《HASEENAH》PAGE 35&36
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*Dan Allah ina me bada hakuri na jina shiru da akayi na wasu 'yan kwanaki, hakan ya farune sakamakon rashin wuta da aka samu, na gode sosai da dakuwarku da kulawarku kaina, wa'yanda suke kirana da masu bina pc na gode sossai expecially meerah novels, I love u guyx much much Allah bar zumunci*
*35~36*
Wuta ne ya bi Haseenah sakamakon buɗe k'ofar da tayi, da sauri ta ja da baya haɗe da salati.
Haseenah na jin salatin Umman ta amma ba halin fita dalilin zafin wuta da hayak'in da ya cika d'akin, tun tana jiyo ummah har taji shuru.
Zubewa tayi wajan tana kuka tana faɗin " wayyo ummah na wayyo Aaman"
Tari ne ya turnuk'e Haseenah, kafin kace meye itama wuta ya mamaye d'akin ta.
Hakan yayi dai dai da dawowan Abba daga masallaci, Mummy na ganin shi ta daka tsalle ta hau kurma ihu tana birgima, ihun tane ya tada Saratu daga barci.
Da gudu ta fito dan ganin abinda ke faruwa, ganin wuta na tashi a side d'in Ummah ya sa Saratu ihu tana faɗin" Mummy Umman Haseenah a ciki"
Abba ko ganin wutan na dad'a tashi ya sashi fita da gudu dan neman d'auki.
Watsa ruwa ake da k'asa amma kamar fetur ake dad'a zuba wa.
Hakan yasa wani mak'wabcin su kiran fire service.
Mummy Zuwaira kuwa tunda tayi asuba ta kasa zaune ta kasa tsaye, haka haseen ma, shi mafarkin Haseenah yayi ta faɗa rijiya.
Hakan yasa shi kasa nutsuwa ya d'au makullin motar shi ya nufa gidan.
Isowar shi yayi dai dai da isowar Mummy Zuwaira.
Ganin mutane cike a gate d'in gidan ga motar fire service yasa Mummy Zuwaira firgice wa.
Haseen kuwa cike da tashin hankali ya fara ture mutane yana kutsawa ciki Mummy Zuwaira na bin shi a baya.
Ganin wuta na tashi wajan su Haseenah yasa Haseen rugawa da gudu ya nufa ciki.
Ganin ana ta shek'a ruwa ya sashi waigawa yana duba Ummah da Haseenah amma baiga kowa ba.
Mummy ya gani can gefe tayi zaman 'yan bori daga ita sai d'aurin k'irji kanta ko d'an kwali babu fuskanta sha6e sha6e da hawaye da majina tana ihu tana faɗin " wayyo Ni na shiga uku ku ceto rayuwar bayin Allan nan"
Advertisement
Nan Haseen ya fahimci abinda Mummy ke nufi.
Da gudu ya nufa wajan da nufin shiga nan aka rik'e shi, fisgewa yake yana faɗin" ku kyale Ni in shiga in fito da su tunda ku kun kasa ceton rayuwar su"
Rik'e shi sukayi suna faɗin ya nutsu amma ina baima san suna yi ba, ganin basu da niyan sake shi ya sa Haseen fashewa da kuka yayi zaman dirshan.
Mummy Zuwaira kuwa zare ido take tana faɗin" ina k'anwata take? A ina kuka barta? Ku matsa in fito da ita"
Abba ma firgici ya hana shi magana, zare ido kawai yake yana sharce zufa.
Da k'yar aka samu aka kashe wutan.
Ana kashewa kuwa aka 6alle k'ofar aka shiga.
Ummah dai babu ita babu alamar ta, cikin d'akunan aka shiga ana dubawa, d'akin Ummah ba kowa, nan suka wuce na Haseenah, can gefe suka ganta kwance ta gama k'onewa da ka ganta babu alamar rai a jikin ta.
Haseen kuwa yana ganinta ya kurma ihu ya yanki jiki ya fad'i.
D'akin Aaman kuwa ganin shi sukayi can gefe kwance, babu alamar k'una ko ciwo a jikin shi, sai dai baya numfashi.
Nan aka kira ambulance, ba tare da 6ata lokaci ba aka fito da Haseenah da Aaman.
Amma Ummah kam an duba ta ko ina babu ita babu dalili.
Mummy Zuwaira ce ta shigo ta fara dube dube, tana zuwa wajan corridor da Ummah tayi sallah taga shatin toka, tsugunawa Mummy Zuwaira tayi nan taga d'an kunnen Ummah sai zoben hanunta.
Hanunta ne ya fara rawa tana maimaita innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Zubewa tayi a wajan numfashin ta na fita da k'yar.
Jin tana salati cikin kuka yasasu garzaya wa dan ganin abinda ya faru.
Ganin abinda Mummy Zuwaira ta tsinta ba k'aramin firgita Abba yayi ba.
Fad'uwan shi kawai akaji nan aka fitar da shi.
Da gudu Mummy ta shigo tana faɗin" ta mutu ko? Halima ta mutu?"
