《HASEENAH》PAGE 41&42
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
Godiya ga duk wani masoyin wannan littafi, na gode sossai da kulawarku da kuma karfin gwiwar da kuke bani koda yaushe, *Rumanah(Auta) kin kasance ɗaya daga cikin masoyana wanda ke mun magana ta pc, na gode da soyayyarki gareni da kuma addu'oinki, nima ina sonki sossai, ban manta da kuba*
Mom of 12
Raleeyerh
Hapcy
Ummu nawwar
umcee
Nanush
hauwee
Da duk sauran wanda ban ambata ba kuna raina, Allah bar zumunci da k'auna.
*41~42*
A firgice ya farka yana faɗin" gawa ta tashi, jama'a fatalwa"
Dariya da haushi ne suka cika Sameer, dubanshi yayi yace" Allah Mahmud in baka nutsu ba ranka zai 6aci"
Shiko sai zare ido yake yi a tsorace, juyawa yayi ya kalli back seat ya ga wayam, marairaice wa yayi kaman zeyi kuka yace" yaya na faɗa maka fatalwa ce baka yarda ba, gashi yanzu ta 6ace"
Nuna mishi k'ofa yayi yace" get out "
Sum sum ya fice zuciyar shi na bugawa.
Suna shiga gida sameer ya hango Mahmud zaune gefen Ammi kaman zai d'ale cinyarta, duk yayi kalan tausayi yace" Ammi wallahi da gaske nake miki"
Hararar da sameer ya zabga mishi ne ya sashi yin shuru.
Bayani ya shiga yi wa ammi, tunda ya fara magana ta nutsu tana jin shi har ya gama.
Duban shi tayi tace" son yanzu wani mataki ka ɗauka?"
"Tana asibiti na barta wajan Dr Abeed, yanzu firstly sai an Fara treating k'onan da tayi, wanda yace indai za.ayi amfani da most effective requirements bazata wuce 2weeks ba zata warke, secondly Kuma shine theatre da za.a mata a fuskanta in order to gain her normal look"
Gyad'a Kai Ammi tayi sannan tace "hakan ma yayi, da safe zan bika muje in duba ta"
Nan suka mik'e kowa da abinda yake sak'awa a ranshi.
Asibiti kuwa Haseenah oxygen aka saka mata, aka saka mata robar abinci ta hanci.
Ba tare da 6ata lokaci ba Dr Abeed ya sa nurses suka cire mata rigar jikinta aka saka mata na asibiti, bayan sun shafe mata jikin da wani magani mai ruwa.
Aaman kuwa kwana biyu yayi aka dawo dashi gida inda Mummy Zuwaira ta amshe shi.
Side d'in Ummah kuwa ana kan bincike yanda aka gano rusted gas cylinder da kuma fasashshen gidan lighter.
Kowa yayi tunanin cylinder Ummah ce, amma abin mamaki da aka duba sai aka ga Tata a kitchen, nan fa mamaki ya cika kowa.
Advertisement
Hankalin Mummy kuwa yayi dubu ya tashi, dan tasan ita kam Tata ta ƙare.
Gashi babu wata hanyar da zata bi ta fita ta siyo wani, wata dabara ce ta fad'o mata da daddare ta zaga ta shiga side d'in Abba ta bud'e store ta d'auko wani.
Tun daga ranan aka saka wa Mummy Ido, bayan masu bincike sun tabbatar da cewa kunna wutar akayi ta hanyar buɗe gas ɗin sannan aka cillo wuta, sanadiyan wutar kenan.
Hankalin Mummy ya kwanta tunda ta samu hanyar wanke kanta.
Bayan anyi sadakan uku ne washe gari mummy Zuwaira tazo ta ciccire kayan Aaman wanda yake store da d'akin shi, sannan ta sa aka kar6o spare key wajan Abban su na motar Haseenah, nan ta loda kayan a ciki ta fito tana faman sharan hawaye hanun ta riƙe da Aaman.
Mummy ce ta fito ta dube ta sannan tace" Malama ina zaki kai motar ko ya zama naki kenan?"
