《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》CHAPTER ELEVEN
Advertisement
💘SHIN SO DAYA NE?💝
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
_Watpadd:Hafnancy_
🌼BABI NA GOMA SHA DAYA🌼
Page 50-55
Akalla mun kwashi kusan Mintuna talatin tsassaye abakin titin ba tare da mun sami kowacce mafita bah don motar tamu taki tashiwa, gashi gari sai dad'a duhu yake wanda hakan ya tabbatar mana da dare ya soma lulawa don wayoyinmu duk ah mace suke balle mu iya cewa karfe kaza ce yanzu.
Motoci kalilan ke giftawa, kuma duk wanda mu kayi mah waving alamar ya tsaya ya taimaka is not willing to stop sai mah dad'a k'ara gudun motar suke.
Tashin hankalina mah bai wuce wacce zanje na tarar agida bah. Muna cikin wannan halin ne na hango wata mota can da nisa apake ta hanyar kano, ta hasko wutar gaban motar, alamu ya nuna kamar motar ta d'an jima apake sai yanzu mai motar yayi niyyar barin wajen.
Tunkaro hanyar da muke naga yayi wanda ganin hakan ya sanya ban san lokacin dana haye har tsakiyar titi bah ina masa waving din ya tsaya.
Cikin ikon Allah kuwa naga motar ta soma slow down ayayin data tukaro ni, sannu ahankali muka ga ta gangara ta gefe na, ta samu wuri tayi parking ah gefen hanya.
Da d'an gudu-guduna babu koh alamun d'igon tsoro atattare dani nayi saurin k'arasawa gun motar, kafin na gama isowa kusa har an saukar da glasses din windows din.Hakan ya bani damar sakale wuyana ta bangaran windon mai zaman banza nace"Assalamu alaykum Mallam don Allah ina ka nufa? "
"Ku ina kuka nufa? " cikin sanyin murya naji ya fad'i hakan.
"Zaria muka nufa..... Please bawan Allah ka taimaka mana motarmu ce ta sami matsala.....Don.... "
Saurin katseni yayi ta hanyar fad'in"Okay.... Bana son dogon surutu ku shigo mu tafi kada ku b'ata min lokaci...... "
Ban damu da attitude d'insa bah sabida mu muke nima kuma dole mu saukar da kai k'asa.
Da ihuna nake fad'in"Malam Iro ku taho mun sami lift... "
Ina jin Ash na fad'in"Malama ba ko wani anyhow car zamu shiga bafa.... "
Mal. Iroro naji ya bata amsa donni bani da lokacinta yanzu, burina kawai na ganni agida.
Ce mata yayi"Sai ki kwana anan.... Kin ga ni nayi nan" Ya fad'i hakan sanda ya k'arasa rufewa motarmu tanfol, sannan ya nufo inda muke.
Musabaha su kayi dana cikin motar wanda bazamu iya cewa ga kamanninsa bah balle mu tantance ko shi d'in wani irin jinsin ne. Burinmu dai kawai mu shige motar. Ash queen has no option than to come with us.Dukkanmu mu matan abaya muka zauna, ayayin da shi kuma Mal. Iroro ya zauna agaba.
Mutumin ya tada motar mu kayi gaba.
Mal. Iroro yace"Insha Allahu idan Allah ya kaimu gobe da safe zan taho da mai gyara ya duba motar sannan na daukota.... Bawan Allah kai dai Allah ne kawai zai iya biyanka da wannan taimakon daka mana wanda kowa ya kasa mana ita... Wallahi ba don Allah ya turo mana kai bah, da bamu san ya zata kasance damu awannan daji bah don duk wasu dabaru namu sun Kare.... "
Advertisement
Na lura mutumin nan miskili ne na k'arshe don ko tari beyi wa Mal. Iroro bah balle asa ran zai tanka masa.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!!.... Tafiyar kusan 30mins mukayi sai gashi mun iso Zaria.Ban san meyasa nake son naji nayi magana da wannan bawan Allahn bah wanda na sanya masa suna da 'miskili'
Samin kaina nayi da ce masa"Don Allah Mal. Karfe nawa? "
"Baki da agogo ne? " atakaice ya bani amsa.
Azuciyata nace"Lallai guy d'innan d'an rainin wayau ne na first class kuwa. Shi kuma habit d'insa kenan kayi masa tambaya, instead ya maido maka da amsa, No sai dai Shima ya wurgo maka tasa tambayar? "
"Duk wayoyinmu amace suke.... "Na sami kaina da bashi wannan amsar tare da zuba mah bayansa wani uban harara, kai kace mah ko yana kallona ne nake masa wannan hararar ba tare da sanin Cewar aikin banza nake bah.
