《HASEENAH》PAGE 83&84

Advertisement

🌸 *HASEENAH*🌸

story &written

By👇🏻

Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

#

# *IG PML WRITERS*

# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on

*83~84*

Mummy ce ta share hawaye sannan ta dubi Haseenah tace" ki bani labari ya akayi hakan ta faru"

Shuru Haseenah tayi kaman ba zatayi magana ba, dan batasan ta inda zata fara ba, da k'yar ta iya buɗe baki nan ta fara basu labari tun sanda ta tsinci kanta cikin kabari da temakon da Sameer ya mata kawo da surgery d'in da aka mata, daga nan ta d'aura da basu labarin rikicin da ya faru da matsalar da suka fara samu kan mutanen gidan.

Dukan su kuka suke saboda ba k'aramin tausaya mata sukayi ba, duk wannan abinda ake Aaman na mak'ale jikin Haseenah ya kwanta har bacci ya ɗauke shi.

Jinjina kai Mummy tayi sannan ta tuno da maganar haseen, wato lokacin da ya tubure kan shi jikin shi na bashi Haseenah bata mutu ba.

Sauke ajiyar zuciya tayi sannan Mummy tace" Haseen yayi gaskiya"

Da sauri Haseenah ta d'ago ta kalli Mummy jin an ambaci sunan abun k'aunar ta, dama tun tuni ta rasa ta yaya zata fara tanbayar Mummy, hakan ya sanya ta cewa" me ya faru Mummy?"

Nan ta kwashe labari ta faɗa mata irin abubuwan da suka faru bayan rabuwa da kuma irin rikicin da Haseen keyi kan shi zaije neman ta.

Tausayin shi ne ya kamata haɗe da k'aunar shi da ya k'aru cikin ranta, sunkuyar da kai kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Mummy ce ta dubi Umaimah da ke manne jikin Haseenah tace" ki kawo mata abinci mana da Allah kin d'afe jikinta kaman zata gudu"

Mik'ewa tayi ta shiga kitchen, Nan ta cika wa Haseenah abubuwan ciye ciye, aiko taci da yawa dan dama yunwa take ji.

Advertisement

Bayan ta gama ne suka shige d'akin su Umaimah tayi wanka sannan ta kwanta.

Aaman na kwance gefen ta yana sharara bacci.

Nan suka cigaba da labari har wajan 12 na dare kafin nan suka kwanta.

Haseenah kam da k'yar bacci ya ɗauke ta dan tunani ne cike a zuciyar ta.

Da safe misalin ƙarfe 8 na safe Mummy ta Kira Haseen tace tana son magana dashi.

Ji yayi gaban shi na fad'uwa, da k'yar ya samu ya shirya sannan ya d'auko hanyar gidan.

Haseenah ko tunda tayi sallar asuba ta koma bacci har lokacin bata tashi ba.

Sallama Haseen yayi daga waje nan Mummy tace ya shigo.

Waje ya nema ya zauna sannan suka gaisa, ganin Mummy na ta faman sakin murmushi ya sanya zuciyar shi ta ɗan yi sanyi.

Breakfast ta d'auko mai nan ya ɗan ci kaɗan sannan ya koma ya jingina da jikin kujera, shi duk ya matsu yaji dalilin kiran.

Aaman ne ya taho da gudu ya faɗa jikin shi, d'aga shi sama yayi yana mishi wasa, shi kuwa sai ihu yake yana dariya.

Dariyar shi ne ya farkar da Haseenah daga baccin da take.

Agogo ta kalla taga har tara ta gota, durowa tayi daga kan gadon ta shiga toilet, wanka ta fara yi a gurguje sannan ta fito ta sanya ɗaya daga cikin rigar Umaimah,

Ko ɗan kwali babu a kanta ta sanya flat shoe ta nufo hanyar palour, k'anshin turaren da taji ne ya sanya gaban ta ke fad'uwa, tanbayar kanta take a ina ta ta6a jin irin turaren nan?

Haka ta iso palour tana faman tunani.

Tunda ya fara jin tafiya ya kafe k'ofar da ido, haka kawai yaji yana son ganin me fitowar.

Ita bata ma kula ba ta k'araso, kafe ta da ido yayi ya runtse idon shi, bugun k'irjin shi ya k'aru lokaci ɗaya yaji kanshi ya k'ara mishi nauyi.

