《HASEENAH》PAGE 101&102
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*101~102*
Jallabiya ya Sanya sannan ya d'au Key ya fice, agogon hanunshi ya kalla k'arfe 12:30 na dare, bai damu da lokaci ba, motar shi ya shige yayi horn me gadi Ya bud'e sannan ya fita aguje.
Zaga Garin kawai yake ba tare da yasan inda ya nufa ba, har wajan k'arfe 2 yana abu d'aya, ganin wajan shiru a dole ya juya ya dawo gida zuciyar shi cike da tunani.
Ji yayi cikin shi na murd'awa sai a lokacin ta tuna da tun breakfast har ynxu ba abinda yaci.
Kitchen ya shiga ya dafa Lipton sannan ya fito yana sha a hankali ba don yana jin dad'i ba.
Haka ya zaune har aka kira sallan asuba.
Alwala yayi ya fice zuwa Masallaci.
Seda gari ya fara wayewa sannan ya mik'e ya dawo gida yayi wanka sannan ya fita.
Ya rasa ya inda ze fara, duk wanda ya gani sai ya tare ya nuna mishi hoton haseenah amma baiyi sa'an sanin wanda ya santa ba.
Sallah ne kawai ke tsayar dashi yana yi kuwa zai ci gaba da yawo.
Da yamma mummy zuwaira ta Sanya haseenah suka tattaro kayan su suka fice a gidan, lokacin kuwa mummy ta fantama gari nema wa saratu maganin Sa'a akan haseen da kuma lalata auren haseenah.
Sai magrib ta dawo duk ta gaji, gashi gidan taji shuru babu su haseenah babu saratu ta fice yawo.
Tsuka ta ja sannan tace " an fita yawon iskanci kenan"
Sai bayan isha saratu ta dawo, mummy kuwa na zaman jiran dawowar haseenah,
Har wajan 10 ganin basu dawo ba ya sanya mum fita wajan idi me gadi.
Tanbayarshi take ko yasan inda haseenah ta tafi?
Girgiza mata kai yayi alamar a'a sannan yace" na dai ganta sun saka akwatina a mota sun fice dukan su ko tafiya sukayi oho"
Hankalin mummy ba k'aramin tashi yayi ba jin ya ambaci tafiya.
Da sauri ta juya ta shige cikin gida tun daga k'ofa ta fara k'walla ma saratu kira.
Da gudu ta fito a tunanin ta wani abun ne ya faru, ganin mum tsaye ya sanya ta cewa" haba mummy wlhy har kin razanani"
" Razana na gaba kuwa dan ubanki, Ni na fice naje can ina fad'i tashi dan ganin na mallaka miki abinda kike so kekuma kin k'ule d'aki hankalin ki kwance ko?'
Tura baki tayi sannan tace" to gani nan ai"
Duka mummy ta kai ma bakin saratu sannan tace" to dan ubanki haseenah bata gidan nan, idi yace min ya gansu da manyan akwatina sun fice basu gidan Dukansu.
Advertisement
Yamutsa fuska saratu tayi sanann tace" to Ni mummy meye damuwata da barin gidan, ai abun farin ciki ne"
Shuru mummy tayi maganganun saratu na k'ona mata zuciya sannan tace" ohhhh kin manta yau saura kwana 28 auren ta da haseen?"
Zabura saratu tayi ta dubi mum tace" yaushe aka saka ranan auren mummy?..
" Ban sani ba"
Tana fad'in haka ta juya ta bar saratu zaune a k'asa.
Kuka saratu ta saka tana birgima wai bazata yarda ba se ta kashe su duka...
Haushi da ya dad'a Kama mummy daga cikin d'aki tace" wlhy In baki tashi kin fice mun ba sena karya ki, banza shashasha kawai"
Kuka saratu take tana cewa mummy ta temake ta Amma ko kallon ta mummy Bata yiba.
Tashi saratu tayi ta shige d'aki, jakarta ta bud'e ta ciro kwalin sigarin ta da lighter ta shige toilet.
Zama tayi kan toilet ta kunna ta fara busawa, yana k'arewa zata sake kunna wani.
