《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER FIFTEEN
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA BIYAR🌼
Page 70-75
Nan da nan kuwa sai gashi hancin Engr. ya fashe, jini ya soma rushing.
Mummy da Hanan suka fashe da ihu suka hau kuka.Hanan ce tayi karfin halin shiga tsakaninsu.
Da karfi Mummy tace"Usman ka rabasu mana ka tsaya Kana kallonsu.... "
Engr. ne ya ture Hanan sai gata tayi baya tangal tangal ta fad'i kasa. Bai damu bah burinsa ya rama naushin da Mubeen yayi masa. Ai kuwa yaci sa'a ya sameshi amma aciki.
Mummy tayi nasarar shiga tsakaninsu tana fad'in"Gani na shiga tsakiyarku... Idan baku da hankali ne ku kasheni tunda dai ban isa na tsawatar muku ku nutsu bah.... "
Da sauri Mubeen ya isa ga Hanan yana kokarin taimaka mata ta tashi, azuciye yace"Wallahi ka sani idan wani abin ya sami matata koh kuma abin dake cikinta toh wallahi sai na lahira ya fika jindadi Mahmood.... "
Cike da mamaki Mummy tace"Ai, wato damar Hanan d'in juna biyu gareta shine kake kunsa mata bakin ciki? Toh idan har da gasken Kana sonta ai bai kamata ace kayi tunanin Kara wani auren bah..... Shashasha, butulu kawai wanda bai san inda ke masa ciwo bah.
Mikar da Hanan d'in yayi, sannan ya zaunar da ita saman wani two seater, sai kuka take sosai don faduwar data yi ya sanya ta fama ciwonta.Idanuwan Mubeen yayi jajawur kamar jan gauta, sai aikin hura mata ciwon yake, yana cewa "Sannu babynah"
Idanuwan Mummy ne suka kai ga hannun ciwon Hanan d'in. Salati ta sake tare da rik'e hab'a tace"Hanan mai zan gani haka? Meya sameki haka har akayi dressing wurin da bandeji? "
"Tsautsayice ta afka mata.... " Abinda Mubeen ya iya fad'i kenan don zuciyarsa sai faman tafasa take.
Engr. Mahmood duk jikinsa ya gama bacewa da jini, Usman ke k'okarin rik'esa, yayi saurin d'aga masa hannu alamun ya k'yaleshi.
Usman yace"Yaya baka ganin yadda jini ke bulbulowa daga hancinka ne? Ka taho muje asibiti kawai... "
Da karfi yace"Nace ka kyaleni koh? "
Ihunsa ne ya maido da hankalin Mummy zuwa gareshi, sai alokacin ta lura da jinin dake bulbulowa daga hancinsa.
Da sauri ta k'arasa gunsa jiki na rawa, tace"Mubarak kaga raunin da kayi wa Dan'uwanka akan mace koh?... Toh Wallahi ka sani tsanar yarinyar nan ya dad'a k'aruwa acikin zuciyata...... "
Jin abinda ta fad'a cewar ta tsani Zahransa, hakan ya sake sanya ya harzuk'a, ya mike yana magana da k'arfi"Haba Mummy meyasa shi baki ganin laifinsa sai ni? Agabanki ya ture min mata ta fad'i kasa baki iya ce masa komai bah... Koh don shi jininki ne ya sanya kika kasa tsawatar masa? Na gode miki da kika sake tuna min da matsayina awajenki....." Kuka ya kufce masa.
Engr. ne ya sanya kai ya fice don idan ya cigaba da sauraron maganganun Mubarak,tofa lallai za'a iya aikata kisan kai acikin gidan.
Ganin fitarsa ya sanya Umma kallon Usman tace"Kai kuma Shashasha, hotiho d'an rakiyar maza yi sauri mu bishi kada yayi wani gun don hankalinsa ba'a jikinsa yake bah.
Tana kaiwa kofa ta juyo ta dubi Mubeen"Mubarak nima na gode kwarai da gaske da ayau ka nuna min cewar bani ce wacce ta tsugunna ta haifeka bah, don haka ban isa dakai bah..... Kuma kuzo ku d'auki 'yarku don tun jiya ta dami mutane akawota wajenku, ganin cewar zamuyi magana muhimmiyace ya sanya ban taho da ita bah.... Kamar na san irin hakan zata faru shiyasa ban kawota d'in bah, da kuwa taga irin abin kunyar da iyayenta maza suka aikata.... Mun barku lafiya..... "
Advertisement
Tasa kai ta fice.
