《HASEENAH》PAGE 11&12
Advertisement
[7/6, 10:37 AM] 💄Meerah💋: 🌸 *HASEENAH*🌸
story nd written
by👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
follow me on wattpad @Aysherabbakar
*long live pml*
*11-12*
girgiza kai Mummy tayi alamar 'kwafa sannan saratu ta dubeta tace " Mummy kigani harda wani rufe k'ofa?"
" ah duk makircin da suke k'ullawa Allah zai tona musu asari"
nan suka gama bambamin su suka kama hanya kowa tayi wajanta.
washe gari ma da wuri Haseenah ta gama aikinta, ta ajiye wa Umma komai na buk'ata ta saka uniform d'inta ta fito, harta fito sekuma ta dawo ta dubi Umma tace " Umma zan kulle k'ofar ta baya, inace ba abunda zaki buk'kata?"
gyad'a kai kawai Umma tayi dan ita bacci ma take ji, nan Haseenah ta fita tasa key ta kulle k'ofar.
tsaye kawai Mummy tayi tana kallon ikon Allah, har Haseenah zata wuce setaga Alamar mutum a tsaye, a razane ta juyo nan sukayi ido hud'u da Mummy, rusinawa tayi ta gaida Mummy, basar da gaisuwar Mummy tayi sannan ta dubeta tace " munafuki ko a ruwa yake sai yayi gumi, wani makircin kuke k'ullawa ne wai, uwar taki ina taje da kika kulle k'ofar?"
cikin sanyi tace " umm tana ciki bataje ko ina ba"
" to meye na kulle wajan? saboda kuna tare da mayu ko? to bani makullin"
ta k'arasa maganar tana mik'a hannu wa Haseenah, ja da baya Haseenah ta fara yi Mummy na binta.
sallamar Haseen ne yasa Mummy juyawa tana kallon shi, aiko nan Haseenah ta fita waje aguje , k'walla mata kira Mummy keyi amma ina itakam tayi nisa.
nan Mummy ta fara zage zage, Haseen ne yake tanbayarta meya faru, nan ta hau sababi tana fad'in " dan uban yarinyar nan har zata fice ta kulle k'ofar uwarta sekace zamu cinyeta, to wallahi yau sena ci ubanki a gidannan"
Advertisement
abun dariya ya bawa Haseen amma ya nok'e yace " to Mummy dan Allah meye dan sun kulle k'ofa sekace taki suka kulle?"
a zuciye ta dubeshi tace " zanci ubanka, ina ruwanka, wato kaima goyon bayansu kake ko? to wuce ka koma yanda ka fito bana buk'atar zamanka a gidannan"
dariya yayi yace" kefa Mummy halina dake masifa wallahi"
bata sake kulashi ba ta koma side d'inta, ya dad'e tsaye a wajan daga bisani shima ya kama hanya ya fita.
lokacin da aka tashi su Haseenah a makaranta ta dawo gida, tsayawa tayi a bakin gate tana lek'e ko zata ga Mummy, ganin ba kowa wajan ne yasa ta fara shiga da sand'a, harta kai bakin palour zata bud'e taji muryar Mummy na fad'in " sannu da dawowa shugaban munafukai"
gaban Haseenah ne ya shiga bugun tara-tara dan tasan yau me k'wacenta wajan Mummy sai Allah.
ahankali ta fara tafiya har ta kai wajan Mummy sannan ta tsuguna a gabanta, janyota Mummy tayi ta sake mata dundu a tsakiyar baya, ta had'a ta cakumo wuyar hijabinta kai kace dambe zatayi da sa'ar ta, wani wawan mari ta d'auketa dashi a jejjere guda uku, hanunta na rik'e da wuyarta sannan tace" ni sa'ar ubanki ne da zanna kiranki har ki kwasa da gudu?"
cikin kuka Haseenah ta fara girgiza kai, Mummy ta cigaba da cewa" ko zaki iya fad'a mun irin mugun halin da nake dashi da har zaki na kulle k'ofa sekace mayya?"
nan ma girgiza kai tayi, " wallahi na sake ganin haka ya faru kisa aranki na lahira seya fiki morewa, 'yar iskar banza karuwa"
tana gama fad'in haka ta wurga ta gefe, nan kanta ya bugu da centre table d'in tsakiyar palour, wani mummunan zafi ne ya ziyarce ta hakan ya sata sake wani irin ihu ta dafe wajan, jini tagani ya fara zuba hakan ya dad'a gigitata tana fad'in " wayyo Allah na"
Advertisement
ko ta kanta Mummy bata sake biba ta wuce abunta.
