《Special Dishes In Hausa》Coconut Oil

Advertisement

(EDITED)

Kayan hadi:

Kwakwa

Ruwa

Kayan aiki:

Grater

Tukunya

Yanda akeyi :

NB. Domin yin kwalba guda na man kwakwa Ana bukatar kwakwa guda Sha biyu 12.

Hanyoyin sarrfa kwakwa zuwa mai daban dabanne, sede wata hanyar tafi sauki akan wata.

1)

Da farko Bayan an bare Bayan kwakwa me tauri se a wanke ta a gurza a Grater.

Bayan an gama gurzawa se a saka a tukunya da ruwa a barshi yayita tafasa.

Man kwakwa Yana dadewa kafin ya kamala.

Bayan ya Dade Yana tafasa man ze fara tasowa Yana tsatsowa ruwan Yana tsotsewa.

2)

A bare kwakwa a markada da ruwa a blender, in babu blender za'a iya grating.

A tace ruwan a bar dusar.

A ajiye ruwan a fridge ya kwana, amma ba dole bane a saka a fridge.

Bayan yayi awa akalla takwas ba tare da ana tabawa ko motsa shi ba, za'a samu ya kasu biyu.

A sama za a samu ya taru ya daskare kamar kakide a kasan koma ruwane.

A samu daskararren a zuba a tukunya a dora wuta ayita juyawa, bayan awa daya ko fin hakan za'a samu ya koma mai da kuma tuka a kasan.

Idan tukar ta koma dark brown se a sauke a tace man kwakwa.

Man kwakwa na da matukar amfani wajen gyaran fata da gashi sannan kuma ana girki dashi.

Na kosa in siyo kwakwa in hada nawa man kwakwar in dinga shafawa harse na fara walki na zama anti yalalash.😉

********************

Vote, comment and share.

Thanks.

PS kada a manta da vote, comment da share

Nagode

    people are reading<Special Dishes In Hausa>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click