kona baki ita ku gaisa ne? "
Jin abinda ya fad'a ya sanya gabana faduwa, ahankali nace"Does dat really matters? "
Yace"Yeah... to me it really matters... Zanji dadi sosai idan kuka gaisa... Ina son ku saba da juna kafin ki shigo gidana... Kinji please baby na bata wayar? "
Lallai namiji kenan! Babu ruwansa da yadda nake ji ahalin yanzu da yake fad'a min wannan maganar, shi dai burinsa kawai ya had'a kawunanmu.
"Ok" hakan naji na fad'a bah tare da nasan lokacin da yayi dabarar fitowa daga bakina bah.
Adaidai lokacin Hanan da Jasmine suka fito daga wanka.Jasmine ce ta rugo da gudu ta haye kan gadon tana fad'in"Daddy baka ce Mummy ta kusan haifar mana babynmu bah? Toh yaushe zata haifoshi don ina son kani, kaga Ummi kawata tana da kani Abbati.... "
Da alamun Mubeen ya manta cewar waya yake da Zahra,don yana masifar son 'yarsa mai shegen surutu.
Lak'atar hancinta yayi, yace"'Yar babyn babanta kin cika surutu da yawa... Don't worry naki kanin ya kusa zuwa kinji? "
Ihun murna ta sanya tana fad'in"Daddy idan mummy ta haifoshi zan k'ara sanyata taci abinci da yawa don ta haifo min wasu kannen da yawa koh Daddyna? "
"Naji mamana jeki saka kaya... "
Hanan ce ta k'araso kusa dashi, bata mah lura da cewar waya yake bah, tace"Hubby tashi muje kayi wanka, koh so kake nayi maka? "
Kafin yakai ga bata amsa taji kamar ance"Hello Mubarak. " kuma muryar mace taji.
Da sauri tace"Abu Jasmine bah waya kake bah? "
Sai alokacin ya tuna cewar waya yake da Zahra kafin Jasmine tayi interrupting d'insu.
Da sauri ya maida wayar kunne yana fad'in"Sorry Zahra ga Hanan d'in. "
Kafin tayi magana, ya mikawa Hanan wayar yana fad'in"Hanan ga Zahra zata gaisa dake... "
Hanan ce ta gwalalo idanuwa waje ah sa'ilin data sanya hannun ta karbi wayar.Gabanta ne ya hau bugawa da sauri da sauri. Kamar tace masa a'a ba zata iya yin waya da Zahran bah, amma ina! tana matuk'ar son mijinta, don haka bata kaunar taga b'acin ransa,her heart really burns musamman idan ita ta b'ata masa ran.
Advertisement
Asanyaye ta kange wayar akunne, tace"Sister Zahra kina lafiya? Yasu mama? Ya kuka kai gida rannan? Angode Allah ya saka da alheri... " hakan ta sami kanta da jerowa Fadima wannan tambayoyin alokaci guda.
"Alhamdulillah Hanan! Ya hannun naki? Mijinki yace kin yanke hannu da glass... "Acewar Fadima.
Da sauri Hanan ta d'ago kai tana kallon Mubeen,Signal yayi Mata da cewar kawai ta amsa mata.
Tace"Naji sauki sosai nagode.... Please sister Zahra ku kara dagewa da du'a'i... Allah ya zabar muku abinda zai fi zama alheri tsakaninki da Mubarak.... "
"Ameen thumma amin sis godiya nake sosai... Agaida Jasmine. "
Mubarak yayi saurin k'arbar wayar, Jasmine ke damunsa wai adole sai itama ya bata wayar su gaisa da wacce ake waya da ita, duk da cewar bata san Fadimar bace.
Ignoring d'inta yayi,Kallon Hanan yayi, yaga har k'walla sun soma zubo mata saman kumatu.
Girgiza kansa yayi, ahankali ya furta"Hanan d'ita zaki soma koh?.... Karki sanya Jasmine tayi suspecting wani abun don kin Santa akwai shegen wayau, and again zaki tayar mata da hankali... "
Ficewa yayi daga d'akin, ya maida wayar kunne, yace"Zahrata am so much happy da kukai waya da Hanan... "
"Mubarak is Hanan pregnant again?? " Ba zato babu tsammani yaji tayi masa wannan tambayar.