Cike da takaici Mummy Zuwaira tace" Lauratu karki furta abinda zaki kasa maimaita da anjima, dan zan miki illa, sannan karkiyi tunanin kinci bulus, i will surely get back to u, wallahi ki kuka da kanki"
Tana gama faɗin haka ta shige motar ita da Aaman suka bar gidan.
Mummy kuwa ranan murna ce fal zuciyar ta, dan yanzu ta tabbatar gida ya zama nata, dukiya ta zama Tata, miji ya zama nata.
Dan haka suka baje kolin su ita da Saratu, ga wasu sabin k'awayen da tayi wanda koyaushe gidan da mutane, wani lokacin kuma in suka fice shikenan bazata dawo ba sai dare.
Abba na gani amma bai isa yayi Magana ba, dan a gaban k'awayen ta zata mishi masifa.
Dan haka ya dena cewa komai ya zuba mata ido.
Tunda akayi rasuwar babu wanda ya sake takowa gidan, can gidan su Ummah suka cigaba da kar6an gaisuwan su.
Dan haka Mummy ta dad'a sakin jiki ba abinda ya dame ta.
Mum Haseen ma tunda haka ta faru bata sake kiran Mummy ba balle ta tako k'afan ta.
Haseen kuwa ko yaushe zaka ganshi d'auke da wayar shi yana kallon hotunan da yayi wa Haseenah last had'uwan da sukayi kafin ta rasu.
Wajan aiki ma ya dena zuwa kullum yana d'aki, da yake a Company daddy shi dama yake sai bai matsa mishi ba, dan ko bai dena zuwa ba shi zai dakatar da shi, dan yana buk'atan nutsuwa.
Haka zai zauna ya zuba ma hoton ido, wani lokacin yayi ta sambatu, in hakan bai mishi ba kuma sai kuka.
Randa abun ya motsa kuma haka zai wuni ba magana, ko abinci baya ci, sai dai Mum d'inshi tayi ta lallashi sannan zai ci yayi wanka.
Advertisement
Da taga abun na son zama matsala sai ta kira best friend d'inshi Habeeb tace dan Allah yazo yana zama da Haseen suna d'an fita yana zagawa ko damuwar shi zata ragu.
Hakan kuwa akayi.
Da safe kuwa Ammi ta shirya dan zuwa duba Haseenah, fitowa tayi palour ta hango Mahmud sanye cikin farar riga da three-quarter, yayi kyau sossai hasken shi ya dad'a fitowa.
Duban shi tayi tace" Auta muje ka rakani asibitin mana"
Bai san sanda ya fad'o daga kan kujerar ba yayi zaman dirshan, zare ido yayi yace" Ammi Allah ba zani ba, ki tafi kawai Allah kiyaye hanya"
6ata rai tayi tace" kaga banason shashanci kaji ko?"
Marairaice fuska yayi sannan yace" nikan ma Ammi cikina ciwo yake yanzu ma da kika ganni nan ke nake jira dama ki bani magani"
Ta sani sarai k'arya yake dan haka tace" kaje wajan yayan ka mana ko yau nice likitar?"
Da sauri ya mik'e yace" barshi ma na tuna inada shi a d'aki na, sai kun dawo"
Bai jira me zata ce ba ya haye sama da gudu har yana tuntu6e.
Dariya Ammi tayi a ranta tace " Allah yaye maka"
Lokacin da Ammi ta ga halin da Haseenah ke ciki saida ta zubda hawaye, dan duk yanda Sameer ya so ya describing Mata situation d'in da take ciki abun ya wuce nan, in ba faɗa maka akayi ba bazaka yi tunanin mutum ne ba.
Dan saboda maganin da aka shafa mata cikin net aka saka ta ga oxygen mak'ale a hancin ta.
Ganin bazata iya juran ganin ta ba ya sata ficewa daga asibitin.
Kano kuwa bayan an gama sadakan bakwai ne Mummy Zuwaira ta rok'a Abba ya bar Mata Aaman, ba tare da wani tunani ba ya amince mata.
