《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER SIXTEN
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA SHIDDA🌼
Page 75-80
Wasa-wasa zazzabi ya rufe Hanan.Jikinta duk ya d'au zafi, da alamun hannun nan ne ya saukar mata da zazzabin.Sai da Mubeen yai mata allurai har uku tare da sanya mata drip bayan ta samu ta danci abinci.Sai aikin bacci take ta Zubawa bana wasa bah.Duk hankalin Mubeen ba'a kwance yake bah sabida duk Hanan ta bi ta rud'ashi, gashi yana son ya k'ira Fad'ima amma bai samu damar hakan bah, and again fushin da Mummy tayi akansa bah karamin damunsa yake bah.
Kanwarsa Labeebah ce tayi masa waya take fad'a masa cewar gata akofar gidansu, don haka yazo ya bud'e mata.Cikin sanda ya fice daga d'akin gudun kada ya tashi Hanan.
Yana gama bud'e gate d'in, Labeebah tace"Wai ni Yaya sai yaushe zaku soma barin kofar gidanku abud'e ne? Wai ace kullum gida baka taba samunsa abud'e sai dai koh wani lokaci akulle... sai kace wani gidan kurkuku? "
"Yo! don sarkin garinku so kike ko wani gardi ya shigo gidan unexpected ya gane mini mata anyhow right? "
Murmushi tayi tare da rik'e hab'a, tace"Hmm! Ina ruwansu brother kakannin kishi kenan..."
"Tukunna dai..... Meya fito dake da goshin magrib d'in nan wanda kamata yayi ace warhaka kina d'akin mijinki? " yayi mata wannan tambayar, wannan karon babu alamun wasa tattare dashi. (watanta shidda kenan da aure).
Tace"Daga Na'ibawa muke.... Shine Mummy tace mu taimaka mu kawo Jasmine tunda duk kusan unguwa d'aya muke daku...... " Ta fad'i hakan tare da nuna Mus'ab mijinta wanda rike yake da hannun Jasmine suna kokarin karasowa inda suke.
Musabaha sukai da Mus'ab d'in, suka gaisa amutunce with due respect.
Jasmine ce ta saki hannun Mus'ab, da gudunta ta rugo ta rungume Mubeen, ayayin da shi kuma ya dagata sama.
Tace"Daddy I really missed you.... amma ina fushi dakai hadda mummy tunda kukai tahowarku jiya kuka banni acan gidansu granny inata kuka.... "
"Sorry babyna bazan k'ara bah kinji... " ya fad'i hakan tare da marairaicewa kamar zai saki kuka.
Juyowa yayi ga su Labeebah wanda suka shagala ga kallon soyayya irinta d'a da mahaifi, yace"Mus'ab bismillah mana ku shigo... "
Duk Jasmine tabi ta dameshi da surutu.
"Daddy kaga Uncle ya siyamin tsirei da youghourt akan hanyarmu ta zuwa nan...ga bag d'in kayanmu ni da mummy can ahannun Anty wanda ta manta dashi acan jiya.... "
"Laah! Lallai wannan uncle d'in yana son 'yar babyn nan tasa... Hope dai kince masa thank you? "
Da sauri tace"sosai mah... Lodi lodi mah Kuwa... "
Aka fashe da dariyar maganarta wanda adaidai lokacin suka shigo cikin falon.Jasmine sai tambayarsa inda Mummynta take.
Advertisement
Yace"Baby mummynki bata da lafiya... she's in the bedroom sleeping, so don't wake her up okay? "
Ahankali ta daga kanta alamar taji maganarsa.
Labeebah tace"Ayyah! brother ya jikin Anty Hanan d'in? Mummy ta fad'a mana cewar bata jin dadi and again taji rauni ahannunta..... "
Da sauri yace"Eh!! tsautsayice ta afka mata... ta yanke ne da wani glass amma da sauki yanzu.... "
Mus'ab yayi masa jaje tare da tambayarsa mai jikin.
Labeebah tace"Bari na d'an dubota.Ta mike zatayi d'akin Hanan d'in, da sauri yace"No, tana dakina.... "
Jin hakan ya sanyata Juyawa ta nufi direction d'in d'akin nasa.
Tana zuwa kuwa taga Hanan d'in har lokacin baccinta take abinta.
