《HASEENAH》PAGE 81&82

Advertisement

🌸 *HASEENAH*🌸

story &written

By👇🏻

Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

#

# *IG PML WRITERS*

# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on

*81~82*

Gefen gadon Haseenah Ammi ta nema ta zauna haɗe da dafe kai, ita ba tafiyar bane ta dameta, ina Haseenah ta je? Tanbayar knan da ke mata yawo cikin kanta.

Mahmud kuwa zaman 'yan bori yayi ya fashe da kuka kaman ƙaramin yaro, sossai yake kuka yana fad'in" wayyo Allah na Ammi why? Wallahi se na nemota kuma na aureta, duk abinda ze faru sedai ya faru"

Sameer kuwa tunda ya fice ya fara zagaya garin Abuja ko Allah zai sa ya ganta, amma ko me kama da ita bai gani ba, haka yayita yawo har wajan k'arfe 12 na rana, duk ya galabaita ya fita hayyacin sa, ganin idonshi ya fara mishi duhu ya sanya shi neman gefen titi Yayi parking, kifa kanshi yayi kan steering motor had'e da dafe kanshi da ke faman bugawa.

Yakai kusan 30mns a haka ba tare da ya d'ago ba, wasu zafafan hawaye ne yaji na sauka mishi daga kuncin sa.

Girgiza kai yake zuciyar shi cike da k'una da baƙin ciki a hankali yake furta " Ammi why? Plx why?"

Abunda bakin shi ke iya faɗa kenan.

Ganin yana 6ata lokaci ya sanya shi ta da motar ya kama hanyar motor park, Nan ma babu ita babu labari.

Abunda basu sani ba kuwa Haseenah tayi nisa a hanyar Kano.

Haka Sameer yayita yawo har yamma ba tare da gane wani abu ba.

Dan dole ya juya ya nufa hanyar gida zuciyar shi kaman zata fashe.

Mahmud kuwa Ammi ce tsaye gefen shi tana dafe da kanshi dalilin zazzaɓin da ya rufe shi.

A hankali Sameer ya shigo kai tsaye stairs ya nufa, jin alamun tafiya ya sanya Ammi lek'awa ta ga Sameer ne.

Duk ya galabaita hakan ya sanya ta duban shi tace " son kazo ka duba Mahmud Baida lafiya"

Advertisement

Ba tare da ya juyo ba yace" ku kaishi asibiti bazan iya yin komai ba ahalin yanzu dan nima ina bukatar me dubani"

Nan ya shige d'akin ya barta nan tsaye ta kasa motsi, dan shi gaba ɗaya ma haushin gidan yake ji da mutanen cikin gidan.

*KANO*

Da yamma Haseenah ta shigo Kano dalilin 6acin da motar su tayi.

A gajiye ta iso saboda rabon ta da abinci tun daren jiya, ko ruwa bata sha a hanya ba,

Waige waige ta fara yi tana kallon garin duk ya juya mata.

A daidaita ta tara ta shiga nan suka kama hanyar gidan Aunty Zuwaira.

Mayafinta ta saka ta yane kanta dashi sannan ta d'au wani makeken glasses ta sanya fuskanta. In ba faɗa maka tayi ba bazaka gane Haseenah bace.

Suna isowa k'ofar gidan ta sauka ta sallame shi sannan ta tsaya bakin gate d'in.

Ji tayi k'irjin ta na bugawa, ta kai kusan minti biyar nan tsaye ta kasa motsa wa, ganin ana ƙoƙarin buɗe gate d'in ya sanya ta yanke hukunci, nan ta fara tafiya ta doshi gidan.

Dai dai lokacin mai gadi ya wangale gate d'in.

Daddy su Baby ne ya fito wato mijin mummy Zuwaira, matsawa tayi ya fice sannan ta doshi cikin gidan.

A hankali ta fara tafiya dai dai k'ofar palour ta tsaya jin ana dariya.

Muryar yaro taji nata dariya, lokaci ɗaya zuciyar ta ya karye hawaye ya cika mata ido, a hankali ta cire glasses d'in ta share hawayen sannan ta mayar ta saka.

Knocking k'ofar tayi haɗe da yin sallama.

Ji tayi daga ciki an amsa da " Yes am coming"

Tsayawa tayi duk jikinta rawa yake yi, ji take kaman ta juya ta fasa shiga, amma ta kasa.

Tana cikin tunanin ne aka buɗe k'ofar, Umaimah ce ta buɗe, ƙura wa juna ido sukayi amma Umaimah ta kasa gane waye.

Ganin sun d'au wasu seconds Nan tsaye ya sanya Umaimah matsawa gefe sannan tace" come in"

Tayi mata turanci ne dan a tunanin ta baturiya ce ko balarabiya, dan bata tunanin tana jin Hausa.

Advertisement

Hakan ya sanya Haseenah murmushi ta ra6a ta gefen ta ta wuce ba tare da tace komai ba.

