《HASEENAH》PAGE 19&20
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
Story &written
By👇🏻
Aysher Abbakar (meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
Follow me on
*Long Live Pml*
'''ban san taya zan fara godiya ba,kwanana biyu banyi typing ba dalilin rasuwar da aka mun,Amma yanda mutane sukemun magana yasa dole na zanyi Koda kadanne,na gode sossai da ta'aziyar ku gareni Allah bar kauna da zumunci,Koda yaushe Kuna raina'''
*19-20*
Ko wannen su d'auke da adda su shida, wata uwar birki Hajiya Saudatu ta taka saida motar ta juya dasu, jikin su gaba d'aya rawa yake barin ma Mummy da tuni ta hau kyarma, nuni d'aya daga cikin su ya musu akan su sauko, Nan suka hau kallon kallo, daka musu tsawa ya sake yi Wanda ya dad'a firgita su, da sauri suka 6alle murfin motar suka fito, ganin irin shigan da sukayi ya tabbatar musu da cewa ba mutanen arzik'i bane dukda yawan shekarun su, wasu zaro zaron 'yan kunne Hajiya Saudatu ta saka Wanda ya sauko har kafad'un ta, ga hujin hancin ta biyu a jere ta ko wani gefe, Mummy kuwa taci bleaching har ya wuce misali, Dan in ka kalli k'afan ta da hanunta bazaka ce itace me wannan fuskar ba.
Mum Haseen kuwa Riga da skirt taci ta buga wani uban rolling ta cakka d'an kwali, hakan yasa su bushewa da dariya ya dubesu yace "ku yi kneeldown",
duban su Mummy tayi tace "menene nildawun kuma?"
Dariya suka saka yayin da bak'in ciki ya Kama Hajiya Saudatu ta dube ta tace
" ai ko Baki shiga aji ba a tunanin Zaki Gane abunda suke nufi jaka kawai"
Ta k'arashe maganar had'e da janyo Mummy k'asa Nan ta kife, d'aya daga cikin su ne ya dube su yace " gidan uban wa kuka fito a Daren Nan Kuma cikin jejin Nan?"
Advertisement
Shuru dukan su sukayi sun rasa Mai zasu ce, kallon wani a cikin su yayi da Ido Aiko basu Ankara ba sukaji d'aya ya d'auke Mummy da Mari da take gaba, ihu ta saki tana "wayyo Allah wallahi ban sani ba ku tanbayi wannan zata muku bayani"
Ta nuna Hajiya Saudatu, d'aga musu hannu Hajiya Saudatu tayi sannan tace" bayin Allah me kuke buk'ata?"
Dariya sukayi sannan babban su yace" da tuntuni abunda kukayi magana kenan da Baku Kai wannan matsayin ba"
Mik'ewa Hajiya Saudatu tayi ta shiga motar ta bud'e jakar Mummy da Mum Haseen ta tattaro kap k'udin ciki kusan dubu dari biyu tazo ta mik'a musu, kar6a sukayi sannan sukace " Zaku iya tafiya ku biyun Nan"
Suka nuna Hajiya Saudatu da Mum Haseen.
Duban su Mummy tayi a razane tace" Dan Allah Nima ku barni in tafi"
Nan ta hau kuka kamar yarinya, d'aya daga cikin su ne yace" su ja motar sukai zuwa can, ya nuna wata bishiya, kekuma seki bisu da tsallen kwad'o"
Ai su Hajiya Saudatu da Mum Haseen na jin Haka suka shige mota da gudu suka barta Nan tsugune.
Nan Mummy ta hau yin tsallen kwad'o biyu tayi ta kife wajan, juyowa tayi ta ga suna magana ko takalmi Bata tsaya sawa ba ta mik'e da k'yar ta arta da gudu.
Dariya sukeyi sossai dukan su, Mummy ko kulasu Bata yiba damuwar ta ta ganta cikin motar ne.
