《HASEENAH》PAGE 117&118
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story & written
By👇🏻
'''Aysher Abbakar ChuChu (Meerah)'''
® *Real Pure Moment of Life Writers* *P.M.L*💭💭💭
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
Follow me on Aysherabbakar
*117~118*
Tsawon minti uku babu wanda ya fito a motar kuma ba a kashe motar ba har lokacin tana diri.
Haseenah zuba ma motar ido tayi dan ta gane sarai saratu ce a ciki, ganin basuda niyar fitowa ya sanya kowa ya cigaba da hidimar gaban shi.
Saratu kuwa ita ke mazaunin driver da wasu friends d'inta su hudu a ciki, dukda motar tinted ne amma suna kallon kowa.
'Daya daga cikin friends d'inne ta dubi saratu tace"kai gaskiya wajan nan ya had'u, kiga amaren fa, wacece sister taki a ciki? "
Nuna haseenah tayi sannan tace" wancan farar me d'an jikin nan"
Duka suka had'a baki tare da fad'in "wow she's cute"
Tsuka saratu tayi tace" da Allah ku zo mu k'arasa wajan muma a mana zanen kafin mutane su cika"
Ba musu suka fito a tare, sanye suke da wasu matsatsun gown wanda aka d'inka musu na material.
Ba laifi sunyi kyau, kowacce tana rataye da k'aramar mayafi da little teddy bags a kafad'ar su.
Kai tsaye wajan haseenah suka nufa suka gaisa, zama saratu tayi a gefen haseenah tace" sis wacece zata mana zanen nida friends d'ina"?
Nuna wata me zanen flower tayi da lokacin kenan ta k'araso tace tazo ta zana musu.
Nan ta fara musu cikin k'ank'anin lokaci aka gama musu.
Su haseenah ko sun sha lalle dan ba k'aramin kyau sukayi ba kasancewar su duka farare ne kuma gashi sun sha gyara.
Sisters d'in mummy ne suka bazama cikin fili aka fara chashewa.
Nan su saratu suka mik'e suka shiga fili suka fara takawa.
Kowa kallon su yake ganin irin rawar da sukeyi.
Photographer haseen ya turo na musamman yace a haska mishi amaryarshi tun daga pictures har video coverage.
Bayan an gama musu lallen ne mummy ta kirasu suka sake wanke aka sake shiryasu cikin wasu materials pink nd white colour dukan su.
Nan amare suka shigo suma dan takawa, liki mummy take musu ita da friends d'inta da suka zagaye su.
Abun gwanin sha'awa.
Har yamma ana abu d'aya, anci an sha an kuma cashe.
Dab magrib aka watse kowa ta fara shirin tafiya gida.
Su saratu kam tana nan har wajan isha ita da friends d'inta sun baje a palour su haseenah ana hira.
Tare suka ci abinci aka zauna ana hira.
K'arfe tara me gyara amare ta iso, dan haka mumjy ta shigo tace su fito su nufa d'akin ana jiran su.
Har ta juya zata fita ta dubi saratu tace" me kikeyi har yanzu baki tafi ba? Ga dare nayi kuma haka zakiyi driving d'in dare? "
Tura baki saratu tayi tace" mummy anan zamu kwana"
Zaro ido mummy tayi tace" kinzo ta shirin kwana ne? "
Advertisement
Girgiza kai Saratu tayi.
Mummy ta cigaba da cewa" to ki tashi ku tafi, gobe seki zo da kayanki bazan hanaku kwana ba, kinsan ni in kikace zaki mun shashan ci bazamu shirya ba kinsan halina ai"
Mik'ewa saratu tayi sanann tace" to mummy goben zamu zo in Allah ya yarda bari mu tafi"
Jakar su suka d'auka suka kama hanya suka yi sallama d haseenah, har wajan mota suka rakasu seda suka fice a gidan sanann suka juya suma.
Umaimah ce ta dubi haseenah tace" aunty wallahi saratun nan ta bani tausayi, ki ganta kamar nitsatsiya wallahi"
Shuru haseenah tayi sannan tace" duk mummy ce ta 6ata ta wlhy ita take daure mata gindi take rashin ji amma ai yarinyar bata da wata lefi in kika fahimce ta"
"Hakane but a rink'a mata fad'a ko Allah ze sa ta nutsu" inji baby.
In shaa Allah i will " exclaims haseenah "
Haka suka shiga suna jimamin rayuwar da Saratu ke yi cike da tausaya wa, duk a tunanin ta ita ta waye kenan.
