《HASEENAH》PAGE 27&28
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
'''Dan Allah masu mun magana ta pc in tura musu novel dina suyi hakuri suna tanbaya a group, ina da matsalar network daga lokacin da nace kowa xan bishi in tura mishi in personal network dina yakan dad'e bai dawo dai dai ba, kuyi hakuri plx'''
*27~28*
Da gudu Saratu ta fito jin irin Kiran da Mummy ke Mata, duban ta tayi sannan tace" Ina wannan matsiyaciyar take?"
Ta nuna k'ofar d'akin su Haseenah.
Ta6e Baki Saratu tayi tace" na dai ga Haseenah ita da Yar Uwarta sun kamo Uwar an fita da ita da sauri, ban dai San menene ba"
Wani shewa Mummy ta saki tana fad'in" Haka akeso, Allah yasa tafiyar kenan"
Nan ta wuce ciki zuciyar ta fari tas, gani take yanzu Kap duniya Bata da wata damuwa, gida ya Zama nata, miji ya Zama nata Haka dukiyar shi ma daga ita sai 'yar ta.
Haka yau Mummy da kanta ta shiga kitchen ta zuba girki, tana gamawa ta fito musu dashi palour suka baje sai Kwasa suke suna Hira ita da Mum Haseen.
Can asibiti kuwa sai son barka ake, Hajiya Saudatu ne ta je har kasuwa ta tasa Abba a gaba suka shiga suka siya kayan abinci, da akwati gudu hud'u, da kanta ta shiga shagon Abba ta had'a kayan Umma akwati guda, sannan suka je baby care aka cika akwati biyu tam da kayan baby, d'ayan Kuma aka cikeshi da kayan shafe shafe sannan tace su taho asibiti.
Shi dai Abba ya rasa Gane kanshi, farin ciki yake ko bak'in ciki oho, Amma kana kallon shi kasan akwai abunda ke damun shi.
Advertisement
Haka suka k'arasa asibitin lokacin har Umma ta tashi, dangi duk sun zagaye ta, dad'i ne ya Kama Umma Dan rabon da taga dangi an taru a kanta tun auran ta.
Tunani take to dama me yasa suka guje ta? Wata zuciyar tace mata halin Mummy.
Abba ma da yazo yaga jaririn shi d'aukan shi kawai yayi ya zuba ma yaron Ido, can sai ya share k'walla, Mummy Saudat ta kula da hakan, duk yanda akayi tasan d'an uwanta Yana cikin wani mawuyacin hali, addu'a kawai yake buk'ata, Dan tasan ba Haka yake ba.
Ganin jikin Umma ya koma normal yasa Mummy Zuwaira ta buk'aci sallama, Haseen ne ya biya duka bill d'in sannan aka kwashi Kaya sai gida, Abba kuwa da sunan Abban Ummah yayi wa yaro hud'uba wato *Abdullahi*, Haseenah tace za.ana kiranshi (Aaman).
Dangin Ummah kuwa murna kaman ba gobe, Nan aka Kira Abban Ummah aka sanar dashi, Nan yace ga tukwicinshi Yana isowa.
Motoci biyar akayi duk 'yan raka Ummah gida ne.
Mummy da Mum Haseen da Kuma Saratu na tsaka da Hira sukaji horn d'in mota, kallon kallo suka Fara yi, can Mummy tayi tsuka tace" Abban su ne fa"
Jin motar ba guda d'aya bane ya sasu duka yin shuru Dan sauraron abunda ke faruwa.
Kafin su yunk'ura su tashi sukaji Muryar Mummy Saudat tana rangad'a gud'a, mutuwar zaune dukansu sukayi, Mummy Zuwaira ce ta Fara shigowa rik'e da Aaman a hanunta an nad'e shi cikin showel farare tas, sai Ummah dake biye da su, sai Kuma jama'ar da suka rufa musu baya anata San barka.
Ko kallon inda Mummy take Basu Yi ba, palour Ummah suka wuce, Nan aka Fara shigowa da akwatuna Wanda Abba ya siya, Nan fa hankalin Mummy ya tashi.
Haseen ne shigowan k'arshe rik'e da basket sun jero tare da Haseenah gwanin sha'awa.
Advertisement
Wani zagi Mummy ta kutuntuma, lokaci d'aya tayi zubur ta mik'e ta fisge d'an kwali, Nan ta hau surfa masifa da zagi tana fad'in
"ba.a Isa a munafurce ta aci amanar ta ba, anje anyo ciki sannan za.a lank'aya wa mijin ta saboda anga yanada dukiya"
D'aya daga cikin 'yan uwan Umma ta lek'o tace" sai gashi kuwa aka haifo namiji Kuma ba"
Ihu Mummy ta sake tana fisge fisge, ganin zaninta na Shirin fad'uwa yasa Mum Haseen janta da k'yar sukayi ciki, tana tirjewa tana komai suka ja ta ita da Saratu suka turata d'aki suka kulle ta.
Dukda Haka bakin Mummy Bai mutu ba fad'i take" in dai da jini aka haifeta wallahi saita hallaka Ummah da d'an data Haifa.
Bata gama tsinkewa da Al amarin ba seda taji ana sake wani gud'an ganin galleliyar motar da Abban Ummah ya siya Mata, lek'awa Mummy tayi ta window Nan ta hango motar ko gama cire ledar jiki ba'a Yi ba, zaman dirshan Mummy tayi Kan tiles ta fashe da kukan bak'in ciki, ganin duk dangin shi sun cika wajan Mummy, gashi ta jiyo yanda ake ta yaba kayan akwati Wai Abba ne yayi Mata.
