《HASEENAH》PAGE 69&70

Advertisement

🌸 *HASEENAH*🌸

Story &written

By👇🏻

Aysher Abbakar (meerah)

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

#

# *IG PML WRITERS*

# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303

# http://

Follow me on Aysherabbakar

*69~70*

Bata tsaya wanka ba alwala ta d'auro ta fito sannan ta tada sallah, bayan ta idar kuma tayi wanka ta fito, wata sabuwar doguwar riga ta d'auko cikin wanda Ammi ta siya mata a Istanbul maroon colour ta saka, ba karamin haskaka ta yayi ba, ko mai bata tsaya shafawa, kwalli kawai ta sanya a idonta, ganin yanda suka canja kala sannan suka kumbura saboda kukan da tayi.

Lokacin wajan 8:30 ne, takalmi ta zira sannan ta fita dan tasan suna can suna jiran ta don yin breakfast, a hankali take tafiya kanta a ƙasa, ganin su tayi duka suna k'ok'arin zama da alama suma lokacin suka iso, Mahmud ko ya haɗe fuska saika ce be iya dariya ba.

Sameer kuwa ko kallon wajan da yake baiyi ba ballan tana ma ya san yana yi.

Tana karasowa ta nema waje ta zauna sannan ta dubi Ammi a hankali ta sakar mata murmushi, zuba mata ido Ammi tayi duk tausayin yarinyar ya kama ta.

Amma ta kasa yin komai gashi ba ta san ta ya zata fara bata hak'uri ba.

Dan haka mik'ewa Haseenah tayi ta fara zuba ma kowa nashi, da ta zo kan Mahmud hanunta har rawa yakeyi saboda tsoro.

Da k'yar ta daidaita nutsuwar ta ta zuba mishi.

Daga Ammi har Sameer bin hanunta suke da kallo, tsantsan tsoron Mahmud ne a ranta.

Dan haka kasa sakewa tayi taci abincin, kadan ta ci sannan ta mike ta bar wajan.

Kai tsaye d'akin ta ta koma ta murxa key sannan ta fada kan gado, kwanciya tayi fuskan ta yana kallon ceiling d'in d'akin, tunani take daban daban na samun mafita, lokaci daya taji jikinta ya dau zafi kanta ya fara ciwo.

Kafin kace meye fever ya rufe ta, da k'yar ta samu ta lalubo blanket ta rufe jikinta da shi.

Takai kusan 30mins a haka, gashi ba halin tashi ta dauko magani, ganin abun na son fin k'arfin ta ne ya sanya ta tashi da k'yar ta buɗe side drawer, paracetamol ta ciro ta balla sannan ta mika hannu ta dauka sauran bottle water Wanda ta ajiye sauran da ta sha.

Advertisement

Da kyar ta iya had'iye wa nan ta koma ta kwanta tana maida numfashi.

A hankali zazzaɓin ya fara sauka, nan wani bacci yayi awun gaba da ita.

Sameer kuwa bayan sun gama cin abinci d'akin Haseenah ya nufa, jin dakin a kulle ya sanya shi juyawa duk ranshi a jagule.

Ammi kam ta kasa yin komai dan bata san ta ina zata fara ba.

Sai wajan karfe uku Haseenah ta farka, duk jikinta a mace yake, mik'ewa tayi ta d'auro alwala tayi sallan Azhar, Nan ta zauna har lokacin la'asar sannan ta tashi tayi.

Can ko duk Ammi ta damu ganin har wannan lokacin Haseenah bata fito taci lunch ba gashi har anyi la'asar, tayi ta buga kofar ba.a buɗe ba.

Zaune take tayi tagumi tunani take anya lafiya kuwa.

Motsin da taji ne ya sanya ta d'agowa da sauri, Haseenah ta gani ta fito daga D'akin jikinta duk a mace, a hankali take tafiya kamar wanda tayi wata aikin wahala ta gaji.

Zama tayi gefen da Ammi take sannan ta sunkuyar da kai.

Ammi ta san cewa abinci take so, dan haka ta mik'e ta zuba mata abincin, a kunyace ta kar6a nan ta fara ci ahankali.

Bata ci da yawa ba ta ture gefe, mai da kai tayi ta jingina jikin kujerar sannan ta lumshe idon ta.

Ammi dai Binta kawai take da kallo dan gani take kaman bata da lafiya.

Ji tayi duk zaman gidan ya daga mata hankali, dan haka mik'ewa tayi ta shiga kitchen ta d'auko ruwa da cup sannan ta zura takalmin ta ta nufa hanyar fita daga palour.

Ta bayan flowers din ta bi badan tasan inda zata je ba, ita dai kawai so take ta ganta ita kadai.

Tafiya take can ta hango kujeru guda huɗu tsakiyar da table a karkashin bishiya, wajan shinfid'e yake da grass carpet gwanin sha'awa, dan haka da sauri ta k'arasa ta zauna wajan.

Iska ne mai sanyi ke kadawa, hakan ya sata lumshe idon ta tana mayar da numfashi a hankali.

Tunanin Haseen ne kawai ke yawo cikin ranta, kwana biyu kewar shi kawai take, ko yana wani hali oho?