Hanan na gama ganin ficewarsu ta saki wata wahalalliyar kuka tana kallon Mubeen,tace"Mubarak why? Meyasa zaka fuskanci mahaifiyarka wacce take matuk'ar k'aunarka, har ka kalli k'wayar idanuwanta ka fad'a mata maganganu son ranka akan wata 'ya mace? Meyasa zaka bi son zuciyarka har tayi nasarar ingizaka ka had'a k'ashi da wanka?.... Abu Jasmine d'ina why? "
Tsagaitar da kukansa yayi,murya k'asa-k'asa ya soma magana"Hanan d'ita am really sorry... Komai da kika gan ya faru,toh wallahi nima ba'a son raina hakan ta faru bah.... Shaid'an ne kawai ya shiga tsak'anina da d'an'uwana..... "
"Hubby ku d'unga kokarin fin k'arfin zuk'atanku aduk sanda irin hakan ta taso wanda bama fatan mah abu makamancin hakan ya sake faruwa... "
"Insha Allah matata nai miki alk'awarin hakan ba zata kuma faruwa bah.... " Ya fad'i hakan tare da rungumota.
Murmushi tare sanda ta kwantar da kanta saman faffad'ar k'irjinsa, tace"Okay uban 'ya'yana godiya nake da hakan... Pls kayi kokari kaje ka nemi gafarar Mummy da kuma Yaya Mahmood idan temper d'insu yayi cooling..... Kaji nawan? "
"Naji Hanan d'ita, Mace ta gari.... Hope dai ciwon ya daina miki zafi koh? " Ya fad'i hakan tare da ruk'o hannun ciwon nata.
"Ya dai rage... Kaima da fatar dai Yaya Mahmood bai ji maka ciwo ba koh?" Ashagwabance ta fad'i hakan sanda ta d'ago kai tana k'allonsa.
"No....ai ke kin san bai isa bah... "
Dariya abin ya bata tace"Laah! Hubby hakan mah zaka fad'a koh? Toh sai na fad'a masa...?
Da sauri yace"Okay sorry... Tashi muje ki samu ki d'anyi baccin da aka hanaki yi d'azun... "
Daki ya kaita, ya dawo kicin ya d'ibi sauran abincin da su kayi breakfast da shi 'potato pie' da kuma ruwa. Ya koma d'aki.Da k'yar ta yadda zata ci,wanda shima d'in sai data ga bacin ransa sannan ta yadda.
Shi yaketa bata abaki hatta k'oshi, sannan ya bata magunguna na pain reliever ta sha.Ba'a wani d'au lokaci bah, bacci yayi awon gaba da ita.Don ba laifi, wannan cikin na sanya Hanan bacci bah kadan bah.
Ganin tayi bacci, hakan ya baiwa Mubeen damar zuwa ya kulle kofar gida, sannan ya dawo ya shiga kicin, ya hau kiciniyar nemar abinda zai dafa mata kafin ta tashi.
Jingina bayansa yayi da kofar kicin d'in.abubuwan da suka faru adazun nan ne suka soma dawo masa aka.Mamakin kansa yake, wai shine ayau ya iya tsayawa yana fad'awa Mummy maganganu son ransa, abinda bai taba yi bah sai gashi ayau yayi shi. Again,Shi da dan'uwansa Mahmood ko kallon banza bai taba shiga tsakaninsu bah, amma wai ayau sune hadda dambe, har ya fasa masa hanci akan mace.Anya Fadima Zahra alherice kuwa ga rayuwarsa?
Da tunane-tunanen nan yake ta girkinsa har ya samu yai musu dafa dukan taliya wanda yasha ice fish,Mubeen gwanin iya girki kenan, don koh Hanan bata isa ta nuna mishi yadda ake girki bah.Dama ya d'aukarwa kansa hutu awurin aiki tun sanda mahaifinsa ya soma rashin lafiya, don dashi akayi jigilar fitar dashi k'asar waje, ah inda akayi masa dashen koda don shi Mubeen d'in bah aspect daya karanta kenan bah.. He is juz a medical doctor.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
BARI MU WAIWAYI SU ENGR. MAHMOOD
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Tun sanda ya fice daga falon, waje yayi,ya shige motarsa, kwantar da kujera yayi, ya kwanta. Sai saukar da wata wahalalliyar numfashi yake, zuciyarsa kamar zata fasa k'irjinsa ta fito waje. Asanyaye ya ciro hankici d'insa dake aljihun wandonsa,sannu ahankali ya soma goge hancinsa, har ya samu jinin ya tsaya dama yana da hab'o.
