《SHIN SO DAYA NE? (Complete)》Chapter Three
Advertisement
💝SHIN SO DAYA NE?💝
_Watpadd:Hafnancy_
TARE DA ALKALAMIN
📝
HAFSAT AL-MUSTAPHA
🌸BABI NA UKU🌼
Page 10-15
Yau ta kama wata larabar wacce ta kasance sati guda kenan da fara haduwata da Leedar, kuma tun daga ranar bamu kara haduwa ko ahanya ba. Hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, don aganina ya kulle chapter dina ne gaba daya. Ash queen ce ma take ban dariya data sanya kanta agaba sai faman neman hanyar da zata rama wulakancin da yai mata take.
Abinda ban sani ba kuwa, ashe tun ranar da muka rabu ba shiri da Leedar ya sanya aka fara masa binciken ko ni din 'Yar wacece..Toh da yake ni ba wani yawo nake acikin makarantar bah ya sanya ba'a wani sanni haka nan ba kuma wanda ya sanya suyi masa binciken akaina, basu gane wani level da dept nake bah.Ayadda yai musu describing dina ya sanyasu bin en mata masu dan yanayin kama dani, sai su kawo masa wrong details na en matan amatsayin niche sai yace "I don't think she's the one"... Wani lokaci sukan taho masa da en matan ko za'ai sa'a ina ciki, su kuwa en matan da zarar sunji cewar Leedar ke son ganinsu, toh da gudu suke zuwa don aganinsu cewa zaiyi yana sonsu.
Shigowata makarantar kenan, na karasa parking space nayi parking motata. Na fito cikin shiga ta alfarma ina takawa sannu ahankali cikin natsuwa. Wata bakar jeep ce ta gifta ta gabana da gudu wanda har sai dana dan tsorata na tsaya cak!! da baki bude na bi motar da idanuwa..Da gudu kuma naga motar na dawowa da baya, daidai gabana aka tsaya cak!
Zubawa dukkan ilahirin motar idanuwa nayi naga ta inda wannan rough driver din zai fito sabida glass din motar tinted ce baka ganin wanda ke ciki.
Wani hadadden guy ne mai zafi naga ya fito daga side din driver wanda ke nuni da cewar babu tantama shine direban. Kallo daya yayi mini naga yayi saurin maida dubansa cikin motar yana fadi da karfi"Guy I told u she's the one... Come out and see it for urself. "
Yana gama fadin hakan, sai kawai naga an budo kofar mai zaman banza da karfi..Daga kafafuwa na soma kallon irin wankan da aka dauka, sannu ahankali nakai kan fuskarsa... Gabana ne ya buga wata irin ganga adalilin fuskar dana yi arba da ita,halittar da atunanina ta gama watsar da lamarina irin totally din nan. Kun san waye? Its Freaking Leedar again!!!
Fitowa yayi daga motar ba tare da ya rufe murfinsa ba,sannu ahankali cikin takun kasaita ya soma nufoni ina dan ja da baya, kirjin nan tawa kamar zata fado kasa don tsoro da fargaba.Soma maganarsa ce ta sanya ni dakatawa daga inda nake.
