《HASEENAH》PAGE 123&124
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story & written
By👇🏻
'''Aysher Abbakar ChuChu (Meerah)'''
® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
Follow me on Aysherabbakar
*123~124
Jin muryar baby na ihu ya Sanya su mummy fitowa da sauri, ganin baby sukayi tana kuka, "lafiya? Meye yafaru? "
"Haseenah ce"
Da gudu suka nufa d'akin ba tare da sun sake tanbayan ta ba.
Su umaimah da su saratu ke tsaye suna jijjigata ta, tsawa mummy ta daka musu ganin duk cikinsu babu me hankali a jikinshi Sannan tace" ku tashi ku bata waje ta sha iska"
Mik'ewa sukayi suka matsa, mummy ta d'auko robar ruwa ta watsa mata.
Wata salati haseenah ta sake lokaci d'aya ta saka kuka.
Kama hanunta mummy tayi tana matsawa.
Rungume mummy tayi tacigaba da kuka.
Shuru duka sukayi suna sauraron kukan ta. Mummy ko kasa janyeta tayi a jikinta, shafa bayan ta kawai take alamar rarrashi.
ba Wanda yayi yunk'urin bata hak'uri, saboda ita kad'ai tasan abunda take ji, shiyasa suka barta Tayi kukanta ko zataji sanyi a ranta.
Ganin its almost 11 gashi 12 akace za'a wuce ya Sanya mummy janyeta a hankali, sai faman ajiyan zuciya take.
Kama hanunta Tayi suka fita a dakin, kai tsaye dakinta ta wuce da ita, suka shiga toilet ta wanke fuskarta.
Tana fitowa suka shige bedroom ta kulle k'ofar, zaunar da ita Tayi a Bakin gado sanann itama ta zauna a gefen ta.
Rarrashin ta ta fara yi Sannan ta fara mata nasiha, wani kukan haseenah ta farayi mummy ma na tayata.
Mutuwar ummah ya dawo musu sabo.
Kasa cigaba da magana mummy Tayi sai kuka da dukan su sukeyi.
Mummy ce kawai ke furta " Allah ya isa mana, Allah ka saka mana ka bi wa er uwata hakkinta, ka gwada wa matar nan ishara ya Allah ka mayar mata da nufin ta, kayi maganinta ka Nuna mata ikonka ya Allah "
K'arar wayarta ne ya katseta Daga sambatun da take, ganin daddy ne ke kiranta ya Sanya ta d'agawa.
ji Tayi na fad'in" ki shirya su motoci suna hanya"
Kafin ta amsa ya kashe wayar.
Kallon haseenah Tayi tace" tashi ki shiga toilet ki sake wanka Kiyi sauri Karki bata lokaci ina jiranki"
Advertisement
Ba musu ta mik'e ta shige toilet.
Waya mummy ta d'auka ta kira sister ta wato mummy hajara ta sanar mata su shirya su umaimah da baby ynxu mota na hanya.
Cikin k'ank'anin lokaci aka fara shiryasu.
Mummy da kanta ta shirya haseenah Cikin voil lace orange colour da touches d'in bak'i a jiki.
Fesheta Tayi da turaruka masu kamshi.
Kallonta Tayi duk se tausayinta ya Kama ta.
Ganin tana shirin kuka ya sanya ta Kama hanunta suka fita.
Sanye take da flat d'in takalmi da mayafi black colour.
Side d'in daddy suka wuce nan tace a taho da su umaimah ma.
Yana zaune dama su yake jira.
Ba wani dogon jawabi ya musu ba, fad'a kawai yayi musu Sannan ya kira abban haseenah ma.
Jikin shi a sanyaye ya kasa magana ma, shuru yayi na tsawon wani lokaci Sannan ya daure yace" kuyi hak'uri Sannan ku kasance masu biyayya"
D'agowa yayi Sannan ya ce" kowacce ta tura mun da account number d'inta, Allah bada zaman lafiya"
Da haka bai sake cewa komai ba.
Sheshshekar kukan su kawai kakeji.
Lokacin masu d'aukan amare suka ISO.
Ciki kuwa Harda su haseen. Sunsha manyan kaya da alama Daga wajan d'aurin aure suka wuco shida abokan shi.
Nan mummy ta sa aka fara fitowa da akwatunan amare kowacce aka saka Cikin motar da za a dauketa.
Haseen se ware ido yake yaga ta inda haseenah zata fito.
Suna zaune palour haseenah na rik'e da Aaman.
Bayan an kammala Saka komai ne aka Sanya su fito da amare.
Hanun Aaman mummy ta Kama haseenah tak'i sake shi.
Duban ta mummy Tayi, ganin hawaye cike a idonta ne ya Sanya mummy fad'in" ki sakeshi ai shima ze rakaku"
Sake hanun shi Tayi Sannan suka mik'e.