Ganin bata da amsar tambayar ta ne ya sanya ta yin tagumi.

Advertisement

Ji tayi zaman ma ya gagare ta, dan haka sauka tayi ta kwanta kan grass carpet din ta rufe fuskan ta da gyalen.

Mahmud ne ya nufo garden din gidan hanunshi rike da wayar shi yana dannawa.

Ganin Haseenah kwance ya sanya duk ranshi ya 6aci.

Yafi kusan minti 2 kanta yana kallon ta, bata ma san yana wajan ba, waige waige ya fara yi dan duba irin muguntar da ze Mata.

Ganin ba komai a wajan ya sashi jin haushi, har ya juya zai tafi sai kuma yayi ido hudu da wannan ruwa me sanyin.

Murmushin mugunta yayi a hankali ya ɗauka ya 6alle murfin, saitin fuskanta yayi ya watsa mata.

Wani dogon numfashi Haseenah ta ja da sauri kuma ta mik'e, ganin Mahmud tsaye a kanta yana watsa mata wani irin kallo ya sata jin jikinta ya fara rawa.

Da sauri ta mik'e ko takalmin bata tsaya sanya ba ta ruga aguje.

Fitowar da zata yi Sameer ya hango ta da gudu kaman zata fad'i , tsayawa yayi dan ganin abinda yake faruwa.

Mahmud ya hango ya fito daga wajan yana dariyar mugunta.

Nufar wajan shi yayi ya sa hannu ya cakumo wuyar rigar shi ya manna shi da bango yace" Mahmud me ka wa yarinyar nan?"

"Kaman ya me na mata? Itace ta fada maka na mata wani abu?"

Dunk'ule hannu Sameer yayi da niyar dukan shi, runtse ido Mahmud yayi yana jira yaji saukar naushin, ko me Sameer ya tuna oho ya naushi iska haɗe da furzar da wata iska a bakin shi.

A hankali Mahmud ya buɗe ido ganin me ya dakatar da yayan nashi, ganin shima kallon shi yake ya sashi kau da kai.

Ba abinda Sameer ya iya furta wa Mahmud sai "last warning"

Yana gama faɗin haka ya bar wajan.

Gyara kwalar rigar shi Mahmud yayi sannan ya fice daga gidan.

Can ko Haseenah ta shigo palour lokacin Ammi bata wajan, hakan ya bata damar wucewa D'akin ta da gudu ta mayar da k'ofa ta rufe, manna jikin ta tayi da k'ofar tana mayar da numfashi.

Kusan minti biyu kuka ya biyo baya.

Itakan ta shiga uku ya zata yi? Wannan wata irin rayuwa ce? Daga wanann sai wannan?

Kuka take sossai, tun tana tsaye har ta durk'usa wajan, tunani take ko dai ta gudu ne? To ina zata je? Ta yaya zata musu bayani? Babu.

Ba tada wata mafita illa tayi hakuri ta zauna har lokacin da ta d'ibar wa kanta yayi, abinda yafi kawai shine ta avoiding duk abinda ze had'a ta da Mahmud that's all.

Da wannan shawarar ta share hawayen ta ta koma ta kwanta gwanin tausayi.

Da dare ma dan kar Ammi tayi tunanin wani abune amma da ba inda zata je ko abincin ma da bazata ci ba.

Haka Haseenah ta koma so silent kwana biyu, duk sun kasa gane mata.

Mahmud ko duk hanyar da zai bi ta shiga damuwar shi taki, ko kallon su ma bata yi ballan tana tasan yana wajan.

Canjawar ta ba k'aramin damun Sameer yayi ba, ɗan hirar da yake samu yayi da ita ma yanzu abu ya gagara, dan cin abinci kawai ke fitowa da ita, tana gama ci kuma zata bar wajan.

Sedai kawai ya dau wayar shi yayi ta kallon pics d'inta Wanda sukayi ranan da suka fita.

Murmushi yake tayi nan zuciyar shi ke faɗa mishi duk duniya Haseenah da shi tafi dacewa, rungume wayar yayi a k'irjinshi yana ta faman sambatu.

Mahmud ma dai abun dai ba sauk'i, dan wanann turaren da Haseenah ta bashi ya kasa fesawa, sedai ya saka a gaba yayi ta kalla, wani lokacin tanbayar kanshi yake to meye ajikin turaren ma, what's so special about it, tsuka yayi ya kwanta yana tunani.

Duk Haseenah ta tsaya mishi a zuciya, in Bai ganta ba duk hankalin shi ya tashi, in Kuma ya ganta sai haushin ta ya kama shi inya tuna ganin ta da yayi da yayan shi suna faman murmushi wa juna.

To me hakan yake nufi?

Sai mu biyo dan sanin abinda ke damun Mahmud.

For comments 08144932303

    people are reading<HASEENAH>
      Close message
      Advertisement
      You may like
      You can access <East Tale> through any of the following apps you have installed
      5800Coins for Signup,580 Coins daily.
      Update the hottest novels in time! Subscribe to push to read! Accurate recommendation from massive library!
      2 Then Click【Add To Home Screen】
      1Click