Aiko komawar shi gida knan ya samu Mummy zaune palour, tana ganin shi ta mik'e dama shi take jira, duban shi tayi a wulak'an ce tace" ya na ganka hannu na bin cinya ina yaron yake?"
A sanyaye yace" na bar musu shi a wajan su ai"
Wata zagi Mummy ta auno tace ya koma ya d'auko shi ita ya kamata ya rik'e shi.
Wucewa yayi ya barta nan tsaye tana surfa masifa da ashar.
Dan yanzu target d'inta kan Aaman ne, dan tasan tunda shi namiji ne to in Abba ya rasu shi zai janye duk kason.
Dan haka idon ta ya rufe bata jira komai ba ta d'au gyalen ta ta shige mota ta fice a gidan.
Bata tsaya ko ina ba sai k'ofar Mummy Zuwaira.
Tun daga waje ta fara fad'in a fito mata da yaron miji.
Babu wanda ya kula ta har ta iso palour.
Su Umaimah da baby da mummy Zuwaira ne zaune suna hira, sai Aaman dake kan cinyar Mummy tana bashi tea.
Nan Mummy ta hau girgiza tana cewa a bata shi.
Ba wanda ya kalli inda take balle Su san akwai wata halitta a wajan.
Hakan ya dad'a 6ata mata rai.
Da zafin jiki ta nufa Mummy Zuwaira ta sa hannu da nufin janyo Aaman.
Carap Mummy Zuwaira ta rik'e hanunta sannan ta ajiye Aaman gefe ta mik'e.
Duban Umaimah tayi da ita ma jikinta ya hau rawa dan ji take kaman ta kashe Mummy.
Mummy Zuwaira tace" Umaimah kulle mun k'ofar palour"
Kaman jira take nan ta rufe k'ofar, Mummy Bata San nufin hakan ba shiyasa bata damu ba.
Sai ma ta shak'o wuyar Mummy Zuwaira.
Aiko Bata yi aune ba taji saukar marin da ya gigita mata lissafi.
Juyawa tayi taga waye da wanann aikin, Umaimah ta gani tsaye jikin ta har tsuma yake.
Ga baby rik'e da sandar moper, d'irka Mata Baby tayi a baya nan Mummy ta saki ihu.
Sake ta Mummy Zuwaira tayi ta koma gefe ta zauna.
Yayinda Baby da Umaimah suka kayar da Mummy k'asa, Nan suka haye kanta suka hau dukan ta ta ko ina.
Seda suka tabbatar taji jiki sannan suka sauka.
Lokacin Mummy kuka take tana numfashi sama sama.
Duban ta Mummy Zuwaira tayi sannan tace" Ni banida lokacin fad'a dake saboda inada dai dai ke, sannan ko kasheki sukayi ba wanda ya isa ya kamani tunda ke kika shigo har gida"
Ta kalli su Umaimah, nan suka ja Mummy suka fice da ita waje.
Kuka sossai take ganin lokaci kaɗan sun sauya Mata halittar jiki da fuska.
Yanda bakin Mummy yayi suntun dama gata da dogon baki, inka ganta ko bakada niyar dariya ba zaka san lokacin da zai k'wace maka ba.
Da k'yar ta ja jiki ta shige motar ta ta fice.
Tana shiga gida ta tarar Saratu zaune a palour,tana ganin Mummy ta tuntsire da dariya tace" Mummy hatsari kikayi ne?"
Bata kula ta ba ta wuce d'aki.
*Abuja*
Yau kwanan Haseenah bakwai a asibiti, jiki da sauk'i sossai dan an cire mata oxygen din, sai dai har yanzu ta hanci ake bata abinci dan ba halin ta6a ta.
Magani kawai ake shafa mata a mayar a kwantar da ita.
K'unan kuwa har ya fara 6arewa da kanshi, har na fuskan ta ma.
Koyaushe sameer kan shiga duba ta fiye da sau biyar.
Ammi ma takan je, Mahmud kuwa da Ammi ta matsa mishi yaje sai ya fashe da kuka ya fara cewa"....
Please vote nd drop ur comments
Advertisement
- In Serial167 Chapters
HP: A Magical Journey
Follow Quinn West, who finds himself in the world of Harry Potter, but are things as they seem, is the world he has landed in the same as the one he once read about.
