《HASEENAH》Page 5&6
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
story nd written
by👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
follow me on wattpad @Aysherabbakar
*long live pml*
*5-6*
Ganin yanayin da Abba ya shiga ba 'karamin mamaki ya bawa Dr ba, kama hanun Abba yayi ya koma ya zaunar dashi, ba musu Abba ya zauna amma ya kasa cewa komai, handkerchief kawai ya zaro cikin aljihun shi yana goge gumi.
ba abunda yaji bane ya d'aga mishi hankali ba, sanin halin mummy da tashin hankalinta duk shi ya kid'imashi, yasan indai taji wannan labari 'karamin aikinta ne ta salwantar da rayuwarsu gaba d'aya.
likita ya kula da halin da ya shiga ganin gumin da yake tsatsafo mishi sekace wanda ya wuni yana aiki a kitchen.
sun d'au tsawon wasu lokuta ba wanda ya iya magana, can likita ya daure tare da d'aura hanunshi kan na Abba sannan yace" Abokina me ya faru ne? kodai akwai matsala ne?"
firgigit Abba ya dawo daga dogon tunanin daya tafi sannan ya 'ka'kalo murmushi me kama da yak'e sannan yace " am ba komai kawai ina tuna irin wahalar da ta shane lokacin haihuwar Haseenah shine kawai"
murmushi shima yayi nan ya fara kwantar mishi da hankali kan addu.a kawai zasuna mata in Shaa Allah ba abunda zai faru.
nan ya bashi shawarwari sannan suka fito tare suka dawo wajan da suka bar Umma.
har drip d'in hanunta ya 'kare zaune suka sameta suna hira ita da Haseenah da Haseen, kamar ba ita ba.
nan ya dad'a dubata sannan yace zuwa dare ma zasu iya komawa gida indai za.a kiyaye abubuwan da likita ya fad'a.
seda Abba ya gama komai sannan ya dubi Haseenah yace zai koma gida da daddare zai dawo su koma tare.
Advertisement
nan ya 'kara mata dubu biyar yace koda zasu nema wani abun kafin ya dawo.
da sauri Haseenah ta sa hannu biyu ta kar6a cike da murna dan koba komai ta samu abunda zata na siya wa Ummanta har Allah ya bata lafiya.
ko da Haseenah taji abunda ke damun Ummanta murna ne sossai ya kamata, Umma ma tayi farin ciki amma da ta tuna halin Mummy duk se murnar ta ya koma ciki amma addu.a shine kawai abunda ya kamata tayi.
da daddare misalin k'arfe tara Haseen suka dawo shi da Abba dan mayar dasu Umma gida, seda ya biya dasu supermarket ya musu siyayya sannan ya wuce dasu gida, can nesa kad'an da gidan yayi parking suka fito, Haseen ne ya taya Haseenah kwasan kayan suka nufo gida Ummah na biye dasu a baya.
da sallama suka shiga, aiko Mummy na zaune a main palour tana kallon news, ganin Haseen da kaya hannu sun jero da Haseenah ya sata kallonshi sannan tace" kaikuma fah? me nake gani a hanunka kaman kaya?"
shuru yayi ba tare da ya bata amsa ba, mik'ewa tsaye tayi tace"ajiye musu abunsu tun kafin naci maka mutunci d'an iska kawai, duk kabi ka tare gindin mace ko uwar me zata baka oho, inkuma nono kake sha sai kamun bayani, inba iskanci ba kabiyo bayansu sekace shashasha, ko kaima sun lashe kanne iyee?"
ranshi ne ya fara 6aci amma ba halin magana in banda sunkuyar da kanshi 'kasa da yayi, ganin fad'an yanaso yayi yawa ne yasa Haseenah ta fara tafiya, tsawa ta daka mata sannan tace
" dan ubanki magana nakeyi kuma zaki wuce ai banzo kankiba tukunna ko?"
ajiye kayan yayi sannan ya koma gefe ya tsaya, duban Haseenah tayi tace" meke damun uwar taki?"
wannan tanbaya ba 'karamin gigita Umma da Haseenah yayi ba, lokaci d'aya taji fitsari na barazanar 'kwace mata, ganin haka yasa da sauri Haseen yace "Typhoid da Malaria ke damunta"
Advertisement
dukansu kallo suka bishi dashi banda Haseenah data sauke wata ajiyar zuciya.
ba tare da ta sake cewa komaiba ta koma ta zauna had'e da d'aura d'aya kan d'aya, duban Haseenah tayi tace"ki wuce kitchen ke nema wa saratu abunda zata ci, dan tun d'azu take jiran dawowarki, kaikuma kazo nan inason ganinka"
ta 'karasa maganar tana me kallon Haseen.
ba musu ya zauna gefenta.
su Umma kuwa jiki a sanyaye suka wuce side d'insu dan ajiye kayan hanunsu.
seda Haseenah ta zubawa Umma naman Kazar da Abbanta ya siya musu da yoghurt sannan ta tura mata gabanta ta fito dan yin abunda mummy ta saka ta.
shiko Haseen yana can tana zuba mishi buhun masifa kan karta sake ganinshi da Haseenah koda kusa da inuwanta ne.