Mummy tana tsakiyar su duka sun rik'eta, zuciyar mummy zafi yake, da akwai yanda zatayi to da itama kukan zata sanya.
Abun fa its not easy lokaci daya an raba ka da yara uku.
Suna kuka suna tafiya har suka isa Bakin motar.
Ganin zasu 6ata lokaci yq sanya daddy fitowa ya daka musu tsawa.
Ba shiri suka shige Cikin motar.
Daga musu hannu mummy Keyi lokaci d'aya hawaye ya zubo mata.
Ganin haka ya Sanya su fashewa da wani kukan.
Daddy ya dubi drivers yace" dan Allah ku shiga ku tafi"
Advertisement
Haka suna gani suka fice a gidan.
Da yake duka motor d'aya suka shiga sai aka rasa me lallasin wani, aunty Hajara dake gefensu ne ta fara basu baki.
Haka aka shiga abuja lokacin ana kiran magrib dan sun 6ata lokaci.
Gidan su Sameer aka wuce gaba d'aya.
Nan mummy da en uwa suka fara hidima da bak'i.
Amare ko d'akin da haseenah ta zauna aka wuce dasu.
Nan haseenah ta fara bin d'akin da kallo, ba abunda aka cnja sai share d'akin da akayi,
Sallah suka fara yi Sannan aka kawo musu abinci.
Su saratu se santin Abuja ake dan bata ta6a zuwa ba, haka friends d'inta ma.
Wanka sukayi suka sauya kaya.
Ammi ce ta lek'o tana musu Sannu da hanya.
Sannan tace" yakamata su kwanta su huta"
Tana fita wata mata ta shigo da alama er aiki ce.
D'auke take da babban Tray, sallama Tayi ta gaishe su sannan ta ajiye a gaban su.
Tana fita wata budurwa ta shigo da basket itama a hanunta ta ajiye ta fita.
Saratu ce ta tashi ta rufe k'ofar Sannan ta dawo ta zauna.
Itace ta bud'e warmers d'in, pepper soup d'in kaji ne a ciki, d'ayan kuma fried rice ne a ciki, se kuma salad bowl guda biyu, d'aya coslaw ne dayan kuma mixed fruits salad da aka jejjefa ice cubes yayi sanyi sossai.
Basket d'in kuma flask ne guda biyu d'aya Lipton d'aya kunun gyad'a, se plates da kuma mugs da spoons a ciki.
Ba 6ata lokaci suka fara ci, dukda basu dad'e da cin abinci ba Amma ba laifi sun d'an ci da yawa.
Suna gamawa kuma aka fara hira.
Haseen ne ya kira wayar haseenah harta katse bata picking ba.
Ya sake kira bata picking ba.
Text ya mata, da sauri ta bud'e.
"Nasan bakiyi bacci ba Cox I can feel it deep inside my heart, zamu had'u gobe u will explain in details"
Dariya kawai Tayi ta ajiye wayar.
Basu kwanta ba sai wajan 1.
Nan kowa bacci ya d'auketa.
Da sassafe suka tashi mummy Hajara ta kawo musu kayan su, bayan sunyi wanka aka shiryasu.
Dan kowacce gidanta za a wuce da ita kuma ranan yan kano zasu juya.
Bayan sunyi breakfast ne akace duka su fito.
Shiga motor sukayi wannan karon kowa motarta daban.
A jere suka fice a gidan.
Tafiya suke kan titi, dukansu gidajen su a maitama ne sedai akwai d'an tafiya sossai tsakanin su.
Gidan baby ne a farko sannan Umaimah, then haseenah at last.
Kowacce an wuce da ita, su saratu suna tare da haseenah.
Sai santin gidanta suke, dayake gidan duplex ne, kai tsaye sama suka wuce da ita.
Tsayawa maganar tsaruwar gidan 6ata lokaci, u guyx should just predict nd guess.
Basu wani jima ba seda suka bi gidan kowa suka gani suka mata sallama, gidan haseenah ne last, nan ma suka had'u suka mata sallama suka fito suka barta ita kad'ai kamar mayya.
Kowa ya watse so quit se kukan tsuntsaye kawai dake tashi.
Tsoro ne ya kama haseenah ganin ba kowa Gashi gidan ya mata girma.
Ringing d'in da wayarta taji ba k'aramar Razana ta yayi ba, dubawa tayi taga mummy ce.
Da sauri tayi picking tace" mummy na"
Se kuma tasa kuka" shshshshhhhhh" abunda mummy ta furta krnan sannan tace "meyafaru? "
"Mummy tsoro nakeji wlhy gidan yamun babba kuma am alone"
" be strong my girl, kefa ynxu babba ce, Karki damu u will b used to it soon, kuma ma ai haseen Yana zuwa so keep calm"
A hankali tace "to mummy"
Nan takashe wayar ta ajiye.