Cewa yayi"who dah hell do u think u ar by walking out of my sight without u even saying a word?...inata magana kin maidani wani banza karshe ma wucewarki kikai.. Do u know hw dat thing hurts? Gaban jama'a kikai humiliating ALIYU HAIDAR AHMAD? Ayau dinnan nakeson ki fadamin ko ke din diyar wacece afadin garin nan kuma da abinda kike takama.... "
"She's d first daughter to His excellency 'Chief justice Muhammad Sa'ad mai nasara.... I guess u knw him well and I knw dat u ar shocked right?...idan kaji ana 'Fadima Sa'ad Mai Nasara' toh itace... Kaga kuwa yanzu matsayinta da naka ko kusa ba daya bane... Becos she's d daughter of a well educated and d most populous lawyer in Nigeria ayayin da kai kuma son of a wealthy person ne wanda agarin Zaria kawai aka sanshi sai kuma garuruwa kalilan.... And again I heard u mentioned humiliation ..har ashe baka da kunyar ambaton cewar an maka wulakanci? Ashe ba dadi ni kamin? Zuciyarka ce kadai take da jini, nama da kuma feelings da har zaka Ji zafin abinda tayi maka?ka taba tunanin abinda kayi min rannan ka kyauta ko baka kyauta ba?... Idan kuwa haka ne zan iya cewar duk ilimin da ake cewa kana dashi toh ni ban gansa ba,hasalima zan iya cewa kwakwalwarka bata ja irin ta masu hankali, don haka gaye da sauranka.... Kuma lemme tel u sumtin.. Idan har ka saba ciwa en mata mutunci toh kuwa ka sani cewar akan Aysha Adam inkiya Ash queen wallahi ka daina..... "
Advertisement
Bude baki nayi nabi Ash queen da idanuwa wacce zuwanta kenan gun, na jinjina irin kokarinta na gaggayawa Leedar maganganu son ranta. Abokin nan nasa wanda suke tare ne naga yana yunkurin kai mata mari, da sauri Leedar ya dakatar dashi ta hanyar rike masa hannun dazai kai Marin.
Cikin zafin rai abokin yace"Haba Leedar kana fa gani wannan kucakar yarinyar take fada maka maganganu son ranta abinda wata 'ya mace bata taba maka ba... Abin mamaki kuma ka tsaya kana kallonta, haka wannan mai fuskar babyn robar kana mata magana rannan ta shareka ta maida ka soko awurin tayi wucewarta, sannan yanzu ka kasa daukar mataki akansu... Ni kuma da nake nemar daukawar kana nemar hanani...Abokina yaushe ka soma daukar raini da amsar wulakanci daga hannun yan mata? Yan matan mah low class babe's.. ? "
Cikin tsawa naji Leedar yace"Fresh its okay... Babu ruwanka dani juz stay out of this... "
Cikin murmushi wanda nake tunanin na karfin hali ne naga ya juya yana fuskantar wanda aka kira da Fresh, yace"Chill guy, saurin daukar matakin na menene? Koh shin ka manta waye Leedar ne? "
Murmushi naga shima Fresh din yayi tare da dan bugun kafadar Leedar yace"Yes hakane kuma faa abokina... I trust you Nawan.. "
Leedar ne ya juyo garemu yana nuna Ash queen yace"You will surely pay for duk wulakancin da kikai wa Leedar, don baayi wata mace da zata taka Leedar ta wuce lafiya ba kuma ba za'a taba yinta ba... "
Ya juyo gareni yana nuna ni nima yace"And you, banda abinda zan iya ce miki for now tunda naga kamar so kike ayi wasan 'yar kurma da dan kurma,well keep calm Leedar wil b coming back for you... "
Yana gama fadin hakan suka shige cikin mota suka figeta kamar zasu tashi sama ayayin da suka bar mana Kura nata mana shawagi.Abin haushi da dariya Ash queen kamar zatai hauka don bakin cikin rashin basu amsa da bata samu tayi ba.Har da fa cire takalmanta masu dan tudu tana jifar bayan motarsu dashi,ni abin dariya mah ya bani.
