《HASEENAH》PAGE 55&56
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
*55~56*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS- 08144932303
# http://
Follow me on Aysherabbakar
*55~56*
Da sassafe Ammi ta tashi ta shirya bayan tayi sallah, haka Haseenah ma dan Ammi ta sanar mata kan zasu fita, dan haka bata koma bacci ba bayan tayi sallan asuba.
Wajan 7:30 sun gama komai, there breakfast is ready, suna kan dinning suna cin abinci, wajan shuru banda k'aran mugs da spoon ba abunda kake ji, sai jifa-jifa Sameer Kan d'ago kai ya dubi Haseenah, wanda tunda ta sunkuyar da kai abinci kawai take ci.
Ganin ya zuba mata ido ne yasa Ammi gyaran murya, firgigit yayi har spoon d'in hanun shi ya fad'i, hakan yasa Haseenah d'ago wa da sauri.
Haɗa ido sukayi nan ya sakar mata murmushi, yak'e tayi sanann ta cigaba da damuwarta.
8am sharp motar asibiti tazo ta tsaya, fitowa sukayi suka wuce.
Kai tsaye wajan likita suka nufa, bayan sun gaisa da Sameer ne nan ya bada umarni a shiga da Haseenah, wani k'aramin d'aki suka shiga da ita da wata nurse, Sameer da Ammi kuma suna zaune a wani k'aramar corridor Wanda aka k'awata shi da kujeru da flowers.
Komai na d'akin fari ne, bayan likita ya shigo ne yayi nuni wa Haseenah ta kwanta.
Kwanciya tayi ta rufe idon ta, shi kuma ya saka hand gloves sannan nurse ta kunna mishi surgery light.
Hasken ya sa dole Haseenah ta rufe idon ta.
Juya fuskan nata ya farayi yana wasu dube-dube.
Sun d'au kusan hour a haka.
Daga bisani ya d'au wata allura ya mata, sannan ya k'ara d'aukar wata kwalba ya shafa mata wani abu me kamada ruwa amma kaman oil.
Seda yayi 30mns sannan ya umarci nurse din tasa auduga ta goge mata shi.
Sannan ta shiga toilet ta wanke fuskan ta ta fito.
Advertisement
Towel suka mik'a mata ta goge ruwan fuskan ta sannan ta saka takalmin ta suka fito waje tare.
Likitan office d'in shi ya wuce nan ya umarci a kira mishi Sameer.
Bayan ya zauna ne yaka mishi bayani cewa" gobe ma zasu kawo ta a sake mata allurar, amma su taho da shiri saboda nan za'a barta ta kwana, Cox d following day za'a shiga da ita surgery room"
Ba tare da wani 6ata lokaci ba suka koma gida.
Haseenah dai zuciyar ta sai bugawa take, duk damuwar ta kar a samu failure, Ammi ta kula da hakan shiyasa tace ta zauna palour suyi kallo dan Bata so ta barta ita kaɗai cikin damuwa.
Da yamma abokin Dr Abeed ya iso masaukin su Sameer, bayan sun gaisa ne Sameer ya fito ya sanar wa Ammi zasu d'an fita.
Allah kiyaye ta musu sannan suka fice.
Basu dawoba sai lokacin ana kiran magriba.
Dan haka ana isha ya shigo gida suka ci abinci, wanann karon basu wani zauna ba dan Ammi tace su kwanta da wuri tunda ga bayanin da likita yayi.
Washegari Ammi ta d'auka musu duk abinda zasu buk'ata sanann suka fita.
Suna isa aka shiga da Haseenah d'akin jiya, wannan karon bayan an shafa mata maganin rufe fuskar akayi, nan suka mata allura.
Bacci ne ya d'auke ta bata tashi ba sai yamma.
Tana tashi aka buɗe fuskar sannan tayi sallah aka bata abinci, bayan ta gama ne ta koma ta kwanta.
Da magriba Ammi ta shigo ta same ta kwance, zama tayi a gefen ta had'e da rik'e hanun ta, da sauri ta d'ago had'e da share hawayen fuskan ta.
Murmushi ta sakar wa Ammi, bata iya mayar mata ba dan tasan tunani ne fal zuciyar ta.