Cillar da hankici d'in yayi waje, adaidai lokacin sun Mummy suka iso wajen.Sanda suka zo, shine ya tukosu amma kuma yanzu zama yayi abinsa akujerar mai zaman banza.
Advertisement
Usman ne ya lek'o ta windon bangaren da yake zaune, yace"Sorry brother... Allah zai.... "
Da sauri ya katse shi"Usman drive the car and let's leave here immediately.... "
Da gudu Usman ya k'arasa bangaren driver ya shige. Ganin ihun da yayi wa Usman d'in ne ya sanya Mummy kasa furta komai, illa kawai ta shige motar itama.
Usman ya ja motar suka bar area d'in. Sun danyi tafiya kad'an.Ya juya ya dubi yayan nasa wanda har lokacin maida numfashi yake, yace"Brother ina muka nufa? "
"Fara sauke mummy sannan ka wuce dani gidana... " Ya bashi amsa atakaice.
Jin abinda ya fad'a ne ya sanya mummy saurin fad'in"Anya Injiniya? Nifa kawai mu tafi asibiti kawai aduba mana kai.... "
Ahankali yace"No, mummy karki damu idan na samu na wanke wajen da ruwan d'umi, na kuma samu na d'an huta shikenan.... "
Azuciye Usman yace"Ai wallahi ni dai Yaya Mubarak ya matuk'ar bani mamaki ayau d'in nan... Idan akace min zai iya yin abinda ya aikata ayau din nan wallahi bazan taba yadda bah... Sai gashi yayi hakan akan idanuwana..... Wat a shameful thing? wani abin kunya ne yakai har ka had'a k'ashi da dan'uwanka akan 'ya mace..... "
"kai dallah rufewa mutane baki anan wurin.... Mai ka iya yi sanda kaga sun soma had'a k'ashin? Bah kallonsu ka tsaya yi bah? Sannan yanzu kazo kana mana kurin banza anan... Mai ya hana kai ka daki Mubarak d'in tunda har ya baka haushi? "
Kokarin magana yake,da sauri mummy ta d'auki takalminta kafa daya tace"Yi min shiru anan idan bah haka bah na mammauje bakinka anan gurin, kasan halina sarai...... "
Azuciye ya had'iye maganganun daya yi niyyar fad'a mata, yaja bakinsa yayi shiru. Shi dai Engr. Kala baice musu bah, balle mutum mah da yake fama da kansa.
Mummy suka soma saukewa. Ana sauketa, Usman yana kokarin jan motar tayi saurin dakatar dashi. Bangaren da Engr. yake zaune ta nufa.
Kallonsa tayi cike da kulawa da kuma k'auna irinta d'a da mahaifi,tace"Anya injiniya wannan numfashin da kake saukewa ni zuciyata is not at rest at all.... Kawai Usman ya juya kan motar mu wuce asibiti kaji Son......... "
Da sauri yace"Mummy na fad'a miki am okay.... Kawai zuciyata ke min zafi.... rai na amatuk'ar bace yake, amma idan kuka k'yaleni na huta, I will surely get back to my senses... So Mother cool ur mind, and thanks for the care. "
Ya juya ga Usman yace"Man ja mota mu tafi.... "
Usman da dama jira kawai yake abashi umarnin hakan, ya figi motar aguje ba tare da sun sake sauraron abinda ita Mummyn zata fadi bah.
Basu wani dau lokaci kan hanya bah suka iso 'court road' wanda anan ne gidan Engr. Mahmood yake.
Mai gadi dake fira da wani akofar gida yayi saurin mik'ewa don zuwa bude gate,ah sa'ilin daya hango motar ubangidansa yana kusanto inda suke.
Yana gama wangale gate d'in, yayi daidai da isowarsu,babu b'ata lokaci Usman ya danna hancin motar cikin gidan,bai tsaya ako'ina bah sai daya ga ya isa wurin parking lot sannan yaja wani wawan burki.
