《HASEENAH》PAGE 49&50
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
Da Allah ina me bada hak'urin rashin jina da akayi na wasu kwanaki, hakan ya faru ne sakamakon wasu uzurori da nakeyi da kuma rashin wuta,wanda ke kirana da kuma wa'yanda suke mun magana privately Dan jin dalilin rashin ganin post Dina na gode sossai da kulawarku da kuma soyayyarku gareni da kuma littafi na, i hope my excuses will b considered.
*Team Haseenah*
Haseenah na Nan tana gaisuwa ga masoyan ta, kuma ta gode da tausayawar ku gareta, tace ku kwantar da hankalin ku Dr Sameer is by her side.
Iya comments d'inku iya d'adin page d'in gaba.
Thnx all.
*49~50*
Haseen bayan sun gaisa da iro me gadi ya dubeshi yace" Baba nazo maka da wata magana ne me girma, da fatan zaka bani had'in Kai?"
Shuru Baba yayi na wasu seconds kaman me tunani sannan yace" ina jinka yaro"
Gyara zama Haseen yayi sanann ya fara cewa" ba wani abu bane ya kawoni baba, Kan mutuwar Umma ce da kuma Haseenah, wanda kowa yake zargin mutuwar akan kunna wutar akayi, ko Kanada wata 'yar masaniya kan faruwar hakan?"
Malam iro shuru yayi, yayin da k'irjin shi yake dukan uku uku, saboda tsananin tsoron dake zuciyar shi, dukda ba wani abu ya sani ba amma yasan halin matar gidan kamar yunwar cikin shi, abinda ya dad'a firgitashi kenan dan yasan ko wucewa ta zo yi tagan su tare da Haseen to Allah ne kawai ze k'wace shi daga cin mutunci.
Ganin ya tafi duniyar tunani yasa Haseen ta6a shi yace" Baba lafiya kuwa?"
A firgice ya d'ago yace" ba komai Haseen, maganar gaskiya bansan komai akai ba nima lokacin ina nan waje naga Alhaji ya fito yana kwalalar wuta"
Haseen ya kula a birkice Baba yake dan haka mik'ewa kawai yayi ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu biyar ya bawa Baba, hannu na rawa ya k'ar6a ya hau washe baki yana an gode.
Hakan ya tabbatar wa da Haseen cewa wannan baban mayen kud'i ne, ta haka kawai ze sa ya ja hankalin shi har ya samu abinda yake so.
Bai sake cewa komai ba ya nufa wajan motar shi ya shiga da niyar barin wajan.
Advertisement
Reverse ya fara yi da nufin juyawa nan ya hango wata mota CRV tazo tayi parking, wani bak'in saurayi ne a ciki bakin shi ma bak'ikk'irin, Bai gama k'arewa na cikin motar kallo ba yaga Saratu ta fito cikin gida.
Wajan motar ya ga ta nufa, sanye take cikin wasu dogayen riga armless, ta d'aura kimono a Kai, kanta yaci uwar attachment, fuskan ta Babu masaka tsinke saboda kwalliya, ga uban glass tafkeke data maka wanda ya kusan rufe mata hanci, k'afar ta kuwa high heel ne kalan kayan sai hanunta d'aya rik'e da jaka d'ayar kuma wayar ta ce tana wasa dashi.
Gayen kuwa yana ganin ta ya hau washe baki itama tana mayar mishi, gidan gaba ya bud'e mata ta shiga sannan ya rufe.
Duban shi tayi suka fuskanci juna sannan suka sake sakewa wa juna murmushi ta manna mishi kiss a kumatu.
Zaro Ido Haseen yayi ya k'ame a wajan saboda tsananin kad'uwa, yaushe Saratu ta zama haka?
Kafin ya samu amsar tambayar shi buzzing d'in motar ne ya dawo dashi daga tunanin da ya tafi, k'urar motar kawai ya gani dan bai ma san ta inda suka yi ba.
Jiki a sanyaye ya bar wajan shima ya nufa hanyar gida.
*Abuja*
Bayan kwana biyu da yin aiki wa Haseenah Ammi ta ce wa Sameer a sallame su kawai su koma gida su fara shirin tafiya turkey, tunda ance nan da sati d'aya zasu tafi.
Ba musu Sameer ya k'ar6a musu sallama suka tattara kaya suka koma gida.
Da daddare ne kowa na zaune a palour, yayin da Mahmud ke zaune chan gefe yana buga game.
Haseenah kuwa duk a takure take ganin irin hararar da Mahmud ke zabga mata.
Hakan yasa jikinta yin sanyi ta sunkuyar da kanta k'asa tana hawaye.
Tausayin kanta kawai take dan bata san inda take ba balle tayi tunanin inda zata ga wanda ta sani.