Misalin k'arfe 9 na dare aka saka mata koren kaya wanda ake sakawa duk wanda za.a wa theatre, fitowa sukayi a d'akin, Ammi ta gani tsaye a bakin k'ofar, idon Haseenah fal hawaye, dan a tsorace take, Sameer kuwa ya hard'e hanun shi a k'irji a zuba mata ido, tausayin ta fal ranshi, kuka ta saka ta rungume Ammi, itama Ammi hawaye ne cikin idon ta k'arfin hali kawai tayi, dan bata son discouraging Haseenah da itama kukan zatayi.
Advertisement
Ganin zasu 6ata lokaci ya sa Sameer k'araso wa ya ja hanun Haseenah, har bakin theatre d'in ya kaita sannan ya tsaya, juyo wa tayi ta dube shi, kana kallon shi kasan shima cikin damuwar yake amma yana son 6oye wa.
Murmushi ya mata sannan ya dunk'ule hanunshi ya buga dai dai saitin zuciyar shi.
Yana nufin *be strong*
Ta Gane abunda yake nufi dan haka ta sakar masa murmushin da seda hak'oran ta suka bayyana. Yayin da hawaye suka zubo kan kuncin ta.
Wani kyau yaga ta mishi, dan be ta6a ganin irin wannan murmushin a wajan ta ba sai yau.
Handkerchief ya ciro ya mik'a Mata, share hawayen tayi sannan ta mik'a mishi, juya wa tayi da sauri ta shige d'akin.
Tsaya wa yayi a bakin k'ofar ya rasa abinda ke mishi dad'i.
Duk abinda suke Ammi na kallon su.
Juyawa yayi ya koma wajan ta ya zauna, dukan su shuru sukayi babu me iya magana.
Haseenah kuwa tunda ta shiga suke faman dank'ara mata allurai da magani, lokaci ɗaya ta gigice ta fita hayyacin ta.
Bata sake sanin inda take ba.
Washegari misalin ƙarfe 10am na safe aka fara aiki wa Haseenah, basu suka fito ba sai 1:30 na rana.
Lokacin da Sameer da Ammi suka shiga an riga da an nad'e mata fuska da bandeji, 'yar robar da ake sawa kawai shine a fili wanda zatana cin abinci ta wajan da kuma numfashi.
Bacci sossai take yi, zama gefen ta Sameer yayi Ammi ma ta zauna a d'aya gefen, dukan su babu wanda yayi magana.
Zaman kurame kawai sukayi, fita Sameer yayi dalilin kiran wayar shi da akayi.
*Nigeria*
Haseen da ka ganshi kasan baya cikin nutsuwa, duk ya fita hayyacin shi kamar ba shi ba.
Mum tayi rarrashi ta gaji ta zuba mishi ido da addu'a.
Saratu kuwa sai abinda ya k'aru, dan wani lokacin tun safe in ta fita bata dawowa Sai 10 na dare.
Mummy kuwa babu abinda take ce mata, ita murna take na 'yar ta ta shigo gari.
Ana haka Saratu ta bud'e wuta akan sai an siya mata mota, hakan yasa Mummy ta samu Abba ta sanar mishi amma ko kulata beyi ba.
Haushi ya kamata ta fice nan ta ba ma Saratu key d'in Tata motar kan ta dauka taje duk inda takeson zuwa.
Dad'i ya cika ta ta rungume Mummy Dan murna.
Aaman kuwa na wajan Mummy Zuwaira, yayi ki6a hasken shi ya dad'a fitowa, da ka ganshi ka ga Haseenah, shiyasa duk wani son duniyar nan Haseen ya d'aura wa Aaman, wani lokacin ma tare suke fita yawo.
Haka zasu ta zaga duk inda yasan Haseenah na zuwa ko ze ganta amma shuru, haka zasu gaji su dawo gida.
Mummy ko tausayin shi take dan inya zauna Yana bata labarin abinda zewa Haseenah in ta dawo sai tausayin shi ya kama ta, dan gani take kaman mutuwar ta ta6a mishi k'wak'walwa.
Amma shi kad'ai yasan yanda yakeji a ranshi.
Abba kuwa Mummy ta bud'e mishi wuta dole sai ya gyara musu gida, dan tun gobarar da akayi da mutuwar Umma da Haseenah ta kasa gane mishi, duk ya dad'a sukurkuce wa.