"Dad'ina dakai akwai iya tuk'in 'yan gareji... (Lol yana nufin rough driving kenan)" Engr. ne yayi wannan maganar sanda yake k'okarin fitowa daga motar.
Da alamun yau dai an kai Usman wuya, amma babu abinda zai iya yi, illa ya k'araci kumburin fuskarsa.
Engr. Ya sanya hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro wallet d'insa. Kud'i ya zaro ba tare da yasan adadinsu bah, ya mik'awa Usman "Gashi kayi kud'in motar komawa... "
Da sauri Usman ya k'arba yana godiya, tuni duk wani kumburin da yake tayi ya gushe, ayayin da farin ciki ya mamaye gurb'insa, don kuwa wannan k'yautar tafi k'arfin kud'in mota. Yayiwa yayan sallama ya tafi.
Maigadi ne ya k'araso inda Engr. Yake, k'okarin magana yake ganin duk gaban rigar Ubangidan nasa duk ya baci da jini.
Engr.yayi saurin katse masa hanzari ta hanyar d'aga masa hannu"Mal. Bello karka sami damuwa bah wata matsala bace.... "
Yana gama fad'in hakan ya sanya kai yayi gaba Zuwa cikin gidan wanda zan iya fassara gidan Engr. Mahmood da aljannar duniya.
Kayan alatun da aka zuba afalonsa kadai mah wani abin tsayawa Kallo ne. Bai tsaya ako'ina bah sai bedroom.wani drawer dake jikin madubin d'akin ya nufa.Bud'e drawer d'in yayi, ya firfito da hotuna masu d'inbin yawa.
Watsar dasu yayi saman tafkeken gadon d'akin.Hotunan suka yi splitting in different directions akan gadon.
Most of the pictures, hotunansa ne shida matarsa Zaynab, kalilan ne wanda ta d'auka ita kadai.Daya bayan daya yake bin Hotunan da idanuwansa.
Can ya nufi wani hoto wanda ta dauka ita d'aya tana dariya.Hakika Zaynab k'yakk'yawace. Daukar hoton yayi, ya zuba masa idanuwa,bah zato bah tsammani, ya rushe da kuka.
Kallon hoton yake yana magana dashi "Zeeyna kin mini nisar da ba zaki taba jin kira bah.... Akullum zuciyata k'ara hura wutar k'aunarki take acikinta.... Ina rokon Allah ya had'ani dake amatsayin mata da miji acikin gida mafi girma da d'aukaka, ma'abociyar kamshi, mai kuma tattare da ni'imomin ubangiji wato Jannatul firdaus!!!.... Allah yayi miki aikin gafara Zeeyna.... "
Wani sabon kuka ne yazo masa akaro na biyu, ya cigaba"Zeeyna ada nayi miki alkawarin cewar bani babu wata 'ya mace koh bayan ranki... But Zeeyna am trying to fail u... I don't know how she manage to get into my heart har naji na fara sonta, because sanyin halinta, maganarta da kuma yanayinta is juz lyk a photocopy of yours.... Zeeyna budurwar k'anina Mubarak nakeso wanda hakan ya janyo ayau na had'a k'ashi da k'anina akanta... Jibi raunin daya ji min, wai mah don bai san ina sonta kenan bah dats why raunin yazo da sauki.... Baby juz permit me to go for her becuz I nid to see my own children.... I promise never to forget u because u are part of every breath I take.... "
Kana ganin wannan halin da Engr. Mahmood ke ciki, tabbas zaka san hankalinsa baya jikinsa, he is almost out of his senses. Kansa yaji yana sarawa kamar zai fashe, da sauri ya janyo wata drawer ya bud'e,pain reliever ya dauko. Ya nufi kicin ya debi ruwa ya had'iye maganin.
Sai daya bari ciwon kan ya d'an lafa masa kafin daga bisani, ya mike yaje ya watsa ruwa. Kan Hotunan yazo ya kwanta,ya debo wasu ya rungume yana murmushi, nan da nan bacci yayi awon gaba dashi.
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
BARI MU WAIWAYI FADIMA SA'AD
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
Tun sanda Mubeen ya yanke call d'in da muke tare da ce mun zai k'irani anjima, na shiga cikin wani yanayi because yadda dai naji muryarsa nasan definitely, there must be something going on then.