Gabansa ne ya yanke ya fad'i, azuciyarsa yace"Does that mean Zahra taji duk maganganuna da Jasmine? "
Azahiri kuma ya daure yace"Kamar yaya kenan Zahrata? Waya fad'a miki hakan? " In a confused voice yake fad'in wannan maganar.
"Haba Mubarak ni fah bah yarinya karama bace da har kake kokarin wayance min... kaf! naji maganganunku kai da 'yarka.... Infact naji sanda matarka take fad'a maka cewar ka tashi kayi wanka.... Does dat mean kayi hakan ne da gangan don naji haushi, ko kuwa mantawa kayi wai kana waya dani? " Fadima ce take wannan maganar cike da k'ishi.
Ajiyar zuciya mai nauyi Mubeen ya sake, don shi har ga Allah bada gangan yayi hakan bah.
Yace"Baby wallahi bada gangan nayi bah,but please juz forgive me... hakika nayi kuskuren yin waya dake agabansu... Masoyiyata ki yafe min don Allah.... "
"Mubarak zuciyata na raya mini cewar kafi son 'akan wannan 'da kake ikrarin kana so.... " Fadima tayi wannan maganar cikin muryar Kuka, wanda hakan na nuni da cewar she is really hurt.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un... "Hakan Mubeen ya fad'a sanda yaji Fadima tayi wannan maganar,da alamun yau so take ta caza masa kwakwalwa.Wai shin ina matan nan suke son yasa kansa ne? Kowacce na ikrarin yafi son d'ayar akanta.Shi kuma agaskiya yana bala'in sonsu duka biyun,amma aganinsa yafi son Zahransa wanda yake ganin bazai iya cigaba da rayuwa bah muddin ya rasata. Yah salam! Wannan wacce irin jarabawace agareshi?
Arud'e yake fad'in"Haba Zahra Wannan wacce irin maganace kike yi? Please ki daina fad'ar hakan... Wallahi kowacce da matsayinta acikin zuciyata... Fadima Zahra all I want u to know is dat Mubarak truly loves you..... "
"Naji.... Wai mah tukun nan dai.... Shekarun Hanan d'in nan nawa? Becuz ni dai tana min kamar mah Suhaima ta girmeta.... "
Dariya yadan saki, yace"No, Suhaima bata girmeta bah... Hanan tana da karamin jiki wanda hakan yake sanya mutane ke mata kallon karamar yarinya sosai... Hakika tana da jiki mai k'yau don she's 23years old..."
Hakika naji k'ishi sosai da yace 'tana da jiki mai kyau',amma na daure nace"Ikon Allah!... ashe shekara d'aya kacal na bata..... dat's good!... Ina tayaka murna baban baby... Allah ya raba lafiya.. " Na fad'i hakan ah sa'ilin da hawayen daya taru cikin idanuwana yayi nasarar gangarowa saman kumatuna.
"Ameen Zahrata.... Ai kema insha Allahu kin kusa shigowa ki Haifa min kyawawan babies.... Yauwa babyna, ina saka ran kwanan nan zan kawo miki ziyara kinji...... tawar tana maraba dani kuwa? "
Cikin rawar murya nace"No, Mubeen d'ina kadan dakata sai ranar dana baka izinin zuwa.... "
Azuciye naji yace"Zahra zaki soma koh? "
Ahankali nace"Man d'ina I hav a reason daya sanya na fad'i hakan... Please try and understand kaji mutumina? "
Da alamun na kashe masa jiki da salon Soyayyata, don ji nayi ya sake wata sassanyar ajiyar zuciya kafin yace"Kai Zahrata kina Kara rikitani da salon soyayyarki... Allah dai ya mallaka min ke... "
Ahankali nace"Ameen Daktana... "
Daga hakan mukayi sallama.
"Anya Mubarak zan iya auranka kuwa? Bazan so na gan ina sharing d'inka da wata 'ya macen bah? Innalillahi! can't believe Hanan is pregnant again for the man I so much love with all my life......Anya Mubarak bai fi son wannan Hanan d'in akaina bah? How I wish u are juz like ur brother Engr. Mahmood.. Halinsa is juz perfectly okay... Daga ganinsa bazai so keeping more than one wife bah.
Ni kadai nake maganganun nan ahankali, alokaci daya kuma ina zubda ruwan hawaye.Ji nayi zuciyata na mugun min rad'ad'i alamun wani irin mugun kishin Hanan ne ya motso min. Ahankali nake furta"Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha".
