《HASEENAH》PAGE 39&40
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*39~40*
Da gudu ya sauko d'auke da wata babbar therapy box, d'aga ta yayi ya Kaita d'akin da yake na baƙi.
Shimfid'a ta yayi kan gado sannan ya warware yadin ya bud'e iya fuskan ta.
Nan da nan ya fara bata taimakon gaggawa, sunkai kusan 30mins amma bata sake motsi ba, waya ya ciro ya kira d'aya daga cikin abokan shi, nan ya fara hura mata iska a baki, da k'yar ya samu ta fara tari daganan ta koma ta kwanta.
Juya kai kawai take da hannu, a hankali idon ta ya fara bud'e wa.
Gaba ɗaya ya kad'a yayi jajir, hawaye ke gangaro wa daga idon ta.
Tsura mishi ido tayi kaman me tunanin wani abu, shiko banda sannu babu abinda yake furta wa.
Wani dogon numfashi taja sai kuma bakin ta ya fara motsi kaman tanason tayi magana amma ta kasa.
Dubanta yayi cike da tausaya wa yace" ruwa kike son Sha in kawo Miki?"
Shuru Bata amsa mishi ba, a karo na biyu ya sake faɗin" me kikeso a kawo Miki?"
Nan ma shuru kamar bata jin shi.
Mik'ewa yayi ya shige kitchen ya d'auko Goran ruwa da cup ya fito, zama yayi a gefen ta, yana son bata ruwa amma bai san ta ina zai fara ba, dan yasan jikinta zafi zai mata.
Wata dabara ce ta fad'o mishi, komawa yayi ya d'auko spoon sannan ya 6alle murfin ruwan, zubawa yayi a murfin robar ruwan sannan ya saka spoon ya d'an bud'e Mata bakin kaɗan ya tsiyaya mata.
Nan da k'yar take iya had'iye wa.
Kaɗan ta iya sha sannan ya fara gangaro wa.
Tagumi yayi yana ta faman mata tambayoyi amma shuru.
Advertisement
Hakan yayi dai dai da zuwan Dr Muhammad, ganin Haseenah cikin wannan hali ba k'aramin kad'a shi yayi ba.
Nan sameer ya bashi labarin duk abinda ya faru.
Sossai ya tausaya mata.
Sameer ya k'ara da cewa" gashi ina ta tanbayar ta tayi shuru tak'i magana"
A sanyaye Dr Muhammad yace" aboki ka manta irin wa'yan nan basu magana, wani lokacin ma sukan rasa hankalin su gaba d'aya"
Shuru sameer yayi dan ya kasa furta komai.
Dr Muhammad ne ya dube shi yace" yanzu ya zakayi da ita gashi naga yau zaka wuce Abuja?"
Cike da rauni sameer yace" shine duk tunani na, kawai tafiya da ita zanyi a mata magani har muga abinda Allah zai yi"
Cike da gamsuwa Dr Muhammad yace" these is a good idea Dr, Nima Nan zan cigaba da bincike through internet muga ko zamu samu wata mafitar"
Gyad'a kai Dr Sameer yayi yace" Nagode abokina"
Nan sameer ya mik'e ya haye sama, d'akin k'anwar shi ya nufa ya bud'e wardrobe d'in ta ya Ciro wata doguwar riga mara nauyi.
Fitowa yayi ya dawo wajan ta,amma ya rasa ta ina zai fara canja mata kayan.
Dr Muhammad ne ya dube shi yace" Dr hakuri zakayi ka canja mata, lalura ce kuma ceton rai zakayi"
Gyad'a kai yayi yace" to plx can U excuse us?"
Mik'ewa Dr Muhammad yayi yace" why not?"
Ficewa yayi ya ja musu k'ofar.
Runtse idon shi yayi sannan ya tallafo kanta, a hankali ya fara saka mata idon shi rufe.
A haka ya zura mata, Haseenah kuwa Allah ne kaɗai yasan azabar da takeji amma ba halin magana.
Hakan ya saka ta suma.