Ahankali Labeebah tace"idan banda abin namiji... Mai mace kamar Hanan ta nema ta rasa, yarinya gata dai k'yakkyawa, mai hakuri da kuma godiyar Allah... She has everything da duk wanda yake jin shi d'in classic man ne zai so atare da Ita... Toh mai zaisa yaya yayi tunanin karo wani aure? "
Girgiza kanta tayi, ta juya ta fice daga dakin zuwa falo.
Tana isa falon tace"Brother please I want to have a talk with u... "
Gabansa ne ya fad'i, ba tare da tunanin komai bah ya mike yana cewa "ok".
Wani karamin falo suka je.Zama sukai akan kujeru daban-daban.
Yace"ina sauraronki.... Kuma kiyi sauri kada Mus'ab ya gaji da jiranki... "
Tace"Yaya Mubarak why? Mai ya shiga cikin kwakwalwarka ne yau da har ka iya tsayawa ka fuskanci mummy ka fad'a mata maganganu son ranka abinda koh amafarki idan akace kayi shi, am very sure bazaka taba iyawa bah? Matar data nuna mana so na tsakani da Allah tamkar ita ta haifemu..... Wai itace ayau kake mata tuni da cewar bah ita ta haifeka bah?...
"The most suprising part shine da aka fada min cewar ka had'a k'ashi da wanka... Wai duk akan wannan shegiyar kake neman b'atawa da family dinka.......? "
Cikin zafin nama ya mik'e ya isa gareta, babu wani b'ata lokaci ya dauketa da wani zazzafar Mari.
Nan da nan ta fashe da kuka don azaba, tace"Yaya ni zaka mara don na fada maka gaskiya? "
Sake dauketa da mari yayi, yana huci yace"An mareki din... Har ke kin isa ki taso kizo har cikin gidana kina min nasiha...har nawa kike Labeebah da har zaki sanyani agaba kina min fada? Iyyeh?.... Okay I understand.... Mantuwa kikai koh waye babba tsakanin ni dake.... toh Lemme remind u...Ni Mubarak nine 'wa' ayayin da kuma ke Labeebah kece 'kanwa'....... "
Afusace ta mike tana fad'in"Yaya Mubarak godiya nake kwarai da gaske.... Amma ina son ka sani cewar ita wacce ka zabeta akanmu, insha Allahu asannu zata gwada maka halinmu na mata..... "
"Fitar min agida before I loose my temper na tattataki anan wurin.... " Ya fadi hakan da karfi.
Advertisement
Ta fice daga falon tana fadin"Shegiya, mayya... Waya sani mah koh wankewa tayi ta baka kasha.... "
Biyota yayi har falon ya sake dauketa da wani gigitacciyar mari agaban Mus'ab. Sakin wani kara tayi don hakika wannan Marin yafi shigarta Akan sauran.
Yace"Ina ruwanki idan mah wankewar tayi ta bani nasha?... Kinga Labeebah kiyi sauri ki bace mini daga gani immediately idan bah haka bah wallahi jikinki zai fada miki gaskiya.... "
Mus'ab ne ya taso zuwa inda suke, don tun suna dayar falon yake tajin hayaniyarsu da kuma karar Marin da matarsa take tasha, amma kunya ya hanashi zuwa inda suke.
Da alamun wannan karon Mubeen yakai shi bango, yace"Haba Yaya ina ganin girmanka, don haka kada ka sake girman nan ya zube ah idanuwana..... ai wannan yawa ne ka daki 'ya mace kuma matar wani akan idonsa mah, babu koh kunya.... "
Azuciye Mubeen ya juyo yana kallonsa, yace"Hey! Man shut the hell up!.... kai kuma waye... Kare da gudun layya.... Who are u to interfere into a family matter?.... Diz is between me and my sister don haka ka cire bakinka aciki.......... "
"Idan kai ce, toh ni kuma E..... Don haka nasan darajar mace, so karka sake ka kuma taba min mata...... " Mus'ab ne ya fadi hakan cikin tsananin b'acin rai.
