《HASEENAH》Page 1&2
Advertisement
🌸 *HASEENAH*🌸
story nd written
by👇🏻
Aysher Abbakar (Meerah)
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
#
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303
follow me on wattpad @Aysherabbakar
'''BISMLLAHIR-RAHMANIR RAHEEM'''
*Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon fara rubuta wannan littafi, wannan littafi ba nayi shi bane saboda wata ko wani, wani littafi kirkirarren labari ne dan isar da sak'on da yake kunshe cikin sa, ina me bada hak'uri cewa duk wanda wannan labari yayi dai-dai da rayuwarta/shi, to yayi hak'uri ba saboda shi nayi ba, da fatan zaku bani goyan baya, kuma ina rok'o duk wanda yaga nayi kuskure cikin wannan littafi to dan Allah a gyaramun, dan kowani d'an Adam ajizi ne, Allah yasa mu dace, ya bamu ikon cin duk wani jarabawar rayuwa.*
jinjina gareku k'ungiyata kuma abar alfaharina, kun taka rawar gani 'kwarai a rayuwata, wajan yimun gyara ko fad'an gaskiya bisa duk wani kuskure dana aikata, ina yinku.
*long live pml*
wannan littafin na sadaukar dashi ga duk wani wanda ya/ta fiskanci matsin rayuwa, Allah yasa mufi karfin zuciyarmu.
*1-2*
k'aran kwanuka da cokula kawai kake jiyowa daga cikin kitchen, jin abu yak'i k'arewa ya sani k'arasawa da sauri dan duba meke faruwa.
Wata matashiyar budurwa na hango wanda bazata wuce shekara sha hud'u ba sanye cikin wata kod'add'iyar dogon riga kai kace mai aikin gidan ne. kiran da naji ana k'wallawa ne ya sani razana da sauri na juya dan gani wani k'ato ne haka da wannan muryar? abun mamaki mace ce ingarma doguwa ga jiki ga k'iba kai kace 'yar wasan danbe ce, da sauri na matsa na raku6e dan ganin ta nufo yanda nake gadan-gadan.
runtse ido na kawai nayi dan sauraron abunda zai biyo baya, 'karan saukan marin da naji ne ya sani bud'e idona a razane dan ganin meke faruwa?
Advertisement
matar na gani ta shak'e wannan yarinyar kamar wacce zatayi dambe da sa'ar ta, daga hannu ta sake yi ta sharara mata wasu tagwayen mari lokaci d'aya sannan ta fara magana cikin dakakkiyar muryarta tace" haseenah, dan ubanki ba gyaran palour na na sakaki ba shine kikazo nan kika rashe dan kin mayar dani 'yar iska ko?"
cikin sheshshe'kar kuka tace"Mommy wlhy ba haka bane, dama inaso in 'karasa wa umma na wanke-wanke ne, batajin dad'i ne shiyasa"
salati ta kama yi tare da fad'in" jimun munafuka, wato saboda bani na haifeki ba shine bazaki mun abunda na saki ba ko? to ki barshi tunda ke ban isa da ke ba ai na isa da ubanki, shi zaizo yamun gyaran palour daga nan ya d'auramun girkin rana"
da sauri Haseenah ta tsame hanunta daga cikin sink d'in tace"yi hak'uri mommy wlhy zanje inyi ynxu"
Haseem ne ya k'araso da sauri dan shigowar sa kenan yaji hayaniya na tashi, ko bai tanbaya ba yasan Mommy da Haseenah ce, da murmushi ya k'araso ya dubi Mommy yace" ah mommy dama tunda naji hayaniya nasan da 'yar taki ce"
a fusace mommy ta dube shi tace" Allah yamun tsari na haifa wannan me kama da mayun, ai gwanda na koma ga Allah ban haihu ba, yarinya daga ita har uwarta munafukai, se anyi magana su fara k'ifi-k'ifi da ido sekace an barbad'awa kifi gishiri" ta k'arasa maganar tana d'aka wa Haseenah duka had'e da hankad'ata waje tace
" wuce shegiya kin tasa ni a gaba sekace wanda nake baki kalmar shahada"
da sauri ta wuce tana share hawayen bak'in ciki dan batasan me suka tsarewa mommy ba, dan tun tasowarta haka ta rayu cikin tsangamar mommy, sekace ba matar ubanta ba, to umman ta ma mommy bata bari ba ballan tana ita haihuwar yau.
Advertisement
Haseem ne ya kalli mommy duk ranshi a jagule ya sanyaya murya yace"haba mommy, dan Allah kina rangwanta ma yarinyar......
tsawa ta daka mishi tare da nuna shi da yatsa tace" kai ko uwarka kaga dai k'anwata ce ko? to batamun katsalandan a rayuwar gidana, shiyasa ma kaga duk munfi shiri da ita, saboda halinmu yazo d'aya, dan haka ka fita hanyata, inba haka ba wlhy zan sa6a maka".
sanin halin mommy ya sashi yin shuru ba tareda yace komai ba ya nufa hanyar waje yana mai Allah wadai da halin su mommy.
