《HASEENAH》PAGE 45&46
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*45~46*
"Ammi yanzu aka fito da ita"
Kashe wayar yayi ya mayar cikin aljihun ward coat d'in shi.
D'akin da aka kwantar da Haseenah ya shiga, tsayawa yayi gefen ta sannan ya zuba mata ido.
Ko numfashin ta ba.a gane wa da alama har yanzu bata farfaɗo ba.
Dan haka juyawa yayi ya fita, kai tsaye gida ya nufa dan ji yayi ba zai iya aikin ba gaba ɗaya.
Da k'yar ya samu ya ci abinci sanann ya kwanta yayi rigin gine fuskar shi na kallon ceiling.
Lumshe idon shi yayi kaman me bacci, yakai kusan awa ɗaya a haka ba tare da ya gyara kwanciyar shi ko ya buɗe ido ba.
A haka bacci ya d'auke shi.
Jin anyi kiran sallar k'ofar gida kuma Ammi bata ga fitar shi ba yasa ta tura Mahmud ya duba shi.
Da gudu gudu ya koma saman a hankali ya tura k'ofar haɗe da sallama.
Ganin ya na bacci ko takalmin k'afar shi bai cire ba ya sa Mahmud k'araso wa ya fara buga pillow a hankali.
Bud'e idon shi yayi da sauri ya mik'e ya zauna Yana waige waige.
Ganin Mahmud yayi gefen shi tsaye yana gyara kwalar jallabiyar jikin shi.
Da sauri shima ya duba agogon da ke manne jikin bangon, ganin lokacin sallah yayi har ana k'ok'arin shiga ya sashi mik'ewa da sauri ya shige toilet ba tare da ya sake duban yanda Mahmud yake ba.
Haushi ne ya kama Mahmud ganin yayi banza dashi, hakan yasa Mahmud tura baki gaba yana faɗin" mutum sai miskilan ci kuma...
Bai k'arasa ba yaji daga toilet Sameer yace " i can hear u"
Da gudu Mahmud ya fice daga d'akin dan yasan in ya fito ya same shi ba makawa sai ya mare shi.
Advertisement
*KANO*
Tun wannan ranan Mummy Bata sake gigin zuwa gidan Mummy Zuwaira ba, seda ta d'au kusan sati sannan kamanin ta suka daidai ta.
Amma ta d'au alwashi ko ta wani hali saita kar6o shi.
Dan haka hankalin ta kwance ta cigaba da hidimomin ta.
Motar Haseenah kuwa lullu6e wa Mummy Zuwaira ta sa akayi cikin garejin gidan tace an barwa Aaman.
Haseen dake zaune ya dubi Mummy Zuwaira yace" wannan motar Ba wani Aaman ɗin da za.a Bama, motor ta Haseenah ce dan haka babu me shiga"
Cike da mamaki Mummy Zuwaira ta dube shi Tace" Haseen wata Haseenar kake magana? Bayan kasan ta rasu to za.a ajiye abu ne ana kalla tunda ga k'aninta nan"
"Mummy Haseenah na Nan da ranta, kuma ina ji ajikina zata dawo, dan kullum seta zo min a mafarki munyi hira da ita"
Dukan su daga Mummy Zuwaira har Umaimah da Baby kallon mamaki suke mishi baki bud'e, dan ba don sun san Haseen lafiyar shi k'alau ba to zasu ce bashi da cikekken hankali.
Gyara zama Mummy tayi ta dube shi a nutse tace" Haseen meyasa kake irin wannan maganar? Baka san k'addara bane? Kaifa da hanun ka ka saka Haseenah cikin kabari amma kake irin wannan maganar?"
Girgiza kai yayi cike da rauni yace" Mummy na San da haka, amma Ni nasan Haseenah na tana nan da ranta kuma zata dawo"
Ya k'arasa maganar yana zubda hawaye.
Umaimah ma kukan ta fara nan ta mik'e ta bar wajan.
Haseen kullum jin mutuwar Haseenah yake sabo.
Kuma har yau inya fita duk hanyar da yasan Haseenah na bi sai ya bi ta wajan.