Seda ya gama saka mata sannan ya buɗe idon shi, gani yayi idon ta buɗe amma bata motsi.
Da sauri ya d'auki ruwa ya yayyafa mata.
Seda ya gyara mata zaman rigar sannan ya fito.
Dr Muhammad ya samu tsaye a wajan, nan suka tsaya tattauna wa kan yanda zasu ɓullo wa lamarin.
Advertisement
Daga nan sukayi sallama ya tafi.
Mahmud kuwa tunda ya haye sama ya kullo k'ofar bai sake fitowa ba.
Sameer wayar shi ya ɗauka ya danna numbar Ammin shi, nan ya mata bayani, shuru tayi tsawon wasu mintina ba tare da tace komai ba.
A karo na biyu Sameer yace" Ammi Are u there?"
"Yes son, Amma kana ganin babu wata matsala?"
Gyad'a kai yayi kaman yana gaban ta yace" Ammi wallahi inkin ganta saikin zubar da hawaye,very tortured"
"Shikenan Allah kawoku lafiya"
"Amin" yace sannan ya katse wayar.
Kiran wayar Mahmud yayi yana d'aga wa yace" Are u ready to go or I should go alone?"
Da sauri yace " on ma way stepping downstairs"
Bud'e k'ofar yayi a hankali, kanshi ya fara sakowa sannan ya lek'o, ganin ba kowa ya sashi saukowa a hankali a fito.
Seda ya rufe gidan sannan ya nufa motar.
Sameer ya hango zaune ya riga yayi key wa motar ma, back seat ya lek'a ya hango Haseenah kwance idon a rufe.
Shiga gaba yayi kafin ya kulle sameer ya bawa motar wuta.
Kai tsaye hanyar Abuja suka d'auka.
Time to time Sameer Kan juyo dan ganin halin da Haseenah ke ciki.
Mahmud kuwa baccin dole yayi dan inyace ido biyu zasu isa to ba makawa yasan wani abu zai biyo baya.
*KANO*
Mummy Tabi duk wata hanyar da zata bi dan ganin ta d'auko wannan cylinder Amma Abu yaci tura, Mummy Zuwaira da Mummy Saudatu sun kasa sun tsare, ko k'wak'k'waran motsi Mummy tayi akan idon su.
Hakan yasa wuni ɗaya ta fice a hayyacin ta, ina baka san halin ta ba zakayi tunanin mutuwar ce ta girgiza ta.
Haseen kuwa addu'a aka fara tofa mishi cikin ruwa da nasihohi sannan ya samu ya fara magana, amma baya wuce yace eh ko a'a, sai in an mishi ta'aziya yace "ameen" shikenan.
Mum Haseen ce tasa Mummy gaba tana faɗin" haba yaya meyasa baki yi tunanin abinda zaije ya dawo ba kika yanke wannan mummunar hukuncin? Yanzu kina ganin alhaki zai barki ki zauna lafiya? Kina ganin shikenan burin ki ya cika ko? Bayan kinsan Zuwaira da Saudat na raye, wallahi kinyi babban kuskure, kuma abinda hakuri bai baki ba rashin sa bazai ta6a baki ba"
Shuru Mummy tayi badon tayi nadamar abinda tayi ba, kawai shuru tayi saboda kudirin haɗa auran Saratu da Haseen,amma ba don haka ba mum Haseen Bata Isa ta sata gaba tana faɗa mata son ranta ba tunda ba uwarta bace.
Ganin haka yasa mun Haseen cigaba da cewa" ki san yanda zakiyi ki fidda kanki, dan wallahi babu hanuna cikin wannan abu, wannan meye inba son zuciya da zalunci ba? Ke yanzu ko da garwashi ne ya k'ona ki ya zakiji? Ballantana rai kacokan ki salwantar da bayin Allah wanda basu jiba basu gani ba kawai saboda son zuciya da kishin banza duk akan miji, to yanzu in mijin ya sake ki ya zakiyi?"