Juyowa tayi gareni kamar zata sauke kwandon masifar akaina, tace"Fadima anya kina da hankali kuwa? Can't u juz see wat dix bush guys did to us? Wancan dan akuyan Mah har kiranki yai da babyn roba and u couldn't take any action u ar here laughing kamar wata tababbiya...Fadima miskilancin nan naki wlhy watarana zai iya kaiki ya baroki don nama lura kin dauki abin nan nasu Leedar da wasa.... "
Maganganun Ash queen sun kaini wuya amma sai na danne na batsar, nace"U juz mentioned action... Ina kike sanda abokinsa ya kiraki da Kucaka? Wani matakin kika dauka?... U ar here telling me dat na kasa daukan ko wani action sai miskilanci...friend my advice to u is dat Ki fita aharkar su Leedar cuz they ar guys and they can do and undo... Wasu mazan basu da imani ko kadan, zasu iya aikata wani mugun abu akanki amma bawai fata nake ba,idan sunzo inda kike pls kiyi kamar baki san da zuwansu wurin ba, idan kuma suna sossoka miki maganganu toh ki ari kunnen kurma kamar yadda kika ga nayi ki sharesu juz lyk shit don nama lura abin yafi ci musu rai, amma idan kina tanka musu shi yake dada sanyasu jin dadi suna ci mana mutunci... My dear atleast for once ki koyi shanye ire iren ababen nan and dat defines your real class... Yawan surutu da kuma masifa Sam ba mutuncin 'ya mace bane don yakan janyo arainata.. "
Nayi fuskar tausayi nace"pls my Aysha ki rage yawan tsiwa da masifa... Daga yau ina son ki kulle babinsu ALIYU HAIDAR.. Kinji Ayshata?"Na lura maganganuna sunyi matukar tasiri ga Ash queen don yadda naga jikinta yai sanyi.
Advertisement
Ba zato ba tsammani, abin mamaki abin tausayi... Hawaye naga Ash queen ta soma zubarwa ta kamo yatsun hannayena tana dan murzasu tace"Insha Allah Fadima I promise u as from today na canza, zan zama kamarki cuz I really love ur lifestyle...zancensu Leedar Kuma I promise u na kulle babinsu ayau dinnan, ba ruwana dasu, ko sun shiga harkata hakuri mah zan kara basu... Fadima Sa'ad u ar more than a friend to me... Tanx for everything I really love you.. "
Tana gama fadin hakan ta rungumoni tana kuka, na shiga jijjiga mata baya ina lallashinta nace"Haba Aysha meye haka? Kukan na menene?ya isa hakanan kinga mutane sun fara kallonmu..kinji pls? "
Da kyar na sami tayi shiru, sannan muka wuce daukar wani lecture wanda har lokaci ya kusan shigewa muna nan muna shirme.Sai kara tunawa da Maganganun Leedar nake ina zuba murmushi ni kadai, ahankali na furta"Leedar, Fadima will keep waiting for you as u said...hmm ji mini ja'irin yaro kai kana son ka taka mutum ka wuce lfy amman kai bakason ko tabaka mah ayi... Am no longer scared of u, sai na ganka!!!"
**********
Misalin karfe goma sha daya na safiyar ranar wata asabar, zaune nake kan daya daga cikin kujerun shakatawa da kuma karatu na dalibai mai hade da tebirinsa dake karkashin wata katuwar bishiya dake amakarantar.
Na bada hankali wajen karatun wani course da muke da exams dinsa ran monday. Jikina ne ya bani cewar ana kallona don haka sai nayi saurin dago kaina, ai kuwa wanda na gani ne ya sanyani saurin mikewa gabana na faduwa... OMG!! Its Leedar again!!!!
Ahankali na soma magana hade da tamke fuska uwa ban taba dariya ba"You again? Wai don Allah mey na tsare maka ne kake ta bibiyata? Sata nai maka koko kashe maka wani nayi?... Idan kuwa babu koh daya toh pls na rokeka don Allah Leedar kayi hakuri ka fita aharkata... Pls juz go I don't want any of ur trouble today..... "
Clapping dinsa ne ya dakatar dani daga maganar da nake,dauke yake da wannan munafukar murmushin nan tasa, yace"wow ashe 'yar kurma na magana? Ko dama can sarauta ce ake nuna min? Iyye tell me pretty? "
Da sauri nace"kar ka sake ka kara kirana da 'yar kurma don ba sunana kenan ba... "
"Toh Prettiest Fadima Zahra " hakan naji ya fada cikin wata irin sweet voice dinsa wanda ya sanya har naji wata yarr acikin zuciyata.
