《Special Dishes In Hausa》Awara

Advertisement

Kayan hadi:

Waken suya

Lemun tsami

Manja

Tattasai da attarugu

Kayan dandano

Yanda akeyi:

A wanke waken suya a jika shi yayi awa takwas zuwa sha biyu ko a jika a barshi ya kwana.

Bayan ya jiku a markada shi yayi laushi.

A samu yadi me laushi sosai a tace kullin, ayi amfanida ruwa kadan wajen tatar. A zubar da dusar in an gama ayi amfani da ruwan.

A dora a tukunya a kan wuta.

Idan ya tafaso a sauke a saka ruwan lemun tsami, ana zubawa ana gaurayawa.

Idan kuma lemun tsamin yaji za'a ga ya dan fara gudaji kanana kamar yadda kuke gani:

Ban cika ruwa ba wajen tata dan haka lemun tsami uku kawai nayi amfani dashi.

Daganan se a mayar kan wuta a barshi yayi minti ashirin.

Anan ne ake diga manja kadan saboda zena kumfa yana zuba daga tukunyar, amma ba dole bane.

Idan awarar tayi Za'a samu gudajin kato da yawa:

A tanaji kwano da yadi me laushi a juye awarar ana saukewa daga wuta, a matse ruwan daga awarar.

Daganan kuma:

1)za'a iya saka jajjagen kayan miya da kaya dandano sannan a kulle yadin a dora abu me nauyi akai a barshi yayi minyi talatin har se ta kame jikinta awarar.

2) A matse ruwan a dora abu me nauyi a bar awarar ta kama jikinta ba tare da an saka komai ba.

Za'a iya yankawa soyawa a soya nan take ko kuma a ajiye a fridge ko yaushe a dauko a soya.

Danyar awara a fridge na iya wata bata lalaceba.

Idan za'a soya awara ana yanka ta wasu su tsoma a kwai wasu a kwabin filawa kafin a soya.

********************

Vote, comment and share

Thanks

    people are reading<Special Dishes In Hausa>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click