《HASEENAH》PAGE 103&104
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*103~104*
Sunkuyar da kai Sameer yayi ya kasa magana se ajiyar zuciya kawai yake.
Seda daddy yace ya kwantar da hankalin shi ya fad'a mishi abinda ya faru.
Cikin mutuwar jiki da sanyin murya ya ba daddy labari tun dalilin had'uwar su da haseenah har kawo matsalar da aka samu da kuma dalilin barin ta gidan.
Shuru daddy yayi zufa na karyo mishi.
Mik'ewa yayi ya shiga ciki ya ce duka su samesu a palour.
Umaimah da ke tsaye bakin k'ofa tana bubbugawa akan haseenah ta bud'e mata k'ofa amma tak'i.
Kallon daddy Umaimah tayi kaman zatayi kuka tace" daddy kazo ka mata magana ko zata ji naka ta bud'e"
Mummy dake cikin d'aki batasan me yake faruwa ba ta fito tana tanbayan lafiya?
K'arasa wa k'ofar yayi a hankali yace" haseenah tashi ki bud'e kofar inason magana dake"
A hankali ta mik'e ta bud'e k'ofar ta sunkuyar da kai tana sharar hawaye.
Mummy ce ta dubeta ganin fuskanta yayi ja idonta sun kumbura tace" me ya sameki haseenah? Bakida Lafiya ne?"
Girgiza kai kawai tayi alamar a'a.
Dady bai sake cewa komai ba yace duk su sameshi a palour shi yanason magana da su.
Juyawa yayi ya tafi.
Hijabi haseenah ta saka sannan duka suka bi bayan shi.
Zaune ya ga sameer kanshi a k'asa.
Dukan su zama sukayi banda haseenah da ta takure waje d'aya kamar mara gaskiya.
Daddy ne ya dubi haseenah sannan ya kira sunanta.
Cikin dashashshiyar murya ta amsa, a karo na biyu daddy ya ce" ki d'ago ki kalleni"
À hankali ta d'ago tana duban shi.
Nuna mata sameer yayi yace" kinsan wanann?"
Gyad'a mishi kai tayi .
Girgiza kai daddy yayi sannan yace" sameer inaso ka basu labarin da ka bani"
Advertisement
Cikin sanyin murya ya fad'a musu komai.
Mamaki da tashin hankali ne kap ya bayyana fuskar su.
Daddy ya cigaba da cewa" Sameer ko kasan auran haseenah saura kwana 28?"
A gigice ya d'ago ya dubeta sannan ya mayar da kallon shi ga daddyn, bakin shi har rawa yake ya kasa magana sai hawaye.
Shuru palour ya d'auka banda sheshshekar kukan haseenah ba abinda kake ji a palour.
Ita kanta ga rasa kukan me take yi.
Shuru palour yayi daga bisani daddy ya yi faɗa ma haseenah kan meyasa ta b'oye musu gaskiya.
Hak'uri daddy yayi ta ba ma Sameer saboda sunyi halacci wa haseenah.
Nazari daddy yake sosai daga bisani yace" In bazaka damu ba zan baka 'yata ka aura in kanada ra'ayi"
Daddy ya k'arasa maganar tare da nuna Umaimah.
Duban Umaimah sameer yayi itama ma shi take kallo.
Sunkuyar da kai tayi k'asa saboda tun da ta d'aura idonta kanshi taji ya mata dama gata da son kyawawa.
Daddy ne ya katse musu shurun ya cigaba da cewa" bazan maka dole ba, kaje gida kayi nazari da tunani in ka yarda kuma kun sasanta kanku zan haɗa auran da na haseenah in har a shirye kake.
A hankali Sameer ya gyad'a Kai sannan yace" ba komai daddy na gode Allah ya saka da Alkhairi, In Shaa Allah zuwa Jibi zan dawo"
Allah kaimu daddy yace sannan sameer ya mik'e jiki ba k'wari ya fice.
Da k'yar ya iya ya ja motar ya isa gida saboda sarawan da kanshi keyi.
Ga wayar shi se faman ringing take, duba fuskar wayar yayi yaga Ammi ce ke kira.
Kasa d'auka yayi, a haka ya isa gida.
