《HASEENAH》PAGE 29&30
Advertisement
: 🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
*29~30*
Tun da asuba dangin Abba Dana Ummah suka Fara hidimar suna, a d'aura wannan a sauke wannan, duk abunda suke Mummy na kallon su ta window d'akin ta, Saratu ma ba ta fitowa saboda Mummy tace ta kuskura ta fito sai jikinta ya fad'a Mata.
Dole dukan su suka maida kansu 'yan prison.
Haseenah kuwa ko yaushe Aaman na hanun ta, ko kar6ar shi Bata k'aunan ayi balle abunda zai d'aga ta daga wajan Umman ta.
'yan uwa da abokan arzik'i anzo, Haseen Kaya masu tsada ya d'inka wa Haseenah Wai na kwalliyar suna har guda biyar, Atampa uku laces biyu takalmi vine da jaka d'aya sai flat shoe d'aya, mayafi black and white kowanne d'add'aya.
Umma kuwa turmi biyar ya siya Mata ya d'aura Mata 5k akai, Aaman kuwa nashi akwati guda Haseen ya mishi harda su Pampers da takalman jarirai.
Lokacin da Mummy taji ana yaba kayan da Haseen ya kawo hakan ba k'aramin d'aga Mata hankali yayi ba, Nan ta dad'a tabbatar wa harda hanun uwarsa a cin amanan ta, hakan ya sata ta dad'a tsanan Haseen ganin yanda yayi banza dasu, ya nuna kaman Bai San iskar da ta kwaso su ba.
Gidansu Abba ma ba k'aramin Kaya suka wa Mummy ba mahaifin su Abba kuwa kyautan kujerar Umarah ya bawa Umma ita da jaririn ta.
Mummy Saudat kuwa haka tasa Abba ya canja wa Ummah kayan d'akin ta tace shine nashi gudumawar.
Lokacin da wannan labari ya iske Mummy ba k'aramin hauka taso yi ba, Dan Saratu ma sai da taci duka ba laifin tsaye ba na zaune.
Advertisement
Tunanin Mummy zasu zo su rarrashe ta, Amma sun manta akwai wani halitta a site d'in Mummy ma.
Washegarin suna da safe Mummy Saudat ta turo 'ya'yan ta Mata su biyu tace suzo su Taya Haseenah tattara gida kafin itama tazo.
Mummy Zuwaira ma Haka tazo aka taro aka dad'a gyara gidan da ita.
Bayan an gyara ko Ina ne aka fito da kyautukan da Mummy ta samu babban palour, Nan suka Fara yaba kayan ganin irin kayan da aka samu, kayan da Umma ta samu kawai ya Kai turmi hamsin, Banda laces da materials, murna kuwa wajan Haseenah ba.a cewa komai Dan gani take yanzu shikenan ba ruwan Umman ta da k'aran cin sutura.
Kud'in da ta samu kuwa Haseen Mummy Zuwaira ta Kira tace suje banki da Haseenah a bud'e account da sunan Haseenah da komai.
Hakan kuwa akayi, wajan dubu d'ari biyu Haka aka zuba, bayan sun dawo Abban Ummah yasa aka tura mishi account numbar ya tura mata da one million yace in ta ji k'wari daga baya itama ta Fara kasuwan ci baya son zaman ta Haka.
Kiran shi Umma tayi tana kuka tana mishi godiya.
Lokacin da aka kaiwa Mummy nata kayan suna Wanda aka soya dasu nama, dawo da 'Yar aikan tayi tace ita ba mayunwaciya bace.
*3 months later*
Aaman yayi wayo sossai yayi 6ul6ul dashi Kai kace yakai 4 months, lokacin Kuma Umma suke ta Shirin tafiya Umrah.
Mummy kuwa tun a lokacin ta kafa wa Abba k'ahon zuk'a duk inda zaisa k'afan shi indai a cikin gidan ne idonta na kanshi, Inka ganshi sai ya baka tausayi.
Yau da yamma jirgin su Umma zai tashi, Dan Haka suna ta faman had'a Kaya, Haseenah ma Mummy Zuwaira tace ta shirya zata turo driver ya d'auketa ya taho da ita, Dan bazata barta ta zauna a gidan tayi aikin bauta ba.
Advertisement
Hakan ba k'aramin murna yasa Haseenah ba, Haseen ma hakan ya mishi dad'i Dan zaifi sakewa in yaje gidan sa6anin gidan su da yake Mummy na binshi da zagi da bak'ak'en magana.
Motar da Abban Umma ya Bata kuwa, parking lot aka shiga dashi aka rufe, Dan Mummy Zuwaira tace sai bayan Ummah ta dawo sannan za.a fara koya Mata kafin Nan Aaman ya dad'a k'wari.
Driver da Haseenah da Haseen da yaran Mummy Zuwaira ne suka Kai Ummah airport.
Haseenah na rungume da Aaman har suka Isa airport, lokacin da su Ummah zasu wuce ciki sai Haseenah taji duk Babu dad'i harda kuka.
Murmushi kawai Ummah ta Mata ta bubbuga bayan ta sannan ta wuce, Aaman kuwa sai k'yakkyata dariya yake wa Haseenah.
Basu baro airport ba sai da suka ga tashin su Ummah, daganan Haseen ya kwashe su sai gidan Mummy Zuwaira.
Mummy kuwa can shirye shiryen d'aukan fansa ne kawai a ranta, Dan a cewar ta ta kula in ta tsaya Haka tana ji tana gani zaman gidan zai gagare ta.
Daga k'arshe dai ta tsaida hukuncin da zata zartar ba tare da neman yardar kowa ko shawarar wani ba.