Washe gari misalin k'arfe 10 saratu ta iso ita da friends d'inta dukan su d'auke da jakan kayan su.
Mumny ce ta nuna musu d'akin da ke jere da na su haseenah tace anan zasu sauka, sannn ta ba ma saratu key d'in d'akin.
Ajiye kayan su sukayi a ciki sannan suka rufe suka nufa wajan amare.
Zaune suka samesu suna karyawa, suma zama sukayi haseenag ta tura wata yarinya ta kar6o musu breakfast a kitchen.
Nan suma suka karya.
Wanka suka shiga suka fito kasancewar yau za'ayi arabian night.
Dogayen riga kawai suka zira da manyan hijabai har kasa dukan su ukun, haseenah ce ta d'au key d'in motar ta sannan ta dubi su Saratu tace" zamu wuce saloon ne mu ya kenan? "
Duban friends d'inta tayi sannn ta dubi haseenah tace" to sis yau meye colour of d day? "
Shuru haseenah tayi sannan tace" kawai de Arabian gown ne, it may b if any colour ba a specifyng ba, but majority dai black colour sukace zasu saka maza kuma farin caftan or jallabiya"
Ok then" muma dai munaso muje saloon d'in daga nan kuma zamu vi mu siya gown d'in cox bamu da shi " saratu tace"
Shuru haseenah tayi sannan tace" to shikenan muje, but bazaki bini da wannan kayan jikin naki ba sedai ki saka hijab"
Tura baki saratu tayi badan taso ba tace" to ki bani naki mu saka"
Ba musu haseenah ta ciro musu hijab dukan su Ta mik'a musu.
A tare suka fita, wajan mummy suka nufa nan ta basu isheshshen kud'in da ze musu, kallon saratu tayi da ta sha hijab har k'asa sannan tace" da haka kike shigar ki saratu da kin more".
Murmushi saratu tayi sanan tace" to mummy zan na sakawa"
"Allah sa"
Dariya sukayi sannan suka amsa da amin.
Kai tsaye wajan saloon suka nufa, Saratu dayake da motar mummyn ta fa fito su boutique suka wuce dan siyan kayan su.
Advertisement
Lokacin aka fara shafa musu relaxer da su pedicure da yake duka anayi a wajan, kuma suna da ma aikata da yawa awajan.
Saratu ma dawowa wajan sukayi suka ciro kayan kowa ta gwada nata sannan suka mayar leda aka fara musu.
Da yake babu gashin arziki seda aka wa su saratu k'ari da attach.
Haseenah ko an gyara gashin an musu styling, kai kace suma sakawa sukayi barin ma haseenah dukan su santin gashin suke.
Basu suka gama ba se bayan la'asar, haseenah ce ta biya musu duka bills d'in sannan suka fito dan dawowa gida.
D'aya daga cikin friends d'in saratu wato khadija wanda suke kiranta da *Dee* ta dubi saratu tace" gaskiya yayarki tanada kirki wallahi"
Murmushi kawai saratu tayi, dan ita ma se yanzu ta gane hakan, kuma take dana sanin irin zaman da sukayi da haseenah, gashi yanzu its too late tunda basu zama tare, she wish sunyi rayuwa n fahimta fa ita da taji dad'i, tsuka tayi a ranta tace " mummy kin cuceni"
A tard suka isa gida, d'aki suka wuce, toilet suka shiga suka d'auro alwala dan yin sallan la'asar.
Suna idarwa abinci aka kawomusu suka ci.
Mummy ce ga shigo ta dubesu sannan ta dubi agogo, k'arfe biyar da rabi.
Kallon su tayi tace" ku tashi ku shiga wanka da Allah kunsan me makeup tazo kuma ga shegen 6ata lokaci a makeup kaman za a canja muku kamanni.
Baby ce ta fara tashi ta shiga sannan mummy ta fice.
Haseenah ce ta dubesu tace" kuma kuje kuyi wankan mana a muku ko banda ku ne? "
Tashi sukayi suka nufa d'aya d'akin dan yin wanka.
Baby na fitowa ta xauna aka fara mata makeup d'in, kowa da wanda ze mata gudun kar a 6ata lokaci.
Se after magrib aka gama musu lokacin har an fara tafiya wajan event d'in.
Haseen ko se faman kiran haseenah yake wai gasunan zuwa d'aukan su.