Sameer ne ya sauko daga kan steps, duban shi Ammi tayi sannan tace" son dama Kai nake jira tuntuni akwai maganar da nakeso muyi dakai"
Zama yayi gefen ta sannan ya dube ta yace" Ammi am here"
Nan ta Fara cewa" magana kan rashin jin yarinyar nan nake so muyi, nace why not mu sami malam Kabir yana mata rubutu ko Allah zesa a dace, tunda in Allah ya wuce gaba sukan dawo da jinsu"
Kafin yayi magana Mahmud yayi karap yace" Ammi karku wahalar da kanku da kud'in ku, kuka sani ko dama tuntuni kurma ce?"
Advertisement
Tsawa Sameer ya daka mishi cikin 6acin rai yace" tashi ka fice a nan"
Mik'ewa yayi yana k'ananan surutu ya haye sama ranshi a 6ace.
Tsuka ya ja sannan yace" Ammi nima dama inaso in Miki maganar sai kika rigani, yanzu da asuba in mun had'u a masallaci zan tsayar dashi in mishi bayani sai muji yanda abun ze kasance"
Nan suka cigaba da maganar yanda tafiyar zata kasan ce.
Tare suka ci abinci sannan kowa ya kama gaban shi.
Dama Haseenah wani d'aki dake jere dana Ammi aka gyara mata.
Seda ta gama cin kukan ta sannan tayi nafila raka'a biyu sannan ta kwanta.
Bayan anyi asuba ne Sameer ya tsayar da malam Kabir ya mishi bayani, ya gamsu da bayanin shi sannan yace yau ze Fara mata rubutu zuwa k'arfe goma zai shigo mata dashi gida.
Nan sukayi sallama ya koma ciki.
Ammi bayan ta idar da sallah ta fito da niyar tashin Haseenah, nan ta hangota zaune kan sallaya , murmushi tayi ta juya ta koma.
Nan Haseenah na idar wa ta koma bacci.
K'arfe bakwai da rabi ta tashi a firgice, sakamakon mafarkin Umman ta da tayi, kuka ta saka tana 6ari, ta rasa da wani bakin zata yi bayani, waye ze Gane halin da take ciki? Wa ze mayar da ita cikin dangin ta? Ina zata ga Haseen d'in ta? Ina zata ga Mummy Zuwaira da su Umaimah da Baby, ga Aaman d'inta ma?"
Wanann abubuwan suke sata kuka.
Mik'ewa kawai tayi ta shige toilet, wanka tayi ta fito sanann ta zura dogon riga cikin kayan da Sameer ya siya mata ta fito, dan ko mai bata shafa ba balle taje garin kallon madubi dan ta dena kalla.
Fitowa tayi ta lek'a d'akin Ammi amma bata nan, palour ta fito nan ma ba kowa, kitchen ta lek'a Nan ta hango Ammi tana k'ok'arin had'a kayan breakfast.
Shiga tayi sannan ta tsaya bayan Ammi.
Knocking k'ofar tayi, da sauri Ammi ta juyo, nan suka sake wa juna murmushi kawai.
Nuna mata kujera Ammi tayi, girgiza kai tayi sannan ta nufa wajan ta d'au wuk'a ta fara fere dankalin da Ammi ta d'ebo.
Tare suka gama komai, nan taje da kanta ta jera su kan dinning ta dawo tayi wanke wanke ta goge wajan.
Shirin da tayi kan table ya burge Ammi, dan haka ta tsaya kawai tana kallon ta.
Yanda Ammi taga Haseenah ta iya sarrafa ko wani na'urar girki da tsarin shirya table hakan ya tabbatar wa Ammi ba daga gidan talaka ta fito ba, to ina iyayen ta suke?
Sallamar Malam Kabir ne ya katse wa Ammi da tunanin ta.
Nan ta bashi umarnin shigowa, hanun shi d'auke da robar swan k'arama, rubutu ne aciki.
Bayan sun gaisa ne yayi wa Ammi bayanin yanda za tayi amfani dashi.
Nan Ammi tace kaga dama ba abinda ta ci sai a fara amfani dashi yanzu.
Nan sukayi sallama ya fice.
Haseenah dake zaune gefe suka haɗa ido da Ammi, da hannu Ammi ta kira ta nan ta taso ta zo.
Cup Ammi ta d'auka ta zuba mata rubutun sannan ta sake tofa addu'a ta mik'a mata, Bismillah tayi itama dukda batasan na meye ba ta shanye.
Kar6an cup d'in Ammi tayi ta ajiye sannan ta jawo Haseenah ta sunkuyar da ita had'e da kwantar da kanta kan cinyar Ammi, kad'an ta zuba a murfin goran sannan ta d'an zuba kad'an cikin kunnen Haseenah, seda ta tabbatar ya shiga sannan ta juya ta zuba mata a d'ayan.
Murna ne fal zuciyar Haseenah dan ta gane ko na menene.
Dama kullum setayi addu'a Allah dawo mata da kunnen ta.