Seda ta sha kwali d'aya sannan ta hak'ura, gaba d'aya wajan ya d'au hayak'i ba abinda kake gani.
Ji tayi kanta na juyawa da k'yar take iya bud'e idon ta, tashi tayi ta wuce bedroom d'inta ta zube kan gado had'e da dafe kai.
Bata san lokacin da bacci ya d'auke ta ba ba sallah ba salati.
Washe gari da yamma su haseenah suka shirya suka fice a motar ta ita da su baby, Umaimah da Aaman.
Dukan su dogayen riguna suka sanya amma kowa da colour nashi, haseenah dake sanye da bak'i ta rolling gyale ta Sanya glasses a fuskanta.
Shiga motar sukayi suka harba titi, kai tsaye wajan shak'wata suka nufa, nan ta ajiye motar ta suka fito.
Neman waje sukayi suka zauna aka kawo musu menu.
Kowa ordering abunda yake so yayi suka fara shan ice cream suna hira.
Umaimah na faman d'aukar su a hoto, nan suka 6ata lokaci ana k'ok'arin kiran magrib sannan suka mik'e sukayi ordering snacks suka fice.
Hold up ne ya rik'esu wajan traffic, tsuka haseenah tayi sannan tace" wannan zasu b'ata mana lokaci gashi mum tace kar muyi dare"
Farar motor ya hango dake d'an gaba da shi, kallon window motar yayi wajan zaman driver Amma bai ci sa'ar hango wanda ke driving d'in ba.
K'irjin shine ya fara dukan uku uku, gani yayi me motar ta sako hanunta ta window ta dafe kai.
Zoben da yagani hanunta ya sanya yaji ta burge shi, haka kawai yaji yana son ganin yarinyar..
Matsawa da motar shi yayi ya iso dai dai wajan da take, gaban shi ne ya bada sautin dammmm, ganin wanda ke cikin motar Ba k'aramin rikicewa yayi ba, k'ok'arin bud'e motar shi yayi dai dai lokacin traffic light ya Basu hannu.
Advertisement
Ganin zata 6ace mishi ya sanya ba ma motar wuta ya rufa mata baya.
Duk da ta mishi nisa amma yana iya hango motar su, wata kwana yaga ta shige nan shima ya bi, amma sedai me? Ba ita babu labarin ta, kalle kalle ya fara yi dan ganin hanya ya rabu biyu, ya rasa wanne tabi, dukan sitiyarin motar yayi yayi wata k'ara ya buga kanshi kan sitiyarin ya fitar da wani iska me zafi.
Dafe kanshi yayi da yaji na faman sara mishi, da k'arfi ya furta " Haseenah why?"
Yakai kusan minti talatin anan ya kasa motsawa, duk wanda ya gani se ya tsare ya tanbaya ko ya ga wata farar mota amma babu.
Komawa gefe yayi ya parking motar shi ya buga tagumi,Allah ya bashi ikon ganinta amma ta 6ace mishi, dafe kai yayi yana kiran sunayen Allah kan ya temake shi ya bayyana masa haseenah a karo na biyu.
Ganin har lokacin ba motor makamanciyar Tata ya Sanya shi ta da motar jiki a sanyaye ya bar wajan.
Saratu kuwa da mummy tayi a gaba tana kuka.
A dole ta saurare ta Nan ta nata alƙawarin zata aura haseen ko me ze faru.
Haka sameer ya rink'a yawon shi ya koma gida.
Bayan kwana biyu ya sake dawowa anguwan.
Tsayawa yayi daga nesa yana ta faman waige waige, wani yaro ya gani ya taho, da sauri ya fito a motar ya tsare shi, nan ya nuna mishi hoton haseenah.
Gyad'a mishi kai yaron yayi alamar ya gane ta.
Da sauri sameer ya dube shi yace "da gaske kake ka santa?"
" Eh na santa sunan ta Haseenah"
Wani sanyi ne haɗe da farin ciki ya kama shi.
Nan yace ma yaron "zaka iya kaini gidan su?"