Kan uba, wallahi bazata yarda ba, ita za.a ciwa Amana, wannan karon ta d'au alwashi ko ta tsiya ko ta arzik'i ba bokan da zataje da kanta zata d'au mataki.
Ganinta kawai suke.
Kuka Tasha bana wasa ba, seda tayi Mai isarta sannan ta koma ajiyar zuciya.
Jin tayi shuru yasa Mum Haseen bud'e k'ofar ta shiga a hankali, Mummy ta hango gashin kanta a tsatstsaye sai kace mahaukaciya, Nan Mum Haseen ta Fara kwantar Mata da hankali, ta Bata shawara ta tashi su koma wajan boka.
Wani ashar d'in da Mummy ta k'unduma Mata ya sata Jan bakin ta tayi shuru, Mummy ta kalleta tace" ba wajan d'an iskan da Zan Kuma zuwa, da kaina da Kuma hanuna Zan d'au mataki"
Girgiza Kai Mum Haseen ta Fara yi tace" Yaya in hankali ya 6ata hankali ke Nemo shi, karkije ki aikata abunda zakiyi Dana sani daga baya, Haka Allah ya nufa ki d'au kaddara sai kiga Allah ya sauya Miki da mafi Alheri"
Tunda Mum Haseen ta Fara magana Mummy ta zuba Mata Ido take kallon ta Kai kace maganar ya shigeta ne, seda Mum Haseen ta yi shuru sannan Mummy ta dube ta tace " kin gama Dan ubanki? Munafuka kawai, dama nasan da saninki aka ci Amana ta, shiyasa naga Haseen bini bini Yana bin Mata kin kasa tsawatar mishi, ba ruwanki da damuwa ta dama nasan ba don Allah kike k'aunata ba, ki tashi ki ficemun a gida karna sake ganinki inba nice na nemeki ba"
Maganganun Mummy ya ta6a wa Mum Haseen zuciya, hakan ya sata mik'ewa ta d'au jakan ta ta fice a wajan, Haseen ta gani ya fito Nan tace ya ajiye ta a gida.
Tun da Mummy ta haihu kullum gidan shiga ake ana fita, Mummy kuwa ko fitowa Bata yi duk ta rame tayi bak'i ta fita a hayyacin ta, ta sak'a wannan ta kunce wannan duk ta rasa abin Yi.
Da Haka har yau akazo shagalin suna.
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial37 Chapters
Seabound
She was determined to reveal the secrets of her past and to do so, she went to Venetta under a false name. But the adventure was more dangerous than she thought. Seabound is the first book of dilogy involving magicians, outlaws, sea monsters, and sweet romance. It's action-packed story set in the mysterious city where everyone hides their true faces behind masks. The translation was made by my sister, Mia Velisarova. This novel was included the short list of the contest Open Eurasia 2020. Now I am writing a second book of this series: Seaspelled
8 126 - In Serial41 Chapters
Kill 10 Rats
You awake in the middle of an unfamiliar woods with nothing but a knife and a pair of pants. You have no idea where you are, how you got there, or even what your name is. Noob Slayer is an average college student, part time computer repair guy, and a full time gamer. He awakes to find himself in a world he does not understand. Follow him as he explores this new world, looks for answers, and tries to remember his name. Authors Note: This is a side-project I started after being widely stumped trying to write another book. It is my first attempt to actually post something I've written online, but don't be afraid to be brutal. Improving myself is why I wanted to write this in the first place. I know the VRMMO genera is a bit over-done but hopefully it has a few good stories left to tell. Warning: This is written in the first person. Will contain brutal fight-scenes, bad pop-culture references, a ton of MMO-tropes, and possibly some light sex if the MC doesn't screw it up too badly. Member of A group of excellent litRPG fictions on RRL!
8 174 - In Serial153 Chapters
Bloom
Everything can grow. Everything can rise, and ascend. Even, a Tree.
8 208 - In Serial8 Chapters
A Thief and a Prince (Inspired by Aladdin)
Nico is Prince of Atlantis. Percy is a lowly thief who is mourning the death of his mother. When Nico gets bored of the Palace life, what will happen when he meets Percy? Will Percy be enough to capture his attention. A Nicercy fic. Boyxboy. Don't like, don't read. Rating may change in upcoming chapters.NOTE: COVER NOT MINE, FOUND ON GOOGLE
8 149 - In Serial39 Chapters
The Hero's Prophecy
In a town in a world called the Imaginarium, a man appears to their aid. With his flaming courage and gleaming shall he face the evil of Prometheus' machinations. The people believe him to be the end to ultimate menace. For that is the Hero's Prophecy. Also on Wattpad. Updates Tue/Fri.
8 173 - In Serial18 Chapters
A Girl and her Goat
Chloe Yinara, she’s a countess, she expects to be a marquis in due time, she’s a mage, and she’s staring at a black goat that appeared in the summoning circle when she called for a familiar and took more power to summon then she could have possibly provided on her own. ___________________________________________________________________________________________________ There has been a major edit of the first 11 chapters, so anyone who enjoyed the story but couldn't take the spellchecker and other grammar mistakes should give this another shot. I can’t promise that there will be no grammar mistakes, but they will be less common and far less egregious. ___________________________________________________________________________________________________ Notes. First for those of you looking at the fact that this story has both the Harem and Female Lead tags I am pleased to relieve your concerns, or disappointed to inform you depending on your tastes, this will not be a reverse harem, Chloe has no romantic interest in boys. Second, I was hesitant to add the Anti-Hero tag, but Chloe certainly dances on that line. Just to prevent any misunderstandings, even when blood and treachery abound and Chloe is at her most amoral this will primarily be a light hearted story.
8 114