Lokacin ƙarfe goma harta gota.
Da yake weekend ne suna ta bacci.
A tare Sameer da Mahmud suka sauko k'asa.
Gaida Ammi sukayi sannan Sameer ya dubi Haseenah ya sake mata murmushi, sunkuyar da kanta kawai tayi.
Idon Mahmud ne ya kai kan table, zaro ido yayi haɗe da furta" wow, Nice deco"
Dariya Ammi tayi sannan tace" k'anwar ka ce tayi"
6ata rai yayi ganin ance wannan mummunar ce k'anwar shi, har zeyi magana yaga kallon da Sameer ke mishi hakan ya sashi yin shuru.
Nan suka hau table d'in suka fara cin abinci.
Bayan sun gama ne Ammi take sanar dashi ankawo rubutun harta fara sha.
Dad'i sossai yaji sannan yace Allah ya sa a dace.
Mik'ewa Ammi tayi ta koma d'aki yayin da Mahmud ya nufa wajan computer ya fara game.
Haseenah kuwa zama tayi a takure waje d'aya.
Hakan ya sashi bud'e side drawer ya d'auko paper da biro ya nufa inda take ya zauna gefen ta sannan ya d'au biron yayi rubutu ya mik'a mata.
For comments only 08144932303
Advertisement
- In Serial430 Chapters
Another World Trip: Journey with My Cat and an Otaku Loli Goddess
Have you ever suffered from cultivation tropes including but not limited to: Arrogant young master living waaaay longer than they should? Genius MC turned trash turned genius again? Peanut galley and everyone else lacking common sense and NOT being called out on their bullsh*t? The MC themselves lacking common sense several times? Cool characters we meet but NEVER see again? Then you're in luck! Here at Another World Trip: Journey with My Cat and an Otaku Loli Goddess we spit in the face of our most hated tropes over and over and over again with reckless abandon and embrace the ones we love! Join our socially inept MC, his cat and a goddess who made the wrong choices in life and is now paying for it in the best of ways. Don't suffer from the tropes, kick your leg up, relax and laugh your ass off! Discord Link: https://discord.gg/9gntC4N
8 132 - In Serial121 Chapters
Re:Paranoia!
Asylums. Narcotics. Forbidden love. And a whole bunch of mad hatters ready to plunge the world's magical underbelly into unrepairable mayhem. Fortunately, nothing is ever too hard with a system backing you up—especially when your moral values are skewed, and the only enemy standing in your way to the top is time. [WARNING: This novel will contain incest and yandere harem] Discord -> https://discord.gg/mkaJpcaQQ2
8 158 - In Serial6 Chapters
A Royal Warrior
Skela has always been proud of its military might, originally a land of ruthless warriors and evolving to a land of warriors with politics. The kingdom, though not large in terms of land, now boasts thriving farms, a hardy and proud people, and a larger royal family than has been the case in years. The king and queen are in wonderful health, with two twins coming upon the age of eighteen. As a young princess, Alena has many skills under her belt; she is fluent in multiple languages, is well-versed in combat, and is beloved by many. However, her twin brother Krin is an expert politician and leader, utterly ruthless, and has a way of appealing to people's hidden desires. As their parents have yet to name an immediate heir to the throne, the siblings must discreetly battle for the Crown of the Night while winning their parent's favor, Alena utilizing her sense of righteousness and virtue, and Krin, his lack thereof. In her efforts to garner support, Alena finds herself in a new land with strange customs, left wondering at the state of affairs she'll return to.
8 147 - In Serial11 Chapters
Drak's Chronicle (old)
This was my first attempt, leaving it up here for posterities sake and for those who are interested. but new version/novel will be up soon.
8 164 - In Serial15 Chapters
Path of the Outsider
Path of the Outsider is the story of Roland, a university student...who's also gained the ability to travel to and from Hristomver, a world filled with magic and barely stepping into its own age of enlightenment. As the Outsider, he acts as adjutant and advisor to Madeline, a Magister in service to the court of the Kingdom of Straskey, where, in that capacity, he is able to bring the wonders of the modern world to Hristomver. But the times are changing. The Kingdom of Straskey is but a fragment of a greater whole, one of the five splinter kingdoms that were born in the catastrophic fall of their parent state of the Strovian Realm. And from these Kingdoms, men and women, both opportunistic and dutiful seek to reunite the Realm - by the pen, or by the sword. The wheel of fate turns, and no Outsider is exempt from being caught in its wake. And as the tides shift, Roland must grapple with his unique position, and find his trail to blaze, across Earth and Hristomver... Updates every two Mondays, Also posted on SufficientVelocity/Fictionpress
8 133 - In Serial20 Chapters
♧ Revealing The Hidden ♧【America fic】
It's about America having wings. This story is big cringe- Guys I'm gonna make a remastered version when I have time.
8 148

