《HASEENAH》PAGE 95&96
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
*55~56*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*95~96*
Washe gari da yamma kaman yanda ya saba zuwa wajan haseenah ya shirya, ƙarfe 5 ya iso nan ya hango Umaimah tana ƙoƙarin shiga ciki.
Ganin shi ya sanya ta tsaya wa tana dariya.
Buɗe k'ofar yayi ya fito Sannan ya dubeta yace" ya akayi ne ina matata?"
Dariya take yi sossai sannan tace" yaushe ta zama matar ka?"
Hararta yayi sannan ya bud'e bayan motar ya ciro leda guda uku ya mik'a mata, karb'a tayi sannan Yace" ki kai mata in bta k'oshi ba ta fad'amun in k'ara mata"
Dariya take sossai sannan tace" mu in ma bamu k'oshi ba ko oho ko?"
"Eh mna ai dama saboda ita aka kawo"
Zatayi magana ya katseta yace" Ni shiga ki kiramun ita na matsu in ganta"
Dariya take sossai tace" haba yaya harda kora ne?"
Kaman ya doke ta yace" Allah kin isheni da surutu Ni bana gane abinda ma kike cewa"
Juyawa tayi ba ta ce komai ba tana dariya.
Tana shiga ta sanar da haseenah, ba tare da b'ata lokaci ba ta fito sanye da atampa dogon riga, hango shi tayi zaune kan plastic chair.
Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallon ta har ta zauna.
Hura mishi iska tayi sannan ta sunkuyar da kai, murmushi yayi ba tare da yace komai ba.
A hankali ta gaida shi ya amsa sannan yace" Abba yana nan ne?"
"Eh" ta bashi amsa.
" Plx kimun iso ina son ganin shi"
To tace sannan ta mik'e ta nufa ciki.
Advertisement
Bata dad'e ba ta dawo tana murza hanunta kanta sunkuye.
A hankali tace " yace ka shiga yana palourn shi"
Mik'ewa yayi ya fara tafiya sai kuma ya juyo yace" saura kuma ki gudu"
Dariya duka sukayi sanann ya shige ciki.
Zaune ya samu Abba hanunshi rik'e da remote yana kallon BBC World.
Yana ganin haseen ya fara murmushi, shima haseen d'in murmushin yake nan ya samu waje ya zauna gefen Abba.
Gaida shi ya fara yi sanann ya sunkuyar da kai ya sanar mishi cewa daddyn shi yana zuwa gobe.
Yasan da maganar dan mummy zuwaira ta sanar da shi, cike da farin ciki ya ce" ba komai ai mamanta ta sanar da Ni, Allah kaimu"
"Ameen Abba"
Hannu ya sanya Aljihu ya ciro kudi kimanin dubu hamsin ya ba daddy yace ba yawa.
Da sauri ya mik'e ya fice dan kar Abba ya ce ya dawo ya amsa.
Dariya kawai Abba yayi sannan ya cigaba da kallon shi.
Yanda ya barta haka ya dawo ya sameta, komawa yayi ya zauna nan ya fara janta da hira.
Ita dai ta kasa sakin jiki suyi hiran, ya kula da har ynxu kunyan shi take ji dan haka ya dubeta yace" swthrt ki dena jin kunyata Kinga auren mu ya kusa, sannan bakisan yanda nake jinki cikin zuciya ta ba"
Dad'i ne ya cika ta jin ya kirata da swthrt.
Ganin tayi shuru ya sanya shi cewa " kinji baby na?"
.da sauri ta d'ago ta kalleshi jin ya sake ambaton wani sunan.
Ya kula da farin cikin da ta shiga dan haka ya cigaba da cewa" wallahi precious na matsu na ganki gidana dan wallahi tsoro nakeji"
Wannan karon seda ta sake maimaita sunan *precious* dubanta yayi jin ta maimaita sunan yace" U like d names huh? Karki damu, sunanki bazasu irgu a bakina ba, cox u deserve it, Ni dai damuwata ki rage wanann kunyar that's all"
Advertisement
Murmushi kawai take ta kasa cewa komai.
Cikin gida kuwa mummy ce ta Sanya saratu gaba tana surfa mata zagi, dan ta gama mantawa gaba d'aya jiya ta shafa kwallin turare ne kawai ya rage.
Jin mummy na fad'in shikenan ai ta rasa haseen ya sanya ta fashewa da kuka.
Tsuka mummy ta ja sannan ta fice ta bar d'akin.
Washegari da safe misalin ƙarfe goma daddyn haseen da yayanshi suka iso gidansu haseenah.
Masauki aka musu a main palour na Abba, zaune suke su huɗu, Abba da yayan shi daddyn haseen ma da nashi.
Bayan sun gaisa ne nan suka gabatar da abinda ya kawo su, ba tare da wani bata lokaci ba aka amince, nan suka bada su goro sweets, biscuits da drinks da yawa sai kuɗi dubu d'ari biyar sadaki.
Abba yace a rage amma sunk'i haka suka amsa suka cigaba da tattaunawa, nan aka tsayar da biki nan da wata d'aya.
Mummy tun da taga daddyn haseen murna ta cika ta, a tunanin ta ya zo ja ma Abba kunne ne akan ya raba haseenah da d'anshi.
Shiyasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, Allah Allah take su fita tayi ma Abba tijara.
Bayan sun gama ne suka tashi suka tafi kowa zuciyar shi cike da farin ciki.
Suna fita kuwa mummy ta shigo palour tana shewa.
Turus tayi ta tsaya ta kasa k'arasa dariyar, duban Abba tayi ganin palour da su sweet da goro tace" wanann fa?"
Ba tare da ya kalleta ba yace" gaisuwa da sadakin haseenah aka kawo.