"Five minutes to 10.... " acewarsa.
Salati dukkanmu muka shiga yi tare da salallami. Mal. Iroro keta masa kwatance har muka iso unguwarmu 'Nassarawa G. R. A. Ko ina yai shiru abinka da dama can silent area ce.
Gabana ne ya tsananta faduwar gaba ah sa'ilin da naga mun tunkaro layin gidanmu.Wuri ya samu yayi parking akusa da gidanmu.
Muka firfito tare da zuba masa uban godiya babu adadi. Akaro na biyu na sake lek'awa ta windon bangaren mai zaman banza don sake masa godiya da k'yau.
"Bawan Allah godiya dubu, Allah ya biyaka da gidan Aljannah..... "acewata kenan.
Daga min hannu naga yayi tare da fad'in"Bana cika son yawan godiya.... "
For the first time, sai yanzu yake kunna wutar motarsa na ciki wanda hakan ya bani damar ganin fuskarsa da k'yau.
Wa zan gani?
Cike da mamaki na furta"
Murmushi ya sakar mini tare da kashe min ido d'aya, alokaci d'aya kuma ya tada motarsa yaja wanda ganin hakan ya sanya nayi saurin tashiwa daga jikin motar.
"Good nite pretty...... " hakan naji ya fad'a tare da figar motarsa aguje, na bi shi da idanuwa har ya bacewa ganina.
K'wank'wasa gate d'in gidanmu dasu Mal. Iro keyi ne ya maido da hankalina gunsu.Sai yanzu na tuna da tashin hankalin dake jirana.
Cikin rashin kuzari na k'arasa gunsu, adaidai lokacin Mal. Abu mai gadi ya budo kofar bayan yayi tambayar koh su waye? aka shaida masa ko su waye din, kafin ya bude.
Har rige-rigen shiga gidan muke.
Abinda ya soma fitowa daga bakina bayan mun shiga gidan shine"Mal. Abu Abba ya dawo? " na fadi hakan atsorace.
"A'ah bai dawo bah.... " ya fad'i hakan cikin magagin bacci.
Tsaki kawai naja don nasan duk cikin shirmensa na bacci ne don babu yadda za'ayi Abba yakai war haka awurin aiki.Dubana nakai zuwa bangaren 'parking lot' naga babu motar Abba, ta umma ne kadai ah ijje.Hakan ya bani tabbacin lallai Mal. Abu da gasken yake Abba bai dawo bah.
"Tunda ya fita aiki ne bai dawo bah ko kuwa ya dawo ya sake fita ne? " nayi masa wannan tambayar cikin tashin hankalin
Advertisement
"Tun fitarsa bai dawo bah amma Haj. Ita keta zirga-zirgar fita nemarku wai kuma layinku duka yaki shiga.... "
Ban k'arasa sauraronsa bah nayi saurin binsu Ash da gudu wanda kad'an ya rage su kai entrance d'in da zai sadasu da babban falo.
Bubbuga kofar muka soma yi wanda koh minti biyu ba'a dau bah sai gashi an budo kofar.
Umma ce ta fito tana mai farin cikin ganinmu wanda ada muke zaton da b'acin ranta zamu soma cin karo.
Cewa tayi"Alhamdulillah Allah na gode maka daka nuna min dawowar 'ya'yan nan lafiya.... Fadima what happened da sai yanzu kuke dawowa kuma lambobinku duk basa shiga?All my thought wani abin ne ya sameku? Kun kuwa san irin tashin hankalin da kuka sanya ni Ciki? God's so kind Abbanku ya kirani cewar bazai sami dawowa yau bah ayyuka sun masa yawa, but yayi tambayarku nace masa tun karfe biyu kuka dawo.... "
Hamdala na shiga jerowa ina mai tsananin murna da Kuma godiya ga ubangiji,jin cewar Abba bai dawo bah kuma bai san halin da ake ciki bah balle Mu fuskanci b'acin ransa.