Ko kulata baiyi ba ballantana yasan tana yi.
Haka zata k'arata surutun ta ta k'ara wuta.
Wani lokacin tayi ta zagi ko kallon ta baya yi.
'''Istanbul'''
Seda Haseenah ta kwana biyu sannan ta farka, dan abun da ya fara ba Ammi tsoro, randa ta farka kuwa murna wajan Ammi kaman me.
Haka Sameer ma ya kasa 6oye murnar shi.
Mahmud kuwa ya dame su da waya wai su dawo.
Seda Sameer ya mishi fad'a sannan ya k'yale su.
Plx vote nd comment
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial16 Chapters
The Arcane Archives
Summary For the light had shone too long, the world had lost and forgotten the history which otherwise would have haunted them for eons. The dream ended, the sun blocked, the dark clouds rose and with them, the fate began to twirl in peril. It was in the winter of Hoinbo, the year 1230 that the long forgotten powers moved and with them, the world will willingly or unwillingly move. Official Website - Faster Releases If you enjoyed the story, and wanted to cheer up the author guy, the very guy who is writing this sentence, then go to the bottom of the fiction page. There'll be 5 empty stars for you to fill. Rate my work, and I'll sleep giggling to myself. And, if you can spare a minute, please vote for The Arcane Archives on TopWebFiction - It's a one click vote - no need to register. TopWebFiction Have a nice day bud Kanna
8 210 - In Serial300 Chapters
Etudie Perpetuity
Cas is a gifted college senior who knows over a dozen languages, studies all sorts of subjects, and has an amazing memory. His only problem? He has no idea what to do with his life. One night, he falls into a river and finds himself reincarnated as an elf in a prehistoric fantasy world. Now, Cas must use his experience and wits to overpower the elements and conquer the supernatural mysteries that plague the world! New chapter every day! Get extra chapters and perks on my patreon: patreon.com/peacefulcatastrophe Join my public discord server to hang out and chat: https://discord.gg/rjRczcpAcu
8 236 - In Serial10 Chapters
Ultra Mega Dragon Divine Obliterating Sect
Rip and tear until it is done. Red wants to get into the prestigious Ultra Skyward Dragon Peak sect, but he isn’t rich or powerful enough to get in. So, his only choice is the only dungeon in town. Unfortunately, the Blood River dungeon is known to eat through hundreds of adventurers per day and drop the best prizes for the lucky few survivors. So, if he wants to enter the best sect, he needs to enter the toughest dungeon and come out on top. Unfortunately, the desk clerk in charge of recording entries into the dungeon won’t let him in because of morals. So, what if Red is lvl1? He’ll rip the A rank dungeon apart and leave the party he’s stuck with behind. Who would want to adventure with a psychic paraplegic, a battle-crazy cultivator addicted to monster implants, a psychotic woman too close to her familiars, and a stoic from a demonic sect? At least they seem strong and more than willing to let him lead the charge.
8 157 - In Serial11 Chapters
Chronicles of Unia: Rise of the Empire
A reincarnator from earth wakes up in the magical world of Unia, where humanity has been driven to the brink of extinction and the magical knowledge to properly protect it has been lost. Follow the journey of Cyclos on his adventures to rediscover the lost magics and guide humanity by building an empire to last ages.
8 75 - In Serial200 Chapters
Face Claim Part II
Just the second part of my Face Claims Saga. Hopefully this will also help you pick a face claim for your stories.
8 169 - In Serial6 Chapters
Mujahadah
"Aku nak move on." Bibir milik Qurrotun Inn tak pernah lekang dengan ucapan sebegitu."Aku dah bosan dengan move on kau tu." Komen Farhana yang merupakan kawan baru yang paling rapat sejak Inn pindah sekolah.Bibir mudah menyebut tapi hatinya masih berbolak-balik dek kerana dicengkam dengan perasaan yang mendalam.***"Saya solat 5 waktu Alhamdulillah cukup,tapi saya banyak buat dosa.Saya nak berubah, tapi susah. Ustaz tolong beri tips untuk saya."Luahan itu ditulis atas kertas kecil oleh Ahmad Seth Yusuf sebaik sahaja Ustaz Syafi'e membuka sesi soal jawab setelah selesai talaqi kitab di surau sekolahnya.
8 91

