《HASEENAH》PAGE 85&86
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
Assalamu alaikum, plx ina me bada hakuri na jina shuru da akayi first a while, these happen due to some circumstances, but in Allah ya yarda if time permits zan na typing da safe ko da yamma in posting, thank you all..
*85~86*
Bayan kwana biyu da gama gyara side d'in ummah Wanda Haseenah zata koma kaya suka iso, Mummy Zuwaira ce da su Umaimah suka zo suka gyara ko ina suka jera, Sa'a d'aya dan tun safe da Mummy ta fita bata dawo ba, haka ma saratu ita bata ma kwana a gidan ba.
Soyayya kuwa tsakanin Haseenah da Haseen sai abinda ya karu, dan ji suke kaman in Suka rabu ba zasu sake had'uwa ba, hakan ya sanya Haseen ya fara yi ma Mummy Zuwaira maganan auren su, da k'yar Mummy ta lallab'a shi tace ya hak'ura komai ya dawo dai dai sannan a fara maganar.
Da k'yar ya hak'ura ba dan ranshi ya so ba.
Haka ya hana Haseenah fita ko ina duk abinda take so sedai ya kawo mata, ita ma bata damu da fitar ba zama take a gida.
Shak'uwa me tsanani ne ya shiga tsakanin Haseenah da k'aninta Aaman.
Duk da ba saninta yayi ba amma yafi sakewa da ita, duk yanda tayi yana biye da ita.
Hakan ba k'aramin dad'i ya mata ba.
Can Abuja kuwa tunda Haseenah ta fita a gidan gaba d'aya gidan ya zama wani iri, barin Sameer da ko abinci baya saukowa yaci in ya dawo office ya hau sama baya sake saukowa sai washegari, in yunwa ya dame shi sai ya ci biscuit da maltina ko coke.
Advertisement
Mahmoud ko sedai in abun ya dameshi ya tasa Mummy a gaba yayita mata kuka yana fad'in taje ta dawo mishi da Haseenah.
Ta rasa yanda zatayi da su itama tausayin su ke sanya ta zub da hawaye.
Bata ta6a sanin Haseenah ta zamo musu sani 6angare a rayuwar su ba seda ta bar gidan.
Ita kanta ba jin dad'in gidan take ba amma haka take daurewa.
Sameer Kam ma ba kulasu yake ba duk yayi duhu ya koma miskilin dole.
Can kuwa ana saura kwana d'aya Haseenah zata koma gida suka fita da yamma Dukansu suka je siyayyan kayan sawa.
Duk Haseen ne ya biya kud'in dan ya hanata biya, haka Umaimah da Baby da Aaman ma yace su d'auka abinda suke buk'ata.
Sossai sukayi siyayya da yake yanzu Haseenah batada wani kayan sawa.
Yawanci dogayen riguna ne sai atampopi da laces wanda suka mik'a wajan tailor sannan suka dawo gida.
Washe gari da daddare Abba ya taho da motar shi yazo d'aukan Haseenah.
Motar Haseenah wanda tun bayan abinda ya faru da Mummy ta sanya aka lullube ta Bama driver ya Kai car wash tun safe.
Dan haka Abba yana isowa aka loda mata kayayyakin ta a Boot sanann suka shiga Dukansu a mota uku suka d'au hanya.
Motar Abba ne sai abokin shi a ciki, d'aya motar Haseenah kuma Mummy ce ke driving sai Haseenah da Baby da Aaman, d'aya motar kuma ta Haseen ce, shi ne a ciki sai sister Mummy wato Aunty sadiya da Aunty zainab a ciki.
A hankali suke tafiya yayin da Haseenah ke faman sak'e sak'e a ranta, tunani take irin zaman da zasuyi da Mummy, Dan wannan karon da shirin ta take, dan bazata d'au wannan rainin hankalin ba.
Jin an tsaya ne ya sanya ta d'agowa da sauri, gani tayi an kutsa cikin gidan, lokaci d'aya taji rayuwar su ta baya ta dawo mata, ummanta kawai take gani a idon ta, bata san lokacin da hawaye ya fara zubo mata ba, haka ma Mummy Zuwaira duk jikinta yayi sanyi, Baby da Umaimah kuwa ganin kukan da Haseenah take suma sai kuka.
Advertisement
Kasa fitowa daga cikin motar sukayi, duk jikinsu nauyi ya musu, tsaye Abba yake da su Haseen suna jiran fitowar su, ganin zasu 6ata lokaci ya sanya Aunty zainab k'arasowa jiki a sanyaye ta knocking window, a hankali Mummy ta sauke glass d'un sanann tace " gamunan fitowa"
Duban su tayi tace" let's go"
Aaman ko yana manne jikin Haseenah ya tsira mata ido ganin tana ta kuka, shiko sai faman share mata hawayen yake yana ce mata "choli aunty na"
Murmushi kawai tayi sannan ta fito daga motar tana rik'e da Aaman.
Suma fitowa sukayi nan suka k'araso wajan su Abba.
Tunda Mummy taji horn na motoci ta ra6e jikin window ita da saratu amma Abba kawai suka gane da yake dare ne basu gane komai.
A tare suka shiga ciki Abba ya sanya key ya bud'e side d'in.