Palour ta shiga sannan ta zauna kan sofa tana bin d'akin da kallo.

Jin kar'ar fad'uwar abu ne ya sanya ta kallon wajan, ji tayi baby na magana da ga kitchen tana cewa" Aaman me kakeyi haka?"

Gaban Haseenah ne ya fara dukan tara tara, da sauri ta kalle shi, kama ta gani ƙarara a fuskar shi sai kace su 'yan biyu ne sedai ynxu tafi da kyau.

Hawayen da take ƙoƙarin mak'ale sune suka zubo, tayi saurin gogesu.

Umaimah ce ta shige d'akin mummy Nan ta tarar da ita zaune kan gado tana gyara kaya.

Duban mummy tayi sannan tace" mum kinyi bak'uwa fa"

"Bak'uwa Kuma?"

"Eh amma ban ta6a ganinta ba kaman baturiya ce ko balarabiya ce oho"

Da sauri mum ta mik'e sannan tace" anya kuwa ba 6atan hanya tayi ba?"

Umaimah tace" nima haka nayi tunani amma muje dai muji"

A tare suka fita, nan suka tarar da ita zaune ta ƙura wa Aaman ido.

Jin alamar tafiya ya sanya ta maida hankali wajan.

Mummy ta gani na taho wa, ji tayi kaman ta tashi ta rungume ta dan farin ciki.

Zama mum tayi sannan ta dubeta ta gaisheta da turanci, murmushi Haseenah tayi sannan tace" ina wuni mummy"

Dam gaban mummy ya buga, ji take kaman ta san me irin Muryar, amma kuma yarinyar batayi kama da bahaushiya ba, kuma gashi tayi Hausa, wacece wannan?

A sanyaye ta amsa sannan tace" ban gane kiba daga ina?"

Hawaye ne ya cigaba da zubowa idon Haseenah amma ba wanda ya gani saboda glasses d'in Bata cire ba.

Cikin murya irin wanda kuka keson fin ƙarfin ta murya na rawa tace" mummy Baki gane niba ko?"

Wannan karon mummy kasa magana tayi dan jikinta ya dad'a sanyi hakan ya sanya gyad'a mata kai alamar eh.

Saukowa ƙasa Haseenah tayi ta zauna sannan ta zare glass ɗin fuskar ta.

Ido 4 sukayi da mummy, ganin irin kallon da mummy take mata ta tabbatar da basu ganeta ba.

Girgiza kai tayi hawaye ya cigaba da zubo mata sannan tace" Mummy har yanzu baki ganeni ba?"

Cikin ƙarfin hali Mummy tace" kaman na san wannan fuskar amma gskya na kasa tunawa"

" *Haseenah ce*"

Abunda ta iya furta wa kenan.

Azabure Mummy ta mik'e ta nuna ta bakin ta na rawa tace" Haseenah fa kikace?"

Girgiza mata kai tayi alamar eh.

Ja da baya Mummy ta fara yi a lokacin hawaye ke zuba a fuskanta, dan ta tuna mutuwar 'yar uwar ta sannan tace" Haseenah ɗaya na sani kuma ta riga da ta mutu"

" Eh Mummy ita ɗin ce dai kuma ban mutu ba"

Umaimah da ta zamo tamkar gunki dan ita ta gane Haseenah ta kurma wa Baby Kira da take kitchen tace" babbyyyy ki fito ga Aunty Haseenah ta dawo"

Baby da ke riƙe da tumbler hanunta taji maganar kamar an sauke mata guduma a kai, bata san lokacin da ta saki cup din ba ya watse wajan.

Da gudu ta fito dan ganin meke faruwa.

Ganin bak'uwa tayi zaune ga Mummy da Umaimah da kuma Haseenah duka na kuka.

Zaman dirshan tayi tace"meke faruwa ne wai?"

Bakin Umaimah na rawa ta nuna Haseenah tace" ga Aunty Haseenah ta dawo?"

Zaro ido waje tayi ta fada wata uwar ƙara ta yo kan Haseenah da gudu ta zube jikinta haɗe da kankameta sannan ta fashe da kuka.

D'ago fuskar Haseenah tayi cikin kuka take faɗin" sister baki mutuba dama? Ina kika shige tsawon wannan lokacin baki dawo garemu ba?"

Ita dai kasa magana tayi dan kuka yaci ƙarfin ta.

Aaman kuwa zama yayi gefen Haseenah ya zuba mata ido.

Janyo shi jikinta tayi ta rungemeshi sanann tace " Aaman d'ina"

Nan Mummy ta dad'a tabbatar wa wannan Haseenah ce, zubewa tayi wajan tayi sujuda tana godiya wa Allah.

Sun d'au tsawon lokaci suna kuka baby kuwa ta d'ale jikin Haseenah kaman wanda zata gudu.

A hankali Mummy ta d'ago ta dubi Haseenah sannan tace"......

For comments 08144932303

    people are reading<HASEENAH>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click