Ban ce masa uffan ba sai ma hada takadduna nayi na sanyasu cikin jaka, sannan na soma tafiya don barin wajen don nasan halin Leedar zai iya janyo mini abin kunya agaban jama'ar dake awurin da suma suke karatu.
Gani nayi ya shawo gabana yana fadin"Fadima idan kina yiwa Allah da manzonsa ki tsaya ki saurareni..wallahi yau da rigar mutunci nazo da kuma nemar gafararku " yadda yayi maganar ya nuna cewar he is damn serious kuma daga yanayinsa ya nuna kamar yayi nadamar abubuwan daya aikata, hakan ya sanya jikina yin sanyi.
Ambaton rigar mutuncin da yayi ya matukar ban dariya amma sai na danne, hakan ya bani damar karewa shigarsa kallo.Sanya yake cikin fararen yadi mai kyan gaske da kuma daukar ido,hularsa da kuma takalminsa bakake ne,Farin agogonsa na Rolex da Farin azurfansa mai masifar kyau na sanye ahannun hagunsa.Sai naga yayi mini wani irin kyau na musamman da kuma kwarjini ah ido.
Kokarin magana nake ya kashe mini ido daya yace"please pretty"
Ban san mey yasa na kasa musa masa ba, muka koma kan kujerar dana baro muka zazzauna, dayake kujerar na iya daukar mutum fiye da biyu mah.
Zamar mu keda wuya nace"Ina sauraronka"
Tsawon seconds goma bece kala ba, can naji ya sauke ajiyar zuciya sannan ya soma magana cikin daddadar muryarsa"Malama Fadima da fari inason na soma da baki hakuri akan abubuwan da suke ta faruwa... Nasan Sam first meeting namu beyi kyau ba wanda ni da kaina na janyo rashin kyan nasa, don da'ace ban tsokani kawarki ba da hakan bai janyo kiyayyar da kike mini ayanzu ba.. "
Da sauri na tari numfashinsa"Kaji na fadi da bakina cewar ni na tsaneka ne?"
Murmushin nan tasa dai yayi, yace"Fadima, action speaks louder than voice, kuma labarin zuciya atambayi fuska.... Ni dai gashi nan ina kallon yadda tsantsar kiyayyar da kike mini ta mamaye dukkan dara daran idanuwarki, ga tanan kuma shimfide saman pretty face dinki.. " Yana bayanin nan yana demonstrating da dan yatsarsa har abin mah yaban dariya.
Akace sai ka zauna da mutum ne zakasan ainihin halayensa. Toh nidai yau na gan different characters agun Leedar.. Na lura shi mutum ne mai son barkwanci da kuma wasa wanda afarko muke ganin kamar dan rainin wayau ne,ashe abin ba haka bane sabida cikin dan kankanin lokacin nan har na dan saba da Leedar da funny characters dinsa. Mun yafi juna da cin mutuncin da akai wa juna wanda dama can mostly fadan tsakaninsa da Ash queen ne.
Ya kuma nemarwa abokin nan nasa gafara wanda ya kira fuskata da fuskar babyn roba wato Fresh, sunansa wai Abdulbasi Bashir.. Ya kuma nemi dana hadasa da Ash queen suyi sulhu, murmushi kawai nayi don nasan za'a kai ruwa rana kafin Ash queen ta yafe, idan har zama ta yafen kenan.
Ji nayi Yace"Yauwa pretty kamar yadda na fadi rannan, kina kama da wacce na sani... "
Dada gyara zama nayi nace"Yes akwai mai masifar kama dani don idan mah ka ganmu tare, idan har dacan bawai saninmu kayi ba toh tabbas dakyar zaka iya tantance wacece wani kuma wacece wace sabida irin tsabar kamar da muke... Sunanta Suhaima Sa'ad Mai Nasara, she's my immediate younger sister whom I so much loved and cherished."
Cike da mamaki naji yace"Are u serious? Suhaima Sa'ad kikace? "
Cikin tuhuma nace"Yes of course ko ka santa ne? "
Da sauri ya tari numfashina"No! No! Nooo!! Kawai nadai taba jin Sunan ne... Yaushe zaki kaini gidanku na ganta?"