Haka batayi tunani hakan me ze haifar ba, ita dai tasan hakan da zatayi shine kawai kwanciyar hankalin ta indai tanason mallakan gidan Nan ita kad'ai.
Hakan yasa take Allah Allah Umma su dawo Dan ta gaji da ganin bak'in ciki.
D'an kwanakin da Haseenah tayi a gidan Mummy Zuwaira yasa ta k'ara haske da 'yar k'iba, ga wata irin shak'uwar da ta shiga tsakanin ta da Haseen.
Kusan ko yaushe indai Haseen ya dawo daga gurin aiki to ko abinci a gidan Mummy yake ci.
Ummah kuwa tana can ita da Aaman, yau satin su d'aya kenan acan, kusan kullum Haseenah Kan Kira Ummah sau biyar ko sama da Haka, wani lokacin tace Umma ta saka wa Aaman taji surutun shi.
Ana sauran kwana uku Umma ta dawo ta shiga kasuwa ta Fara siyan tsaraba ma 'yan uwa da abokan arzik'i.
Amma Haka kawai sai taji gaban ta na yawan fad'uwa tun abun baya damunta har ya hankalin ta ya fara tashi.
Ana sauran kwana d'aya ta dawo taji duk batason komawa ta rasa Gane me yake Shirin faruwa, itadai da ka ganta kasan akwai abunda yake damun ta.
Can Nigeria kuwa Haseenah dasu umaimah da baby wato yaran Mummy Zuwaira ne suka tafi can gidan su Haseenah Wai suna shara wa Mummy.
Kayan da Mummy ta samu na suna Kap suka kwashe suka jibge a store, sai wani k'aramin d'akin da yake kusa Dana Haseenah suka gyara shi aka yi penti suka jera wa Aaman su gado da kayan wasa tam a d'akin Dan Haseenah tace kusa da d'akin ta zaina kwana.
D'aki ya tsaru yayi kyau, ko Ina sai k'amshi.
Sai yamma suka gama sannan Haseen ya maidasu gida.
Washegari Ummah zata dawo, Dan Haka da sassafe su Haseenah suka sake dawowa, kowa d'auke da kayan shi Dan Umaimah da baby sunce ba yanzu zasu dawo ba gidan su Haseenah zasu zauna.
Haka Mummy Zuwaira tace Allah tura k'eya dama sun addabeta da fitina.
Murna suka rink'a yi Nan Haseen ya kwashe su suka tafi.
Suna Isa kowa ta ajiye gyale suka hau aiki, wannan girki wannan snacks wannan homemade drinks.
Haka suka rarraba, kafin yamma duk sun gama komai sun feshe gidan da air freshener da turaren wuta, kafin kace meye ko Ina ya d'au k'amshi.
Jirgin su Ummah k'arfe biyar na yamma ya sauka, Dan Haka tuni su Haseenah sun hallara Dan taryo Umman su.
For comments only 08144932303
Advertisement
- In Serial1363 Chapters
VRMMO: The Unrivaled
Lu Chen used to be a ranker of the most popular VRMMO game, Spirit of Grief. After a car accident turned his dreams into dust, his disability left him incapable of escaping the pit of mediocrity he was thrown into. Helpless and defeated, his story ended.Two years later, the Eternal Moon Corporation launched a new VRMMO called "Heavenblessed", and Lu Chen stumbled into another terrible accident that left him in a complicated situation far beyond his ability to handle. That won't stop him from rising to the top, however. Not again.Come witness the rise of the sword-wielding zombie and the relationships he makes during his journey to the apex! For riches and bi- ahem, for career and love!He wields a demonic sword from Hell, he dons armor shining with Heaven's light. His boots stride across the sky as his helmet devours the souls of his enemies. On his left side sits the Goddess of Death. On the other, the Angel of Beauty.From the land of ice and death, a generation of Asura Kings rises, their roars reverberating throughout the world.Tremble in fear, noobs!
8 8156 - In Serial1353 Chapters
Refining the Mountains and Rivers
A young man's life changes when he stumbles upon a mysterious item. Qin Yu had never been a lucky person. Weak of body, bullied by his peers, and with only his friend as his family, he struggles day-by-day to live. But everything changes when he stumbles upon a little blue lamp. An immortal and demonic cultivating adventure.
8 3344 - In Serial2455 Chapters
Mortal Cultivation Biography
A poor and ordinary boy from a village joins a minor sect in Jiang Hu and becomes an Unofficial Disciple by chance. How will Han Li, a commoner by birth, establish a foothold for himself in in his sect? With his mediocre aptitude, he must successfully traverse the treacherous path of cultivation and avoid the notice of those who may do him harm. This is a story of an ordinary mortal who, against all odds, clashes with devilish demons and ancient celestials in order to find his own path towards immortality.
8 1050 - In Serial1503 Chapters
Dragon Prince Yuan
Destiny stolen at birth, the prince of the once mighty Great Zhou Empire, Zhou Yuan, has been plagued all his life by a fatal poison, forced to suffer powerlessly until one day when fate draws him into a mysterious domain where he meets a beautiful girl in green, a bizarre dog-like creature and an unfathomable old man in black.Join Zhou Yuan as he is thrust into the whirlpool of destiny while he seeks the pinnacle of cultivation.
8 1057 - In Serial677 Chapters
Ranker's Return
In the early days of the virtual reality game, Arena, meleegod was the strongest ranked player! He deleted his character and suddenly left. In order to restore his bankrupt family, he returned to Arena!"Do you want to create a character?"
8 1715 - In Serial1525 Chapters
Monarch of Evernight
Qianye rose from hardship but was felled by betrayal. From then, one man, one gun; he tread the path between Evernight and Daybreak and became a legend. Even if Evernight was destined to be his fate, he still intends to become the ruler who dictates.
8 22861