Tana shiga motar Hajiya Saudatu ta bushe da dariya tace " a dai koma makaranta saboda 6acin Rana.
Bata kula ta ba sai haki take tana wangale hanci, takai kusan minti biyar sannan ta daidai ta, duban su tayi tace" koma menene tunda na tsira da abunda boka ya bani shikenan, bashi zai hanani dawowa ba indai buk'ata ta biya"
Dariya sukayi sannan Hajiya Saudatu tace" dama Waze ja da d'iyar makafi mabarata Kuma 'yar jagora, Kinga jiya Kinga yau saura gobe, duk Wanda ya ganki ai yaga manyan arna Kuma wahalalliya, keda kika san layi- layi na titina da shagona ai zakiyi abunda yafi haka ma"
Advertisement
Haushi ne ya turnuk'e Mummy Amma ta kasa furta komai Dan tasan tana magana ba mutunci zata ajiye ta cikin wannan tsakiyar dajin.
Sai wajan k'arfe 10:30 na dare suka hau Kan titi, zuwa 11:00 kuwa sai ga su k'ofar gidan Mummy, duban Hajiya Saudatu tayi dukda haushin da take ji tace " na gode sossai fa sai kin jini"
Ko Kula Mum Haseen Bata yi ba ta figi jakar ta tayi ciki.
Gidan shuru ba kowa hakan ya sata wucewa side d'inta da sauri, d'akin saratu ta fara lek'awa ta ganta zaune ta buga tagumi, Nan ta had'e Rai, duban ta Saratu tayi tace"Mummy Ina Kika shiga tun safe"
A tak'aice Mummy tace" gidan uwar wata"
Bata sake bi ta kanta ba tayi wucewar ta d'aki, Allah Allah take asuba tayi ta fara aiwatar da aikin ta.
Kasa bacci tayi Kota Fara sai ta mik'e ta duba agogo, a haka har asuba tayi, tana jin ficewar Abba zuwa masallaci ta d'auro zani Kan kayan baccin ta ta fito, side d'inshi ta nufa cikin sand'a Nan ta tsaya dai dai bakin shiga palour shi, rasa ta inda zata fara tayi Dan ganin wajan duk mamaye yake da tiles, takai kusan 5 mins Nan tsaye tana neman mafita, jin anyi sallama a masallaci ne ya firgitar da ita Dan tasan yanzu mijinta zai shigo, Nan wata dabara ta fad'o mata, Wani dariyar mugun ta ta saki sannan ta tsuguna ta d'aga k'asan carpet din ta tura maganin sannan ta juya da sauri ta koma ta la6e, Nan kuwa ya shigo hanun shi rik'e da carbi, Yana wuce k'ofar d'akin yaji zuciyar shi tayi bak'ikk'irin, zuciyar shi tayi zafi kamar an chaka mishi mashi haka yaji, lokaci d'aya yaji ranshi ya 6aci, wata tsuka ya ja Wanda baisan dalilin ba yayi k'wafa sannan ya wuce ciki had'e da banko k'ofar.
Wata tsalle Mummy ta daka ta murna ta taka rawa Wanda Bata San ma ta iya shi ba sannan ta wuce ciki tana Allah Allah gari ya waye taga irin dramar da za a kwashe.
Wajan k'arfe 9 da yake yau weekend ne Mummy taci wanka ta nufo d'akin su Haseenah, Nan ta fara knocking, da sauri Haseenah ta diro daga gado ta sako slifas ta fito, zubewa tayi gaban Mummy tana kwasar gaisuwa, ko amsawa Mummy batayi ba tace " ki shiga kitchen ki had'a mana breakfast da Abbanki inkin gama kizo ki jera a dinning.
Da sauri Haseenah ta mik'e ta wuce kitchen ta hau aiki, tana gama ta jere su cikin babban basket ta d'auka ta nufa wajan dinning, Abba ta hango yanata faman dariya ko me Mummy ke fad'a mishi oho.