Murmushi Mubeen yayi tare da fad'in"Kasan mey? Ku tafi kawai... Amma kasan meyasa zan kyaleka?... Its because u are my inlaw kuma bazan so ace na had'a kashi da siriki na bah... ai kaga da kunya koh? So u guys should get the hell out of my house with immediate effect right away!!!! "
Mus'ab yace"Koh baka fada bah... Dama Muna da niyyar wucewa"
Juyawa sukai suka fice, Labeebah sai kuka take ayayin da Mijin ke aikin lallashinta.
Koke-koke kunnuwansa suka jiyo masa daga bayansa, juyawarsa keda wuya, idanuwansa suka kai ga Hanan wacce take rungume da Jasmine, sai aikin kuka suke.Hannun Hanan wanda aka sanya mata drip dashi sai d'igar jini yake, sabida cire drip d'in tayi ta fito jin hayaniyarsu.
Da gudu Jasmine ta ruga ta rungume Daddyn nata tana kuka"Daddy mai yasa ka mari Anty Labee kuma kayi wa Uncle Mus'ab fada.... Gashi yana da kirki sosai ya siyo min tsirei da youghourt....mey suka maka? gashi Anty Labee sai kuka take"
"Yanzu dai kaji dadi tunda 'yarka taga abin kunyar daka aikata akan idanuwanta.... Don mah bata ga na dazun kenan bah wanda yafi wannan tashin hankali.... Haba mijina akan 'ya mace kake neman b'atawa da family dinka? Ni naga mah wannan yarinyar ba wani damuwa tayi akanka bah sai idan mah kai ka nemeta.... Wannan yarinyar Sam bah alheri bace ga rayuwarka Abu Jasmine.... Pls ka gaggauta rabuwa da ita tunda yan'uwanka basa so......... "
"Hauwa'u!!!!!! " kiran sunanta yayi da karfi wanda tunda yake bai taba ambaton ainihin sunanta bah sai ayau.
Gabanta ne ya hau bugawa da sauri da sauri,ignoring d'in Jasmine yayi, ya nufi inda Hanan din take zaune.
Tsugunnawa yayi daidai saitinta, yace"Daga yau sai yau... Karki sake interfering into my relationship with 'Nagode kwarai da gaske da dukkan taimakon da kika min... Amma daga yau, karki kara sanya baki acikin maganarta tunda naga kin soma gajiyawa da taimakon nawa, tunda har zaki iya cewa na rabu da ita...... Hauwa'u Ina sonki amma ki sani bazan iya hakura da Zahra bah...... "
Mikewa yayi ya nufi daki, yana jin sanda ta rushe da wani sabuwar kuka mai ban tausayi wanda sai daya ji kukan na dukar zuciyarsa.
Dawowa falon yayi da auduga ahannunsa, ya goge mata inda jinin ke fita.Ya rungumo 'yarsa wacce har yanzu kuka take. Lallashinta ya soma yi tare da mata wasu 'yan dabaru da wasannin.. Kun san yara ai,nan da nan ta ware, ta dauko tsirenta da youghourt ta hau ci.
Komawa yayi inda Hanan take,zama yayi agefenta tare da ruko hannayenta, yace"Hauwanah!! Pls am so sorry... Forgive me... Wallahi na rasa koh wani irin soyayyace nake wa Fadima wanda hakan yake sanyani fada da family d'ina... Buh I promised u, as from today am a changed person... No more fighting da yan'uwana akanta.... "
Hanan bata san lokacin da wani murmushi ya subuce mata bah,rungumeshi tayi tana murna.
Yace"Buh hakan ba wai yana nufin na hakura da ita bane........................."
Kallonsa take cike da mamaki........
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Har zuwa lokacin nan Mubeen bai nemeni bah, haka zalika nima d'in ban nemeshi bah(hahaha fadima akwai jijji da kai).
Tunanin Suhaima ne ya fado min arai.Atlast, ayau ta gane cewar da gaske son Leedar take wanda ada take musa min.Hmmmm! Dat means game d'ina da Leedar will soon be over wanda bah hakan naso bah... Becuz game d'in ya soma min dadi. Lallai Suhaima da sauranki, becuz I will make sure dat diz game will insha Allah be very tough and hard for you baby................