Mal. Iroro ne yai mata bayani"Haj. Kiyi hakuri don Allah wallahi yau ruwa ake ta tsulawa akano tamkar da bakin k'warya..... Kuma mutanen gidan suka hanamu tasowa wai sai ruwan ya tsaya... Ruwan bai tashi tsayawa bah har sai bayan magrib.... Mun taso kuma motarmu ta lalace awani k'auye.... Da k'yar muka sami wani bawan Allah ya taimakemu ya kawo mu har nan kofar gida.... "
Ambaton bawan Allahn dana ji yayi ya sanyani murmusawa tare da furta"kenan.... Ka hadu ta ko'ina.... halinka ya mugun min"
Maganar Umma ce ta katse min 'yar gajeriyar tunanina na"Allah mun gode maka.... Shi kuma bawan Allahn nan Allah ka jagoranci rayuwarsa ka kuma saka masa da mafificin alherinka.... Sannu mal. Iroro Allah ya biyaka kaima, jeka ka huta abinka.. Gobe sai kakai mai gyara ya duba motar idan yaso sai ka daukota... "
"Eh Haj. dama hakan ke raina... "
Tace"Toh Masha Allah ahuta gajiya... " Yai mana sallama ya tafi b'angaransa don yana da d'aki agidan wanda wani lokaci matarsa takan zo tadan masa kwana biyu sannan ta koma.
"Aysha back to you.... Yanzu mai zamu ce wa iyayenki gobe....? " Umma tayiwa Ash wannan tambayar tare da tsareta da idanuwa.
"Laah!! Umma wallahi babu wata matsala ta bangarena... Dad d'ina baya gari kuma dazun na kira mum na fad'i mata cewar anan gidan zan kwana...... " acewar Ash kenan.
Mum tace"Masha Allah komai yazo mana da sauki amma gaskiya diz is ur last time of going to places like dix.... Inaaa!!! Bada yawuna kuma bah....hakan bazata k'ara faruwa ba na gaya muku "
Kallonta kawai nayi don ni kaina nasan tama yi mana kokari da bata mana fad'a bah. Muka shige ciki, dakunanmu straight muka nufa.
Na baiwa Suhaima panadol tasha don tace ciwon kai kawai take ji,dama can zazzabin na Sanyi ne kuma yanzu ta daina jinsa.Na tambayesu koh sunyi salloli? Suka tabbatar min da cewar lallai sunyi, magrib ce kawai da Isha'i suka rage masu.
Anan nasan cewar wato yau nice na zama precilia bah sallah ba salati. Banyi azahar bah, la'asar ga kuma magrib da isha'i.
Ban biye takan wayata bah don har yanzu amace take, jonata kawai nayi ah chargy, sannan na tafi na dauro alwala.Na hau biyan sallolin da ake bina babu gaggautawa kai kace koh sallar tahajud nake.
Umma ce ta kawo mana abinci adaidai lokacin na idar. Tunawa nayi da cewar yau komai ban sanya aciki bah idan ka cire 'ice-cream' d'in dana sha.
Da sauri na tankwashe kafa na soma cin abincin har sai dana jini nayi Kat! Kafin na hakura.
Zan iya cewa yadda naga rana haka naga dare don ko runtsawa banyi bah.Tunani suka bi suka addabar mini zuciya suka kuma hanani sukuni..
Mubeen shine first subject na tunani na, because koh wani tunani zai biyo baya, he waz the caused.Arayuwata ban taba tunanin Mubeen zai iya yi min hakan bah sabida yadda na bashi 100% trust.... Ban taba tunanin yana da aure bah hadda 'ya 'yar shekaru hudu bama..... abinda mah na manta na tambayesa shine.... How old is her mum sanda ya aureta? Because yarinyar tana min Kamar mah Suhaima ta girmeta.
Abin daya fi d'aure min kai bai wuce wulak'ancin dasu Ash sukace Mummynsa tai musu bah.....its hard for me to believe dat sabida irin tarban mutuncin data mana ah farko da kuma k'arramamun da tayi ta hanyar entertaining d'inmu with abinci da tayi.... Koda yake ance d'an Adam ba d'an goyo bane.... Hadda mah korarsu waje? Hmmm lallai ta nuna mana cewar fuska biyu gareta,musa ah fiska sannan fir'auna azuci.
Hmmm coming to Ina kuma zashi da wannan daren alokacin? Har muka samu ya taimaka mana? Abu sai kace plan??...... Wats really going On?
Da dai naga wannan tunane-tunanen na nemar haukata ni and again bani da amsoshin tambayoyina ya sanya ni sake d'auro alwala don gabatar da nafilfilfili don samin kusanci da ubangijina.................... 📝
Hafnan's POV
Toh guys gashi kuma an sako mana ENGR. MAHMOOD MUSTAPHA wanda wa ne ga DR. MUBARAK MUSTAPHA..... Toh meke shirin faruwa ne?