Haseenah kuwa shiga toilet d'in tayi ta fara aikin wanke wa, tana gamawa ta fito bedroom ta gyara ta mopping ta had'a burner na turaren wuta, hakama ta gyara palour sannan ta shiga kitchen d'in mommy dan had'a mata breakfast ita da 'yar lelenta wato saratu, chips ta soya musu sannan ta dama kunun gyad'a ta tafasa lipton, tana gamawa komai ta juye a flask ta gyara ko ina sannan ta fito, gajiya ne ya rufe ta gashi tabar ummanta can ba lafiya, kuma ko abinci bata girka musu ba.
kitchen d'insu ta koma ba tare da ta 'karasa wanke-wanken ba ta 'daura musu lipton ta musu d'umamen sauran tuwon jiya sannan ta fita da sauri ta nufa d'akin umman ta.
zaune ta sameta kan carpet ta jingina bayanta da gado tana mayar da numfashi a hankali, ajiyewa Haseena tayi sannan ta dubi umman tana mata sannu, abincin ta zuba musu nan suka ci . kowa shuru yayi cikinsu babu mai magana kowa da tunanin da yake a ransa.
haseena ne ta dubi umma sannan tace"umma ya zamuyi da maganan kud'in makaranta na, gashi jibi zamu fara exams"
shuru umma tayi daga bisani tace" ki d'au 'dankunne na kije kisiyar a shagon da mukaje dake na siya, saiki siya duk abunda zaki buk'ata da canjin bayan kinbiya school fees d'in".
jikin Haseena ne yayi sanyi duk taji ba dad'i, umma ta kula da hakan hakan ya sata cewa"ko bakiji abunda nace bane?"
ahankali ta mik'e ta saka hijabinta da d'au d'ankunnen ta fita, a gate sukayi kici6is da Haseem zaune kan mota, d'auke kai tayi kaman bata ganshi ba, ganin haka ya sashi 'kwalla mata kira, kaman bazata juya ba sekuma ta juyo tare da amsawa, gaidashi tayi sannan tayi shuru.
dubanta yayi sannan yace"ina zakije da safen nan?" shuru tayi batace komai ba, ganin batada niyan magana ne ya sashi saka hannu cikin aljihu ya ciro wata 'yar paper ya mik'a mata sannan yace "dama receipt na school fees d'inki ne gashi nan seki adana"
binshi tayi da ido ba tare da ta amsa ba, kama hanunta yayi ya saka mata sannan ya juya ya bud'e bayan motar shi ya ciro wata 'katuwar farar leda ya ajiye mata yace seki d'au wannan ki tafi da ita taki ce, tunda yau bakida niyar magana miskilanci ya motsa"
yana gama fad'in haka ya shiga motarsa yabarta nan tsaye.
ba yanda ta iya haka ta d'au ledar ta juya ta koma cikin gida.
a harabar gidan sukayi kici6is da mommy, sunkuyar da kai tayi gabanta na fad'uwa dan tasan ba makawa in mommy taga kayan hannunta to wani sharrin ne zai biyo baya.
hakan ya sata 'kara sauri dan gudun kar momny ta kula da abunda ta rik'o.
kaman daga sama taji andaka mata tsawa, ba makawa tasan mommy ce hakan yasa ta fara kyarma kaman zatayi fitsari, dubanta mommy tayi sannan tace......
for comments 08144932303
Advertisement
- In Serial47 Chapters
Checkpoint
as an anomaly sweeps the world, many gain strange abilities. as for Mal, the power makes it so they cannot die, or more accurately, they get sent back in time to the last place they were safe at. A power that seems like a blessing until you’re crushed under rubble, drowned in sewage, shot, stabbed, all while having the royalties to feel all the pain from such fates. And to put the icing on the cake, a strange message appeared before everyone’s eyes stating that unless someone breaks down the gate within 17 years, everyone will die”. now Mal needs to find a way to “break down the gate” (whatever the hell that means) or they will be forced to die and revive, only to die again for the rest of time. Which would suck, probably. /————————————————— this is technically a time loop novel. the MC is chaotic neutral with a worryingly lack of care about how their actions affect people. i want to interact with my readers so give critique and suggestions. I will sometimes host polls for the personality for new characters, story decisions, and the ability to cancel annoying characters, besides Mal, if they get enough complaints. I am also impatient and will end decision polls when I want to write more. If no one votes, I choose, so don’t let that happen. if you’re want world building check out hitchhikers guide to checkpoint (an encyclopedia of what I made up with lots more explanation)
8 112 - In Serial12 Chapters
Overpowered Sadistic Cat
Teddy IV was a cat. Not just any cat, he was a very spoiled cat. At least until one day he was chased by a few crazy people. They tried to capture him but he escaped but unluckily as he was escaping his tail was ran over by a truck. This caused the spoiled cat to hate humans, and as he died by bleeding to death due to his tail being crushed he wished for the power to crush them... "I-is this the truck I saw my owner reading about in a manga?!" And magically his wish was fulfilled. The celestial white tiger guardian made him reincarnate into a magic world with overpowered powers. How will this cat do in this absurd fantasy world?
8 229 - In Serial30 Chapters
Eaten By A Slime?!
While picking medicinal materials in the forest, Eri was suddenly devoured by a slime. When she woke up, the slime turned into a man! He's claiming to be her husband?? Then he's solving all her problems!? Oh dear, there's a sudden influx of memories from her past life too! "Who's your wife, you Slime!" "It's destiny, my beloved Eri." "Damn destiny, you're nuts." "Shh, less words, let me prove it with love." "God save me..."
8 181 - In Serial13 Chapters
Elf anew
Felia wouldn't brag about her life. As the Church's of Parva Cleric nothing really happens in her life to justify bragging about it. Until one day, she fails the most important quest in her life and is forced to leave her old life behind and seek future in the lands of Moria. However, she has no idea what kind of adventures she'll get herself into, and what mischievous acts the world powers plot against each other.
8 180 - In Serial19 Chapters
Whodunnit
After the death of her mum, Amy has to adjust to a new life with new people. She meets the newest member of her life; Cassandra who she slowly creates a bond with.
8 196 - In Serial12 Chapters
50shades Of Jungkook
SPG: R-18Jeon Jungkook Fans Can Relate.
8 179