Wanka nayi na tafi school don yau Monday. Ash na kira don zuwa makarantar nan da zanyi ayau,it is mostly because of Ash and Leedar, don bamu cika yin much lectures ran Monday bah.Ayau nake son na bayyanawa Ash komai dake tsakanina da Leedar........................... 📝
HAFNAN'S POV
Tofa jama'a akwai bidiri kenan.
Shin wani game kuma Fadima da Leedar suke playing?
Wannan kuma wani irin mahaukacin so ne Mubeen kewa Fadima da har ya sanya yake fada da yan'uwansa akanta?.... Ku dai ku biyo Hafnan.
Sorry pls, I know dat diz episode is too scanty buh u guys juz have to bear with me... Wutarmu ta lalace kuma da kyar nake samun chargy yanzu!!!
SAHIBARKU CE
©QUEEN HAFNAN©
Advertisement
- In Serial68 Chapters
Changing My Life with A Level System
As years went by and Earth evolved into a foreseen futuristic, sci-fi world, everything went through changes; the buildings, vehicles, weapons even the vegetation and animals didn't remain unscathed. Yet one thing stayed the same throughout all history, something indispensable for the human race, something no one could ever think of leaving out in their daily lives and yet being the very cause of human demise, work.During the whole change process not even once was the human work ethic thought of as a problem causing a rise in the demand for entertainment and distraction from the daily routines. Those a new game system called Virtual Reality was created, giving everyone the possibility to fully immerse in other worlds and escaping the trials of life. Bao, threw himself in such a world but without thinking of the consequences of such a deed, for nobody asked themselves, what if life in this virtual world is better than reality and even worse what if the boundaries between the two become indistinct? © 2021 All rights reserved to the author under the pen name Q_Yuumo.
8 450 - In Serial25 Chapters
The Flesh is (Not) Weak
Machines that have slept for millennia awaken, blaring alarms of impending doom.A human finds himself lost in a world with monsters and no memory of how he got there.An alien travels through space in search of technology to scavenge, finding more than she expected. Follow Damon, the only human on a planet where its inhabitants are either monsters or people who've integrated technology into their very bodies.Stranded in this strange world, the only escape is to unearth ancient secrets of a civilization long gone. -- Release Schedule: Tuesday and Saturday 22:00 CET.
8 195 - In Serial113 Chapters
BEHEMOTH
What is luck? What is fate? All we can do is stumble along blindly, a noose ever around our necks. And for what? Why do you struggle on. Every day, every single day I wake, I ask another day? Is this it? I want strength! I want power! I want to be above all, to stand on the highest peak of the highest mountain, to look down on everything and everyone! I want, I want, I want . . . Fool. Naive. Idiot. Again and again, you have neither the skill nor the talent, not the body of a warrior or the mind of a sage. What can you do Magnus Lund? Are you happy? Ha ha . . I forgot about happiness the day I died. The second time I died I forgot about love. I've died so many times, forgotten so many things . . what doesn't kill you makes you stronger, right? Well, I'm going to kill you, and it's going to make me stronger. Look forward to it.
8 127 - In Serial10 Chapters
Psycho in a fantasy world
Psycho reborn in a fantasy world attempts to make himself the most infamous killer. Game like elements and other magical stuff to help the character.
8 135 - In Serial566 Chapters
Marauding Gods (First Draft)
The world is a dangerous place teeming with powerful creatures known as monsters. The first Dragons, the first Gods, at the top of the food chain, brought these lands the everlasting that eventually led the world to its current state. The only way humanity has found to survive is to construct a massive magical barrier that spans an entire continent: the human continent. The story follows Ronandt, a young nobleman who, despite his noble origins, has never met his parents. Except for maybe at the time of his birth. He thus finds himself without parents at the Manor Rosetta, under the close supervision of Mathilda, his nanny, and Syrus, his Butler. Follow the adventures of Ronandt, a young nobleman unlike any other, born from a very unordinary pairing and bestowed with an unique advantage over his fellow humans. Disclaimer: This novel is clearly tagged gore, and this within reason, so please keep that in mind while reading. Though the early chapter suggest that this novel is slice of life one, especially in the first 40 chapters, it must be clarified that this novel is first and foremost a progression fantasy tagged gore and grimdark.
8 1006 - In Serial19 Chapters
How it all began
It's a story about a 14 yr old who is a foster kid and gets treated like a little child Will she escape or is it all just a dream ?
8 93