'''2 days ltr'''
Ummah ta warware sossai har da 'yar 'kiba dan kullum Abba yana bawa mai gadi gasassun kaji da yoghurt in Haseenah ta fito seya bata a 6oye.
yau an koma makaranta da sassafe Haseenah ta tashi duk ta gama abunda zatayi, 'karfe 7:30 ta shirya cikin sababbin uniform d'inta wanda Haseen ya siya mata.
seda ta tabbatar babu abunda Ummah take bu'kata sannan ta fito 'dauke da jakarta a hannu.
fitowanda zatayi bata kula ba sukaci karo da saratu, wani uban zagin da saratu ta saki ne ya sa mummy fitowa da sauri tana fad'in "me aka miki?"
ganin saratu ta sha'ko Haseenah ne ya sa mummy 'karasowa tace"fad'amun menene?"
nan saratu ta fara fad'in "mummy dan tsabar iskanci tana kallona ina tahowa ta bangajeni wai zata wuce"
"meyasa baki daki shegiya ba kika tsaya iskanci, ko tafi 'karfinki ne?"
bata yi wata wata ba ta janyo Haseenah ta d'auketa da mari, ko motsi Haseenah bata yiba balle tayi yunk'urin tarewa.
kamata Mummy tayi tace"ubanwa ya baki wannan sabin uniform d'in iye? wuce kije ki ciresu ki kawomin"
ba musu Haseenah ta fara tafiya dan cika umarnin mummy, bata ankara ba daga bak'in k'ofa sukaji ance" tacire akan akwai shegen daya siya mata?"
da sauri mummy ta juya dan ganin wake shirin mata katsalandan, amma me?.......
for comments 08144932303
Advertisement
- In Serial1363 Chapters
VRMMO: The Unrivaled
Lu Chen used to be a ranker of the most popular VRMMO game, Spirit of Grief. After a car accident turned his dreams into dust, his disability left him incapable of escaping the pit of mediocrity he was thrown into. Helpless and defeated, his story ended.Two years later, the Eternal Moon Corporation launched a new VRMMO called "Heavenblessed", and Lu Chen stumbled into another terrible accident that left him in a complicated situation far beyond his ability to handle. That won't stop him from rising to the top, however. Not again.Come witness the rise of the sword-wielding zombie and the relationships he makes during his journey to the apex! For riches and bi- ahem, for career and love!He wields a demonic sword from Hell, he dons armor shining with Heaven's light. His boots stride across the sky as his helmet devours the souls of his enemies. On his left side sits the Goddess of Death. On the other, the Angel of Beauty.From the land of ice and death, a generation of Asura Kings rises, their roars reverberating throughout the world.Tremble in fear, noobs!
8 8158 - In Serial1353 Chapters
Refining the Mountains and Rivers
A young man's life changes when he stumbles upon a mysterious item. Qin Yu had never been a lucky person. Weak of body, bullied by his peers, and with only his friend as his family, he struggles day-by-day to live. But everything changes when he stumbles upon a little blue lamp. An immortal and demonic cultivating adventure.
8 3346 - In Serial2455 Chapters
Mortal Cultivation Biography
A poor and ordinary boy from a village joins a minor sect in Jiang Hu and becomes an Unofficial Disciple by chance. How will Han Li, a commoner by birth, establish a foothold for himself in in his sect? With his mediocre aptitude, he must successfully traverse the treacherous path of cultivation and avoid the notice of those who may do him harm. This is a story of an ordinary mortal who, against all odds, clashes with devilish demons and ancient celestials in order to find his own path towards immortality.
8 1057 - In Serial1503 Chapters
Dragon Prince Yuan
Destiny stolen at birth, the prince of the once mighty Great Zhou Empire, Zhou Yuan, has been plagued all his life by a fatal poison, forced to suffer powerlessly until one day when fate draws him into a mysterious domain where he meets a beautiful girl in green, a bizarre dog-like creature and an unfathomable old man in black.Join Zhou Yuan as he is thrust into the whirlpool of destiny while he seeks the pinnacle of cultivation.
8 1060 - In Serial677 Chapters
Ranker's Return
In the early days of the virtual reality game, Arena, meleegod was the strongest ranked player! He deleted his character and suddenly left. In order to restore his bankrupt family, he returned to Arena!"Do you want to create a character?"
8 1719 - In Serial1525 Chapters
Monarch of Evernight
Qianye rose from hardship but was felled by betrayal. From then, one man, one gun; he tread the path between Evernight and Daybreak and became a legend. Even if Evernight was destined to be his fate, he still intends to become the ruler who dictates.
8 22867