Shiga duka sukayi a tare har cikin palour.
Ba k'aramin kyau yayi ba ganin tsarin da akayi ma wajan.
Komai na palour pink nd purple ne,.
Zama dukan su sukayi ba tare da ance komai ba, dan ji suke kaman yau akayi mutuwar.
Da k'yar Abba ya iya share hawayen dake gangara mishi sannan ya fara musu nasiha.
Sunkai kusan hour suna tattaunawa daga bisani Abba ya fice.
Mummy ya gani tsaye jikin k'ofar d'akin shi sai girgiza take, kau da kai yayi da nufin shigewa, tsare shi tayi cikin masifa tace" ban gane abinda kake nufi ba a kwanakin nan, su waye naga an kawo su wajan nan eye?"
Ko kallon ta baiyi ba illa ma yana neman hanyar shigewa ne, tare hanya ta sake yi sanann tace" kana nufin aure ka k'ara?"
Ba tare da ya kalleta ba yace " eh, ko babu kyau ne?"
Kasa magana tayi nan tayi zaman dirshan.
Hakan ya bashi daman wucewa ya banko k'ofar ya rufe.
Kuka Mummy ta sanya tana shura k'afa.
Da sauri saratu ta taso ta tsuguna tana tanbayan dalili, kasa magana Mummy tayi, ganin tana neman tara musu jama'a ne ya sanya saratu dagewa ta kamo hanunta suka wuce side d'insu.
Hauka da surutu kam Mummy take da zage zage.
Babu wanda ma yasan tanayi ballantana ya kula ta.
Snacks d'in da sukayi a gidan Mummy Zuwaira Suka baje sunaci abunsu suna hira.
Ganin wajan 10 na dare yayi ya sanya Mummy mik'ewa ita da sauran zasu tafi.
Mik'a wa Haseenah key d'in motar Mummy tayi sannan ta dubi su Umaimah tace" kukuma sai yaushe zaku dawo?"
" Mummy kawai kije kinga yanzu hutun school ake, sai kin ganmu kawai"
Duban haseen Baby tayi sannan tace" uncle gobe in zaka taho plx Kabi gida ka taho mana da kayan mu harda na Aaman ma"
Amsa mata yayi sannan ya fice.
Suma bin bayan shi sukayi sannan sukayi sallama da Abba suka kama hanyar komawa gida.
Ayi hakuri da wanann plx....
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial1363 Chapters
VRMMO: The Unrivaled
Lu Chen used to be a ranker of the most popular VRMMO game, Spirit of Grief. After a car accident turned his dreams into dust, his disability left him incapable of escaping the pit of mediocrity he was thrown into. Helpless and defeated, his story ended.Two years later, the Eternal Moon Corporation launched a new VRMMO called "Heavenblessed", and Lu Chen stumbled into another terrible accident that left him in a complicated situation far beyond his ability to handle. That won't stop him from rising to the top, however. Not again.Come witness the rise of the sword-wielding zombie and the relationships he makes during his journey to the apex! For riches and bi- ahem, for career and love!He wields a demonic sword from Hell, he dons armor shining with Heaven's light. His boots stride across the sky as his helmet devours the souls of his enemies. On his left side sits the Goddess of Death. On the other, the Angel of Beauty.From the land of ice and death, a generation of Asura Kings rises, their roars reverberating throughout the world.Tremble in fear, noobs!
8 8156 - In Serial1353 Chapters
Refining the Mountains and Rivers
A young man's life changes when he stumbles upon a mysterious item. Qin Yu had never been a lucky person. Weak of body, bullied by his peers, and with only his friend as his family, he struggles day-by-day to live. But everything changes when he stumbles upon a little blue lamp. An immortal and demonic cultivating adventure.
8 3344 - In Serial2455 Chapters
Mortal Cultivation Biography
A poor and ordinary boy from a village joins a minor sect in Jiang Hu and becomes an Unofficial Disciple by chance. How will Han Li, a commoner by birth, establish a foothold for himself in in his sect? With his mediocre aptitude, he must successfully traverse the treacherous path of cultivation and avoid the notice of those who may do him harm. This is a story of an ordinary mortal who, against all odds, clashes with devilish demons and ancient celestials in order to find his own path towards immortality.
8 1050 - In Serial1503 Chapters
Dragon Prince Yuan
Destiny stolen at birth, the prince of the once mighty Great Zhou Empire, Zhou Yuan, has been plagued all his life by a fatal poison, forced to suffer powerlessly until one day when fate draws him into a mysterious domain where he meets a beautiful girl in green, a bizarre dog-like creature and an unfathomable old man in black.Join Zhou Yuan as he is thrust into the whirlpool of destiny while he seeks the pinnacle of cultivation.
8 1057 - In Serial677 Chapters
Ranker's Return
In the early days of the virtual reality game, Arena, meleegod was the strongest ranked player! He deleted his character and suddenly left. In order to restore his bankrupt family, he returned to Arena!"Do you want to create a character?"
8 1715 - In Serial1525 Chapters
Monarch of Evernight
Qianye rose from hardship but was felled by betrayal. From then, one man, one gun; he tread the path between Evernight and Daybreak and became a legend. Even if Evernight was destined to be his fate, he still intends to become the ruler who dictates.
8 22861