Advertisement

Dafe kai yayi dan gani yake kaman gizo idon shi ke mishi.

Hannu ya sanya ya mutsike idon shi dan kawar da wannan gizon.

Amma seya ga yarinyar ma dad'a matsowa takeyi.

Sai a lokacin Haseenah ta d'ago da kanta dan ganin me wannan turaren.

Cak ta ja ta tsaya bakin ta na rawa ta nuna shi da hannu sannan cikin rawar murya tace" yaya Haseen?"

Tsam ya mik'e shima ya dubeta sannan yace" kece Haseenah?"

Kasa bashi amsa tayi illa gyad'a mishi kai da take faman yi alamar eh nice.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, abunda bakin shi yake iya furta wa kenan.

Is this real life or just dreaming and imagination?

Kuka Haseenah ta fashe dashi dai dai lokacin da mummy ta fito daga kitchen.

Da sauri ta k'araso ta ja Haseenah ta zaunar da ita ganin kukan da take, shiko Haseen din hawaye ke zuba a fuskar shi.

Wayyo dad'i, duban Mummy yayi sannan ya fara cewa" mum ban faɗa miki ba? I told u she's alive but u denied me keda mum D'ina, har kuna cewa na haukace, Ni kaɗai na san abinda nake ji cikin raina"

Alhamdulillah.....

Ita dai Haseenah ta kasa magana se kuka, ita kaɗai ta san ynda take ji a halin yanzu, kwantar da kanta Mummy tayi a jikin ta ta na faman rarrashi.

Nan Haseen fa ya kira mum d'inshi yace ta zo yanzun nan.

Cike da tashin hankali ta k'araso tunanin ta wani abun ne,

Amma tana zuwa labari ya sha bambam.

Da farko da taga Haseenah tsorata tayi, seda Mummy ta Basu labari sannan ta nuna murnar ta a fili.

Farin ciki biyu takeyi, na dawowar Haseenah da kuma nutsuwar d'anta Haseen.

Mummy ce ta kira abban Haseenah, nan ya taho da sauri, ganin Haseenah ba k'aramin ta da mishi hankali yayi ba, kuka yake sossai dan shi sai yanzu yake jin mutuwar umman Haseenah.

Nan yace Haseenah ta biyo shi su tafi.

Murmushi Haseenah tayi tace" Abba nima inason in dawo kusa da kai, amma ba yanzu ba, se an gyara side din ummah na"

Cikin rawar jiki yace" Haseenah ko yau kikace a fara gyara wa za'a gyara"

Nan suka cigaba da tattaunawa, kafin Abba ya bar gidan har ya kira wani architecture ya sanar dashi abinda yake so ayi.

Nan ya mishi transfer kuɗi na duk abinda zasu bukata sannan sukayi sallama da niyar gobe zasuzo su fara aiki.

Mum Haseen sai wajan azahar ta tafi, while Haseen shi ko niyar tafiya bayida shi, hakan ma Haseenah dama ba so take ya tafi ba.

Hirar su suke kaman yau suka fara haduwa dan ji yake ta dad'a shiga zuciyar shi.

Washe gari kuwa nan aka zo aka buɗe side d'in mum aka fara gyara.

Nan fa hankalin Mummy da saratu ya tashi tunanin ta kishiya zai mata, ta tada hankali tace bazai yiwu ba.

Abba ko kallon ta baiyi ba balle ya bata amsa, nan ta tada hauka da bori, Abba yace su cigaba da aikin su kar su kula ta.

Aiko hakan a kayi, kafin kace meye waje ya fara kyau, cikin kankanin lokaci zuwa yamma sun kammala.

Nan aka taho da masu saka POP da penti.

Basu gama ba sai washe gari.

Matasa Abba ya kwaso suka share wajen.

Da kanshi yayi ordering furnitures da komai da su kayan kitchen.

Bayan an gama share wajan ne ya kulle da kanshi.

Yanzu jiran zuwan kayan kawai ake.

Mummy kuwa duk ynda ta kai da maitarta dan gano me yake shirin faruwa amma abun yaci tura.

To me yake shirin faruwa ne?

For comments 08144932303

    people are reading<HASEENAH>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click