Shiryasu duka akayi cikin arabian white gowns wanda yasha ado da stones black colour, yane kansu akayi da k'ana nan mayafin sukuma black colour, ta baya aka warware gashin ya zuba ta baya, chains na k'afa da bangles da chain na hanu duka na gold aka sanya musu da zobuna dukan su.
Tsayawa fad'an kyan da amaren sukayi 6ata lokaci ne, au saratu ma an fito an sha dogayen riguna bak'ake tun kafin su fita aka fara selfie.
Turaren da aka had'a musu na musamman daga sudan aka feshe su, ka d'auko na gaushi ma aka turare su dashi.
Lokacin motocin daukan amare sun iso.
Dan haka sisters d'in mummy su uku sukazo suka musu rakiya zuwa bakin motar.
Saratu ma motar ta suka shiga suka rufa ma su haseenah baya.
Mummy ma ita da friends d'inta lipaya suka saka dukan su pink colour ba k'aramin kyau sukayi ba.
Waje ya cika da jama'a 'yan uwa da abokan arziki duka daga family uku na angwaye.
Red carpet aka shimfid'a wanda ya sha farare da jajayen roses na flower da aka watsa.
Kid'an larabawa kawai ke tashi.
Lokacin da su haseenah suka iso haseen ji yake kaman ya fito a motar ga iso wajan ta.
Nan aka sanar da isowar amare.
Friends d'insu suka k'araso wanda suka sha dogayen riguna duka bkack colour.
Lokacin da akace amare da angwaye su k'araso su haseen ma suka fito.
Wajan motar su haseenah ya nufa ya bud'e, zuba mata ido yayi ita kuma ta sunkuyar da kai.
Hannu ya mik'a ya kama hanunta ta fito a hankali.
Haka sauran ma suka fito kowa ya tsaya gefen amaryar shi.
Kamshin dake tashi a jikin su duk shi yafi gigita su, kasa daurewa haseen yayi a hankali yace" precious ko dai zamu wuce gidanmu ne? "
Da sauri ta dube shi ta zabga mishi harara, dariya yayi yace" to ai ni wanann kamshin wallahi ya hanani sakat ne kawai daurewa nake"
Murmushi kawai tayi batace komai ba.
Nan aka umurcesu su wuce ciki.
Ahankali suke takawa, haseen na rik'e da nanun haseenah.
Photographers kuwa da masu video se haska su suke.
Ba k'aramin kyau da dacewa sukayi ba.
Nan ko DJ ya sake musu kid'a.
Mummyvda tawagar ta suka taso tun daga bakin k'ofa aka fara musu ruwan naira.
Su saratu kuwa da yake suna cikin tawagar amare nan akayi layi aka rufa ma amare baya ana chashewa.
Seda suka rakasu har inda aka tanadar wa amare da angwayen sanann suma suka zauna daga gefe.
Nan aka fara program fa, waje yayi waje ango da amare suna fili su kad'ai, yayin da MC yace yau yanason yaga irin soyayyar da angwaye suke wa amare ta hanyar musu ruwan naira.
Aiko ranan anga gata.
Sameer da Mahmud bandir d'in 500 aka 6alle, ganin haka ya sanya Haseen balle 1k ganin haka ya sanya wajan ihu da tafi.
Saratu ko lokaci d'aya taji jikinta yayi sanyi, wato fa fitsara da iskanci da rashin kunya baya kawo miji, da yana kawowa to da ta dad'e da samun nata.
Nan fa dangi suka shigo suka ana fafatawa, se abn ya koma kaman gasa, mum haseen ko ba a magana, saratu ma ba a barta abaya ba ita da friends d'inta sun lik'a kud'i sossai, ganin yanda jama a suka zagaye su ya sanya idon haseenah cikowa da hawaye, lokaci d'aya ta tuna da Umman ta, da yanzu tare ake wanan hidimar da ita.
Hawaye ya fara zubo mata, ji tayi haseen ya dad'a rik'e hanunta sossai, duban shi tayi da jik'akk'un idon ta, girgiza mata kai kawai yakeyi, murmushi tayi ta amsa tissue ta goge hawayen ta.
Duk se jikin su yayi sanyi.
Anci an sha an kuma yi hidima, an d'auka hotuna sossai, ba a tashi ba se wajan k'arfe 11 na dare.
Haseen da kanshi ya mayar dasu gida, su saratu ma suka rufa musu baya.