Koma wa falon Abbanmu nayi, ah inda dukkan family d'inmu an taru ana hira. Dayake every Saturdays and Sundays babu inda Abbanmu ke zuwa.Acewarsa diz two days, ya kamata ace yana tare da family d'insa, showing his love, time and care.
Abba ne yace"Fadima gobe ki shirya zamuyi wata muhimmiyar magana dake... Idan kin tuna 2days ago na fad'a miki hakan.... Yau time din kannenki ne, kowa ya fad'i duk abinda yakeso.... And ur own turn is tomorrow..... "
Ahankali na furta"Okay Abu Fadima... Allah ya kaimu"
Na fad'i hakan cikin tashin hankali... Toh shin wata muhimmiyar magana ce Abba yake son yayi dani?............... 📝
HAFNAN'S POV
Sorry masoyan.... Yau nayi latti da posting... Wlh was busy ne... Dats why na d'anyi muku typing a little bit much don gobe through out bazaku jini bama. Sabida wani uzurin nawa... Pls bear with me... Thanks!!!!!
TAKU HAR ABADA
©QUEEN HAFNAN©
Advertisement
Renegade Immortal
Renegade Immortal / Xian Ni (仙逆) – Wang Lin is a very smart boy with loving parents. Although he and his parents are shunned by the rest of their relatives, his parents have always held high hopes that he will one day become someone great. One day, Wang Lin suddenly gained the chance to walk the path of an immortal but found that he only had mediocre talent at best. Watch Wang Lin as he breaks through his lack of talent and walks the path towards becoming a real immortal!
8 557Gods, Monsters, and a Fuzzy-tail
Magic is life, and Magic to spare is power. Everyone has Magic to spare, except Eli Wisp, who has just enough to stay alive. Despite this, he dreams of becoming the first of the premier Magic users. He wants to be a Maestro. When an old enemy of the world's greatest hero—with the power to destroy everything Eli knows—threatens to return, he must prove that he's not all talk. Join him in an epic quest where he meets new friends, old heroes, and evil's like no other on his path to becoming the best.
8 83Prince of the Wild
After her mentor is murdered, a young goblin must leave to request the help from human heroes. But not all is as it seems. Soon they all become entangled in a master vampire’s evil scheme. Will our heroes survive when the undead are already creeping outside their door? Step into The Wyrding. A land of gods, skin-changers, magic, and adventure. Blessing of the Wild to all who enter. ----- Cover art by RacecarArt.
8 185The Nocturne Society
For the first time on Royal Road The Nocturne Society is a series of urban horror stories centered around the remains of a dissolved secret society called … you guessed it … The Nocturne Society. Thirty years ago all monsters vanished and nobody knows why. The secret society dedicated to research and containment of these supernatural threats slowly fell apart and the dark age where dangerous things unknown to men slowly became legend. Finally nobody believed in the existence of such otherworldly threats anymore. But when thirty years later a young woman is killed in Hamburg and a tentacled monster seems to be the prime suspect an aging operative is forced out of retirement and together with the tech-savvy boyfriend of the victim he must return to the shadows to hunt the monster the world does no longer believe in. The Nocturne Society contains six novels available on Amazon, with another one in pre-sale. The Nocturne Society Series There are No Monsters Wormking Leviathan Let them burn Worst Case Scenarios The Secret Friend Mother (pre-sale)
8 79Control [Carlisle Cullen]
•They send me away to find them a fortune•[Carlisle Cullen][Twilight-Breaking Dawn Part 2][cover by: @kingsmaria][Started April 2018][Ended March 2019]
8 85Bootcamp Profile Guide
Learn what it means to be a Bootcamp mentor and mentee. Get to know who's manning the battle stations. Discover Wattpad profiles that offer challenges and opportunities for writers. Rummage through links to helpful online resources. Read tips on platform etiquette so you don't embarrass yourself.DISCLAIMER: THE WATTYS BOOTCAMP MENTORSHIP IS INDEPENDENTLY RUN BY WATTPAD MEMBERS. PARTICIPATION IN THE PROGRAM WILL NOT AUTOMATICALLY INCREASE YOUR CHANCES TO WIN A WATTY.
8 73