Bangaren Mubeen kuma bayan ya gama waya da Fadima, komawa cikin falo yayi because har tsakiyar gidan ya fito yana waya gudun kada akuma maimaita abinda ya faru rannan.
Yana shiga falon ya tarar da Jasmine zaune har Mummynta ta gama yi mata homework, wanda hakan ya bashi tabbacin lallai ya dade yana waya da Fadima awaje kenan.
Jasmine na ganinsa tace"Daddy nayi fushi dakai tunda kaki bani waya mu gaisa da wacce kake waya da ita dazun... "
Wurinta ya isa, ya tsugunna daidai tsawonta,Kama kunnensa yayi, in a pitiful way yace"Haba babyna am so sorry... Da antinki mai kyau d'innan nake waya..tace mah na gaisheki "
Da sauri tace"Laah! Wannan antin wacce taki cin abinci agidansu granny rannan? Daddy shine kaki bani waya mu gaisa? Wallahi nayi kewarta yaushe zata kuma zuwa? "
Ahankali yace"Ta kusa dawowa nan gidan da zama..... "
Jin hakan ya sanyata sakin ihun murna, alokaci daya kuma suka ji k'arar zubewar abu ta bayansu.
Juyawar da zaiyi yaga Hanan ce ta saki tray din Hannunta, ta barar da abinci, alokaci daya kuma hawaye na zubo mata, wani na korar wani.
Jasmine ce ta saki ihu tana fad'in"Laah! Daddy Mummy ta barar mana da dinner d'inmu.. "
Azuciye yace"Shut up! Jasmine kin fiya surutu... Oya maza zoki tafi dakinki, ki kuma natsu kiyi azkar d'in dana koya miki...... "
Da rawar jiki ta nufi dakinta, don ta matuk'ar tsorota because dadyn nata bai taba mata ihu cikin fushi bah irin na yau.
Sannu ahankali ya taka zuwa ga Hanan wacce wannan karon kuka take sosai.
"Hauwanah! Hakan kike son mu cigaba da zama ni dake kullum kina tada min da hankali? So kike 'yarmu tasan halin da ake ciki?So kike wani ciwon ya kamaki idan kina saka damuwa acikin ranki? Ko kuwa so kike ki min asarar babyna dake kwance amararki idan kika cigaba da yiwa kanki illa.......? "Azuciye yake fad'in wannan maganganun.
"Mubarak ba laifina bane....ka sani laifin zuciyata ce da take matuk'ar sonka da yawa....karka damu da duk wani hali da zan shiga, juz focus on Zahra.... Kuma insha Allah! nayi maka alkawari,nothing will happen to ur unborn baby..... "
Rungumeta yayi,lokaci daya yaji kuka na neman kufce masa sabida tausayinta.
Ta maza yayi, ya soma rarrashinta"Hauwa'u Hanan d'ita ina kaunarki har cikin raina.... Ji nake kamar na hakura da Zahra kawai, because bana son na cigaba da ganinki cikin wani hali...... "
Da sauri ta tari numfashinsa"No, mijina farin cikinka shine nawa.... Ka cigaba da abinda ka sanya agaba... Insha Allahu, Allah zai baka sa'a tunda dai abin alheri kake nufinta dashi, wato '
"Hanan d'ita nagode sosai... Ina sonki matata... "
Murmushin dole ta sake, tace"Nima ina mutuwar sonka mijina, Mubarak d'ina.... "
Daga hakan sukayi clearing abincin daya zube, sai tsiya yake mata"Kinga yanzu kinyi masa asarar dinner kamar yadda 'yar babyna tace... "
Ashagwabance tace"Toh ai laifinka ne... Gashi ka korar mana ita... "
"Bari naje na lallashi abata" ya fadi hakan yana dariya, Sannan ya nufi dakin da Jasmine ta shige.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Engr. Mahmood ne zaune saman daya daga cikin kujerun falonsa.Karamin tebur ce agabansa mai dauke da al'kaluman Zane da kuma fente-fente. Sai sketchboard wacce ya sanya mata farar takarda ajiki.Alamu ya nuna cewar Engr. Mahmood is ready to draw.
Toh shin mai kuma Engr. Zai zana?
