《HASEENAH》Page 3&4
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
story nd written
by👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
follow me on wattpad @Aysherabbakar
*long live pml*
*3-4*
cak Haseenah ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, tsawar da mommy ta 'kara mata ne ya sata tsugunawa a wajan jikinta na rawa, dubanta Mommy ta sake yi tace " menene a hanunki nace?"
cikin rawar murya ta bata amsa da " kayan umma na ne na kai wajan tela aka gyara mata"
dariya mommy ta saki sannan tace"kice paci kika kai wa tsohuwarki mana, tashi kije da nayi tunanin maula kikaje ai"
wani ajiyar zuciya Haseenah ta saki sannan ta tashi da sauri ta nufa cikin gida. da sallama ta shiga nan ta tarar da ummanta zaune yanda ta barta, zama tayi a gefenta sannan ta dubi Umma tace " gashi ma yaya Haseen ya biya kud'in makarantar"
shuru tayi sannan ta dubi ledar hanunta a hankali tace " wannan fa?"
sai a lokacin ta tuna da ledar da ta shigo dashi, janyo wa tayi ta bud'e nan ta fara ciro kayan ciki, school uniform ne set biyu sai na islamiya shima biyu, sai socks dozen d'aya sai turare da sauran tarkacen kayana makeup da sabon sneakers wanda suke amfani da shi a school sai flat shoe da bathmilk, bayan tagama ciro kayan ne kuma 'karamin envelop ya fad'o, sa hannu tayi ta 'dauka ta fara bud'ewa a hankali.
kud'i ne a ciki 'yan dubu 'da'ddaya guda goma, da sauri ta duba Ummanta sannan tace" Umma harda kud'i fa aciki, a mayar mishi kawai ko Ummah?"
ta 'karasa maganar cike da damuwa.
dubanta Umma tayi sannan tace"ke kika rok'eshi?"
Advertisement
da sauri ta girgiza kai alamar a.a, gyad'a kai Umma tayi sannan tace" to shi yaga dama kuma ba a mayar da hanun kyauta baya, ki adana kud'in sekiyi hidimar makaranta dashi.
batace komai ba ta tattara kayan ta mayar leda sannan ta samu waje ta adana kud'in.
sallaman da sukaji ne ya katse shurun da sukayi, ko bata tanbaya ba tasan Abban tane, sunkuyar da kai tayi ta gaida shi, murmushi ya saki mata sannan ya k'araso ciki ya zauna bakin gadon, duban Umma yayi sannan yace " Maryama ya jikin naki?"
da 'kyar ta iya amsawa saboda yanda takeji numfashin ta na fita sama-sama, hankalinshi ne ya tashi ganin yanda take mayar da numfashi, kallon Haseenah yayi yace " Uwata me yasa baki sameni kin fad'amun ba, kina ganin yanda take wahala amma kikayi shuru?"
sunkuyar da kai tayi dan in tayi yunk'urin sanar mishi ma to a ina zata ganshi? Mommy ma bazata barta ma, sedai ta bita da tsinuwa da kuma zagi.
sanin halin Mommy yasa shi basar da maganar yace su shirya su sameshi a mota su wuce asibiti.
yana gama fad'in haka ya fice, dai dai fita daga side d'insu Haseenah sukayi kici6is da Mommy, dubanshi tayi tace" uwar me ka shiga yi wajanta?"
cikin rawar murya yace" ni ba d'akinta naje ba, warin 'kauri naji nayi tunanin metre ne sekuma naga ba nan bane"
girgiza kai tayi ta wuce wajanta ba tare da ta sake mishi magana ba.
ba 6ata lokaci suka tarar dashi a mota, suna shiga da sauri ya figesu gudun kar Mommy ta le'ko ta gansu, kai tsaye Apple Clinic suka wuce, da yake asibitin na abokin shi ne ba 6ata lokaci aka kar6esu, kwantar da ita akayi sannan aka fara duba ta, test d'in farko da aka mata aka gano tana d'auke da cikin wata biyu, sedai damuwa da zama da yunwa ya sa ulcer ya mata mummunan kamu wanda yake baraza ga cikin jikinta.
Advertisement
taimakon gaggawa aka fara bata, sannan aka d'aura mata drip, aka had'a mata da allurai da magunguna.
likita ne ya lek'o yace a taho mata da abinci mai ruwa wanda zata iya ci.