Yana shiga ya fad'a kan gado ya dafe kanshi.
Wayarshi ce ta cigaba da ringing, yasan Ammi ce, da k'yar ya d'au wayar ya kara a kunnen shi, a hankali ya ce" ina wuni Ammi"
Jin shi wani iri ya sata fara jero mishi tambayoyi, " son me yake faruwa ne? U sounds somehow baka da lafiya ne?"
Advertisement
Girgiza kai yayi sannan yace" Ammi na rasa haseenah, Ammi haseenah Auré zatayi, Ammi ya zanyi da rayuwa ta? Ya zanyi da son haseenah cikin zuciya ta?"
Kuka ya fara yi kaman k'aramin yaro, hankalin Ammi a tashe ta ke bashi baki nan ta shaida mishi gobe zasu taho Kano.
Washegari Ammi da Mahmud suka biyo jirgin k'arfe 9 na safe, ba 6ata lokaci suka iso gidan.
Kwance yake kan kujera sanye da jallabiya fara, fuskan shi na kallon ceiling, maganganun daddy kawai ke mishi yawo, ga kuma fuskar Umaimah da ke gani duk da yana cikin tashin hankali amma ya ga tana da kyau sossai.
Shafa kanshi yayi had'e da furzar da iska me zafi.
Shigowan Ammi da Mahmud ya sanya shi tashi ya zauna, zama Ammi tayi gefen shi ta dafa shi sannan tace" son kayi hak'uri komai me wucewa ne, duk abinda kaga baka samu ba dama can ba rabon ka bane"
Nan ta cigaba da mishi nasiha, ko ba komai hankalin shi ya kwanta, kuma zuciyar shi ta amince mishi da Umaimah.
Nan ya sanar da Ammi yanda sukayi da daddy, sossai taji dad'i sanann tace" to son kai ya kace musu"
"Ammi nace gobe zan dawo duk yanda ake ciki zan sanar mishi"
Dariya tayi sannan tace" ai ko tare zamuje nima inason ganin haseenah"
Haseenah ko na can duk damuwa ta ishe ta , bata cika magana sossai ba se In ya zama dole, mummy ce tayi ta bata baki sannan ta d'an sake.
Washegari da safe k'arfe 10am Ammi suka iso, me gadi ne ya shiga yace ana sallama da daddy.
Fitowa daddy yayi, ganin Sameer ya Sanya shi murmushi, fitowa a motar Sameer yayi ya gaida daddy sanann ya sanar dashi tare da momyn shi suke.
Nan yace su shigo ciki.
A palour Ammi Dukan su suka zauna, nan ya shiga ya sanar da mummy zuwan su.
Nan aka kawo musu drinks da snacks aka ajiye musu.
Mahmud ko se baza ido yake yana jiran ganin ta inda haseenah zata fito.
Daddy ne ya Sanya aka kira mishi haseenah da bby da Umaimah.
Ba 6ata lokaci suka iso, k'ura mata ido Mahmud yayi.
Gaban Ammi ta k'arasa ta zube tana gaida ta
Girgiza kai Ammi tayi sannan tace" bazan amsa ba haseenah, dan baki kyauta ba"
Hawayen da bata so ya fito ne ya k'arasa gangaro wa.
Cikin rawar murya tace" dan Allah Ammi ki yafeni bazan saké ba"
Janyota Ammi tayi ta rungume ta tana buga bayan ta.
Seda tayi shuru sannan Ammi ta d'ago ta ta zaunar da ita gefen ta.
Gyaran murya daddy yayi sannan yayi bayani wa Ammi yanda sukayi da Sameer.
Murmushi Ammi tayi sannan tace" ya fad'amun kuma mun amince da wannan halacci Allah bar zumunci"
Duka suka amsa da Ameen.
Ammi ce tace " to wacece surukar tawa a ciki?
Nuna Umaimah dady yayi da ta sunkuyar da kai...
" Masha Allah taho kusa dani 'yata"
À kunyace Umaimah ta k'arasa ta zauna gaban Ammi.
Shafa kanta Ammi tayi sannan tace" Allah muku albarka"
Nan daddy Yake tanbayar su ko sun shirya a had'a auran su da na haseenah?