Zane ya soma yi babu gaggautawa,cikin mintuna da basu wuce talatin bah ya kammala zane-zanen nasa.Daukar farar takardar yayi tare da Kura mah hoton daya yi sketching idanuwa.
Ahankali ya furta"Wow! tsaf! na samo kamannin nata..... Sincerely speaking, she is truly gorgeous..... "
Hoton '' ya zana, wacce take sanye cikin hijabinta.wannan hoton nata daya zana,yayi capturing face d'inta ne sanda take jifarsa da murmushi ranar daya je kiran Mummynsa adakin da suke. Kuma exactly ya samota, yadda tayi murmushin, hakan ya zana tana murmushin. Duk wanda ya Santa, karya ne yaga wannan sketch d'in yace bah ita bace.Engr. Mahmood kenan,akwai iya zane-zane gashi shi dai bah Architect bah.
Magana ya soma yi da hoton"Fadima Zahra tun ranar farko dana soma had'a idanuwa dake, kawai naji kin tafi da imanina.... Ma'ana naji kawai ina sonki at once.... Ke kadai nake yiwa tanadin soyayyata ahalin yanzu.... Kuma ina son na rayu dake please.... "
Haka dai yake ta Zubawa hoton kalaman soyayya. Can wani tunani ya fad'o masa arai.
Da sauri ya dauki wayarsa ya sanya kiran Mubarak.
Ringing daya, biyu, ana ukun Mubarak ya dauka. Kafin yakai ga magana, Mahmood ya rigashi, yace"Brother kana gida? "
"Yeah!....Yaya lafiya kuwa? "acewar Mubarak.
"lafiya Kalau... Kai dai gani nan zuwa...we need to talk. "
Yayi hang up!. Da sauri ya tafi yayi alwala don an soma kiraye kirayen sallar magrib.
Sai daya tsaya yayi sallar ah masallacin gidansa, kafin ya tafi gidan Mubarak.
HAFNAN'S POV
Tofa.... Meke shirin faruwa ne? Wani abin sai ah episode 20.
Guys ga alkawarinku nan na cika, duk da cewar ba wani jindadi nake bah... Amma nayi kokari nayi muku typing.. Hope u guys really appreciate?
*Votes
*Comments
*Follow &
*Share
SAHIBARKU CE MAI YI MUKU FATAR ALHERI AKODA YAUSHE!!!
💝©HAFNANCY©💗
Advertisement
Shadow Pack Stories [Completed]
You do know that Werewolves live in a pack, hence, these stories will be picking on Shadow Pack from Cyprus Island. Come on the journey to know what kind of werewolf pack it was. Of course, the hierar...
8 333Stray Cat Strut — A Young Lady's Journey to Becoming a Pop-Up Samurai
In the year 2057, the world has become a corporate-run utopia for the super-rich, and a hellhole for all the rest. Catherine 'Cat' Leblanc is an orphan that is about as far from super-rich as one can be. When the Incursion alarms start blaring and the sky starts raining hungry xenos, it's just another blemish on an already piss-poor afternoon. A cyberpunk magical-girl alien-invasion LitRPG. It’s exactly as wild as it sounds.
8 580Moonborn
Ainsel Madan was found by the roadside without any memories three years ago. She's settled into a new life in high school and she tries to be an ordinary girl: she likes baking, walking barefoot, and hanging out with her few friends. But she has secrets, too. She can heal with a touch, and she doesn't seem to age. Oh, and lately, almost everybody at school has started to hate her, and her only remaining friend has started losing time. When a pack of wolves shows up in the forest outside her small Washington town, everything gets worse. And when the most frightening of the wolves walks into her classroom as a gorgeous new transfer student... well, then things get *complicated*.
8 160Realm Traveler
Mia, an American college student finds herself mysteriously sent to a world filled with magic. However, the magic in this world holds many similarities to science, her related college major. What secrets will she be able to unravel in this new world?
8 95Blood and Bones
From the darkest reaches of Elms To bloody battlefields that rage between nations From the tyrants who believe they rule him To the people who hate him to a fault He reigns over them all And those who dare to cross his path are now only blood and bones
8 155Tangled Hearts| Shu x Valt yaoi fanfic|
[#1 in #shuxvalt (2.8.2018)]Sooner or later, shu and valt both know that they need to show their feelings to each other, will they suceed, or will the plan fall apart? But what they didn't know was that there was something hidden beneath Shu after this...Continue reading....
8 123