Abba kuwa gaba d'aya ya gama sukurkuce wa, dan sai yadda Mummy tayi dashi, kashe musu kud'i yake kaman ba gobe, amma duk da haka saita mishi k'orafi.
Saratu kuwa tunda ta gama secondary school ta yi sabin k'awaye, kullum sai sunzo wajan ta.
Wani lokacin su wuni a gidan wani lokacin kuma su fita da yamma sai wajan tara na dare zasu dawo.
Advertisement
Mummy bata ta6a tanbayar ta inda take zuwa ba kuma meyasa take kai dare ba, dan tace 'yar ta nitsatstsiya ce kuma she's 18, atleast she's matured enough.
Dan Haka tana da 'yancin kanta.
Hakan kuwa ba k'aramin dad'i yayi wa Saratu ba dan suna fita zasu je su canja kaya su bazama zuwa gari sai yanda Allah yayi.
Mum Haseen kullum cikin rarrashin Haseen take, wani lokacin ya kula ta wani lokacin kuma yayi shuru.
Shidai yasan Haseenah tana nan kuma yana zaman jiran ta.
Amsar da yake bawa Kowa kenan.
Mummy Zuwaira ce ta Kira Haseen tace ya zo gida ya same ta.
Hakan kuwa akayi, bai wani d'au lokaci ba ya same ta.
Zaunar dashi tayi bayan ya gama cin abinci sannan ta dube shi Tace
" Haseen kan maganar k'onewan su Haseenah ne, daman na bari sai komai ya lafa sannan zamu d'aga maganar, da farko dai kasan an samu cylinder da kuma empty lighter, hakan nan masu bincike sun mun bayani kan cewa kunna wutar akayi, ko ba.a faɗa ba kasan aikin wanene, to amma bamu da cikekken shaida kan wannan abu, dan haka nakeso ka taimaka ka je gidan kayi tambayoyi wa masu aikin gidan ko za.a samu wani information akai"
Tunda ta fara maganar kan shi yake sunkuye sai da ta gama ya d'ago idon shi ya kad'a yayi ja, duban Mummy yayi yace
" Ni na riga da nasani abun nan shirya wa akayi, amma nayi shuru saboda bansan ya binciken ya kasan ce ba, amma in Allah ya yarda daga yau zan fara bincika wa ko Allah zaisa a dace"
Gyad'a kai Mummy tayi alamar gamsuwa sannan suka cigaba da tattaunawa.
Bayan kwana uku da aiki wa Haseenah ta dawo normal, Amma ba halin motsi dan ance sai bayan kwana biyar za.a warware.
Haka dai take kwance gashi ba halin magana balle tayi tad'i da mutanen wajan.
Haka zata farka ta gaji ta koma bacci.
*2 Days later*
Yau ne za.a warware aikin da akayi wa Haseenah, dan haka tun safe Ammi da Sameer suka iso asibitin, wajan k'arfe takwas Dr Abeed ya iso.
Kai tsaye office d'in Sameer ya wuce, nan ya same shi zaune ya kife kai kan table..
Gaisawa sukayi sannan suka mik'e suka fice gaba d'aya.
A&E suka wuce nan suka shiga, Ammi suka hango zaune gefen ta tana matsa mata k'afa.
Gaisheta Dr Abeed yayi sanann ya kira nurses.
Fara warware wa yasa suka fara yi, tunda aka fara warware wa k'irjin Sameer yake dukan tara tara.
Runtse idon shi yayi hanun shi na rawa kaman shi ke warware wa.
Zuba mishi ido Ammi tayi tana kallon shi, mamaki take ganin yanda Sameer ya canja lokaci d'aya.
Ana gama warware wa duka suka zuba mata ido.
A hankali Haseenah ta fara bud'e idon ta, dishi dishi ta fara gani daga bisani idon ta ya washe, binsu da kallo ta fara yi tana waige waige.
Ba laifi an samu progress but ba yanda ake tunani ba.
Mirror Dr Abeed yasa aka d'auko sannan suka mik'a wa Haseenah.