D'agowa Mummy Zuwaira tayi cike da tuhuma ta dubi Mummy, ganin yanda take ya sa Mummy Zuwaira mik'ewa ta shak'o Mummy, turata tayi har bango ta d'auke Mummy da Mari sau uku, duban ta tayi cikin wata irin murya sannan tace
" Lauratu wallahi na rantse da Allah in na samu da hanunki wajan mutuwar er uwata sai na d'au fansa akan ki,kap zuriyar ku sai sun k'are".
Da k'yar aka k'waci Mummy hanun Mummy Zuwaira, kafin kace meye magana ya karad'e family.
Advertisement
Gida ya cika Mak'il ba masaka tsinke, banda sautin shesshek'ar kuka ba abinda kake ji.
Haseen kuwa allurar bacci aka mishi.
Mummy Zuwaira masu investigation ta d'auko Nan tasa aka kewaye side d'in Ummah ba shiga ba fita har sai an gama bincike.
Hankalin Mummy ba k'aramin tashi yayi ba dan tasan ba makawa za aga cylinder d'in gas d'in.
Da k'yar aka samu Aaman ya farfaɗo sakamakon hayak'in da ya shak'a ya mishi illa.
Haseenah kuwa dama likita ya sanar musu ta riga da ta rasu.
Lokacin da wannan labari ya iske su anga tashin hankali, barin Umaimah da baby, Suma Kan suma, ba abinda ya d'aga musu hankali sai in sun tuna jiya ma suna tare da ita.
Hakan ya jefa kowa cikin rud'ani da tashin hankali.
Abban Ummah kam jinin shi ya dad'a hawa.
Ummah kam ruwa aka yayyafa aka tattara tokan aka saka cikin likkafani.
Haseenah ma dawowa da ita akayi aka shiga da ita side d'in Abban ta, Nan aka mata wanka aka sutura ta.
Nan akace a shigo a mata addu'a.
Lokacin Haseen ma ya farfaɗo, k'arfin hali kawai yake, yaci kuka har ya gaji.
Shigowa shi gidan kenan daga asibiti, yana ganin kowa nata faman alwala zuciyar shi ta tsinke, nan ya tabbatar da ya rasa masoyiyar shi kenan har abada.
Tafe yake kaman wanda zai fad'i, yana shiga cikin gidan cikin kuka yaji Umaimah ta faɗa jikin shi tana faɗin" ya Haseen sun kashe mun Ummah da Haseenah na, Ya Haseen ko wanene yake da hannu karka barshi"
Kasa magana yayi dan kuka yaci k'arfin shi, zubewa yayi gaban Mummy Zuwaira cikin kuka yana faɗin" Mummy Kinga abunda sukamin ko? Kinga tozarci da wulak'ancin da akamun ko? Meyasa za'amun haka? Meyasa Ni basu kasheni ba? Meyasa....
Bai iya k'arasawa ba dan kuka yaci k'arfin shi.
Kama hanun shi kawai tayi tana girgiza mishi kai.
Nan ta mik'ar dashi ta duba su Umaimah tace" suje su mata addu'a za.a tafi da ita"
A tare suka shiga su hud'u, Haseen, Mummy Zuwaira, Umaimah da baby.
Ganinta shinfid'e cikin makara an gama shirya ta, ga tokan Ummah a gefe shima cikin likkafani.
Zubewa duka sukayi a wajan, baby kuwa tunda ta zube bata sake motsawa ba.
Addu'a kawai Haseen da Mummy Zuwaira keyi suna kuka, Umaimah kam ta kasa cewa komai sai rungume Haseenah da tayi tana wani irin kuka.
Bud'e gefen fuskan ta Haseen yayi, da sauri ya sake ganin irin k'onewan da tayi inba fad'a maka akayi ba bazaka gane Haseenah bace.
Kuka sossai yake ya dubi Mummy Zuwaira yace" dan Allah Mummy ki fad'a Mata ta tashi, wallahi zan aure ta a haka, Mummy ina sonta ki tashe ta dan Allah, inaso tamun magana ko da sau ɗaya ne"
Da ka ganshi kasan baya cikin hankalin shi.
Hakan yasa Mummy ta Kama hanunshi ta d'ago Umaimah suka kama hanyar fita.
Mummy Haseen ya hango tsaye bakin k'ofar ta, kallon da ya mata ya sata sunkuyar da kai k'asa alamar rashin gaskiya.
Saratu kuwa duk ta daburce saboda mutuwar tagirgiza ta.
Aaman kuwa na can asibiti ana mishi k'arin ruwa.
Lokacin da aka zo fita da gawar su ba k'aramin tashin hankali aka shiga ba, dan Mummy Zuwaira Suma tayi, haka baby Kam an rasa gane kanta.
Tunda suke basu taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba.
Abba ma tafiya kawai yake kai kace mara hankali ne, janshi kawai ake duk yanda aka bi dashi nan yake bi, ji yake kaman ba shi ba, mafarki yake ko gaske sai Allah.
Seda akayi sallar su a masallacin juma'a ta anguwan sanna aka wuce dasu mak'abar ta, Haseen ma shuru kawai yayi amma idon shi bai dena zubar da hawaye ba.