Gyad'a kai Ammi tayi tace ba wani damuwa, gobe zan koma Abuja in Allah ya yarda zamu kawo komai nan da sati d'aya".
Mahmud da ke satan kallon baby ya dubi daddy kaman zeyi kuka yace" Daddy Nima a bani wancan"
Ya nuna Baby.
Dariya duka suka sa sannan daddy tace" in dai kun daidaita kanku shikenan"
Duban Baby Mahmud yayi sannan yace" dan Allah ki soni kinji?"
Dariya duka suka sake yi, duban Baby daddy yayi yace" uwata kina son shi?"
Sunkuyar da kai tayi cike da kunya.
To Alhamdulillah Allah sa mu dace.
Nan suka cigaba da tattaunawa, daddy ne ya dubi Ammi da mummy sannan yace" to ku tashi mu shiga ciki mu barsu su zanta.
Ba musu suka mik'e palourn ya rage daga haseenah, Sameer, baby, Mahmud da kuma Umaimah.
Tsumul Mahmud ya mik'e ya zauna gefen baby ya dubeta sannan yace".....
For Comments 08144932303
Advertisement
- In Serial49 Chapters
Spire Dweller
The 1st floor of the World Spire has been humanity’s home for as long as anyone can remember. With cities and towns scattered across several million square miles, most residents live out their years within protective walls. Simultaneously guarded and oppressed by powerful cultivators—people who can utilize qi to perform superhuman feats—the average citizen learns early on to both respect and fear those that keep the deadly Spirit Beasts away. When Samantha receives a quest notification to become a cultivator herself, she goes against her family’s wishes and leaves the relative safety of her town to complete it. She knows that becoming a cultivator will change her life, but she has no idea how much the journey will cost her.
8 207 - In Serial15 Chapters
Story of a Killer
Damon Jaeger had always known he was different. Yeah, he was more talented than others his age and even older. Yeah, he could learn things and remember them after a few glances. But he knew he was even more different. He was a Killer. He wanted to hurt people. Or at least he wanted to. Damon finally let loose and hurt a group of people who he felt deserved it. And because of that, an Organization found out about his knack for violence and killing, and they wanted to recruit him. Join Damon as he gets trained to become a Killer and tries to stay himself along the arduous journey. (Author Note: Grammar may or may not be quite shit, so please go easy on me. Also, the story may come across as edgy, so sorry about that. Oh and I don't own the cover photo either, I picked it up off of Google~)
8 262 - In Serial51 Chapters
Origin Of The Forsaken
Randomly selected by the system Darius is sent to another world to learn and grow stronger to prepare his world for the coming threat. Chapters will generally be released Monday, Wednesday, and Friday. (This is my first attempt at writing, criticism and suggestions are encouraged.)
8 128 - In Serial6 Chapters
His Royal Ballerina. (completed)
A magical tale between a ballerina who comes across a prince who can't feel pain. she gets involved in a dangerous quest which will change an ordinary ballerina's life.will she get back what was lost? or lose herself in this enchanting story of a prince and his royal ballerina. Read the Review done by@angellover36 http://read-a-holic-reviews.blogspot.com/2012/08/review-his-royal-ballerina-by-sanayakant.html
8 159 - In Serial114 Chapters
Forbidden Love || Anakin x Reader
Y/n Amidala was only known as Padme's little sister until she met Anakin Skywalker. Her whole life was changed upside as she found herself in love with Jedi. This isn't a regular love story, no. Y/n Amidala had so much power in the force; she became one herself. Their love was forbidden amongst the Jedi Order. Throughout the story, both lovers go through the most challenging levels of their love. Defeated by the dark side one will go through, but who? ✧・゚: *✧・゚:* *:・゚✧*:・゚✧"Have faith my love." Anakin says. he placed his hand on my cheek and caressed it. Panic filled the city, in the far distance was the temple burning into flames. I sensed fear and hatred in him. I trusted him. I knew him. I know what his intentions are.. or so I thought.----DISCLAIMER: I do not own of any Lucas Film Disney or anything related to Star Wars. I do now own any of the iconic characters except for my own characters that I have created. ---
8 918 - In Serial65 Chapters
Jack Dylan Grazer Imagines
Freddie F.Fraser W. Eddie K.Jack G.
8 87