8 192 - In Serial36 Chapters
Old Version - The First Magician
INDEFINITE HIATUS I always seem to make these too long when I ask for peoples opinions so I’m not gonna try an exciting description anymore but instead just give you an idea of what to expect. First off, this is my 2nd attempt at a story but my foundation for this one is much better than the 1st already and I see this going much further and so far its coming together much faster and easier. So please excuse me if things are not up to publishing standards. Also I tend to confuse your, you’re and so on so sorry to people that triggers ahead of time. The First Magician follows the story of 15 year old Alex in a post apocalyptic rpg-ish world in the near future. Earth was transformed, monsters appeared and people began being able to use Ki but could not figure out how to use magic. Alex ends up becoming the first human able to use magic through a series of events and sets in motion events that will change the very future of the human race. He will be somewhat OP simply because he is the only human (at least to start, who knows about later?) who is able to use mana. Many classic RPG elements have been removed. I didn’t want the story to be like all of the other lit rpg stories on RRL but it also makes the writing easier for me hence the watering down of rpg elements. UPDATES: I am doing this to relieve stress and for fun so I will release chapters when I can. So far though ive managed to keep up with 2 most days. CONTENT WARNINGS: There will be some light language but it won't be insane. I might have some gore later on but am unsure and the same for the sexual content. Sexual content isn't super likely as I doubt I can write it well but I put the tag so people cant yell about it if I add some in the future but forgot to add the tag. COVER ART: Yes it is from the anime Log Horizon. It is a good representation of what earth looks like despite it not being many years in the future. DISCORD: https://discord.gg/s6V3hGV
8 129 - In Serial10 Chapters
To Their Rest
The arid mountains and plateaus of Karshoi have always been a difficult place for life to take root; now it is stalked by the Undying--those who at the moment of their deaths were granted immortality using the souls of others. Sidri, a necromancer trained in the old ways, pursues them in hopes of freeing the sacrificed souls and finding out who is responsible for creating the Undying and tampering with the boundary of life and death. She is joined by Jiriga, a man gifted in the hunting and killing of other people, but who keeps his reasons for helping her secret. But their hunt for the Undying has not gone unnoticed, and there are signs that they might soon become the hunted.
8 82 - In Serial20 Chapters
Prince of Destiny
Karl is the last prince of a royal house that has been overthrown by brutal revolutionaries. Orphaned by the revolutionaries, he was rescued and has been raised in secret by Leevana, a green skinned night-hag, for the past ten years. When Karl turns sixteen and is old enough to embrace his destiny, he and Leevana must set out on a quest to find his royal grandmother. But the depraved new leader of the revolutionaries, Joe Steel, is on their trail... Somewhat inspired by the basic concept of Don Bluth's fairy tale animated feature, purporting to be based on the myths surrounding Anastasia Romanov. I don't think this counts as a fanfiction, because it does not use anyone else's characters and it is in its own self-contained world, but please keep in mind the inspiration. Leevana and Karl are completely original characters, but Joe Steel, the bigger bad, is inspired by Stalin. Maybe let me know if you think it should have a fanfiction tag or not.
8 84 - In Serial19 Chapters
The Sea Tower
Sea witches were monsters of legends, capable of routing armadas and wreaking havoc across entire realms by controlling the weather. It was rumored that even the mighty krakens were under the control of the sea witches. Who, what, or where these witches were, no one knew. But no one sought them out either. The avarice of a mad king leads to the folly of a kingdom. Only a single turret survived the catastrophe, a single tower which protrudes outwardly from a boundless ocean, rumored to house the very creature which wreaked havoc and devastation. Sailors are warned to give the relic a wide berth, for few who have seen the tower ever return to speak the tale, and none who have approached it ever have. Do not approach the tower, they said…
8 195 - In Serial10 Chapters
Coffeeshop × Malum
You see, this wasn't intentional. Michael never planned on making it a routine to order the same exact drink as the cute boy in front of him every day, it just sort of happened.AboardTheBandShip - 2020
8 180