D'aki suka wuce suka zauna suka cire kayan jikin su.
Kowaa gajiye yake barin haseenah da duk jikinta yayi sanyi.
Wabka kawai sukayi kowa ya nema wajan kwanciya.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial29 Chapters
Verbundener Geist
Yolthem. To be born here is a curse for some and a blessing for others.The Eldritch create havoc, “blessing†some with their power and driving others to utter madness. Spirits give people the ethereal power of Arcane, a force that no mortal can naturally wield that defies all laws of the universe. Blood and those that devour or revel in it reign supreme during the night and bide their time during the day. Mortals cower and pray to beings they do not understand for salvation that will not come while those of the cloth fight to protect them. None of this concerned our protagonist until their souls was bound to another against their will. Now they have two options.Help or hinder.Tags subject to change.**Once we get going past the set up expect very detailed description (of everything) and topics that may make you very uncomfortable. This may include but is not limited to: Religious fanaticism, extreme violence and gore, morally disgusting actions (torture, abuse, etc.) and more. You have been warned.**
8 105 - In Serial63 Chapters
Mana-Script
When a holographic diary is found in a ruined building, the story of one of the greatest groups to ever live unfolds; the highs and lows, the hookups and heartbreaks, the comedies and tragedies. Mana-Script is the story of friends moving through life and living in a fantastical world. I am hoping to update this whenever I can, usually about 3 times a week.
8 93 - In Serial9 Chapters
Yggdrasil Story
Six-years-war has ended, by the strength of only one man. Everyone calls him "Swordmaster". Unfortunately, this is not the story of such time of glory, bloodshed and.....Ruby, interrupting: Sola, why don't you just tell them that this is the story of a man in a harem full of beautiful flower girls.Almond: Could you not disturb her? This is the most important part of our story, and it could decide the future of us all.Ruby: And I want to ask you why the novel cover doesn't have me on it? Since I'm the main heroine and all.Sola: I am so fed up with pen tool.. uh... better not talk about it. So, we used a photo of flowers instead, and I think you are not the main heroine.Almond: It's a budget cost too. Those artists charge us over US$200. We are broke. Plain and simple.Ruby: That's really expensive, huh.Sola: Could you girls stop talking? So, I can continue with the synopsis....Ruby: I don't understand why this is so important.Sola: Ruby, listen. If we don't have a good synopsis, people will not buy our book, and then.....Iris: Then what? I want to know it too.Sola: Then there will be no book 2.Iris: No book 2, so what? Why should I care?Sola: Our universe will collapse, and we will disappear forever..Iris: What did you say?Almond: Well, too late now. You talked too much. We have run out of writing space...Ruby: What!!!!!NO!!! I don't want to DIE!!!!You do something sis!!! I should have done that human thing with our lord when I still had a chance. Noooooooo......Iris: Buy it now. People!! Yes, I mean, you!! YES! YOU!!! BUUUUUUUUUYYYYYYYYYY....Iris is shouting as loud as if this is the last moment of her life, but no one listens.
8 148 - In Serial3 Chapters
Soul Manifestation
The Soul Manifestation is an exclusive program that helps you to find the secrets of attaining thetruly fulfilling romantic relationship with your soulmate and to improve your ability to attract your soulmate. ... Attract your soulmate. Get rid of your health challenges. Reveal ideal career. Enjoy beneficial gifts.
8 116 - In Serial11 Chapters
The Next Saturday - John Bender
John Bender still has several Saturday detentions left to serve. Last Saturday's group is moving on with their lives. Bender is bored out of his mind until a pretty face walks in.Well, well. Who do we have here?#1 in #johnbender as of 7/3/2021#1 in #thebreakfastclub as of 1/23/2022
8 151 - In Serial33 Chapters
My Boyfriend's Best Friend
Alexis Reed, a certified good girl. Her parents died when she was sixteen years old and so, making her boyfriend, Carson Matthews, stay with her. Meaning, they live together. Besides that, everything has become beyond perfect. She isn't that popular nor beautiful so to score the heart of the heart throb in school is something. One day, Carson was said to leave the country because of his sick grandmother abroad. Leaving Alexis under his best friend, Darren Christopher's care. Alexis is aware of Carson's friends to be like him. A kind, handsome gentleman who treats girls with respect. Even if she doesn't talk to his friends, she thinks they are the same with him. So what will happen if Darren stays in Alexis house? Is he the guy Alexis thinks he is?
8 106

