《Special Dishes In Hausa》Dambun Tsakin Masara

Advertisement

Kayan hadi:

Tsakin masara

Zogale

Kayan dandano

Albasa

Tattasai da attarugu

Kayan aiki:

Colander

Tukunya

Cokali

Yanda akeyi:

Idan an tankade Garin masara Ana samun Tsakin masara.

A wanke Tsakin masara kamar yanda ake wanke gari, ta hanyar zuba ruwa a ciki a gauraya sannan a zubar da ruwan Har se datti ya fita da ragowar Garin masarar.

A wanke Ganyen Zogale a tsige tsinke da sandar jiki.

Za'a Iya amfani da busasshen Zogale.

A samu Tsakin masarar a saka masa Garin Zogale yaji se a gauraya.

A saka gishiri, yankakkiyar Albasa, Tattasai da attarugu a gauraya.

A dora tukunya a wuta a saka ruwa kadan se a dora Colander akai.

A juye hadin Tsakin masarar a ciki se a rufe shi sosai a barshi ya turara.

A dinga dubawa duk Bayan minti goma ana Dada gauraya shi, sannan in ruwan tukunya ya kare a Dada wani.

Idan ya daho zeyi laushin Kuma Albasa zata dahu.

Za'a Iya cin wannan dambun hade da kuli-kuli, tumatir, Mangeda da yaji da maggi.

Ya zanyi in ba nida Colander?

Se a samu katuwar tukunya a zuba ruwa a ciki, a samu kwanon silver wanda ze Shiga cikin tukunya a zuba dambun a ciki a rufe.

Daman shi dambun tiriri steam ne ake so ya dafa shi Dan kada ya cabe.

--------------------

Vote, comment and share

Nagode

    people are reading<Special Dishes In Hausa>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click