Umma ko a d'aki sai sharar k'walla takeyi aranta tunani take wai yaushe zasu samu sassauci daga wannan wulak'anci da cin mutuncin ne wai, wata gefe daga zuciyarta ta bata amsa da fad'in " randa kuka bar duniya"
haka Haseenah ta tashi da k'yar taja jiki ta kama hanyar palour, key ta lalumo ta bud'e k'ofar ta shige ciki, kai tsaye bedroom ta shige ta fad'a kan gado, lokaci d'aya ta saki wani irin kuka mai ban tausayi, ta kwashi kusan minti talatin tana yi, mik'ewa tayi ta shiga toilet ta bud'e wani d'an akwati.ta ciro bandage ta nad'a a goshinta, sannan tayi wanka ta d'auro alwala ta fito, da k'yar ta iya yin sallah saboda wani irin ciwon kan da yake damunta, fitowa tayi ta shige kitchen d'insu ta yi jelouf na sphagetti da kifi sannan ta juye a flask ta fito d'auke da plate da spoon a hanunta, wajan Umman ta ta wuce sannan ta zuba mata ta tura mata gabanta ta koma can gefe ta zauna, nan Umma tace tazo suci tare, ba musu taje suka fara ci, sunci da d'an yawa kuwa suna gamawa ta kwashe komai ta mayar kitchen ta yi wanke-wanke ta goge sannan ta fito.
zamanta knan taji Mummy na k'walla mata kira, da k'yar ta mik'e ta fice, a palour ta sameta suna zaune ita da saratu tana kwance kan cinyar ta, ahankali take tafiya zata isa wajan Mummy ba tare da ta kula ba ta taka wani abunda taji ya shige mata cikian k'afa, azabar da taji yanzu ya ninka na d'azu, tsugunawa tayi awajan nan taga fasassun kwalabe ne wanda ya fashe, jini tagani na zuba a k'afanta, ko sannu babu Mummy tace " ki dauko parker da moper ki tattara wannnan glasees d'in tumbler daya fashe sannan ki goge wajan"
d'an kwalin kanta ta cire ta yaga shi gida biyu tayi zaman dirshan a wajan sannan ta runtse idonta ta zaro kwalban daya shiga mata k'afa sannan ta d'aure da d'an kwalin, hawaye na xuba haka ta tattara komai ta goge.
zuciyarta wani irin zafi da zogi yake mata, maimakon tayi side d'insu kawai setayi hanyar fita daga palour, wajan parking lot d'insu tabi taje wajan flowers d'insu ta 6uya a bayan motar Abban ta ta had'a kai da gwiwa ta fashe da kukan bak'in ciki.
kuka take har kamar numfashin ta zau d'auke, idonta sun kad'a sunyi ja sun kumbura, ga bugun goshinta ga wani azaba a k'afarta.
kuka take tun muryarta na fita har ya dishe ta fara sambatu ita kad'ai sekace zararriya.
ganin inuwan mutum a gabanta yasata d'ago jajayen idonta dan ganin waye?......
for comments only 08144932304
Advertisement
- In Serial245 Chapters
I Can Turn into a Fish
A chance to change, to challenge destiny, making dreams a reality, and live a legend! A regular man gains a system that allows him to turn into a fish!
8 613 - In Serial15 Chapters
Lord Of Horrors [DISCONTINUED]
In the year 2378, the people of the newly-colonized planet Eredea did as all colonialists often do. They dug deep into their new world, exploring each nook and exploiting every cranny it had to offer. Again, much like everyone else, there came a time when they dug a bit too deep... but what they found on that day is not what they would learn to fear. --- For those who do not know, every chapter with the " Lemon: A chapter which contains, is made up entirely of or is a prelude to a sexual or highly erotic/suggestive scene. --- Lord Joyde The Madman: I've been convinced by a couple people that posting my new story on multiple sites is the best course of action. Other site - https://www.fictionpress.com/u/879573/Lord-Joyde 2. https://www.scribblehub.com/series/3440/lord-of-horrors/
8 136 - In Serial40 Chapters
Dungeon Maker
Ace Cross is not your typical NEET, although he has all the making of one and is recluse, he is still a very outdoor type of person. One day he is killed (by a truck no less even after dodging off the road) his soul was going to white light in the sky (the sun) but before he could arrive a magical circle appears and he is pulled in and given a second chance at life in a magical world under the most cliche trope of anime, as a summoned hero. He isn't 'the' hero though, he got the most uncommon hero class and something that has been extinct in all the nations blocking the advance of the demon lord. That is the Dungeon Maker. As a very unusual class that makes not only death traps but proper dungeons with ecosystems, this is the life of humanities first dungeon maker in 1,000 years since the demon lord war began. This is not just a story of battling the demon lord but also of how our heroes making a new life force themselves as all of them died in their original worlds.
8 200 - In Serial9 Chapters
World apocalypse
No one could have really said how it would all end, but I guess we were pretty close...
8 201 - In Serial14 Chapters
Loving him from afar [Completed]
Ruby Williams has had crushes that came by and went within a few days or weeks and she knew it was going to stay that way. However, when she encountered Sam Miller in her sophomore year, she knew this wasn't just a mere crush. A short story of unrequited love, filled with heartbreak and regrets. ..."That night, I got my heart broken by someone who wasn't even mine to begin with."...🥇Highest rankings🥇#1 first heartbreak#1 highschoolcrush#1 untold love#2 lettinggo#3 teenage crush#4 highschool crush#5 non fiction#7 first crush#12 letting go#19 one sided#20 unrequited #23 unrequitedlove#40 regret
8 183 - In Serial10 Chapters
EU: Novum Orbis Terrarum
Year 2014 AD, Modern Europe has flourished thanks to the collective efforts of the European Nations that has led to several of the EU's policies to ensure an equal development among European Nations but it all changed when they somehow got into an unrealistic situation....
8 179