Da sauri Mummy ta mik'e ta bud'e k'ofar ta nuna wa mum Haseen sannan tace" tashi ki fita tun kafin nayi abinda baki tunani"
Cike da 6acin rai mum Haseen ta mik'e ta nufa hanyar fita, har ta kai bakin k'ofar ta juyo tace" zan tafi amma ki sani duk abinda yaje ya dawo karki nemeni"
Tana kaiwa nan ta fice ta nufa wajan su Mummy Zuwaira ta zauna.
Sai bayan la'asar Sameer suka shiga Abuja, tun kafin ya k'araso ya Kira Dr Abeed dake aiki a asibitin FMC ya sanar mishi da abinda ya faru.
Saboda haka suna isa asibitin ya wuce, an rigada an gama komai yana isowa aka d'auko gadon marasa lafiya aka d'aura Haseenah suka wuce da ita ciki.
Saida ya gama duk abinda zeyi sannan ya dawo ya ja motar ya nufa gida, har lokacin Mahmud bacci yake yi dan yana farkawa zai koma ya kwanta.
Suna isa Sameer ya d'aga hannu ya kwad'a wa Mahmud mari saida hular kanshi ta tuntsire, a firgice ya farka yana faɗin....
Plx vote nd drop ur comme
Advertisement
- In Serial155 Chapters
Parallel
Following the death of his popular online persona, seventeen-year-old Suzuki Mato decides it's time to retire from professional VR gaming. However, his plans are abruptly cut short when he's kidnapped from his high school and forced to be a guinea pig for Genaco Gaming, the world's largest esports and entertainment company. Armed with nothing but his wit and a new online persona, he's thrown headfirst into the virtual reality of "Live No Evil," a VRMMORPG littered with overpowered bosses, secretive NPCs, and backstabbing gods. His mission? Find a way to conquer this new world and get back at the company that took over his life, all while avoiding 'Parallel' -- a condition that would make it impossible to separate his real and virtual personalities. Because in a world obsessed with VR gaming, Parallel means death, and Suzuki just doesn't have time for that...
8 145 - In Serial10 Chapters
Where My Demons Lie (Fairy Tail SI)
Thrust into a world after a character selection wasn't what I was expecting. Does it matter though? At least I got what it takes to protect myself, what to do now? Self-insert and a few OCs.
8 153 - In Serial9 Chapters
Reborn-----the unexpected tales
In a small town there was one boy,he lived normally with his family but he was always diffrent,but it all changed the day he died.This is a tale of reincarnation and a young """"man"""".However he has little to no past memories and has only vaguely kept his thin line to humanity.Now he is reborn in world with magic and countless fierce beast.But his reincarnation was….unexpectedThis is a story about young man that has been human in previous life however in his last moments of life he received a big shock which caused him to loose almost all memories.What was he reincarnated as? ….well you will find out in storyP.s there will be gore
8 336 - In Serial146 Chapters
Cherry Scent
Scarlett Delmonico is your average teenage girl, she takes dance classes and plays volleyball. She lives with her single dad in Atlanta Georgia where he's a baseball coach, after a few moments of persuading, Scarlett finally agrees to see the team. It doesn't take Scarlett long to decide to try out for the team, her father thinks it's because it gives her something to do but in reality, it's someone on the team that gives her a certain bliss feeling. A Jaden Walton ff Started: March 3rd, 2022 Ended: April 2nd, 2022
8 590 - In Serial18 Chapters
Human Crisis
The fictional setting of Felarya, a dimension where larger people eat smaller people alive, is turned on its head when one of its most notorious predators ends up as a mere human. Note: Felarya and Crisis along with some other characters belong to Karbo, other characters belong to FrenchSnack, and a few characters are mine. The creators of each character will be credited at the end of each chapter in which the character appears.
8 213 - In Serial16 Chapters
Late Night Conversations ✔ [COMPLETED]
{Highest Ranking: #2 in Short Story} One collision.Two strangers.One unorthodox way to pay off her debt.Three weeks of late night conversations.One Date.
8 103