Abin yaban dariya nace"Lol why ar u in a hurry? "
Murmushi yayi yace"Sabida inason naga resemblance dinnan da kikace kuna dashi.. "
Ban kawo komai araina ba nace"its alryt amma wacece wannan da kace muna kama da ita kuma? "
Yace"Sunanta Fadima Sa'ad Mai Nasara "
Dariya sosai nayi nace"come on Leedar kai dai wallahi baka gajiya da zolaya, so dama jan kafata kake tayi tun rannan wai ina kama da wacce ka sani ashe duk karyace? "
Dariya shima yai kafin yaci serious yace"Fadima can we be friends?"please don't say no.. "
Ahankali nace"Okay ba matsala Allah ya tabbatar mana da alherinsa. "
Yace"Ameen"
Fira muke tayi sosai kamar dama can mun saba da juna, mutane sai kallonmu suke kila suna zaton ko ni din budurwarsa ce, anan yake fada min cewar ya taba soyayya da wata yarinya amma basa tare ayanzu. Ya bani labarin abinda ya rabasu Wanda ko kusa banji dadin hakan ba.Nayi matukar mamaki da yace mini ahalin yanzun baida wata budurwa, hasalima shi yan mata mah basa gabansa, kuma na yadda da zancen nasa sabida nasha jin mutane na fadin cewar duk irin class din da yake dashi bashi da budurwa ko daya, Wannan yarinyar ce dai mutane suka sansu tare gashi kuma basa tare kuma dama can wai ba yar makarantar bace. Shima yayi matukar mamaki dana fada masa bani da saurayi don ni batun soyayya mah bana kawo shi aka.
Atake anan mukayi musayar lambar waya, mukayi sallama ya tafi ya barni wai na samu nayi Karatu.
***********
Abin mamaki, Ba'a sami wata matsala ba awurin Ash queen kamar yadda mukai tunani, don cikin ruwan sanyi ta yafe masa, hatta Amininsa Fresh sai dayazo akayi sulhun dashi. Daga nan fa muka zamo best of friends mu hudun, wato ni, Leedar, Ash queen da kuma Fresh.
Cikin kankanin lokaci Leedar ya bijiro mini da batun soyayya wacce nayi kwanan murna ina farin ciki akai sabida dama can na soma crushing akansa.Abdulbasi wato fresh da Ash queen suma ba'a barsu abaya ba, sun kulla soyayya mai tsafta don zan iya cewa tsananin son da sukewa juna ya zarce tamu nida Leedar.
**********
Watarana muna zaune da Suhaima muna fira,acikin firar tamu ne nake fada mata cewar nayi saurayi.
Cikin ihun murna tace"Wow big sis ar u serious? "
Murmushi nayi nace"Of course! I am.. "
Ta cigaba"Atlast my Anty big Sis is finally inlove...who's dat lucky prince? "
Na bata labarin fafatawarmu da Leedar wacce atlast yayi resulting into serious relationship, sabida yanzu duk ABU babu wanda baisan cewar Leedar ne ke nemana ba.Muna da masoya da yawa ayayin da kuma muke da makiya dubu agefe.Soyayyar tamu abin birgewa ce sosai sabida yadda muke gudanar da ita cikin tsafta, wayewa, mutunta juna da dai sauransu.
Mikewa naga tayi ayayin da annurin fuskarta ya dauke, tace"Sis Aliyu Haidar (Leedar) kikace fa..? "
Nace"Of course! Ya naga yanayinki ya canza kodai kin sansa ne?"
Da sauri tace"No! No!! Noo!! Kawai dai naji gayen bai kwanta mini arai ba.. I juz felt lyk am beginning to hate him tun ban gansa ba"
"Kodai don abinda yai mana nida Ash queen ne ya sanyaki tsanarsa too early haka?"