Nan ya shiga motar suka kama hanya.
Tsayawa sukayi bakin gate d'in yana neman d'an aika.
Gani yayi an buɗe gate d'in, wata budurwar yarinya ce ta fito, sallama ya mata ta amsa sannan yace" dan Allah haseenah nake nema"
Shuru tayi sannan tace " to barina mata magana"
Tana shiga ta samu haseenah ta fito wanka tana shafa mai.
Kallon ta tayi sanann tace" Aunty kinyi bak'o"
Da sauri ta dubi baby tace" Ni Kuma?"
" Eh"
" Bana nan"
Nan baby ta fara magiya tana bata hak'uri amma ko kulata batayi ba.
Daga waje taji muryan mummy na cewa" jeki bud'e mishi guest palour tana zuwa"
Tura baki haseenah tayi a shagwab'e tace" mummy Dan Allah wlhy...
" Ki tashi ki shirya kije ki sallame shi"
Harara ta daka ma baby tayi k'wafa.
Umaimah dake kitchen Bata San abinda ake ba.
Nan baby ta fita ta k'arasa dashi palour sanann ta fice..
Kusan 30mns haseenah bata fito ba, seda mummy ta koro ta sanann ta fice sanye da atampa dogon riga.
Gaban ta ne taji na fad'uwa saboda jin warin turaren da tayi, kuma ta rasa a ina tasan me irin turaren.
A hankali tayi sallama ta shiga.
Ba tare da ta d'ago kai ba ta shiga ciki ta zauna nesa dashi.
Tunda ta shigo ya zuba mata ido har ta zauna amma bata d'ago ba.
Jin Muryar shi tayi ya doki kunnenta jin an ambaci sunanta.
A razane ta d'ago da sauri tana son gasgata me Muryar.
Zaro ido tayi bakin ta na rawa ta mik'e tsaye tanuna nuna shi.
Kasa furta komai tayi sai hawaye.
Mik'ewa shima yayi ya k'araso ya zube kan gwiwar sa ya fara magana cikin wata irin murya ya fara cewa" haseenah mesa Zaki gujemu? Me muka miki? Kinsan halin da kika samu ciki? Kinsan me kika bari me ya faru bayan tafiyar ki? Kinsan halin da Ammi ta shiga da Ni kaina dalilin ki?"
Shuru yayi jin ta tsananta kuka, Muryar ta ba k'aramin k'ona mishi zuciya yayi ba, banda sautin kukan ta ba abinda ke tashi.
Nan ya cigaba da cewa" gidan mu ya zama kaman gidan mutuwa, ga Mahmud can ba lafiya dalilinki"
Toshe kunnenta tayi da duka hanunta biyu tana kuka.
Shima hawayen yake yi yana mata magiya yana fad'in" ki temakeni ki temaki rayuwar 'yan uwana ki dawo cikin rayuwar mu"
Shuru duka sukayi.
Nan ya cigaba da cewa" haseenah ki temakeni ki aure Ni na miki alk'awari zan miki duk abinda kike so, plxxxx haseenah"
Ya k'arashe maganar had'e da zubewa gabanta shima kukan yakeyi..
Ji tayi jiri na neman zubar da ita ga kanta dake faman juyawa.
Da gudu ta fice daga palour ta nufa hanyar shiga gida lokacin Abban su baby na parking.
Ganin halin da take ciki ya sanya shi kallon inda ta fito.
Fitowa yayi a motar sannan ya nufa yanda Sameer yake.
Ganin shi yayi durk'ushe ya rik'e kai yana kuka kaman k'aramin yaro.
Hakan ya tabbatar ma Abba akwai wani babban al amari...
Kama hanun shi kawai Abba yayi ya mik'ar dashi tsaye.
Hanyar palour shi suka nufa ya zaunar dashi.
Ruwa ya d'auko a fridge da cup ya zuba ya mik'a mishi.
Ba musu ya amsa hanun shi na rawa , da k'yar ya iya kur6a sau d'aya sannan ya ajiye.