Ji tayi komai ya tsaya mata kaman an d'auke wuta haka taji duhu ya ziyarci tun daga cikin kwakwalwar ta har zuwa idon ta.
Kaman k'iftawar ido taga wata haske ta wulga mata, hakan ya sata dawowa cikin k'aramar firgicin da ta shiga ta dubi Abba tace" me kace wai?"
"Abinda kunnenki yaji"
Nan mummy ta fara zagi tana fad'in anga kud'i an shiga an fita an asirce mata d'an 'yar uwa haseenah ta lashe masa kurwa.
Shidai baice da ita komai ba hakan ya sanya ta dad'a fusata.
Juyawa tayi tana fad'in " ayi auren mu gani"
Kai tsaye d'akin ta ta wuce ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Haseen kuwa tun da yaji ansa bikin su nan da wata d'aya ya kasa 6oye farin cikin shi, godiya yake ma daddy da mum d'inshi Yana murna.
Mik'ewa yayi ya shirya ya fito da nufin zuwa wajan haseenah.
Mummy ya hango a palour tana zaune hakan ya sanya shi k'arasowa ya zaune gefenta sanann yace"....
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial136 Chapters
Silver Amelia
Amelia used to be a positive, brimming girl loved by those around her. Once tragedy had befallen, her view of the world has changed. Her sight was no longer filled with blooming flowers. Her eyes bore those of an actor. Her body knew what true pain was. Lastly, her heart was filled with the resolve to continue her Grandfather's legacy. The dream of a world that accepted diversity. However, in a series of events, Amelia was jolted with another realization. The ancestors of her family, Laurel's Royalty, descended from a being far from what humans could call a relative. Now, her ancestral blood forcefully awakened by a grand scheme, Amelia found herself unsure of her own identity and purpose. Would she live as a human and only lay the foundations for diversity? Would she accept her newfound identity and become immortal? Even so, no matter what option she chose, she needed to prepare on how to accommodate the Heroes summoned from another kingdom. _____________________________________ Author's Notes: This novel is a participant of WriTE This novel will be re-written after I finished it and gained more experience in writing. Anyway, feel free to join Amelia's journey. My first work. Light gore only. Added traumatizing content just in case. Comedy is less prioritized when the story moves. Tags will be added as the story goes. Feedbacks are appreciated. Release schedule: 1-3 chapters per week (Updates on Weekends) Unknown Chapters: Stalled (Read at your own risk, but the continuation will be posted at a later time) Feel free to join this discord: https://discord.gg/duFTzZr *Cover is mine.
8 129 - In Serial195 Chapters
High-Class Mob
As Leo opened his eyes, he found himself in the body that is not his. Colt Edgeworth is a man with little to no information in the story Sword of Heaven. The character Colt Edgeworth died in the hands of his fiancé after experiencing some stabby-stabby action. And that is who Leo had become. ‘I am in a world that has magic, different technology, customs, races, and Gods actually do shit, and I have a woman who loves me but also wants to turn me into swiss cheese...’ He looked at the mirror, contemplated his fate, and came to a single conclusion... ‘So be it, I’ll try living.’ Note: This is my first time writing and English is not my first language, so there are mistakes, I only managed to Re-edit [Volume-1 Chapter 1 - 20], please tell me about the mistakes. The cover is not mine, I just saw it and thought it was awesome...all rights reserve to the original creator Kolsga https://www.deviantart.com/kolsga/art/Drake-571265818
8 520 - In Serial27 Chapters
Bound in the Dark
About a kid who escapes his darkness by harnessing it, along with his friend who helps him find a cause to use what powers they have as they fight against the dark and...the light.
8 73 - In Serial47 Chapters
Forced Development (What does it truly mean to live a fulfilling life?)
To get things started I would like to admit that this story does not bring much new to the table when it comes to the over-saturated Litrpg genre in terms of things like mechanics and power systems. Then what exactly am I trying to bring to the table with this work? A nice slow-paced novel about people maturing and growing older think of it as the re: zero or jobless reincarnation of Litrpgs. A story that tries to take into consideration how a worldwide system would affect the economics and culture of a world. A story that is much more character-focused than the typical heavy progression-focused novels this genre is known for. The RPG system, like any good power system, is there to actually explore the themes of the story and not just as a plot device for characters to get stronger. This is a story where we will see the growth of the Mc from being a baby to when he dies of old age. With plenty of heart-racing actions and intriguing plot developments along the way. Exploring themes like; What does it mean to improve at something and what does it mean to mature as a person? How does magic, the constant threat of monsters and people so much stronger than the average joe that they can destroy countries affect one's culture both on the micro and the macro scale? How people are affected by the culture in general? Generational trauma Nature vs Nurture Talent vs hard work What is morality, society, and people's opinions on both? What does it mean to be human and what does it mean to be alive in the context of a world with multiple sapient species vastly different from one another in basic biology? All these questions are going to be explored from multiple angles using the system as a catalyst for those discussions. So if any of does questions sound interesting to you what are you waiting for, I'm sure you are going to love this story. PS - Chapter come out every Friday at about the same time.
8 193 - In Serial30 Chapters
Hey stupid, i love you!
+ دوستت دارم!_ بخاطر سیب ترشهام؟+ اونم هست...ولی حتی اگه اونها هم نباشن، بازم دوستت دارم.🍏 کاپل: کوکوی🍏 ژانر: امگاورس، رمنس، انگست، فلاف🍏 وضعیت: تکمیل شده.
8 129 - In Serial53 Chapters
Henry Cavill imagines
I feel we don't have enough of Henry Cavill and I've decided share some of my favourite tumblr imagines!(Disclaimer: I do not write these imagines I'm just sharing them on here) ENJOY!!
8 198