Lokaci ɗaya gaban ta ya fad'i dan tunda abun ya faru bata ta6a ganin fuskan ta a madubi ba balle tasan ya kamannin ta ya koma ba.
Ganin yanda ta dawo ya sata razana ta sake mirror a k'asa, nan ya tarwatse wanda ya razana kowa a d'akin.
Rufe fuskan ta tayi da duka hanun ta guda biyu ta fara girgiza kai, sai ganin hawaye sukayi na bin hanun ta.
Lokaci ɗaya kuma ta saki kuka.
Juyawa Sameer yayi ya kife kanshi jikin window, wato ba haka fuskan ta yake ba kenan? Ya zaiyi ya dawo mata da farin cikin ta? Meyasa ya damu da yawa a kanta? Wata zuciyar tace mishi tausayi.
D'akin gaba d'aya shuru yayi kaman ba kowa, sai sautin kukan ta da ke tashi a hankali wanda ya d'aga hankalin kowa.
Sameer zuciyar shi ta karaya bazai iya juran sauraron ta tana kuka ba.
Da sauri ya fice daga d'akin ba tare da yayi Magana ba.
Hakan yasa jikin su duk yayi sanyi.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial47 Chapters
Aeterna Saga, Volume 1: Walking With Giants
A man in his twenties gets "reborn" in a fantasy world, seemingly with no special abilities. Read on as he and his family go through events that will change the world they live in, for better or worse. Also found in Fantasy-Books, and NovelUpdates.
8 434 - In Serial54 Chapters
Into the Hulk
Space Hulks : vast amagations of wrecked ships, stray astroids, and precious lost technology. Casth through the hell-scape of the Warp for uncountable yeras, Infested with the Damned and the Alien, and hazardous beyond reason, they are incomparable prizes to anyone who can take them over. Ships that would take hundreds of years to build can be pried from their sides in only decades, relics of bygone eras fetch fortunes large and small, and every data-vault could contain secrets to shake the foundations of reality.Part 3 of the Aegisverse Saga. Second Person is used throughout. If that isn't kosher with you, best to back out now. A Warhammer 40,000 Dark Heresy / Deathwatch fanfictionComplete, with a total of 53 chapters. On the series - This series was first written as a Choose Your own Adventure (CYoA) on the /r/HFY forum. The between chapter votes have been omitted, as they are not part of the story, despite their influence on it. On the the Author's notes - These were included in the original document, and are included here for the purpose of completeness. Spelling, grammatical, and formatting changes have been made in the process of archiving this story and re-formatting it for publication on Royal Road. None of the contents of the story has been substantially affected. Cover by gej302!
8 119 - In Serial9 Chapters
Tale of Careless Goddess
After getting fried to death, the woman appointed as a goddess in the newborn world. Using her new power will she create her own cult? built an unstoppable empire ? or just sleep thought the entire time? The cover picture MTGA fan art found taken from google.
8 98 - In Serial10 Chapters
Eden's Promise
A World teeters on the precipice of destruction, in a desperate attempt to escape their fates they send their chosen hero to the world of the gods. A Hero who carries the name of her world as well as the hopes of everyone in it. A Tower that can only be ascended by the chosen and the powerful. To ascend is to become closer to the gods. To ascend is to obtain all that you desire. What truths will Sola uncover about herself and her world as she ascends the Tower of Eden? Burdened by the hopes of a world, what lengths will she go to to fulfill her purpose? Hey all, Z here This story is something I've been sitting on and thinking about for a while, and now with the new year I finally have the time to give a proper attempt at writing it. Any feedback or criticism is appreciated, and I hope that people enjoy the story!
8 161 - In Serial24 Chapters
Revolutions
Detective Sergeant Tarine Dominion, of the RCMP, is set to participate in the Intergalactic Bowling Competition on Earth when a dead body is found in the men`s washroom at the Revolutions bowling alley. Her superior insists she take over the murder investigation and resign from the competition. Much mayhem, murders, and intergalactic politics ensue.
8 199 - In Serial7 Chapters
spin my feelings - Chris sturniolo
"all because of a game."Who knew a stupid game could make someone's life go wrong? But maybe it wasn't wrong and it was right after all..?
8 120