Abba ne ya dube ta yace" yanzu me zaki mata wanda baze d'au lokaci ba?"
shuru tayi kaman me tunani sannan tace" sedai gwate"
da sauri yace"to kiyi sauri nima bari naje nan bakin asibiti innemo mata abunda zataci kafin ki dawo"
dubu biyar ya ciro cikin aljihun shi ya mik'a mata sannan yace" ga wannan ki siya duk abunda babu ki hau a daidaita ki dawo, ni zan tsaya nan kafin ki dawo"
kaman zata ce mishi akwai komai to amma data tuna wataran zasu nema seta kar6a ta fice da sauri.
ba 6ata lokaci ta gama komai sannan ta dama mata kunun gyad'a ta had'a komai a flask ta zuba a basket.
d'aki ta koma ta d'au babban sallaya da hijab da kayan Mommy kala biyu sannan ta fito ta kulle 'kofar ta fito da niyan tafiya.
'Kwalla mata kira Mommy tayi, ganinta d'auke da kaya yasa ta fad'in " sai ina kuma a yawo?"
a tak'aice tace" Ummata ce batada lafiya an kwantar ta a asibiti"
ta6e baki tayi tace" Allah kyauta"
da sauri itama ta fita dan komawa asibitin, Haseen ta hango yana k'ok'arin shigowa cikin gidan da motarshi, ganinta da kaya yasashi fasa shiga ya fito ya dubeta sannan yace" ya na ganki da kaya a hannu, waye ba lafiya?
" umma ce take asibiti"
da sauri ya dubeta sannan yace" dama bata da lafiya amma jiya baki fad'amun ba?"
shuru tayi bata ce komai ba.
sanin halinta ya sashi cewa"shigo muje wani asibiti take?"
ba musu ta shiga nan ta fad'a mishi sunan asibitin.
cikin 'kan'kanin lokaci suka iso, Abba suka hango zaune a reception, da gani kasan ita dama yake jira, yana ganin Haseen ya washe baki yace" tare kuke tafe knan?"
nan suka gaisa ya musu jagora zuwa inda Umma take, har lokacin drip ke hanunta, amma ta farka daga baccin, gefen side bed d'in kuwa kayan tea ne da su maltina da fruits da Abba ya siyo mata.
murmushi Haseenah ta saki wa Umma ganin ta dawo dai-dai, nan ta zuba mata abincin ta zauna gefenta tana bata ahankali tasha sossai.
nan Haseen ma ya gaidata suka zauna suna hira, Doctor ne ya shigo suka gaisa da Abba ya d'an dubata sannan yace yana son ganin Abba.
fita yayi ya barsu shikuma ya nufi Office d'in Abokin nashi.
Abunda Dr ya fad'awa Abba shine ya firgitashi ya sashi mik'ewa tsaye ba shiri had'eda zaro ido waje.......
for comments 08144932303
Advertisement
- In Serial59 Chapters
The Pen Is Mightier
This story is in the process of being rewritten and has big chunks missing. If you're interested in it, please follow for alerts regarding release updates. I'm aiming to finishing the first to books in the series before I start putting them on Royal Road and expect to release in late March or early April.
8 92 - In Serial9 Chapters
Web of Worlds: Empire. GUARD. Book 1. litRPG series
The God of Light fell. The Demon Lord rules the world. Sentient beings were forbidden to develop technology, and people were never able to shift from the steam engine era to the age of electricity and the internal combustion engine.But as long as you are the Light host, you may hope for the best. Even if your house is burned to the ground, even if you lose your family, even if your overlord sends you to your death. The Black Guard never gives up and continues on his way.Every word here is true.And every word here is a lie.Where is the truth? You can't guess...Choose what you want..
8 176 - In Serial16 Chapters
Being
First it was nothing.... I think A story about a being who could do almost anything My first story and english is not my first language + i'm not so old Posting one chapter every other day or something like that
8 72 - In Serial6 Chapters
Rune
A forsaken kingdom, an empty throne, a dwindling population and the blame is one young girl? Can she overcome the darkness in her heart and the stigma of her people and become something great? This is my first attempt at a series so if anyone has any critiques on my work, grammatical or plot wise feel free to leave them in the comments; also, don't be afraid to be brutally honest in the reviews. Gonna leave it at (14+) for now. PS- The description is a work in progress.
8 176 - In Serial8 Chapters
Granger-Swan reunion
'Mione goes to a family reunion after not seeing her family for 19 years because they were excessively rude to her "buck tooth bushy haired" cousin. Watch as she surprises them with her achievements,including her mystery husband and kids.All rights go to J.K Rowling except the storyline.I'm changing ships so no #HINNY OR #RONMIONE. Weasley bashing involved.
8 198 - In Serial36 Chapters
Never Would Have Thought(Princeton Love Story)
Yn And Jacob Are Brother And Sister They Live In LA And Go Through It All Drama,Fights,Breakups,Makeups,Pregnancy,Being Betrayed By Friends,All Of ItRead To Find Out
8 154