Yana ganin Haseenah ta nufo yanda suke ya had'e Rai kaman Bai ta6a dariya ba, tsuka ya ja ya kau da kai, Kai kace wani mak'iyin shi ya gani.
Tana zuwa ta gaidashi Amma ko kallonta baiyi ba, ta sake gaidashi karo na biyu tunanin ta ko baiji bane.
Wata tsawa ya daka mata sannan yace" ki ajiye da Allah ki 6acemun a nan"
Razana tayi da firgici ya sata tsayawa cak Nan ita batayi baya ba Kuma batayi gaba ba, k'afan shi ya saka Nan ya tokare ta ta kife wajan, jini ne ya fara zuba a hancin ta, a firgice ta mik'e ta zuba a guje ta bar wajan, saboda tsabar rikicewa ma bata san inda ta nufa ba.....
For comments 08144932303
Advertisement
- In Serial84 Chapters
A Slayer’s Diary
“I am Brion. Wanderer of strange lands, slayer of mighty beasts. And this diary details the dangers I have endured, and my encounters with the fierce monsters that plague this world.”
8 300 - In Serial38 Chapters
Apocalypse on Endless Earths: Apocalypse How? A LITRPG Adventure
Declan Mason is just an average guy who is about to pop the question to the woman he loves more than anything when his whole world gets turned upside down. No, that's not right, it gets crushed, pulped, eviscerated, and apocalypsed to hell before he even realizes what is happening. He suddenly finds himself working for an Extradimensional Entity that has tasked him with committing genocide on a daily basis. As Declan's new job, it seems, consists solely of him eliminating alternate versions of his Earth. Not content to just destroy, he vows to save the woman he loves one planet at a time. Soon, he's up to his armpits in doppelgangers of his dearie, and he starts to get a clue as to why he has to destroy each world. Just to complicate matters the Horseman, the person who held his station prior to Declan taking over, has decided it is up to him to stop the Entity's murder spree and has placed Declan in his cross-hairs. Apocalypse on Endless Earth's is seriously silly and actively adventurous. Can one man learn to destroy numerous worlds in new and creative ways while simultaneously saving copies of the woman he loves? Find out!
8 240 - In Serial21 Chapters
Point of View
Adrian Shepherd is alive in Santa Monica. Successfully fleeing from the target zone of a nation-wide terroristic threat was not easy, nor did it come free. Adrian had to abandon parents who turned deaf ears, but even more heart-crushing was leaving behind someone who meant the world to Adrian, someone who he had shared his whole life with. Now, he survives with broken memories chasing him. Confliction turns him from wanting to live and wanting to die. Guilt wretches him as he craves the forgiveness he can never have. Maybe tomorrow will bring a brighter day, or maybe more problems. **Cover Photo is Temporary** **I would say the story has light gore and traumatizing events, to the point that I originally didn't check the content warnings. Be advised.**
8 86 - In Serial13 Chapters
The Young Hokage
On the night of his birth Naruto is forced to house the nine tails. But what if he also had a sister and was to be made Hokage upon his fathers orders. A stronger and wiser Naruto.
8 158 - In Serial22 Chapters
The Alphas Baby (undergoing major editing)
Penelope Rivera is a nice quiet girl who has respect for everyone and everything but what happens when she finds her mate and new alpha River Vermont who is engaged to Jennifer his lovely high school sweet heart.So river rejects Penelope on her birthday and on Penelope's birthday she ends up pregnant and he rejects her and he never knew she was pregnant until his beta, Marcus informs him and months later she comes back and he starts to develop feelings for her what will happen then and what happens when Penelope has a dark past she didn't even know she had?
8 170 - In Serial48 Chapters
The Retribution Contract
Revenge. A word that can blindfold people and prevent them from seeing the light around them. It can destroy lives and love. It's not meant to be kept in the heart but sometimes it just stays there. Jungkook could never forgive the person who destroyed him. He could never forgive the person who played with his heart. So, he did what he thought was right. He took his revenge.Written in : March 2022
8 174