Tace"No, sis pls ki rabu dashi, wlhy ni da kin fada mini da wuri da ban bari soyayyar nan taku tayi nisa ba.. "
Da sauri nace"Ai bamuyi wata nisa ba.. Juz 2month.. Amma wai don iskanci don ke bakya sonsa shikenan akace ni kada na sosa? Ko ke zaki zauna min dashi?"
Ji nayi tace"No sis Fadima, kawai nidai ki rabu dashi bai kwanta mini arai ba... Pls cant u juz do diz for ur Suhaima Sa'ad?"
"Gaskia Suhaima baki da hankali... Agabana kike cewa kin tsani Saurayina? Lallai dix is wat we called hatred at first sight, baki ma gansa ba kenan har kin tsanesa.? "
Bata kara cewa komai ba but na lura hankalinta atashe yake. Ni abin nata mamaki ma ya cigaba da bani, haka kurum wai ta tsanesa, for what? Wai harma na rabu dashi.Toh tun daga lokacin Suhaima ta dauki tsanar duniya ta kara daurawa Leedar,kuma ni na rasa dalilin tsanar,kullum idan na tambayeta dalili sai tace min juz lyk dat,once suka hadu shima sama-sama suka gaisa don ma wai ina wurin ne da bansan mai zai faru ba kuma hasalima nice na matsa mata da taje su gaisa sanda yazo gidanmu.Abu kamar wasa har iyayena sun sansa, sai ya zama dan gida gaba daya.
Muna haka ne fa har Allah ya hadani da Dr Mubarak (Mubeen) awaya,wanda na lura shi Suhaima yafi kwanta mata arai, saisa ban san ya akai na fara sonsa ba kuma ban taba fada masa cewar ina da Leedar ba sai yau da Suhaima ta janyo mini wannan rigimar wacce da kyar zan iya kashe wutarta sabida sanin da nayi wa Mubeen dina da bala'in kishi.
Sorry pls Fans zan dunga updating each part kullum. Pls bear wit me kun san d typing is not easy. Thanks and don't forget to vote!!!!
YOURS
©QUEEN HAFNAN©
Advertisement
Into a Fantasy
“Dream World” is the most popular realistic VR (virtual reality) game that caters to more than half of the people on a futuristic Earth. An ordinary teenager who sets his game name to Scott Wayland enters the virtual world as an orphan near the city of Lucis. The story starts when, a few years later, his mentor dies and gives him an ultimate quest which Scott has no choice but to strive to complete. In the middle of his mission, he encounters a high-level Sorceress who helps him on his quest by recruiting five other players to raid the fortress of the man who killed his mentor in cold blood. [UPDATES EVERY TUESDAY]
8 199Re: Generic Isekai - An Isekai with a loooooooooooooong title.
Bob got hit by a truck and died. He then was reincarnated into a different world, where he built his harem, battled demons and saved the world. (Sorry, still early chapters, no harems yet.)
8 135It's the Federation Navy(Azurlane x Battleship OCs)(ON HOLD)
This book is just made to crossover with Syria's Kristal Fleet book. Enjoy.
8 159From FPS Game to Another World
After 2 Years of absence in the game, one of the top player named Truend returned.Many things changed but some still remains.One thing he never expect to happen, that is...
8 52Dark Lord
He was finally back. After so long, he was able to break the seal that had condemned him.After suffering for so long, he finally can get revenge.He now remembered the day the blood of his love was spilled.The day that he was killed, taken away from his arms. Now that he was back, he swore to get revenge.He was known as the Dark Lord.AN: My second book written, probably a bit confusing overall. There is definitely some mistakes in it, but I will keep it as it as. This book is over two years old but was finished about a year ago. Beware, there's definitely a bit of mistakes and editing errors that I never caught.
8 116little miss Penny-wise has a crush (Richie Tozier X reader)
Y/N is a young girl who is your avarage girl. She lives with her father in a big house and has her friends like everyone else. But there's one thing her friends don't know. That she is the daughter of the evil monster Penny-wise.
8 160