A jere aka tona kabarin Ummah da Haseenah, tare da Haseen aka kama gawan da kanshi ya saka Haseenah.
Lokacin da aka gama rufe su kuwa Haseen durk'ushe wa yayi wajan yana kuka yana faɗin
" me yasa zakimun haka? meyasa Baki barni na fara mutuwa ba? me yasa kika za6i jefa rayuwata cikin garari da tashin hankali? Meyasa kinsan bazaki rayu tare da niba kika barni na shiga rayuwar ki? Meyasa baki bari munyi ban kwana ba kika tafi Haseenah? Why? Why?"
Kamashi daddy shi yayi cike da tausayin ɗan nashi ya rungume shi, cikin kuka Haseen ya k'ank'ame daddy shi yana faɗin" daddy kaga abinda rayuwa tamun ko? Kaga abunda mutuwa tamun ko? Kaga Haseenah ta tafi ta barni? Daddy fad'amun ya zanyi? Ka tashe ta dan Allah kace mata zan aure ta a haka, daddy ka fad'a mata ina sonta a haka daddy...
Toshe mishi Baki daddy yayi yana faɗin" haba Haseen kar ka zama mara tawakkali mana, ka rungumi k'addara sai Allah ya musanya maka da wata"
Da sauri ya dubi daddy yace....
Na gaji wlhy....
Plx vote nd comments
Advertisement
- In Serial16 Chapters
The Call of the Void
The Void calls out to you, it whispers to you in your ear, it offers you comfort in your darkest hour. They are coming, and you are their herald. You offer comfort, freedom and oblivion, let the Void call out to them like they called out to you, let them know the freedom that you now know. Let the rebellion begin, let the Void take all! Glory to the Void! Let the corruption set you free!
8 144 - In Serial10 Chapters
Soul sacrifice [POETRY]
POETRY COLLECTION BOOK We met by accident, but fell in love on purpose And a promise runs my mouth, Leaving my soul open To never let your heart be broken✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ ✿ With kindness and open heart, join to this ship with me, and may we sail the sea of emotions and fears, with laughter and tears, following us on the way.♡♡♡In this book, I will write from my soul, I will bleed trough ink.Reading this poetry book will get you inside the deepest tunels of my heart.I may feel vulnerable, but dont mind,this might be the biggest opening to humankind I will ever achive.~copyright~All rights reserved. No part of this book may be reproduced or used in any manner without the written permission of the copyright owner.© 2022#2 in deeppoetry 11. 8. '22#3 in deeppoems 11. 8. '22#2 in wordsofwisdom 11. 8. '22#3 in latenightthoughts 11. 8. '22
8 151 - In Serial8 Chapters
we got reincarnated to be parents
a great disaster occurs and the world is changed forever, it is swarmed by monsters and strange beings.but luckily the gods have given the humans a chance to fight back but this chance comes at a price, this story follows a couple that has been together since they were 16 years old having chosen the power to fight they paid a price that seems insignificant to others but has had a great impact on their lives
8 101 - In Serial18 Chapters
The Dao of Eros
Synopsis Power, glory, happiness, revenge, love, lust, knowledge... Everyone has desires. What do you want more than anything else? What would you sacrifice to achieve your goals? How strong must you become before you are satisfied? Levi Ares was just another random virgin on Earth, when he was mercilessly cut down at the age of twenty. However, it turns out that death isn't really the end. Thrust into a brand new and magical world, the reincarnated loser must embrace his true destiny! To become a Shaman! Able to form bonds with creepy ghosts and demented hellish ethereal monstrosities, he must abuse his overpowered Innate Talent in order to cultivate fast enough to become an Immortal or whatever... (Warning: This story includes profanity, numbers, humanity, nudity, uncomfortable realism in a fantasy-world, awkward but mild sexual-content, descriptive violence and gore, bizarre and disturbing sexual-content, offensive language, Xianxia, martial arts, plus all of the other things that disclaimers usually have to tell you about. Do not read this if you dislike transportation, virtual reality, fantasy, or other similar genres… or me, because I’m the author.)
8 179 - In Serial51 Chapters
The Puppy Project
"Give me my puppy!" I demanded, my eyes ablazed with fiery anger."Correction, it's not your puppy. It's our puppy," He smiled, but it was anything but sweet nor happy."You know what? Damn you! You're nothing but a cold, emotionless, and heartless bad boy!" I sneered, glaring at him fiercely.He chuckled at my words, taking a step closer to me. He slammed his hand unto the wall, trapping me, before leaning in close. "You got that right sweetheart but I think you got one thing wrong." He said, his eyes piercing straight into mine."And what is that?" I managed to asked, my throat seeming to get drier the more he looked at me."I'm neither one of those when I'm with you," and with those words, slammed his lips into mine.#1 in Strong-Female Character - 1/29/21#1 in Sarcasm - 2/4/21#2 in BadBoy - 2/13/21#3 in Teen Fiction - 2/13/21#1 in Mysterious - 3/4/21Copyrighted 2017. All rights Reserved.
8 144 - In Serial63 Chapters
RiAnsh Os
Some Short Stories on RianshCover credits @Rrahul_Helly_Lover3
8 160

