《Special Dishes In Hausa》Indomie Me Kwai

Advertisement

Kayan hadi:

Indomie 1

Kwai 2

Albasa

Tattasai da attarugu

Curry

Mangeda/butter

Kayan aiki:

Prying pan

Tukunya

Colander

Yanda akeyi:

A samu tukunya a zuba ruwa Rabin karamar tukunya, in ya tafasa a saka indomie a ciki ita kadai kada a saka seasoning da spices din.

A dafa ta kamar yadda ake dafa taliyar spaghetti.

Idan ta dahu se asaka colander a tace a barta har se ruwa ya tsane.

A fasa Kwai biyu a kwano a saka seasoning da spices na indomie aciki, za'a Iya dada kayan dandano kadan a ciki.

A saka jajjagen Albasa, Tattasai da attarugu se a saka Curry a kada Kwan.

Idan indomie ta gama tsotsewa ruwan ta ya tsane se juye ta a cikin Kwai a gauraya.

A saka Mangeda cokali biyu ko Kuma butter teaspoon dayan a Prying pan yayi zafi.

In mai yayi zafi ko butter ta narke se a dakko indomie a juye a ciki.

A soya Akan wuta karama.

Idan kasan ya soyu se a juya sama Har se ta soyu gabadaya.

************************

Vote, comment and share.

Thanks.

    people are reading<Special Dishes In Hausa>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click