Sallama da motsi taji alamar bud'e k'ofa.
Duban agogo tayi its almost 5pm..
Da sauri ta tashi ta shiga toilet.
Alwala ta fara yi, jin k'arar ruwa a toilet ya Sanya haseen ajiye kayan hanunshi ya fita.
Tunanin shi wanka take.
Yana fita ta fito da sauri ta fara sallah.
Dawowa yayi yazauna bakin gado ya zuba mata ido Yana kallonta.
Jira yake ta idar amma tana yin sallama zata tashi ta cigaba.
Abun ya fara bashi dariya, aranshi yace to wannan sallan kwana nawa take biya oho...
Ganin its almost 6 ya Sanya shi shiga toilet ya watsa ruwa. Fitowa yayi d'aure da towel har lokacin sallah take.
Fita yayi ya Je ya sauya wasu kayan.
Yana dawowa aka kirashi a waya.
Yana dubawa yaga numban d'aya daga cikin friends din shine da suka yi school tare.
Picking yayi yace" Ahmad kun iso? Ok ganinan fitowa"
Duban haseenah yayi dake faman sallah yace" ki shirya my friends are here, kisamemu a palour kasa"
Yana gama fad'in haka ya fita dan shigowa dasu.
Am tired wlhy...
For comment 08144932303..
Advertisement
- In Serial109 Chapters
Alternate Dreams
People always go to sleep. Everyone everywhere and anywhere must sleep. Generally we welcome sleep as a time to rest and relax, but what if that changes?. This is a story about 4 young adults whom dont remember how they got together in a supernatural cavern after falling asleep in their homes. Follow them as they hope to emerge from their unexpected circumstances while wondering what could have possiblly taken them there. *Authors Note: Feel free to give me pointers, this is my first time trying to write and I'm doing it in hopes that practice indeed does make make perfect. If your going to say bad things about it please say it in a constructive and professional manner. I'll try to get a chapter out every week around Friday-Saturday.
8 164 - In Serial11 Chapters
Intercessor
"In my defense, I hadn't actually been trying to get hit by a truck." Artemis wakes up alone in a giant futuristic facility with no hint of where she is, how she got here, or what this means. Yet within two weeks, she is shot at with all the guns, a voice is beginning to speak in her head, and she is tormented by a seemingly sentient and possibly trollish space Roomba. Her only hope is Scarlet, another girl who is a complete stranger and almost shot her in the head. Oh, and she has fox ears and a tail. That is possibly worth mentioning. Artemis is not a nerd. She has never heard of the isekai genre, she can't fight worth a damn, and the blue-collar skills she learned at her community college are absolutely useless in a universe where technology is often indistinguishable from magic. She only has one thing going for her: A mysterious ability to interface with highly advanced technology left behind by the Antecessors, the long lost precursor civilization with technology that no one has been able to adequately replicate. Finding herself in a universe where civilizations are locked in an interstellar Cold War, where societies are so stratified that the aristocracy commands fleets of starships while slaves wash clothes with their hands, Artemis decides to run away from it all. She has a ship. She'll find a crew. She'll find a way to make a living at the fringes of civilization, learn how to cope with danger, and survive the affections of a universe where everyone is a cute girl with animal ears and tails. Welcome to Intercessor. AKA Kemonomimi Yuri Space Fantasy. Commissioned by Shaderic. Please leave your sense of shame at the door.
8 123 - In Serial63 Chapters
The Day We Met Was The Day I Fell For You ♥Tom Felton♥
Cassie had her normal life flipped upside down one day at a theme park where her and her two friends ran into three Harry Potter Stars: Daniel Radcliffe, Rupert Grint, and Tom Felton. They end up spending the day together, and Cassie ends up having her life changed forever.
8 144 - In Serial83 Chapters
FYATT & B. FR (Z.M.)
Book 1 - Fuck You All The Time (FYATT) Book 2 - Babydoll. Fuck Reality (B. FR) Abu sezonai vienoje vietoje!
8 179 - In Serial47 Chapters
New Earth: Arrow
My name is Oliver Queen. After giving my life to create a new multiverse, I was given a second chance, not only at life, but to correct my mistakes and save those I lost before. I am the Paragon of life and the spectre, but most importantly, I am once again, the Green Arrow. Lauriver pairing. part one of New Earth saga.
8 196 - In Serial134 Chapters
❥Dreaming In Pictures - A Varia IG Story | Book 1
•We take photos as a return ticket to a moment otherwise gone. Follow Alia and Varun's journey as best friends to lovers to a married couple and more.Explore their friendships and love through pictures.Varun Dhawan Alia Bhatt
8 108