ADVICE
Don Allah ina son ku natsu ku baiwa labarin nan kyakkyawar fahimta don idan baku manta bah ah farko nace muku.... 'Wannan littafi ne mai matuk'ar d'aure kai da ban al'ajabi'..... So pls give ur full attention....
NEMAR GAFARA
Pls my deari'es ba zaku ga posting d'ina bah yau har sai gobe da daddare sabida wani uzuri nawa daya taso.... Pls bear with me.... Thank you💗!!!!!
YOURS
©QUEEN HAFNAN©
Advertisement
- In Serial96 Chapters
Undermind
Saskia thought her life was finally getting back on track after the accident. Then she got trolled. Now she's up a tree the size of a planet, and all who meet her either run screaming or attack on sight. If everyone would just calm down and stop trying to kill her for one moment, she might get a chance to explain that this has all been a horrible misunderstanding. Contains light GameLit/LitRPG elements, but no number crunching. Chapters average around 4500 words / 16 pages. Updated weekly. Cover art by Ben J.
8 196 - In Serial26 Chapters
Pokemon Black & white: The Complete Story
This is a fanmade take on the story of the Pokemon Games, Pokemon Black and White, and Pokemon Black and White 2. Enjoy!
8 84 - In Serial59 Chapters
Soten (Book I in The Saga of Mira the Godless)
Anyone on the Isle will say Lady Mira caused the Twenty Years' War. While they're at it, they'll call her a witch, a whore, or a heathen, maybe all three in the same breath. Soten is Mira's version of the story. Captive in a Northern village, Mira expects brutality from the rough climate and harsh Northerners. Instead, she discovers a land where people speak their thoughts out loud, where women are free to be with any they desire, and those who divine messages from the gods are listened to, not burnt at the stake. Mira's idyllic new life is threatened when she hears of her brother's growing army to the south; she doesn't need rescuing; she's far too attached to the life she's building (and the lighthearted raider who is quickly becoming a central part of it). Then she meets Arik, the enigmatic Norsern king, a man who has drastic plans for next season's raids, plans that involve the sister of a great southern commander. To Mira, this is a story about love. To the rest of the world, it is a story about war. Book II: KAKEN coming soon!
8 191 - In Serial172 Chapters
Conquest of Avalon
Revenge. The Kingdom of Avalon swept across the Empire of the Fox a generation past, conquering the heartlands and leaving the broken remnants to stew in the island duchy of Guerron. This isn't a story of Good versus Evil, of kindly kings doing their best to lift all subjects, or of unvarnished heroes doing battle against evil. Instead, this story is about power: who has it, who wants it, and what people will do to obtain it. It is about the violence inherent in the imperial project and how even the most well-intentioned rulers and conquerors are, still, engaging in systemic violence against those conquered and defeated. Our three point-of-view characters are a peasant turned fire wizard, an excitable duelist with more enthusiasm than sense, and a scheming mage-priestess bent on reclaiming her family's birthright and waging war on the foreign oppressors who rule her home... no matter the cost in blood or treasure.
8 157 - In Serial15 Chapters
Ashes of the New World 2: The Divine Mess
The world is overpopulated. Gods are thrown into prison. Vita's troops are invading kingdoms with no opposition. But Norah isn't confident she's on the right side of history no matter how good her new life is. Meanwhile a boy, Helsing Curseblood, is given an opportunity to free his family from a curse causing his fate to intertwine with hers.
8 142 - In Serial16 Chapters
Brave Realm Odyssey - Adventurer Resolution
Grinding, farming, sleeping. Brave Realm Odyssey was everything Astre's life revolved around for the last two years. All of his actions focused on achieving a single goal. Saving enough money to save his sister. To not fail again. As the time limit crawled closer, he sees his final chance. Brave Realm Odyssey's greatest tournament and it's first place reward.[participant in the Royal Road Writathon challenge] *** Hello there. It's just my rambling here, so nothing exciting. I have been writing quite a bit since the last time I posted on this site. Honestly, I wanted to get rid of that failure of mine, but I keep it up both to embarrass and motivate myself. I keep thinking to myself that one day I will go and fix it. Something more, well, this is an excuse, but English is not my first language. It will never be, and I think it will always hold me back in some way or form. That said, don't fear to berate me and to criticize my work or being toxic. I think I can take that. I somehow want that. Any attention is better than none, isn't it? That's all! I hope you will enjoy this work.
8 189