D'aki Abba ya wuce ya canja kaya sannan ya dawo ya zauna ya fuskanci Sameer sannan ya fara cewa....
Cikin gida kuwa haseenah d'aki ta shige ta kulle k'ofa ta fad'a kan gado ta saki kuka me k'arfi.
Abba ne yace" ka nutsu ka fad'amun me yake faruwa?"
Da k'yar Sameer ya fara da .....
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial16 Chapters
A world with two moons
Ever been in love? well I know I weren't at first except... I met them 1 by 1 with different circumstance's and situations. I did not even know that we were meant to be together. hell I did not know it was still possible for me to learn what is love. and to actually fall in love. with all the crazy things that happened I though that I would forget all about love and such. but I was wrong. at the end of things it came to me. not just one, not two. but A lot of them came to me, chased me and showed me how much they love and cared for me.It all started when I met her, she was my very first love. she was my everything and now she is part of my everything. I lost her then I found her again this time I shall not let her go and so the others that love and cared for me.I really am glad that I manage to came to this planet. I have a harem*cough* I never knew life could be so wonderful if we just have to live it fully and enjoy it while we can.----------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------WARNING- this FF will contain Mature content as I update this,* Sexual *Gore *Foul language's---------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------(I warned you guys, now enjoy yourself and have fun reading my FF)
8 171 - In Serial17 Chapters
The Ice Fairy
After the apocalypse a young fairy is born. The girl named "Ice Fairy" awakens in a world of ice. There she looks for her first none frozen love and tries to save the world by the way. It's a story about "love", fanatic tendencies and unique characters. ---------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------- I am happy about every comment and/or suggestion. I hope you like my story.
8 435 - In Serial194 Chapters
A Suspicious Lack of Horses
World: The framework of reality. The rules which govern interaction. The dimensions within which existence takes place. Soul: Mind. The source of thought, of consciousness. The means by which reality is observed. Body: Form. The means by which one interacts with the World. The substance from which reality is formed. Spirit: Life. The connection between Soul and Body. The anchor to the World. What happens when these foundational forces are given human form? When they're confronted with the truths of human nature, of human frailty? When the evils of reality are thrown in their face and the question is asked: What are you going to do about it? Why did anyone ever think they'd need horses? I upload ~30k word chunks at the beginning of every month, rotating through each character in order. I have at least four extra chunks on my Patreon. I suggest setting your reading preferences to indent and 30 pt paragraph spacing for the best reading experience.
8 224 - In Serial39 Chapters
Dragon Princess Reborn
Original version here: http://www.royalroadl.com/fiction/1180 Who can stop the humans' greed when what they seek is right in front of their eyes? A girl whose fate has been stolen away by her relatives finally obtain freedom within death... But is death truly the end of her suffering? Or maybe it simply was the beginning of her story. "This world is filthy..." Said a girl wielding a black sword covered with blood "Maybe...but it actually just makes it even more beautiful." Follow her adventures as she swears to keep her destiny within her two small hands, followed by friends and enemies in a merciless world.
8 161 - In Serial14 Chapters
BORNEO
2113, the Earth has finally solved the climate change issue caused by the loss of forests and technology entering a new era. A world of virtual reality is created by a genius scientist in a VRMMORPG game called "BORNEO", taken from the 3rd biggest island in the world famous for it's forest and wildlife. An orphan stumble across the game during military service, not forgetting his roots and experience in the world he starts to create his own legend in the game. He is not alone though, billions of other people are also trying to do the same. This is my first ever novel after so many years as a reader. I hope it would bring the same feeling like the other novels bring to me in this site, I also take inspiration from various novels so you might notice some similarities. Please bear with me during my new journey as an author here. I won't set a schedule for releasing the new chapter yet, I might try to do so after a few chapters in and I started to get the feeling of how things work.
8 152 - In Serial9 Chapters
Dangerously
Samantha Collins tiene 18 años, nació en Londres pero se mudo a New York para escapar de su acosador anónimo. Ella creyó que podía escapar de aquella persona que hacia su vida imposible.Ella no se imaginaba que habia otras personas que les pasara lo mismo.
8 103

